Showing 33001 words to 34919 words out of 34919 words
Chapter 12 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
rashin kuzarin nashi zai sa ya iya morewa yadda ya kamata a matsayinsa na ango? Duk yadda ya so ya daina istimna'i na ɗan wani lokaci ya kasa, sannan abin da ya sake ba shi tsoro cikin satin auren da ya gwada kusantar Sabila sam kasawa ya yi, abun ya zama kamar alayyahun da ya ji rana, shiyasa yaƙe kawai yake yi a kwana biyun.
A cikin wannan yanayin aka ɗaura auren Sunusi da Karime, ita dai ta yi biki gagarumi, sannan dakinta ta saka kayan gado masu tsada, ba ta ma damu da rashin kitchen ko falo ba, ita indai dare zai yi Sunusi ya ɗebe mata kewa to ko a zaure za ta iya zaman gidansa.
Ita ma Sabila sai da ta ɗan yi taro, saboda 'yan'uwanta sun zo, sannan maƙota ma sun shigo, sai fakar ido take tana share hawaye, yau ɗin sosai take jin kishin Sunusi wanda ba ta san tana da shi ba.
Haka dai aka dinga ba ta haƙuri, har aka kawo amarya ɗakinta, kowa ya watse Sunusi ya shigo da rakiyar abokansa, suka gama nanayensu suka tafi, shi kuwa Sunusi yaƙe kawai yake yi, zuciyarsa na bugu, saboda ɗazu da la'asar da ya shiga banɗaki shi kaɗai ya san abin da ya gani a tare da shi.
Ƙara shiga banɗaki ya yi bayan kowa ya watse, bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, ganin har lokacin babu abin da ya canza, sai ya shiga ɗakin Sabila ya zauna a bakin gado, saboda ba zai iya jewa amarya a wannan yanayin ba, amaryar ma bazawara wacce ya san kar take kallon namiji.
Sabila tana zaune a sallaya lokacin, ta yi kamar ba ta gan shi ba, kusan minti ashirin suna a haka, tana ta mamakin zaman da yake yi, amma ta fi zargin kuɗin kazar amarci ne ba shi da shi, shi ne ya zo ya yi mata daɗin baki t ba shi, babu zato kawai sai jin shassheƙar kukan shi ta yi, ta kalle shi a firgice ta ce"Baban Amal! Lafiya? Kuka fa kake yi".
Ya ƙara bolum ya ce"Sabila idan ban yi kuka ba me zan yi?"
Ta ce"Me ya faru?"
Ya ce"Zo, zo Sabila ki ga ikon Allah".
Ta taso a sanyaye, gabanta sai faɗuwa yake yi, ta yi turus ganin yana ƙoƙarin zuge tazugen shi, ta ce"Lafiya? Mene ne haka ga yara a kwance?"
Bai saurare ta ba, ya ƙarasa kunce tazugen, ya buɗe mata wandon yana cewa"Sabila leƙo ki ga ikon Allah! Yau ni Sunusi ina zan kai abun kunya?"
Ta kuwa leƙa, gabanta ya faɗi gano abu kamar ɗan yatsa a ciki, kuma a yamushe, ta ce"Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Sunusi me ya same ka? Me zan gani haka?"
Daidai nan kuma Karime da ta gaji da jira ta fito tsakar gidan tana cewa"My Love! Me kake jira ne? Ko lallashin ne har yanzu?"
Ya yi saurin gyara wandon ya ɗaga murya ya ce"E, ba ta da lafiya ne, kin ga kawai zan kwana a nan".
Sabila ta fita tana cewa"Lafiyata ƙalau, ki je ki ɗauki mijinki, wai kunyarki yake ji, tun ɗazu nake cewa ya tafi ya ƙi".
Karime ta ce"Kunya kuma?"
Ta kuwa shiga ɗakin Sabilar da sallamarta, da mamaki ta kalli Sunusi fa ya sadda kansa ƙasa ta ce"Sunusi ƙalau kuwa?"
Ya ce"Ba ni da lafiya ne".
Ta ce"To taso mana, don ba ka da lafiya dai ka bar ni ni kaɗai?"
Ta ja hannunsa suka fito,yana riƙe da wandonsa a ƙugu, saboda bai gyara tazugen ba, haka suka shige ɗaki yaba waiwayen Sabila kamar mai neman ta cece shi.
