Showing 30001 words to 33000 words out of 46005 words

Chapter 11 - SHIN SO DAYA NE BOOK COMPLETE BY HAFSAT ALMUSTAPHA.doc

14 Sep 2025

2025

shigar da kaina gareki ba,xanyi kokari naga na koya miki yadda zaki soni,sannan daga baya na aureki kota halin k'ak'a. "



Ya bata labarin yadda sukai tayi da Mubeen,yadda Mubeen din keta nemarta awaya baya samunta da kuma yadda yayi masa karyar wai sabuwar wayace take jira,da kuma hana masa xuwa Zaria da yayi don dubata,da kuma wucewarsa India da dramar da kullum suke sha awaya.



Yace"Wallahi ko jiya mah se daya k'ira amma naki dagawa.... "



Afusace na mik'e nace"Agaskia Mahmood kaci amanar Mubarak ba kadan ba,Allah sarki bawan Allah inata tunanin kila dama can yaudarata yake baya qaunata shiyasa be damu yasan halin da nake ciki ba,ashe abinda ban sani ba,kai kana can kana shuka masa bishiyar k'arya har tayi nasarar tasiri da kuma girma acikin xuciyarsa,why? Because ya yadda dakai,yasan bazaka tab'a masa k'arya ba,Mahmood meyasa zaka ci amanar Mubarak? Why? Meh yayi maka arayuwa da har zakayi tunanin ramuwar gayya irin wannan? Kamar yadda kake ikrarin kana sona,toh wallahi Mubarak ya fika sona sau dubun dubanni,ka kuwa san irin tashin hankalin da kake kokarin haifarwa acikin zuri'arku? Ka tab'a tunanin cewar anya xuciyarka ta maka adalci wajen sona kuwa? Tukunna mah de gaya min wanene *'BABA MU'AZZAM'* agareka,sannan kuma ina family dinka suke da akayi wannan auran?"



Jikin Mahmood ne yayi sanyi qalau kamar kankara,ahankali ya bud'i baki ya cigaba da mata bayani"Baba Mu'azzam shima family dina ne ba hayarsa nayi ba kamar yadda kike tunani,k'anin mahaifina ne,shak'ikinsa kuwa,ma'ana ciki daya suka fito da mahaifina,matarsa daya itace Haj.Fa'iza wacce akafi sani da 'Mami',ya'yansu biyar kuma duk mata,Zaliha itace ta farko wacce take kusan sa'ar Maryam (Meema) qanwata,nasan kin ganeta don da aka kawoki mah tana gidan,tana auran wani dan sanda ne anan kanon,sae Zaineema meh bi mata,ita kuwa sa'ar Usman kaninmu ne,ita kuwa tana aurene ah katsina,ita bata zo bikin ba amma nasan yan'uwanta sun gaya mata,sae meh sunan Kaka rigima wacce ake k'ira da 'Afreen',ita kuwa sa'arki ce,sae Hafeezah sa'ar Suhaima,sannan auta Rafi'ah.Sanda kika fada min cewar ai mahaifinki shine chief justice ta yankin federal high court Zaria,sosae nayi murna don na sanshi da dadewa,Baba Mu'azzam ya tab'a zuwa dani wurinsa sau daya ah office dinsa,mahaifinki abokin baba ne sosae don ta sanadiyyarsa ya samu aikin alk'alanci,lokaci daya sukaje nemar aikin,se akace mutum daya kawai za'a dauka,anso daukar Baba ne amma se kuma yaga kamar abokinsa Sa'ad ya fishi buqatar aikin,se ya haqura ya bar masa,shi kuma ya tafi ya soma kasuwancinsa kadan da kadan har Allah ya sanya albarqa,ya tallafa masa ya habbak'a kasuwancin nasa ta man fetur.Sosae justice ke ganin mutunci da kuma darajar Baba don aganinsa ya taimaki rayuwarsa ba kadan ba,sati daya da soma aikina ah A.B.U naje office din mahaifinki,sosae yayi murnar ganina don ya shaidani,bayan yan gaishe-gaishe,na gabatar masa da kaina amatsayin meh sonki da aure,dan Jim yayi yana tunani."



