Showing 27001 words to 30000 words out of 46005 words

Chapter 10 - SHIN SO DAYA NE BOOK COMPLETE BY HAFSAT ALMUSTAPHA.doc

14 Sep 2025

2028

ya kunno mana da tasa k'alar takun basajar wanda ya shallak'e tunanin duk wani meh tunani,friends dina sunsha fad'a min cewar kamar brother inlaw dina is having a crush on me!,amma kasan meh? Saurin k'wab'arsu nayi akan karsu sake min wannan zancen banzar,and do you know why I said so? Sabida aganina brother inlaw dina baze tab'a tunanin cin amanar dan'uwansa ba,kawai de k'yautatawace da kuma kulawa kake nuna min amatsayina na budurwan k'aninka,sae gashi tashi daya ka shayar dani madaran mamaki,sae da kasan ta yadda kayi ka aureni,ayau gani ga *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA NAKOWA'* wan *'DR.MUBARAK MUSTAPHA NAKOWA'* amatsayin mijin auran '*FADIMA SA'AD MAINASARA'*... gaya min,isn't dat a shameful thing to us? Sannan kuma mutane sun sami abin fada cewar ai 'wa' ya auri budurwar 'k'aninsa,kaga wannan shirin taka itace *'BASAJA TAKUN K'ARSHE'* don daga kai,wallahi insha Allahu babu wani d'a namiji da xan yarda ya sake tsara wata takun basajar akaina......never wallahi........ "



"Fadima please listen....... " ya fada awahalce.



Da sauri na daga masa hannu"Malam saurara min nan!.... lokacin zancen soki burutsunka ya riga da yayi expire,yanxu kuwa lokacin maganata ne,it's my turn to speak out and take actions,lokacin zartar da hukunci yayi......... "



"Bayan igiyoyin auren na rataye ah wuyana shine kike tunanin zartar da hukunci da kanki?taya zaki zartar da wannan hukuncin baby doll? ko kuwa atunaninki ni Mahmood xan tab'a furta kalmar '*SAKI'* ne agareki?toh kuwa idan hakan kike tunani,toh ina son ki sani,Ni Mahmood baxan tab'a sakin matata Fadima sa'ad ba,Mahmood ba ragon namiji bane ko kuma wani sok'on ba da har zeyi tunanin rushe ginin daya dad'e yana ginata ba,baxan tab'a gangancin sakinki ba don na dad'e ina jiran zuwan wannan ranar ta mallakarki amatsayin matar aurena,Fadima ina son kisa aranki cewar ni dake aurenmu mutu ka raba ne takalmin kaza,don haka baxan tab'a sakinki ba,ruwan daya tafasa ya dad'e be k'one ba...... "



Gabana ne naji ya yanke ya fadi da jin maganganunsa,amma kuma se na d'aure nace"Mahmood wallahi se ka sakeni adaran nan ba sae an kai gobe ba,don banzo da shirin fuskantar tashin hankalin dake shirin kunno kai acikin family dinka asanadin aurena ba,baxan tab'a yadda Mubarak ya min kallon 'maciya amana' ba balle har na lamunci tsaya jin yana jifana da wannan kalmar ba,never! wallahi I'll never permit dat..... "



Cikin d'aga murya nace"Mahmood ina meh umartarka daka gaggauta sauke igiyoyin aurena duka ukun dake rataye ah wuyanka don bazan tab'a so ayi mah tunanin gyara wannan auran nan gaba ba....... "



Cike da takaicinta Mahmood yace"Ban tab'a tunanin cewar ke din dak'ik'iya bace sae yau,atunanina ilimin arabi ya gama ratsa k'wak'walwarki,ashe abinda ban sani ba da sauranki,kin kuwa san girman laifin duk wata matar data buk'aci saki da bakinta daga wurin mijinta? Nasan kin fini sanin abinda Allah (SWT) ya tanadar mata,amma shine ke don toshewar basira da kuma tsananin b'acin ran da kike ciki yasa har ke kike nemar mah ayi miki sakin da manzon Allah (SAW) yayi mana hani da yinta,wato saki uku!!,,wa'iyazubillah!! wallahi Fadima ki gaggauta yin istigfari ga ubangiji,sannan kuma ki nemi tsari daga shed'an don duk shine ke neman sakaki ki k'auce hanya,Fadima ina son ki rungumi kaddararki da hannu bibbiyu,ina son ki sanya aranki dama can Allah ya rubuta cewar ni din mijinki ne,ke kuma matata,saki de kamar yadda na fada,kinji nace wallahi bazan tab'a sakinki ba,aurena dake mutu ka raba ne,zaman auranmu daram!,,ni dake kamar magnet da k'arfe haka zamu kasance,am fully ready to face any problem coming soon............ "



Wasu hawayen bakin ciki ne suka soma shatato min saman kunci,xuciyata ta sauya zuwa xuciyar kafirai marasa imani,idanuwana sun rikid'e sun koma na tsantsar bala'i.ko daya daga cikin karatun daya karanto min babu wanda yayi nasarar shiga cikin k'wak'walwata.