GIDAN HAMZA
Babu abin da ya canza a halin Hamza sai ma ƙaruwa da ya yi, saboda har cikin azumi haka yake noƙewa ya ƙi yin cefane mai kyau, saboda abubuwa sun matso yana ta tanadi, don ma dai ya gama haɗa lefe an kai ana saura kwana biyu a fara azumi, su ma kuma ba su fasa yin mai daɗi su hana shi ba, haka zai kai azumi ya ci fara da mai, da asuba ma ya saƙime ta, tsoro ma yake kar basir ya kama shi, an kai azumi na biyar Mardiyya ta yi masa jar miya mai rai da lafiya ta ji nama, sannan ta yi cake da donut ta ce ya dinga haɗawa da shayi yana yin sahur, Hamza farin ciki ji ya yi kamar ya yi tsalle ya rungume ta, ya dinga godiya yana shi mata albarka, nan ya ɓarke yana faɗa mata dama suna nan da halinsu, ba su fasa hana shi miya ba.
Mardiyya ta ce"Ni fa ina mamaki wallahi, ka yi cefane ka yi komai a hana ka miya?"
Ya ce"To gane mini hanya My Mardis, ai idan ba ka yi dacen mata ba ka shiga uku, ni dai Allah Ya cece ni da ya haɗa ni da ke,wallahi ke haske ce a rayuwata Mardis".
Ta ce"Amma kuwa Allah Ya shirye su".
Hamza ya ce"Amin dai, ni fa wallahi ba don kar na jibga miki wahalar kula da yara ba da dukansu gida zan tura su, ni ke kaɗai ma kin ishe ni rayuwa wallahi".
Ta ce"To my Love kuma idan ka ɗora min kula da yara ta ya zan iya kula da kai? Ka bar su kawai, ai na san dai idan na shiga gidan 'yan kallo za su zama".
Hamza ya ce"Ƙwarai ma kuwa".
Suka gama shan fira, Hamza ya ɗauki ledar kayansa ya ce"My Mardis bari na wuce, dare yana yi, ki shiga ki huta kin sha aiki yau".
Ta ce"Haba ai yi wa kai ne, na ce wannan account ɗin nawa ya samu matsala, ka saka mini kuɗin a opay".
Gabansa ya faɗi ya ce"Wane kuɗi?"
Ta ce"Na cefanen, a wajen Mama na ari dubu hamsin na yi".
Ai nan take wata zufa ta yanko masa, ya kalli kayan hannunsa da nauyinsu ashe na dubu hamsin ne, ya ce"Amma Mardis..." Sai kuma ya yi shiru saboda kar ya ja wa kansa abun kunya.
Ya ce"Shikenan zan tura miki in sha Allah!"
Ta ce"To sai da safe, a opay fa, wannan lambar tawa opay ce".
Can ƙasan maƙoshi ya ce"Ok".
Sanda ya yi nesa da gidan sai ya ji kamar ya kurma ihu, yana fafutukar na kayan sallar yara da 'yan kajin sallah kuma ta yanko masa dubu hamsin, gabaɗaya miyar ma bai ji daɗinta ba saboda baƙinciki, kuma wannan karon ya ɓoye ta sosai, bai yarda sun gani ba, sanda ya tura mata kuɗin kuwa har ƙwallar baƙinciki ya yi. A ransa ya ce'Saude da Sahura ku kuka ja mini, kuma za ku gani a kajin sallarku, ko kai da ƙafa ba zan siya ba'.
Da azumi ya je ƙarshe Mardiyya ta ce za ta sake yi masa snacks ɗin sallah, ya ce Saude ta riga ta yi. Ta ce"To kaji fa? Na iya jar suya mai daɗi, idan ma dambun nama kake so duk zan yi maka".
Da sauri Hamza ya ce"A'a wallahi, kar ki wahala, duk suna yin wannan, idan Allah Ya kai mu babbar sallah sai ki soya min a ɗakinki".
Da haka ya lallaɓa aka bar zancen, duk da haka sai da ya yanka kaza ɗaya babba ya kai mata. Gidan nasa ma kowa kaza ɗaya ta samu, suka yi ƙorafi ya ce abin da ya samu kenan, bayan ya fita Saude ta ce"Sahura abun na Hamza fa gaba yake yi, me za mu yi da kaza ɗaya mu da yara? Kenan da ba mu shiga watanda ba sai dai mu sha takaici".
Sahura ta ce"Ai na faɗa miki dama".
Saude ta ce"Ai kuwa wallahi haƙarƙari zan ajiye masa da fukafukai".
Sahura ta ce"Kina da imani, ni wallahi kai da ƙafa ne rabonsa".