(Alokacin tunani yake akan Haidar kada ya watsa musu k'asa ah ido don bazai iya hana dan Baba Mu'azzam auran 'yarsa ba,kawai zeyi tunani akan hakan)



"Ni kuwa gani nayi kamar bazan samu abinda nakeso ba,atake anan naji gwiwowina sunyi kasa,can ya karbi lambar wayata tare da ce min zeyi tunani akai. "



(Bayan kwana uku da ganawarsa da Mahmood,shine al'amarin su Fadima ya bullo,ya danyi murna da hakan,kenan ai Haidar bazai ce an watsa mishi kasa ah ido ba,yanxu yana da damar baiwa dan Alh. Mu'azzam auren Fadimar don kwarai ya yaba da hankalin Mahmood).



"Bayan kwana biyu sae ga k'iran Baba Mu'azzam wai yana son ganina,koda naje sosae ya nuna min murnarsa na samo 'yar gidan mutunci da tarbiyya amatsayin wacce nakeson na aura,wai justice na musamman ya kirashi ya labarta masa komai tare da bada go ahead din aturo,toh anan ne na rokeshi kan don Allah kada asanar da mahaifiyata don bata qaunar yarinyar,sannan kuma kada ayi wata gayyata don kada maganar ta bazu har ya isa kunnanta,sosae yayi mamaki da zancena har yace shi baze goya min baya nayin auran nan ba har se naje na nemo izinin mahaifiyata da kaina,rok'ansa nake tayi harda kuka akan ya taimaka ya shige min gaba na samu na aureki Insha Allah bayan auran sae asanar da mahaifiyar tawa,dakyar da sudin goshi ya amince ya shige min gaba don shi kansa yana bala'in son wannan hadin har ransa,toh kinji-kinji yadda akai na sami auranki,sannan ko daya acikin yan'uwana babu wanda yasan da wannan auran hatta shi Mubarak din........ "



Kallonsa nake cike da tsanarsa da kuma k'yamar hanyar daya bi ya aurena ba tare da samun albarqan mahaifiya akan wannan auran ba,hawaye sae bulbulowa suke saman kuncina babu gaggautawa,kuma ko kadan ban damu nasa hannu na sharce su ba...............??Qd



A/N

Ga alqawarinku nan na cika,Insha Allah zaku dunga ganin update kullum as frm now on!!!



*HAFNAN*??c

*??
cSHIN SO DAYA NE???c*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION???g*

*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*

'''THE PEN OF LOVE ???i HEART TORCHING B??? TEARS OF SORROWS ???i CURDLES ???i GIGGLES ???i AND MARRIAGE THINK ???b'''

*JUST GIVE US FOLLOW.....*A???



*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*



*WATPADD:HAFNANCY??c*



*IG:Hafsy___mustee*



A?"1jn



*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*



??2\BABI NA BAKWAI??2\



_*please kindly show me some love by voting & commenting to let me know dat u guys are really enjoying the novel*_



*page 18-20*



_"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj alal hazna iza shi'ita sahla...... "_addu'ar da nake ta nanatawa kenan babu gaggautawa sabida wani irin radadi da naji xuciyata ke min.Ina addu'ar ina hadawa da dukan kofa,alokaci daya kuma ina meh rera kuka kamar raina ze fita.Xuciyata cike take da nadamar abinda ta aikata.



"Mahmood don Allah karka tuka mota da kanka acikin irin wannan halin daka fita,don Allah ka bari ni da kaina nazo na kaika asibiti,pls dear nah am really sorry forgive me...... "



Na sake rushewa da wani sabon kuka ina meh cike da jin haushin kaina na abinda na aikata.Ina jin sanda ya tada motarsa ya fice atsiyace daga gidan.