Cike da isa da gadara nace"Mahmood ga shawara idan har zaka k'arbeta.... Ka sakeni ta ruwan sanyi tun muna shaida juna,idan kuwa kaki,toh ina meh tabbatar maka da cewar lallai kuwa za'a ji kanmu don ta tashin hankali da kuma k'eta za'a rabu,now its left to you to choose one of conditions listed........."



Murmushin leb'en baki kawai Mahmood yayi,kana yace"All of the conditions listed sunyi tsauri da yawa matar Mahmood,don haka none of the conditions listed will be picked up...... "



Da sauri nace"Haka kace ko? "



"Ba wai haka nace ba,hakan de take.... " ya fada tare da kashe min one eyes.



Gani nayi yana nema ya kawo min taurin kai,ni kuwa xuciyata sae ingizani take,tana meh raya min wasu al'amura araina,ai kuwa da hanxari nayi kitchen ina waigensa,shi kuwa sae murmushi yaketa wulla min.



Ahankali nace"Dan iska yanzun nan kuwa zaka yi abinda nakeso.... "



Shi kuwa Mahmood he wonder wat Fadima is upto,atunaninsa wani abin take da buqata shiyasa taje kitchen din.Babu zato babu tsammani sae ganinta yayi ta fito daga kitchen rik'e da wata sharb'ebiyar wuk'a ahannunta.wata irin zabura yayi tare da mik'ewa da sauri.



Cike da tashin hankali yace"Fadima meye haka? Meh kenan kika rik'e ahannunki?"



Ni kuwa ganin tashin hankali da kuma zallar tsoron dake shimfid'e akan fuskarsa ya sakani bushewa da wata dariyar shekiyanci.



Axuciyata nace"Wow! Plan dina yayi aiki,nasan tabbas baxan sha wata bak'ar wahala ba kafin na sami takaddar saki nah... "



"Fadima nace meye wannan ahannunki?" Ya sake tambaya.



Mur! nasha,nace"Ai! wai tambayata mah kake?okay cokalin cin abinci ne....."



Na fadi hakan tare da tunkaran inda yake,jaa da baya ya soma yi yana fadin"A'ah Fadima wuk'ace fa nake gani ahannunki,meh zakiyi da ita? "



"Au! na aza koh idanuwan mijin nawa sun dena aiki ne,ashe tunanina was wrong,the two eyes are still working tunda har ya gano wuk'a ce ahannuna...."



Dad'a tamke fuska nayi kamar ba Fadima meh sanyin xuciya da imani ba,nace"zancen kuma abinda xanyi da ita,so nake nayi gunduwa gunduwa da namomin jikinka idan har kaki bani takaddar saki nah......"



Da tsawa yace"Ke Fadima! kinyi hauka ne? Kisan kai fa kike shirin aikatawa? Wai ni Fadima meya shiga cikin k'wak'walwarki ne?Dama ashe haka kike ban sani ba? Musa ah fuska sannan fir'auna azuci?"



Ni kaina nasan baxan iya aikata abinda nace ba,barazana ce kawai nake son na masa.



Ban tankashi ba,kawai na nufi inda yake tsaye,da sauri naji yace"Tsaya Fadima karki k'araso don naga abin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? naki da gaske ne,kina iya aikata abinda kika fada,xan baki takaddar sakinki donni lafiyar jikina ya fiye min komai..... "



Ajiyar xuciya na sake,kana nace"Da kuwa ka shafawa kanka lafiya.... "



Yace"Muje daki na rubuta miki don takadda da biro na ciki..... "



"Oya! shige gaba muje..... " na fad'a da k'arfi.Da hanxari yayi gaba yana meh daga hannayensa duka biyun asama kamar wani barawon da dan sanda yayi arresting.(hohoho! Fadima the seargent).



Na take masa baya ina meh nuna wuk'ar adaidai saitin bayansa,shi kuwa lokaci xuwa lokaci yake dan waigowa yana dan dubana.



