Showing 6001 words to 9000 words out of 34919 words
Chapter 3 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
aiko mata da abinci, amma tana yi ne idan abincin ya yi mata yawa, ko kuma idan ta canza girki ta yi abun marmari, ba wai don tunanin a cikin yunwa suke ba.
Sai dai kash! Yau Minal ta tona asirin, don kuwa cewa ta yi"Ni ina da lafiya, yunwa kawai nake ji". Ta yi maganar cikin muryar kuka.
Kunya da haushi suka kama Sabila, sai ta sunkuyar da kai kawai, Maman Nawal ta ce"Kar dai ki ce ba su karya ba har ƙarfe goma".
Sabila ta ce"Mantawa ya yi ba mu da abun karyawa, ya fita, kuma wayarsa babu caji bare ba kira shi".
"Subhanallah! Ga abinci can na saka a firji, don jiya ba wanda ya ci abincin daren, dayake ya shigo mana da gurasa da nama, ina zuwa". Maman Nawal ɗin ta faɗa tana tashi da sauri ta fita daga gidan.
Tana fita Sabila ta kalli Minal ta ce"Minal ban hana ki wannan surutun mara kan gado ba? Wannan abin da kika yi fa roƙo ne da kwaɗayi, ke sai yaushe za ki fara jin magana ne?"
Ta cigaba da share hawayenta ba ta ce komai ba.
An ɗan jima kaɗan kafin Maman Nawal ta dawo don sai da ta kunna gas ta ɗumama abincin, ta kuma dafa shayi, ta shiga gidan da babbar kula da kuma jug, wanda ta haɗa musu shayi mai kauri, Sabila ta buɗe kular tana godiya, haɗaɗɗiyar jollof ɗin shinkafa ce, wacce ta ji kayan lambu da nama sai ƙamshin curry take yi, ta ɗakko faranti da kofuna ta zuba musu, suna ci suna fira, maman Nawal ce ke cewa"Yanzu da ban shigo ba haka za ku yi ta kiransa? Ni da ke ai mun zama ɗaya, gaskiya idan irin haka ta faru ko a waya ki dinga faɗa mini, ko ki aiko yaran, ni dai a yadda na ɗauke ki don kin zo gidana kin shiga kitchen kin dafa son ranki ba komai ba ne wallahi".
Sabila ta ce"Na gode sosai maman Nawal, Allah Ya bar zumunci".
Haka suka dinga fira, dai da aka kusa taso su Nawal daga makaranta sannan ta bar gidan. Sunusi bai dawo gidan ba dai bayan la'asar, ya zo da garin tuwo kwano ɗaya, ya ba ta ɗari biyar, shi fa duk a zatonsa har lokacin ba su karya ba, amma kuma ya kawo garin tuwo da la'asar, wacce tun safe ba ta ci komai ba ina ita ina aikin tuwo? Ita kanta ɗari biyar ɗin ba don tana da barkono da kuka ba ai ba za ta isa cefane tuwon ba, dayake yaran sun je islamiyya ita da kanta ta fita ta yi cefanen ta ɗora tuwon.
Da daddare suka ci tuwon tare da yara, suka yi bitar karatun islamiyya da na bokon, sannan ta yi musu shimfiɗa suka kwanta, har suka yi bacci ita tana zaune tana nazarin rayuwa.
Wajen ƙarfe tara ita ma ta fara jin baccin, ta tofe su da addu'a duk da sun yi da bakinsu kafin su yi baccin. Ta koma ɗakin gadonta ta kwanta, shiru ta yi tana tunani da ƙirge a zuciyarta, idan ba ta ɓata a lissafi ba yau kwana talatin da uku kenan rabon da wata mu'amalar aure ta shiga tsakaninta da Sunusi, ita har mamakinsa take yi, kamar ba namiji ba, dama can tun farkon auren a haka suke, sai su fi sati bai neme ta ba, amma yanzu aka yi shekaru da auren nasu sai abun ya ta'azzara, babban tashin hankalin ita Sabila tana cikin jerin mata masu yawan buƙatuwa, lokuta da dama tana jin kamar ta neme shi, amma sai kunya ta taushe ta, haka take ta daurewa, wani lokacin ta yi ta fama da ciwon mara.
