Showing 3001 words to 6000 words out of 34919 words

Chapter 2 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt

sam ba ita ba ce, kawai takaicin mijinsu Hamza ne ya hana ta sukuni.

Ta ce"Saude".

Saude ta juyo ta ce"Na'am".

Sahura ta ce"Ni fa ina zargin Hamza, ina tunanin akwai abin da yake ɓoye mana wallahi, to a kan me da muna shiga ɗakinsa mu yi kallo yanzu rana tsaka zai ce kar wacce ta sake shigar masa ɗaki, ki duba fa ki ga yanzu shara da mopping ma sai dai ya yi da kansa, shi kuwa uwar me yake ɓoyewa a ɗakin da ba ya so mu shiga mu gani?"

Saude da ita ko a jikinta, tun da ba yau ta saba shanye takaicinsa ba, ta taɓe baki ta ce"Uhm! Ke ma dai Sahura kina da neman magana, kin iya tada zaune tsaye, to idan ba shiga shoro ba shanu ba ina ruwanki da ɗakinsa?"

Sahura ta ce"Ai kuwa da ruwanmu, Saude mijinmu ne fa, amana ce Allah Ya ba mu, kuma tun da yanzu ya bar gaban iyayensa ya dawo zama tare da mu, mu muke da hakkin kula da tarbiyyarsa, idan ya lalace ai mu ma mun shiga uku".

Saude ta yi dariya ta ce"Tabɗijan! Lallai Sahura kina da ƙarfin hali, to kin ga ni dai babu ruwana da rayuwarsa, ya je ya yi ta rufe ɗakinsa, ba dai duk me girki tana shiga ta kwana ba? To me za mu shiga mu yi da rana?"

Sahura ta ce"Da me muke yi idan ba kallo ba?"

Saude ta ce"Yanzu tun da ya hana ba sai mu haƙura ba?"

Sahura ta ce"Ni fa Saude na fara zargin anya Hamza ba aure yake shirin ƙarawa ba?"

Saude ta ce"Babu mamaki".

Sahura ta ce"Ke kam ba a taɓa haɗa kai da ke Saude, gara na yi ta kaina, ba dai yau ni ce da girki ba? Wallahi sai na gano mana abin da yake ɓoyewa".

Saude ta ce"A'a Sahura, ita fa kaza a garin tone-tone take tono wuƙar yankata".

Sahura ta ce"Ai kuwa sai dai ta yanka mu tare da shi, amma tabbas yau akwai operation ɗin tsakar dare, sai na ga ko me yake ɓoyewa".

Saude ta ce"To Allah Ya sa a wanye ƙalau, amma idan abun ya kai wanda za a bawa hammata iska don Allah ki ƙwala mini kira, saboda na kashe kwarkwatar idona".

Ta ce"To Saude me zai hana na kira ki mu bincika tare?"

Saude ta ce"A'a, ni yanzu sai tawa ta yi zafi idan kwaɓar ta yi ruwa, kin san dai ni karkatacciyar kuka ce a wajensa, har gara ma ke ɗin".

Sahura ta ce"Allah Ya kaimu daren da rai da lafiya".

Saude ta amsa da amin, kowa ya cigaba da sabgarsa.

Gidan Hamza gida ne wanda za a kira shi da gidan talaka, amma mai rufin asiri, yana samu a kasuwa daidai gwargwado, tun sanda Ogan shi ya yi masa freedom wato ya yaye shi, aka ba shi shagonsa yake cin gashin kansa, yana sauke nauyin iyalansa daidai arziƙinsa, kuma yana yi musu adalci, suna zaune lafiya, hankalinsa a kwance, tun da matan ba su saka kishin juna a ransu ba.

Shi son mata a jinin Hamza yake, don haka ba ya rabuwa da 'yan kule-kulen mata, a sha soyayya kawai ta rage dare, amma yanzu da yake ganin ya samu faragar da zai iya riƙe mata uku sai ya fara shirin yin aure, wata yarinya ya samu Mardiyya, a kasuwa suka haɗu, tana yawan siyan kaya a shagonsa, suna son juna sosai, musamman da Hamza yake kambama mata arziƙinsa da zuzutawa fiye da yadda yake a zahiri, yana sakar mata bakin aljihu sosai, shiyasa ya yi nasarar korar duk samarinta, ya tsaya shi kaɗai yana ta kanainaye zuciyarta.