Babu zato babu tsammani naji kawai ya juyo yana k'ok'arin warce wuk'ar ahannuna,kokuwa muka soma yi,dayake k'arfin d'a namiji da 'ya mace ba daya bane,sae kawai yayi nasarar k'arbeta ahannuna.Ni kuwa ganin hakan yasa na sake kwasa aguje nayi kitchen din.



Wata kwalbace da ban san kota mecece ba na gani saman wata cabinet,wawurarta nayi,na nufi waje,adaidai Kofar kitchen din muka jame.



Ba tare da wani b'ata lokaci ba na daga hannu na rotsa masa wannan kwalbar aka,ai kuwa ta sameshi agoshi.



Ji kake "Ahhhhhhhhh! Wayyo Allah,innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Fadima kin kasheni......."



Agigice na cillar da sauran fasasshen kwalbar daya saura ahannuna.



Fashewa da kuka nayi,nace"Wayyo! Allah na shiga uku na kashe mijina... " na fadi hakan ina meh k'ok'arin kai hannu na tab'a inda jini keta bulbulowa.



Ture hannunta gefe yayi,da hanxari ya shige kitchen din ya kunna famfo,ya wanke fuskarsa gabaki daya har inda jinin ke bulbulowa,kana ya koma falo duk ina biye dashi ina kuka sae cewa nake ya yafe min,amma k'ala bece min ba.Keys din motarsa ya kwasa da wayoyinsa,yayi waje,nabi bayansa.



Kafin na k'arasa ga k'ofar naga kawai ya rufota tare da kulleta da padlock.



Mahmood na fita waje,ya duba agogonsa,its to eleven.



Daga murya yayi yace"Mal.Bello yi sauri ka bud'e min gate...... "



Da hanxari ya nufi motarsa,sae daya k'ira wani abokinsa dake aiki ah Aminu kano teaching hospital,yaci sa'a kuwa yana kan aiki ne,babu b'ata lokaci ya tada motarsa,yayi reverse,yana jin sanda Fadima keta girgiza kofa kamar xata ballata.



Ah 360 yabar gidan,Mal.Bello ya rakashi da "Yallabai ashe bakace bazaka sake fita ba? "



Ina!! Mahmood ya riga ya masa nisa,maida Kallonsa yayi ga b'angaren su Fadimar,ahankali yace"Anya lafiya kuwa? Kai ban tsammani komai sumul yake ba don yadda Yallabai ya fice acikin mota atsiyace dole akwai ayar tambaya anan,Allah de ya kyauta.............. ??Qd



*HAFNAN*??c

*??
cSHIN SO DAYA NE???c*



*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*



*WATPADD:HAFNANCY??c*



*IG:Hafsy___mustee*



A?"1jn



*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*



??2\BABI NA BIYAR??2\



*page 12-15*



"Fadima I have to take us back,sabida yana da matuk'ar muhimmanci kiji labarin Zeey Maleek d'ita,jin labarin ne ze saka kisan yadda akai naji sha'awar son na aureki,amma kafin na cigaba da baki labarin pls let's eat first don yunwa nakeji sosae...." Ya fadi hakan tare da rik'e cikinsa kamar da gaske,so yake kawai ta d'an tab'a wani abin.



"Ni bana jin yunwa,kaci abinka kawai,kuma ka min sauri........ " na fada atakaice ina meh hura hanci.Da mamaki naga ya bini da kallo,kana yace"Saurin meh kike ne baby doll? Remember from now on,we hav the whole moment to spend together for the rest of our lives,Fadima ina son ki sani cewar aurena dake Insha Allah mutu ka raba ne...... "



Naso tanka masa amma kuma se naga idan na biye mishi zamu ta jan magana ne gwara kawai nayi shiru na bishi ahankali donna samu ya warware min zaren daya sak'a.



"Ki sakko muci idan ba haka ba nima baxan ci ba kuma bazan baki labarin komai ba,kinji nace wallahi... " yanayinsa ya nuna sam babu alamun wasa atattare dashi,hakan ya sa ba tare da na tsaya wani dogon tunani ba na sakko sabida na k'osa naji takun basajar daya k'ulla.Shi da kansa ya firfito mana da abubuwan dake shak'e cikin k'atuwar ledar daya shigo da ita.



"Baby doll wanne zakici aciki? Pizza ko garnished chicken???`? Or u will like to take all?? "



"Lallai guy din nan ya mugun raina min wayau ba kadan ba,wai ni yakeso ya yaudara da salon soyayyarsa ko meh?hadda wani *'Baby doll'*? ba damuwa duk kayi ka gama xan bika asannu don mu wanye lafiya."