Haka kuwa aka yi, Sahura ta ajiye masa kai da ƙafa, dama ranar Saude ce da girki, dayake ya siyo kayan miya na miyar sallah, sai ta saka masa fukafukai da maƙogoro, don haƙarƙarin ma sha'awa ya ba ta ta cinye. Hamza ya baje zai ci abinci, ya kalli naman ya ga abubuwan da aka saka masa, ya ce"Saude ina naman? Ko sai a miyar gobe za a ba ni rabona?"
Saude ta ce"Kaza ɗayar ce har za ta kwana? Ga rabonka nan an yi maka wasali da shi".
Ya haɗe gira ya ce"Ba na son haka Saude kamar ya ga rabona?"
Ta ce"To kaza ɗaya me za ta yi mana? Ni ai na zata ma nufinka ba sai mun ba ka ba".
Ya ce"Hmm shikenan, yanzu da kika cinye ƙiba kika fi ni?"
Ta tashi ya bar ɗakin, ya ƙwalawa Sahura kira, ta tashi ta ɗauki farar ledar da ta saka masa kai da ƙafa ta shiga ɗakin nasa, ta ajiye tana cewa"A ci fa haƙuri yara sun cinye".
Ya daga ledar ya kalla yana cewa"Sahura! Sahura! Innalillahi wa alaihi raji'un!" Ba ta kula shi ba ta fice daga ɗakin.
Ya zauna shiru, kafin ya ce"Ai shikenan".
Daga yara har manya a gidan kowa kayan sallah kala ɗaya ya yi musu, ya zo da atamfofi guda biyu ya ce Saude ta zaɓi ɗaya tun da ita Sahura an yi mata leshi, ai kuwa Sahura ta yi tsalle ta dire ta ɗauke ɗayar atamfar ta ce ta faɗar kishiya ce, haka ya gaji da tijara ya rabu da ita, ya zamana Saude ce ba ta samu kayan faɗar kishiya ba.
Hamza an gama duk wani shirin aure, saura kwana uku ɗaurin auren aka zo aka yi jeren kayan amarya, tuni ya ƙauracewa matan nasa yana ta shirya kansa da magungunan maza, don ya more yadda ya kamata. Ana gobe ɗaurin aure Mardiyya ta ce akwai yayanta da ya zo daga Kalaba shi da matarsa, sun zo biki, a gidan shi na nan suka sauka, kuma ya ce yana son ganin shi, ya je su gaisa, Hamza aka buga wanka suks tafi da Mardis da ta yi masa jagora.
A hanya take ba shi labari ai soja ne, aiki ne ya kai shi Kalaba, ita ta fara shiga ta yi masa iso, suka shiga suka zauna a falo, yayan nata ya shigo ya zauna suna gaisawa, matarsa ta shigo rike da jug ɗin da ta kawo musu lemo, babu zato Hamza ya yi mummunan gani, ya zabura miƙe tsaye yana kallon Asiya tsohuwar matarsa da ta daskare a tsaye riƙe da kofin tana kallon shi, yayan Mardiyya ya ce"Malam Hamza lafiya kuwa?"
Sai ya zauna yana murmushin yaƙe ya ce"Lafiya lau, ina ga cinnaka ne ya cije ni".
Asiya ta kalli Mardiyya ta ce"Wannan ne wanda za ki aura?"
Ta ce"Shi ne, kin san shi ne?"
Hamza ya fara kame-kame, ya janyo mafici ya fara fifita ya ce"Waske Asiya maze kawai".
Mai gidan ya ce"Kamar ya ta Waske? Me yake faruwa ne?"
Hamza ya tashi yana cewa"Oga na bar babur ɗina a waje ina zuwa".
Kafin ya fita Asiya ta ce"Baban Haidar wannan fa shi ne Hamza tsohon mijina".
Baban Haidar ya zaro ido ya ce "Da gaske? Tsohon mijinki dai wanda ya gana miki azaba? Wanda ɗa ya mutu a cikinki kina gidansa?"
Ta ce"Shi ne dai".
Ya ce"Wanda muka so zuwa har garin nan mu karairaya shi aka ce mu rabu da shi?"
Asiya ta ce"Wallahi shi ne".
Ya ce"Shi ne ya lallaɓo zai aure ƙanwata? Kan uban nan! Ashe yau akwai fareti a gidan nan".
Ya fara kokowar cire riga, a guje Hamza ya zuba yana cewa"Mardis sai kin taho". Ba zai bari kansa ya yi murfi ba don haka bai bi ta kan babur ɗinsa ba, saboda gani yake ma tsayawa tada babur ɗin ɓata lokaci ne.
LAST FREE PAGES! Daga wannan shafin free pages sun ƙare, mai son cigaba ya hanzarta biyan kuɗin karatunsa, 700 ne, idan ya zama complete 1k ne.
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015