Sam Mardiyya ba ta damuwa da wai Hamza yana da mata biyu da 'ya'ya, saboda ya gama sanar da ita matan nasa duk gidadawa ne, zaman haƙuri kawai yake yi da su, duk sun tsufa kamar yayyunsa, uwargidan ta zama kamar ƙanwar babarsa saboda yadda ta fara tsufa, ya gaji da ba su kuɗin gyara, kawai ba za su gyaru ba, don haka ya yanke hukuncin ƙara aure, ya auri 'yar shawalwala kamar Mardiyya ko ya huce takaici.

Yanzu haka ya kai kuɗin aure har an saka rana, kuma dalilin da ya sa ya hana su shigar masa ɗaki kayan lefe ya fara haɗawa, suna nan a cikin sif ɗinsa yake tarawa, so yake sai ya gama komai na shirin auren sannan ya sanar da su.



To sai ga shi kuma yau Sahura ta yi ƙudurin bincikawa, ko ya za a kaya?


08028966015
[06/07, 8:04 am] Sadiya Abdulrazak: *AURE A YAU*



SADIYA ABDULRAZAK

MARUBUCUYAR
Sandar dukan uwargida
Miji goma
Wani zaman
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Wutar ƙaiƙayi
Da walakin
Matar shige, dss

*First class writers association*

Page 2


IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!

Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?

To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
👉 Join Here

Za ki sha mamaki! 🤩

Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau

📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture



Da daddare bayan Hamza ya dawo daga sallar isha'i Sahura ta kai masa abinci ɗakin, yana danna waya yana cin abincin, ita kuma ta nemi waje ta zauna tana ta kallon ɗakin, don sanin makamar aikinta, ma'ana tana son gane anjima ta ina za ta fara bincike, sif ce mai biyu a dakin, da gado, sai wata tsohuwar akwati babba dake gefe, ga kuma takalmansa a jere, babu wasu shirgi da yawa a ɗakin. Hamza ya ajiye wayar ya mayar da hankalinsa gabaɗaya kan abincin, ba tare da ya kalli Sahura ba ya ce"Kuma me kike jira?"

Ta ce"Fira zan taya ka, ka san an ce yana da kyau mace ta zauna a gaban miji idan zai ci abinci, wai ko gishiri ya yi yawa ba zai gane ba". Ta ƙarasa maganar da 'yar dariya.

Shi ɗin ma dariyar ya yi, amma ta fi kama da ta takaici, sai kuma ya yi guntun tsaki ya ce"Hmm Sahura kenan, to ai ba mata irinku ke da Saude ake nufi ba, mata ake faɗa wanda suke kan ganiyar ƙuruciya, kuma suka iya ado da kwalliyar zamani, sannan suka iya kalamai masu kwantar da hankali da sanya nutsuwa, yanzu nan inda wacce ta san kan miji ce ai da a bakina za ta ba ni, yadda kike rusheshiyar nan ga tsayi ga ƙiba idan wata ce ma har a cinya za ta ɗora ni, to shi ne ka san ka yi aure".

Sahura ta ce"Au wato dai kana nufin mu kana zaune da mu ne kawai ba don kana samun yadda kake so ba".

Ya ce"Ƙwarai kuwa, ai ku ma kun sani, sai dai kawai ku maze, a ce ba za ku kwana cir a ɗakina ba, saboda kuna kula da yara, wataran ma sai na kira ku za ku zo, amma idan ka auro buduruwa sai ka ɓarje guminka hankali kwance, babu ciki babu goyo".

Sahura ta ce"Amma ita ma ai za ta haifa ko?"

Ya ce"To kafin ta haifa ɗin ai na mora dai".

Sahura ta ce"Duk tsiya morewar ba za ta wuce shekara ba, amma a shawarce me zai hana kawai ka auro juya? Ka ga sai ka dawwama kana morewa".

Ya ce"Sai kuma ki yi ai, amma dai wallahi ku kiyaye ni, don kana zaune da mutum ne ba ka san shirinsa ba, daga lokaci ya yi sai dai kawai ku ji ɓurum wata shawalwalar ta banko ƙofar gidan nan".