Shi kuwa Mal.Bello k'asa kunnuwa yayi yana sauraro don yaji kamar bugun k'ofar cikin gidan ake da k'arfin gaske kamar za'a ballata.Da hanxari yayi ciki yana fadin"Oh! ni Bello dan Abu wai meke faruwa ne? "



Koda Mal.Bello ya iso sae gani yayi an garkame k'ofar da k'aton kwado,windunan dama arurrufe suke ta ciki,kuma labulayen asauke suke,don haka duk wani kukan kuran da Fadima take ba'a jin komai.



Mal.Bello dai ya tabbatarwa kansa da lallai babu lafiya yau agidan,daga kawo sabuwar amarya kuma sae tashin hankali tun ba'a kwan ba?ina kuma uban gidan nashi zaya je acikin daren nan da har ya rufe wannan baiwar Allahn aciki sannan yayi ficewarsa cikin mota atsiyace kamar ze tashi sama? Toh kodai wani laifin ne ta masa da har ya kasa hak'uri har gari ya waye shine ya tafi kai k'ararta gidan iyayenta?



k'ara k'arfin girgiza k'ofar da tayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunane-tunanen daya lula ciki.



Duk da cewar yasan ba wai jinsa zatayi ba,amma still ya daure yace"Hajiyata hak'uri fa zakiyi ya dawo ya bud'eki da kansa,addu'ata agareku shine Allah yayi muku tsari da shed'an,ya kauda fitina atsakaninku,sannan kuma ya baku zaman lafiya.... "



Ya juya ya koma bakin aikinsa yana d'an raye-rayen wakokinmu na gargajiya yana meh cike da al'ajabin wannan al'amarin.



Fadima meh kika aikata?kin kuwa san idan wani abin ya sameshi you will definitely be held responsible?meyasa ke bazaki rungumi kaddararki ba kamar yadda kowa keta baki shawarwari akan hakan?shi kansa idan kin lura dashi cike yake da nadamar hanyar daya bi ya sami auranki ba tare da saninki ba,amma duk da hakan ya yadda da kaddararsa,maganarsa gaskiyace dayace *'MATAR MUTUM KABARINSA'*,kenan wani baya tab'a auran matar wani,haka mah wata bata tab'a auran mijin wata se dai idan har Allah ya kaddara.



Toh ita wacece da har bazata rungumi kaddararta ba?wace 'ya macece mah da har zata ga *'MAHMOOD NAKOWA'* bata ji sha'awar son ya kasance mijinta ba sabida haduwarsa da kuma iya tattalin mace?komansa ah ilimance yake yinsa,ji bi yadda yake ta ankarar da ita idan ta nemi k'auce hanya,kenan bayan ilimin boko,na arabi mah ya gama ratsashi?



Wani irin zazzafar soyayyarsa ce taji ya soma kai mata cafka acikin xuciyarta,da sauri ta kai hannu ta danne daidai saitin xuciyarta,ahankali tace"Mahmood wallahi na haqura ka dawo wallahi xan gaya maka cewar na haqura xan xauna dakai,zan fada maka cewar na soma jin sonka araina,kuma xan gaya maka cewar am also fully ready to face any problem coming soon frm both Mubarak & the rest of ur family members....... "



Wani kuka ne naji ya kufce min,ina yi ina cigaba da sambatuna,kaina naji yayi min wani irin girma,ga wani ciwon da yake min alamun kukan da nake ne ya haifar min da hakan.Sassauta kukan nayi don kada na janyowa kaina wani sabon ciwon don ban gama warkewa ba.Idan naji wani motsi awaje saurin mik'ewa nake na nufi Kofa wai azatona ko Mahmood ne ya dawo.