Yau ya dawo da wuri, ƙarfe goma da 'yan mintuna ya dawo, tuni bacci ya ɗauke ta, bugun da yake yi tare da kiran wayarta ya sa ta gane shi ne, ta je ta buɗe masa ya shigo, warin sigari da wiwi ya daki hancinta, kamar ba shi ne ta fita yana ƙamshin turare ba, idan da sabo ta saba, amma takan ji haushi a duk sanda ta ji yana warin kayan maye, ta ce"Sannu da zuwa".
"Yawwa" Ya amsa a daƙile, ita har mamakin yadda ya ƙware a kan fushin rashin dalili take, amma tana zargin hakan yana da nasaba da ƙwayoyin da yake afawa.
Ta sake cewa"Na kai maka ruwan wanka?"
"E" Kawai ya ce, ta zuba ruwan ta kai masa, ya shiga, ta ɗakko kulolin da ta zuba masa tuwon ta ajiye, bacci ne a idonta don haka ta koma ta kwanta.
Sunusi bayan ya fito daga wankan ya buɗe kular, sai da ya yi tsaki ganin koriyar miya, duk da dama ya san abin da zai tarar kenan, shiyasa ya tsaya ya ci indomi a waje kafin ya shigo gidan, don haka kwanciya kawai ya yi ba tare da ya ci tuwon ba.
Wayarsa ya janyo ya kunna data, ya dasa chatting da 'yan mata, ya yi da wannan ya yi da waccen, kuma duka na batsa ne, bai yi bacci ba sai da ya samawa kansa nutsuwa ta hanyar wasa da al'aurarsa, ya tashi ya je ya sake yin wanka, sannan ya kwanta bacci ya ɗauke shi, wajen ƙarfe ɗaya.
08028966015
[07/07, 7:58 pm] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
*AURE A YAU*
NA
*SADIYA ABDULRAZAK*
MARUBUCUYAR
Sandar dukan uwargida
Miji goma
Wani zaman
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Wutar ƙaiƙayi
Da walakin
Matar shige, dss
*First class writers association*
Page 3
A ƙa'idar Sabila idan ta tashi da asuba ba ta komawa bacci, idan ta idar da sallah za ta yi ta karatun Qur'ani ne, domin ita ɗalibar hadda ce kafin aurenta, tana ɗaya daga cikin ɗalibai masu ƙwazo a makarantar islamiyyarsu, duk musabaƙa ita ce kan gaba, ta yi saukar biye, ta yi ta hadda, kuma Allah Ya taimake ta har yanzu bayan ta yi aure ba ta watsar ba, gari ba zai taɓa wayewa ba dare ya yi ba ta karanta Qur'ani ba, tana kyautata zaton hasken Qur'ani yana rage mata kaso mai yawa cikin ƙunar zuciyarta. Sai ƙarfe shida saura kwata take tashi, ta kunna wuta ta dafa ruwan wanka sannan ta ɗora abin da za su karya da shi, yau ɗin ma haka ta yi, bayan ta dafa ruwan wanka ta ɗora ɗumamen tuwon jiya, ta ɗumama masa nashi na jiya da bai ci ba da ban, ta kai masa ɗaki ta ɗora a kan mudubi, har yanzu bacci yake yi, babu niyyar yin sallar asuba. Bayan yaran sun karya ta yi musu wanka ta shirya su, ba ta da ko ficika, kuma makarantar ba a zuwa haka yaro babu abinci babu kuma abun motsa baki, biskit ake siya a basu su tafi da shi, kuma wataran ba ya siya, sai dai idan tana da kuɗi ta siya, idan ba ta da shi ta karɓa bashi a wajen mai kantin kusa da su, matashi ne mai hankali da fahimta, don haka ba ta jin nauyin karɓar bashin, idan ta samu sai ta kai masa.