Sahura ta ce"A haf! Ai dama na zargi haka wallahi, kenan Hamza aure kake son ƙarawa?"

Ya rausayar da kai ya ce"Kanki ake ji".

Ta ce"Hmm, ashe shiyasa ka rage mana cefane? To kuwa wallahi da sabon lale".

Ya ce"To ai sai ki lalo mu gani, zan zauna ne mata babu mai tarairayata yadda ya kamata? Saboda raini a ce tun da na rabu da wacce matar tawa jinin sojoji babu wacce ta sake ce mini My love ko ɗan Sweety? Kun mayar da ni tsoho, Hamza gatsal kuke kirana kamar wani dankali ko gurasa, wallahi na gaji gara na samo mai maƙe murya tana ce mini sweety, don na gane da saurana ban tsufa ba".

Sahura ta ce"To Hamza inda ka san suna kake so mu canza maka ai da tuni an wuce wajen, indai don suna za ka ƙara aure ni na ji zan dinga ce maka sweetyn".

Ya ce"Daga baya kenan an yi sadaka da karuwa".

Ta ce"Haba Sweetyna tun da mun ɗauki gyara ai sai a sassauta".

Ya ce"To idan kun gyara kanku, kuma ba wai na ce miki zan ƙara aure nan kusa ba, amma dai ina ra'ayin ƙarawar".

Sahura ta ce"Hmm ka dai gama kwan-gaba kwan-bayanka".

Bai sake magana ba, har ya gama cin abincin, ya sha ruwa ya tashi kenan wayarsa ta fara ringin, Sahura ta leƙa, ta ga sunan My Baby ne yake yawo a screen ɗin, ta jinjina kai, Hamza ya duba sai ya yi banza da wayar, ya fara rage kayan jikinsa don wanka zai shiga, ya gama tsaf ya ga Sahura ba ta da niyyar fita daga ɗakin, ya kalle ta ya ce"Ni Sahura akwai abin da kike jira ne?"

Ta ce"Babu, ai na faɗa maka fira na zo taya ka".

Ya ce"To ai mun yi, ki je ni wanka zan shiga".

Ta gyara zama ta ce"To kuma ka shiga ka fito mana".

Ya ɓata rai ya ce"Idan na fito ma ai ba zama zan yi ba, fita zan yi".

Ta ce"To je ka, idan ka fito sai na shafa maka mai".

Ya yi mata mugun kallo ya ce"Kin ga Sahura fita kar ki ɓata mini rai".

Ta ce"Ba zan fita ba, wai ni Hamza me kake ɓoye mana a ɗakinka?"

Ya ce"Yankan kai na fara".

Ta ce"To idan ba dai da wata a ƙasa ba na ga da a gida kake barin mukullin mu shiga da rana ko ba ka nan mu yi abin da za mu yi".

Ya ce"To yanzu na janye, idan kuma ɗakinki ne sai ki hana ni na hanu".

Ta tashi tana cewa"Hmm idan ta yi tsami dai za mu ji".

Ya ce"In sha Allahu ƙamshi za ta yi ba tsami ba, wuce dai".

Suka fita tare, ya datse ɗakin da mukulli yana cewa"Mace sai naci babu zuciya, wallahi har gara Saude, da ita ce da tuni ta yi zuciya".

Ya zuba ruwa ya shiga wankan, ya fito ya shirya ya baza turare, ya tafi gidan su Mardiyya, don ita ce take ta jero masa kira.

Yana fita Sahura ta shiga ɗakin Saude, inda take ta jiyo duka yaran gidan suna ta wasa, ta same ta da jimami ta ce"Saude! Mutumin nan fa da gaske aure zai yi, kin ji yadda yake kushe mu kuwa? Wai suna me daɗi ba ma faɗa masa".

Saude ta taɓe baki ta ce"Wallahi ko a jikina, Allah Ya ba shi sa'a Ya sanya alkhairi".

Sahura da mamaki ta ce"Wai da gaske kike?" Saboda ita har zuciyarta take jin kishi da ƙarin auren.

Saude ta ce"Wallahi har raina ba na kishin Hamza, to da can ma da sana'ata ba ta yi ƙarfi ba ban damu da aurensa ba, ballantana yanzu da ko shinkafa ce bai kawo ba zan iya ci da kaina? Dama fa a ƙa'ida ke za a yi wa kishiya ba ni ba, ni ai ke ce kishiyata" Ta karasa maganar da dariya.