Ji nayi kamar na sanya k'iran Umma na fada mata halin da nake ciki amma kuma se naga dare ya lula,ayanxu haka duk inda take tana tare da Abba,kuma bazanso yasan halin da nake ciki ba,yanke shawarar k'iran Ash nayi wacce ko dan flashing bata min ba tunda suka koma. (Dayake aranar da za'a kaita Abbanta ya maida mata da wayarta tare da zuba mata sabbin layuka biyu aciki).



Bugun farko akace min switched off,ba tare da b'ata lokaci ba na latso dayar layinta wanda acikin wata k'aramar wayarta ta saka wannan layin,shima switched off aka ce min.Ji nayi kamar na aza hannuwana duka biyun aka na kurma uban ihu,can baya ada,rayuwata nake cike da jindadi da walwala,sam ban san wata rayuwar kunci da damuwa ba,amma shigowar Dr.Mubarak Nakowa da kuma Engr.Mahmood Nakowa ya kawo min canjin rayuwa,suka sauya min rayuwa xuwa zallar damuwa da kuma kuncin rayuwa.



***



Ita kuwa Ash tasan tabbas Fadima ta riga tasan Mahmood shine mijinta tun kafin mah su baro kanon,kawai tasan taki tada wata rigima ne acikin jama'a,tafi son sae sun keb'e,toh tasan muddin idan suka rage su biyu dole Fadimar zata nemeta awaya,dalilin daya sanya ta kashe wayoyinta gabaki daya kenan tunda suka dira Zaria.



Zuciyarta cike yake da damuwa da kuma tsananin son tasan halin da Fatin tata ke ciki.



Ahankali ta furta"Yah Allah ka sanyaya xuciyar Fateenah aduk halin da xata tsinci kanta,kasa ta haqura ta rungumi *'MIJIN KADDARARTA'*,ya Allah na rokeka,ka wanzar da zaman lafiya tsakanin Fadima,mijinta da kuma danginsa....... "



Haka de ta cigaba da kwararo addu'o'i wa Fadimar tata,daga bisani ta shafa,dama nafila raka'a biyu tayi,sannan ta zauna tana zubawa Fadima addu'ar samun zaman lafiya da mijinta da kuma danginsa.Can ta mike tana duban agogon dake manne asaman bango,taga 10:35pm,zuciyarta ce ta soma ingizata akan ta latso Fadima,amma sae ta danne taki kunna wayar,tabi lafiyar gado ta kwanta,ba'a dau wani tsawon lokaci ba,wani nannauyar bacci yayi awon gaba da ita.



_Ashwairiyyar Bash asubahi ta gari_



***

*A??MINU KANO TEACHING HOSPITALA???*



*11:10pm*



"Subhanallah!!... wai ni babban mutum meya ji maka wannan raunin ne haka? Wallahi karka so kaga yadda ciwon yayi rami sosae.... " Dr.Jabir ne yayi wannan maganar sanda yake wanke wa Mahmood rauninsa da spirit.



"Kaga Jabir,idan har zaka wanke min abu toka maida hankali ka wanke bana son neman jin ba'asi,nace maka tsautsayi ce kawai ko kunnuwanka sun toshe ne? " yayi masa wannan tambayar cikin hargowa.



Kwantar da murya Dr.Jabir yayi yace"Allah ya huci xuciyarka abokina, ni damuwa nayi da wannan situation din naka amma tunda baka son tambaya,kayi haquri bazan sake ba.. "



Sae duk Mahmood yaji ba dadi,amma kuma kala bece masa ba har ya gama wankin,ya lik'a masa k'aton cotton wool awajen,sannan ya manna plaster asama don ya agaza ya rik'e wool din.



Yace"Allah sarki da'ace Dr.Mubarak nanan da shine ze k'arbi wannan aikin don nasan baze tab'a bari wani yayi in bashi ba.... "



Gaban Mahmood ne ya bada ras!! jin an ambaci sunan 'Mubarak'.