Ita da kanta take raka su makarantar, duk da babu nisa sosai da gidan nasu, amma duka yaran unguwar da suke zuwa suna da mai babur ɗin kai su, shi kuwa Sunusi ya ce ba shi da halin ɗaukar musu mai babur, hakan ya sa take zuwa ta kai su, idan an kusa tasowa ta je ta ɗakko su.
Ta tsaya a shagon ta karɓi biskit ɗan dari biyu guda biyu ta sakawa kowacce a cikin jakarta, sannan suka kana hanya, tana tsakiyarsu riƙe da hannayensu, suna taɓa fira har suka ƙarasa, ta dawo gida, sai a lokacin ta zauna ta ci nata tuwon, sai da ta gama wanke-wanke ta share gidan sannan Sunusi ya fito, tana jin ya shiga banɗaki ta fito ta zuba masa ruwan wanka, ya gama wankan ya ɗakko tuwon ya dawo falo, yana ta ɓata rai kamar dole aka ce sai ya ci, ya kai loma ta uku ya ja tsaki yana cewa"A ce girki ma mace ba ta iya ba, miya ma ba za a nutsu a yi ta ba, abu sai ka ce a gidan yari".
Mamaki ya kama Sabila, domin ita dai ba ta ga aibun miyarta ba, ta ce"Amma baban Amal ya kake so miyar nan ta kasance? Ko ka manta a naira ɗari biyar aka yi cefanen? Ka lissafa ka gani mana, gawayi, mai, magi, daddawa, attaruhu da albasa, ba don ina da wasu mahaɗin miyar ba da dole sai na yi ciko, a zamanin nan cefanen tuwo da ɗari biyar yaushe za a sha miya mai daɗi? Ai ba wai rashin iyawa ba ne rashin cefane mai kyau ne".
Ya ce"To ai sai ki fara fita kina neman wanda za ki yi cefanen mai kyau! Aikin banza, wallahi ke wannan ko duka kasuwar aka kawo miki girki ba zai yi daɗi ba, na ga da har naman miya siyowa nake, kawai dai kina yin abin da kika ga dama ne, kuma lokaci ne, wallahi waje kika samu, nan gaba kaɗan ba za ki yi ba".
Don son kawar da firar ta ce"Mai ruwa ya zuba kana bacci, zai dawo ya karɓi kuɗin".
"Allah Ya ba ni, na ba shi". Ya faɗa cikin halin ko'inkula.
Ya gama ci ya tashi, ya ajiye mata dubu ɗaya da ɗari biyar ya fita tana yi masa a dawo lafiya, tana zaune tana jan lissafin yadda za ta yi girki da kuɗin ya isa har dare sai ga ƙawarta wato maƙociyarta Maman Nawal ta shigo gidan, suka gaisa ta nemi waje ta zauna, Sabila ta kalle ta sosai ganin yau sam babu walwala a tare da ita, ta ce mata "Maman Nawal lafiya kuwa? Na ga kamar ranki a ɓace".
Ta fara hawaye kafin ta ce"Wallahi Maman Amal na gaji, na gaji da auren nan haka, gara kawai ya sake ni tun kafin mu tara 'ya'yan da na san ba za su yi alfahari da shi a matsayin mahaifi ba". Ta fashe da kuka ta kifa kanta a kujera.
Sabila ta yi mamaki sosai, saboda tun da suke ba ta taɓa ce mata suna samun matsala da mijinta ba, duk da dai ba su saba firar mazajen nasu ba, da tausasa murya ta ce"Subhanallah! Ke kuwa maman Nawal me ya yi zafi haka da har kike maganar saki? Me yake yi miki da har kike ganin rabuwarku ce maslaha?"