Sahura ta ce"Lallai na ga sam ba ki ɗauki abun da muhimmanci ba, shikenan, ni kuwa zan ɗaura ɗamarar yaƙi".

Daga haka ta fice daga ɗakin, Saude tana cewa"Allah Ya ba ki sa'a".

Ƙarfe goma na dare da 'yan mintuna Hamza ya shigo gidan, Sahura dake zaune tana jiran zuwansa ta tashi ta fito daga ɗakinta, ta gan shi a tsakar gidan yana kafe babur ɗinsa, ta ƙarasa taba cewa"Sannu da zuwa".

A daƙile ya ce"Yawwa".

Don shi yau sam ba ya gayyatarta zuwa ɗakin nasa, musamman ma da ya taho da ƙunshin balangu zai ci a lafiyarsa.

Cikin dabara ya cusa ledar a aljihunsa don kar ta gani, yana buɗe ɗakin ta mara masa, ya ɓata rai ya juyo ya ce"Sahura lafiya kuwa?"

Ta ce"Ka manta yau ni ce da girki?"

Ya ce"Ban manta ba, sai dai kuma ba na gayyatarki yau ɗin".

Ta ce"Ni kuma ina gayyatarka, idan kuma ka fara tauyewa matanka hakkinsu ne sai na ji".

Ya yi tsaki ya ce"To ni dai a gajiye nake wallahi, idan ma kin kwana a ɗakin nan haka za ki kaɗe zaninki ki tashi".

Ta ce"E dai na yarda, ko iya numfashin Sweetyna na ji ai zan rage zafi".

Ta raɓa shi ta shige ɗakin, ganin ba shi da niyyar shiga. Ya yi huci mai zafi ya shiga shi ma, har ya haye gadon, ya cire kayan jikinsa, ya duƙunƙune rigar dake ɗauke da balangun ya saka a ƙasan filo ya kwanta, a ransa yake rayawa, ga shi ya yi wa Mardiyya alƙawarin za su yi waya idan ya dawo, wannan basamudiyar ta zo ta kafa ta tsare.

Yana kwanciya Sahura ta ji ƙamshin balangu ya daki hancinta, abun ya ba ta mamaki, can anjima ta ɗan matsa kusa da shi, ta ji ƙamshin ya ƙaru a ta wajen filon da yake kwance, ta ɗan danna wayarta ta haska, ta ga rigar da ya cire a ƙasan filon, hakan ta tabbatar mata da lallai akwai magana a rigar tasa, amma ita ba wannan ba ne a gabanta, burinta ya yi bacci ta sakko ta fara bincikenta. To kamar yadda take jira ya yi bacci, shi ma haka yake jira ta yi nisa a baccin, ta yadda zai samu damar cin balangunsa, sai juyi suke yi kowa ya ƙi yin bacci.

Can dai sai kowa ya yi baccin ƙarya, har da jan munshari, ita a zatonta baccin gaske ya yi, haka shi ma ya za ta na gaske ta yi, shi ne ya fara tashi zaune, ya haska fuskarta ya gani, sannan ya ɗaga filo ya ɗakko rigar ya ciro balangunsa, har ya zauna a ƙasan gadon sai kuma ya tashi ya fita waje, a tsakar gida ya zauna ya fara cin abunsa yana mita ƙasa-ƙasa "Ban da masifa, kai da ɗakinka da kuɗinka ba za ka ci guminka ba? Mata kamar wasu mayu?"

Yana fita Sahura ta tashi zaune, ta haska wayarta wajen filonsa tana ganin babu wannan rigar ta gane naman ya fita ci, don haka ta sakko daga gadon da sauri, ta je ta saka sakata a hankali, ta dawo ta buɗe sif ɗinsa, ta fara rarraba ido, a hankali ta dinga bincika kayan ba ta ga komai na rashin gaskiya ba, ta zo ta buɗe tsohon akwatin, ta ga babbar riga tsohuwa a sama, tana yaye ta ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ganin leses da shaddoji sababbi a ledarsu, ta fara fito da su tana ƙirgawa, nan kuma ta ga wasu kayan bacci kamar ma na gwanjo don a leda suke a ƙulle, ta shiga jinjina kai.