Axuciyarsa yace"Kode ze mah k'ara lalata abin? Kila mah ciwon ze dada caccakawa da kwalbar daga bisani ya aika dani barzau in har akan Fadima ne...... "



Azahiri kuma ignoring dinsa yayi,yace"Malam kana da damuwa wallahi ka cika hayaniya,pls nawa ne kudin aikinka? "



Dr.Jabir ya bushe da wani irin dariya yace"seriously yanzu sae na karbi kudi daga hannun babban mutum kamarka?haba idan nayi hakan ai na cika babban butulu mara tunani,kai dai jeka kawai fatana Allah ya baka lfy ya kuma kiyaye tsautsayin gaba.... "



*'BABBAN MUTUM'* sunan da Dr.Jabir ke kiransa dashi kenan,wai don Mahmood din akwai kirki sosae,tausayi,mutumci,iya mu'amala da mutane,da sauransu,shiyasa ya cancanci da ah kirashi da *'BABBAN MUTUM'*, sae de ance dan'adam tara yake be cika goma ba,matsalar Mahmood daya,wato miskilin k'arshe ne na gidan gaba kuwa,sam baya wani cika son hayaniya,idan kaga ya zage yana hira,toh kuwa tabbas da Zeeynsa ce,gashi yanxu itama Fadima tana kokarin samin wannan matsayin na Zeey.gashi da shegen zurfin ciki,sam bashi da abokin shawara,kai tsaye yake aikata duk abinda ransa yaso,shiyasa acikin duka friends nashi mah babu wanda yasan ta yadda akai ya auri Fadima,su de kawai zancen auren ne suka ji daga bakinsa.



Murmushin jindadin xancen Dr.Jabir yayi,kana yace"Shikenan nagode Jabir,bari naje dare na k'ara lulawa,sae da safe.... "



Ya kwashi keys da kuma wayoyinsa daya xuba saman wani table,adaidai lokacin kuma Dr.Jabir ya mik'o masa wata 'yar farar leda.



Cike da rashin fahimta yace"And wat is in? "



"Maganin pain reliever ce ke aciki.... "



B'ata fuska yayi sosae yace"Amma kasan de tun ina karamina na tsani shan tablets ko? Shine don iskanci zaka wani xuba min aleda? Gaskia ka barshi bazan sha ba,tunda ka wanke raunin its okay kawai..... "



Babu yadda Dr.Jabir beyi da Mahmood ba,juyin duniya yaki karba don shi arayuwarsa ya tsani ace yasha magani,gara-gara na gargajiya yana iya sha,amma na bature sam baya sonta,haka mah idan baya da lafiya ya gwammace ayi masa allura da ace masa yasha magani.



Sallama yayi wa Dr.Jabir ya fice,shi kuma ya rakashi da"Ace wa amarya muna nan xuwa mu kwashi girki.... "



Ai! tuni ya b'ace masa amma ya tabbata yaji abinda ya fada.



Murmusawa yayi yace"Kai Mahmood wallahi wani irin bahagon mutum ne meh dan wuyar sha'ani,idan baka xauna ka fahimci rayuwarsa ba,kana iya zaton ko sam baya ganin darajar dan'adam,amma abin ba haka yake ba,he's juz too simple but difficult to understand..... "



A?"1jnA?"1jn



Wata k'awar mominsu Mahmood wacce take zaune unguwa d'aya dasu Baba Mu'azzam ce ta k'ira ita Momin awaya take kala mata xancen auren Mahmood wanda shi Baba Mu'azzamun ne ya shige masa gaba.



Wata irin zabura ce Momi tayi kamar wacce aka manna mata shocking tare da dafe k'irji da k'arfi,tace"Dakata Rabi..... wannan wacce, irin xancen banza ce kike min haka?taya za'ai Mahmooda nah yayi aure ba tare da sanina ba?taya mah za'ai Mu'azzam ya shige masa gaba ba tare da nemar izinina ba?"