Ta ɗago tana share hawayen ta ce"Na gaji ne, idan an tara mata dubu da ƙyar za a samu guda ɗaya da za ta iya zama da mijina, na fi kowa rashin dacen miji, rayuwata tana cikin hatsari, aure yana zama silar farinciki ni nawa ya zama silar ƙuncina, kuma na san ƙarshe shi zai yi ajalina".
Jikin Sabila ya yi sanyi saboda sam ita ba ta yi mata kama da wacce take cikin matsala a gidan aure ba, ta ce"Maman Nawal mene ne matsalarki don Allah? Abinci yake hana ki? Haƙƙin mu'amalar auratayya? Ko aure zai ƙara?"
Ta ce"Idan don waɗan nan ne ai duk da sauƙi, da a ce duka matsalolin nan aka haɗe mini wallahi da zan fi jin sauƙi, kuma ba lallai ma na shiga damuwa ba".
Sabila ta ce"Hmm Maman Nawal don dai bai bar ki da yunwar ba ne, ina mamakin matan da suke cewa da wata rayuwar gara zaman yunwa, abinci ai shi ne gaba da komai, kin san tashin hankali da ƙuncin da mace take shiga idan aka wayi gari ba ta da abin da za ta ci ta bawa yaranta? A bar mace da yara ƙanana wanda yanzu suka fara rayuwar, ba su san ƙalubalenta ba, ke ba namiji ba ballantana ki fita ko dako ki yi ki nema, to ya ake so mace ta yi? Wallahi Sabila inda ni ce ke, mijina yana ba ni abinci ko da zai yi mini kishiya kuma ba zai dinga ba ni haƙƙin auratayya ba zan zauna lafiya da shi, don haka ki ma daina saka kanki a jerin mata masu matsala wallahi, ke 'yar gata ce".
Cikin kuka ta ce"Ba za ki gane ba maman Amal, ba za ki gane ba, wallahi da gaske gara zaman yunwa a kan zaman aurena, ni da ana canjin rayuwa da zan so a ce kin musanya mini da taki rayuwar, don wacce ta zauna da mijina ce kawai za ta fahimce ni".
Sabila ta yi murmushi mai ciwo ta ce"Kina ganina ne kawai ina murmushin fuska ba ki san mene ne a zuciyata ba, Maman Nawal yawanci zaman yunwa nake yi a gidan nan, abinci mara daɗin ma ba kullum ba, babu sutura, tun kayan lefe rabon da ya yi mini sutura, idan kin ga kaya mai kyau a jikina to 'yan'uwana ne suka ba ni, ban taɓa haihuwa ya siyawa yaron ko wando ba, ragon suna kawai yake yi, sabulun wanka, omon wanki, man shafawa duk ni nake yi wa kaina, idan ba ni da shi sai dai na zauna haka, inda a ce na san kwata-kwata ba ya samu da sauƙi, ba zan damu har haka ba, yana sana'a, wannan sana'ar kayan gwarin tana kai masa, yana samu daidai gwargwado, amma kuɗin a shaye-shaye yake ƙarewa, har caca yi yake, sannan wulaƙancin safe da ban na dare da ban".
Ta share hawaye murya na rawa ta ce"Ban taɓa zaton haka daga gare shi ba, wai miji ba zai zauna ya yi fira da kai ba? Babu magana mai daɗi? Sannan babu hakkin auratayya, kamar ba namiji ba fa,ba ya sha'awata, ya raba dare yana chatting kuma na san da mata yake yi, yanzu irin wannan rayuwar tawa kike sha'awa?"
Maman Nawal ta girgiza kai ta ce"Shiyasa na ce ba za ki gane ba, wallahi da a ce irin matsalolinki nake fuskanta da ba zan damu ba, da ban nemi rabuwa da mijina ba,naki mai sauƙi ne, kukan daɗi kike yi".
Tsoro ya kama Sabila ta fuskance ta da kyau ta ce"Ke kuwa Amina wace matsala kike fuskanta haka? Hankalina ya tashi, don Allah ki faɗa mini".