Daidai lokacin kuma Saude ta fito fitsari, fitilar hannunta ce ta kusa kufcewa sakamakon haska mutum da ta yi zaune a tsakar gidan, "La haula wa la ƙuwwata illa billah" Ta furta ƙirjinta yana bugu, tun da dai ta ga agogo kafin ta fito, ta san zuwa sha biyu da rabi ba wanda zai fito tsakar gidan fira.

Shi ma Hamza zabura ya yi yana cewa"Subhanallah!" Ya ƙunshe ledar ya miƙe tsaye, sai kuma ya tura ƙofar ɗakin nasa da sauri, don kar Saude ta ga balangun, ita kuwa da mamaki ta ce"Hamza lafiya kuwa? Me kake yi a waje?"

Ya ce"To ina ruwanki? Ni da gidana za ki kafa mini dokar zaman waje ne?"

Ta ce"To ai wai da na ga dare ne?"

Ya ce"Sai me? Kin san fa ba na son saka ido cikin lamurana ko Saude?"

Daidai nan kuma ledar ta kufce masa, balangun ya tarwatse, Saude ta haska shi ta ce"Ikon Allah! Wai dama saboda za ka ci nama ne ka fito waje ka zauna sauraye suke ta gallarka?"

Cikin borin kunya ya ce"A'a ba nama ba, mahauta nake ci".

Ta shige baɗaki tana cewa"Allah Ya kyauta".

Ita kuwa Sahura tana jinsu daga ɗaki, da sauri ta zazzage wani danƙareren leshi daga ledarsa, ta ɗauki ƙunshin kayan gwanjon nan, ta kai can gefen gadon ta watsa su, ta lulluɓe su da hijjabinta, ta gyara akwatin yadda ta gan shi, Hamza ya fara ƙwanƙwansa kofar yana mamakin yadda aka yi ta tashi ta rufe ta, ita da ya bar ta tana bacci, Sahura ta tashi ta buɗe masa ƙofar, ta koma ta kwanta, shi kuwa duk jikinsa ya yi sanyi saboda bai so Saude ta kama shi ba, balangun ma sai ya fita daga ransa, shiyasa ma bai bi ta kan Sahura ba, ballantana ya tambaye ta dalilin tashi ta rufe kofar alhalin ta ga ya fita daga ɗakin.

Haka ya duƙunƙune rigar da sauran naman ya cusa a sif, ya kwanta. Ita kuwa Sahura ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta mamakin Hamza, wai har da gwanjo a lefen nashi, wato su na gida bai siya musu ba sai ta waje, a ranta ta ce'Ai kuwa sai dai ka gan shi a jikina'.

Da asuba tana jin kiran sallar farko ta kwashi kayan cikin hijjabi ta bar ɗakin nasa.


GIDAN SUNUSI

Sabila da yaranta suna zaune cikin yunwa, wajen ƙarfe goma maƙobciyarta Maman Nawal ta shigo gidan, ta zauna suka gaisa da Sabila tana cewa"Wash! Wai ni kuwa maman Amal anya akwai abin da ya fi sharar tsakar gidana wahala? Kin ji ƙuguna kamar zai karye?"

Sabila ta yi dariya ta ce"Ke dai akwai ki da raki, ni kuwa dayake na saba sharar gidan babana, na san da ni ce a gidanki sam ba zan ji wahala ba, kuma ke ma ya kamata a ce kin saba".

Maman Nawal ta ce"A'a ba a sabawa da wahala wallahi, almajirin nawa ne ya tafi ƙauyensu, duk na gaji na matsu ya dawo".

Sabila ta ce"Rashin sabo dai kawai, amma ni ban ga wani abun gajiya ba".

Maman ta kai dubanta ga Minal da take share hawaye, fuska kicin-kicin, ga Amal kwance ta yi luf kamar mage ta samu katifa, ta ce"Yaran nan ba su da lafiya ne? Me yasa ba su je makaranta ba?"

Sabila ta ce"Ba su da lafiya, amma sun sha magani". Saboda tana iya kokarinta wajen ganin maƙota ba su gane sirrin gidanta ba, duk da maman Nawal tana yawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login