Hura min idanuwa naji yayi wanda hakan ya maidoni daga duniyar tunanin dana lula xuwa duniyar da muke ciki.



"Matar Mahmood ya naga kinyi shiru? Ko so kike na baki abaki? Iyyeh fada min karki ji kunyata am ur husband.... " ya fadi hakan tare da kashe min one eyes.



Dan guntun tsaki naja,nace"Bannaso ai nima ina da hannun da xan iya ciyar da kaina,garnished chicken???` din kawai xan iya ci.... "



Murmushi naga yayi yace"An gama my all,bari na dauko plate" ya mik'e tsaye,naga ya nufi b'angaren dinning,ata gefen dining din naga ya bud'e wata kofa ya shige ciki,atake na gano nan ne kicin din gidan.Ji nayi kamar na arta aguje nabar gidan kafin ya fito,amma se kuma naga rashin dacewar hakan,sam yin hakan ba class dina bane,kuma ai ina son nasan ta yadda akai ya sami aurena,don haka be kamata na gudu ba,xan bari mu wanye ta salun-alum idan yaso hakan,idan kuma ta tashin hankali da kuma k'eta yakeso arabu,then Fadima Sa'ad is ever ready for that.



Murmushin yaudara na sak'ar masa sanda naga ya nufo inda nake da plate ahannunsa.Cike da kissa da kisissina na mik'e na k'arbi plate din hadda wani duk'awa wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bashi ba.



"Dear ya naga plate daya kawai ka dauko? " na fadi hakan ahankali tare da lank'wasa murya.



"Ah plate daya xamuci.... " ya fada yana kallonta cike da mamakin wannan sudden sauyawar tata,daga shiga kicin ya dawo har ta canza ta koma Fadimarta daya sani? Ko dai tunani tayi taga rashin dacewar abinda take masa da kuma maganganun da take ta kwakkwab'a masa? Ko ta haqura ta rungumi kaddararta ne?



Axuciyarsa yace"No Fadima am not getting you at all... I guess you are upto something freakish & very mean... "



Ni kuwa axuciyata nace"Dan iska mamakin canzawata yake,besan cewa so nake na lallab'ashi ya gayan komai sannan nasan nayi ba,hadda wani wai ah plate daya xamuci abinci,shege daga yau sae de kaci abinci ah kwano daya da uwarka ba dai da Fadima Sa'ad kuma ba.... "



Sosae na sake jiki mukaci mukayi Kat! damu,mafi yawanci shi da Kansa yaketa feeding dina,ni kuwa sau uku kawai na bashi abaki ina meh cike da takaicin kaina.



Bayan mun k'are cin abincin,naga ya kasa haqura yace"Baby doll wat happened? Wannan sudden change din nan taki am suprised fa?kodai u're upto something ne? "



Murmushi meh ciwo na sakar masa,kana nace"No ba komai wallahi,ni de kawai kaban labari.... "



Saukar da ajiyar xuciya yayi,kana ya soma bani labarin rayuwar soyayyarsu shida tsohuwar matarsa *Zaynab Maleek*,mace meh tsananin sonsa da tattalinsa,mace meh gudun b'acin ransa da son kowa nashi,wani abin nasu da idan ya fadi sae muyi dariya,wani kuma na abin atausaya musu ne yanda wai matar babanta ta sanyata agaba,ashe wai tun tana 'yar karamarta mahaifiyarta ta rasu.Ta taso ne ahannun matar babanta wanda sam ko kadan bata qaunarta,har tayi aure wani lokutan mah takan zo har gida idan baya nan ta lakadawa ita Zaynab din dukan tsiya ita da 'ya'yanta mata,yayun Zeey din.Dakyar da sudin goshi ya taka musu birki ya kuma sanya aka masu iyaka da gidansu.Gashi ita Zeey din tana da haqurin gaske,komai aka mata sae kaji tace"wallahi dear nah na yafe musu har cikin xuciyata. "



Hakan ya saka Zaynab ta sake samun gurbi acikin xuciyarsa,sae ji yake kamar duk duniya babu ta biyun Zeeynsa,baya jin ze iya rayuwa da wata 'ya mace face Zaynab dinsa ko bayan ranta.



"Sae gashi rana daya na k'aryawa Zeey dita alkawarin dana daukar mata,yau gani ga wata 'ya macen amatsayin *'Matata'*, *'Matar Mahmood din Zaynab Maleek'*... Fadima ranar dana soma ganinki alokacin da kuka kawo ta'aziyya kano,aranar se dana danyi jinyar xuciyata,don ganinki ya tuno min da Zaynab dita,everything about you was juz lyk hers,infact! hatta kamanninki da nata yanaso yayi iri daya.Ah yinin ranar na lura sosae na kamu da matsananciyar sonki,why? Because gani nake kamar Zeey dita ce ta dawo.