Ta share hawaye ta ce"Wannan sirrina ne Sabila, ba zan iya tonawa kaina asiri ba, kuma a haka kun ƙi fahimtata, ga shi mahaifiyata ta ce muddin na bari aurena ya mutu ba ta yafe mini ba, kuma ta kwashe albarkarta dake kaina har abada, na san darajar uwa, na san illar fushinta a gare ni, saboda haka na zauna nake ta cutuwa, amma na gaji matuƙa, sotari idan ban shigo gidanki ba to ina can ina kuka ne, inda hawaye suna ƙarewa da nawa sun ƙare".
Sabila ta ce"Kenan ba ni da matsayin da za ki iya faɗa mini sirrinki? Ban kai na ji matsalarki ba? Ko ba ki yi mini yardar da za ki iya ba ni sirrinki ba? Na yi miki alƙawarin riƙe miki sirrinki, Maman Nawal barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, da za ki furta ɗin ƙila ki samu mafita".
Ta share hawaye ta ce"Ba komai, ba rashin yarda ba ne ya sa na ƙi sanar da ke, amma nan gaba idan lokacin sanin ya yi dole za a sani ko da ban faɗa ba, sai dai na san a lokacin matsalar ta yi girman da ba za ta gyaru ba".
Sabila ta ce"Shikenan tun da kin zaɓi riƙe matsalarki a cikinki, zan saka ki a addu'a Allah Ya yi miki magani, Ya kawo miki mafitar alkhairi, Allah Ya sanyaya miki zuciyarki, sannan ku rage bacci, ki dinga sallah kina faɗawa Allah, za ki samu mafita in sha Allah".
Ta ce"Allah Ya sa".
Sai kuma suka yi shiru na ɗan lokaci, kafin maman Nawal ɗin ta ce"Maman Amal dama halin da kike ciki kenan a gidan nan? Abinci ma wahala yake yi miki amma shi ne ba ki taɓa faɗa mini ba? Kina kallo kullum bayan kwanon almajirina sai na zubawa almajirai guda uku sadaka? Ashe ba ki ɗauke ni yadda na ɗauke ki ba?"
Sabila ta ce"Wallahi kar ma ki yi zaton haka, ban da yau ai kin ga ba mu taɓa yin firar matsalolin ba, yau ɗin ma dalili ne ya sa kika ji waye mijina da kuma halin da nake ciki".
Maman Nawal ta ce"Amma kuma shikenan a haka za ku zauna ba za ki taka masa burki ba? A ce yana sana'a ya dinga hana ki abinci? Wannan wulaƙanci ne".
Sabila ta ce"Lokaci ne, ina ta faɗawa Allah, in sha Allah komai zai canza, ai Allah ba ya bacci, kuma na san yana sane da ni, idan ban yi haƙurin ba ya zan yi? Yanzu maza duk haka suke, idan ka fita daga nan ba ka san ina za ka fita ba, ba na hasashen wai aurena zai mutu zan bar mijina na farko, a kullum fatan shiriya nake yi masa da canjin hali, domin rabuwa ba mafita ba ce, kowa a rayuwa yana da tashi jarabawar, to ni wannan nake kallo a matsayin tawa jarabawar, kin ga kuwa ba zan ce zan guje mata, domin wanda Ya jarabce ni ɗin ya san zan iya ne, Allah ba ya jarabtar bawa da abin da ba zai iya ba, ni da ke duka mu yi haƙuri, mu ɗauka ibada muke yi, Allah shi zai biya mu, idan sun cuce mu shi zai saka mana, ni dai ba na jin akwai abin da Sunusi zai yi mini na ce ya sake ni, sai dai idan shi ya sake ni don raɗin kansa, ke ma kuma don Allah ki cire batun rabuwa a zuciyarki, zai gyara in sha Allah, za ku zauna lafiya".
Ta ce"Hmm ke dai Allah Ya ganar da shi ya canza ku zauna lafiya ɗin".
Sabila ta ce"Har ke ɗin ma, kin fara haihuwa da mutum