Haj.Rabi tace"Haba Binta meh zan tsinta acikin k'arya face zubda girma,daraja da kuma mutunci?kin tuna da wannan kawar tawa Haj.Nera?"



"Eh eh na ganeta...... " momi ta fada tana meh daga kai da sauri-sauri kamar Haj.Rabin na gabanta ne.



"Toh ai k'awar haj. Fa'iza matar Mu'azzamun ce,aminai ne sosae,kuma komai na haj.Fa'iza ita Haj.Nera ta sani,toh ita Neran ce tazo har gidana take fada min donni ban mah sani ba,wai daga wurin walimar auran take wanda akai acikin gidan Alh.Mu'azzam,toh anan take kala min gashi-gashi,wlh da farko na k'aryata xancen akan cewa babu ta yadda za'ai ah b'oye miki xancen auran,rantse-rantsen da take tayi ne ya sanya na yadda da ita don Haj.Nera idan har kaga ta kuke da rantse-rantse toh kuwa xancen gaskiyace take gaya maka,shine nace bara na k'iraki na d'an fesa miki zancen,amma don Allah karkice ah bakina kika ji............. "



Da hanxari Momi ta tari numfashinta"Dalla can rufemin baki anan,munafukai kawai masu bacci da ido daya,ana ruwan sama suna k'irgawa,'yan adawa da kuma hana ruwa gudu,wato yadda kuke ganin d'ana ke samun cigaba arayuwarsa shine kuke bakin ciki,kuke masa hadassa da k'yashi,soyayyar dake tsakanina da dana shine kuke bakin ciki,kuke kokarin so ku shiga tsakaninmu,toh kuwa da sakel,Haj.Rabi kin shayar dani madaran mamaki,da har kika shiga sahun masu mini hassada..... "



Cike da mamaki haj.Rabi tace"Haba Binta wannan wacce irin maganace kike haka?taya zan shiga tsakaninki da danki?taya zan masa hassada kan cigaban da yake ta samu arayuwarsa? Nifa na gaya miki babu abinda zan tsinta acikin k'arya face zubda girma da daraja,idan har baki yadda ba toh kiyi bincike,Haj.Fa'iza tace zasuyi kusan sati uku agidansa nanan kanon kafin su koma Zaria inda yake aiki,ita kuma take karatunta,don haka kije kiyi bincike da kanki,amma don Allah idan har kika ga zancena ya tabbata gaskia,na hadaki da Allah karkice ah bakina kika ji...... "



Bata jira taji ta cewarta ba tayi saurin datse call din cike da jin haushin zazzafar kalaman da Haj.Binta ta jefeta dasu.



Haj.Rabi kenan akwai shegen gulmace-gulmace nakin karawa kuwa,sae da Haj.Nera ta rok'eta akan tayi shiru da bakinta,har ta dau mata alqawarin cewar babu wanda ze ji zancen,har da ce mata ah inda ta gaya mata toh anan wurin zata watsar da batun.Taso din tabar wa cikinta zancen,amma dayake meh hali baya fasa halinsa,zancen har tsingulinta yake tayi shiyasa ta yanke shawarar fesawa Haj.Binta.



Haj.Binta kuwa jiki ah sab'ule ta koma da baya ta zauna agefen gado,alokaci d'aya ta rasa abinda ke mata dadi acikin duniyarta.Taya mah za'ai Mahmood yaje kai tsaye yayi auransa ba tare da saninta ba? Taya kuma za'ai Baba Mu'azzam ya shige masa gaba ba tare da an nemi izini daga gareta amatsayin mahaifiyarsa meh kuma iko akansa ba? Idan kuwa zancen Haj.Rabi ya kasance gaskia,tabbas zataso jin dalilin b'oye mata zancen auran kafin ta dauki duk wani mataki daga baya.Taso latso Mahmood din taji daga bakinsa amma kuma tafi son taje masa abazata ta gano gaskiyar lamari da ganta.



Da rawar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login