"Titsitseyar Hanan nayi,na sakata dole ta bayyana min alak'ar dake tsakaninki da Mubarak wanda ko kusa banso hakan ba,naso ace babu alak'ar soyayya atsakaninku,kuma wallahi banso kika bishi wani gun ba,Fadima sam be kamata ace amatsayinki ta 'ya mace musulma, kuma kamilalla kiyi trusting namijin da baki taba sanin halayyarsa,ki yadda dashi kai tsaye har ki bishi for only Allah knows inda zai kaiki ba,wannan abin ba k'aramin sosa xuciyata yayi ba,amma se na batsar nace toh wai ni miye nawa da damuwa akanki? Ai ke kika kai kanki,duk da cewar na yadda da kanina sam ba mazinaci bane,amma ban san meyasa na kasa sakewa da fitarku tare ku biyu kadai ba,ashe de sonki nake ban sani ba,koda naje gida kasa xama nayi,naji kamar na sanya k'iransa na rufeshi da fada akan ya maido dake gida,amma se naga zagewar zatayi yawa and he might get to suspect something."



Jan gwauron numfashi yayi kana yace "Na takaice miki labari,dawowa nayi na xauna jiran dawowarku awaje,ita Hanan duk ta tsure duk aganinta tashin hankali xan haifar sanin da tayi na cewar mahaifiyarmu bata qaunar wani acikinmu yayi tunanin qara matar aure,aganin ita Hanan din xan taya Mummy hukunta Mubarak ne,na nuna mata cewar karta damu ba wani tashin hankali xan haifar ba kawai Fadimar ta min kama da wata wacce na sani ne.Kamawa daga wulaqancin da mummy tayi wa 'yan'uwanki,da korosu waje da tayi duk akan idanuwana ne,koda naje ina bata haquri zageni tayi tass! ta ajje agefe wai har ni ina da bakin magana? Ai gwara Mubarak din tunda shi yayi tunanin qaro aure amma ni fa? dayar mah na gagara ajjewa ina nan kamar wanda aljana ta aure,sae kace kaina farau aka soma yiwa mutuwa. Maganarta daya fi sosa min rai har ya saka na dan zubda kwalla shine wai,da alamu haka xan k'arashe rayuwata babu magaji,wanda ze dunga daga hannu sama yana min addu'ar samun rahamar ubangiji,sae de nata daukar 'ya'yan abokaina ina sha'awarsu,hakan data fada shi ya k'ara min kaimi da kuma k'warin gwiwar gwada sa'ata awurinki,ban damu da cewar ke din budurwar kanina bace,burina kawai nasan ta yadda xan bullo miki har na samu shiga awajenki,because nima ina buqatar asake sona,I want to share dat love again with someone,Fadima I really want to see my own children,kuma ke kadai ce naga kamar Kinfi dacewa da rayuwata shiyasa nayi tunanin xuwa gareki,nabi bayanku don nasan gidanku,koda naga motarku ta lalace,sae na samu wuri nayi parking adan nesa daku don Kar nayi saurin tunkaranku ku d'ago wani abin.Sae dana dan ja lokaci kuma na tabbatarwa Kaina lallai bazaku dago ba sannan na tunkareku."



Anan Mahmood ya baiwa Fadima labarin komai na yadda akai yata fama da xuciyarsa da kuma kokarin son ya yakice soyayyarta acikin xuciyarsa,amma hakan ya faskara,akan dole yabi son xuciyarsa,ya kudura aransa cewar dolene ya baiwa xuciyar abinta takeso.



Yace"A.B.U Zaria ta dade tana aiko min da request akan suna matuk'ar buqatar nazo na dunga aiki dasu,don suna da labarina yadda nake da basira da kuma fasahar sarrafa na'ura meh k'wak'walwa,I hav turned down their requests on several occasion,ganinki ya saka ni da kaina na aika musu da sak'on amincewata da offer dinsu,wanda tsananin murnar hakan ya saka suka bani k'yautar wata madaidaiciyar gida don nuna godiyarsu agareni.Ni kuwa gani nayi rayuwata xata dawo sabuwa dal kamar an ciro daga kwali,xuciyata fes! raina yayi haske ganin nayi close dake,wani abin dadin dadawar kuma,wai kema A.B.U kike schooling, hakan yasa naci alwashin bazan tab'a wahala wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login