Showing 33001 words to 36000 words out of 46005 words

Chapter 12 - SHIN SO DAYA NE BOOK COMPLETE BY HAFSAT ALMUSTAPHA.doc

14 Sep 2025

2030

hannu ta lalub'o wayarta ta latso babbar d'iyarta Maryam (Meema).Ta kora mata zancen nasu da Haj.Rabi.



Dama duk acikin 'ya'yanta Meema tafisu sanyi da kuma kauda kai kan abubuwan da basu taka k'ara sun k'arya ba.



Cikin sanyinta tace"Hajiyata nasan idan mah hakan ta kasance gaskia,toh tabbas Yah Mahmo bazai tab'a rasa dalilin b'oye miki ba,don Allah hajiyata ki masa uzuri ki kuma fahimci dalilinsa if dat happened to be true..... "



"Ke dallah rufe min baki marasa tunani kawai,ai duk daga ke har shi din halinku daya,matacciyar xuciya gareku sam bakwa da kawa zucina kamar yadda nake dashi akanku,har ke kin isa kice kada na dauki mataki idan har hakan ta kasance gaskiya? Toh! sannu Haj.Hafsatu uwata.... "



"Haba! Hajiyata ki baiwa zancen nawa k'yakk'yawar fahimta..... "



Da sauri tace"Saurara min nan kafin inci ubanki,gobe k'arfe bakwai ta muku anan gidan sannan mu dunguma xuwa gidan nasa muje mu ganowa idanuwan namu,kuma kada wata ta sake acikinku ta k'irashi ko baba Mu'azzam din har se munje mun ganowa idanuwanmu,kina jina ko? "



"Ehh! naji bayananki duka.... "



Bata sake wata magana ba ta katse call din,kai tsaye ta latso autarta Khairat ta kora mata zancen itama.



Dama Khairat sam bata haquri kamar zawo take,duk acikinsu tafisu d'aukar Zafi da abu sosae.



Cewa tayi"Kan babban burauba,Momi shine baki soma ci mana ubanta awaya ba kafin ku had'e?Fisabilillahi Momi taya za'ai Yah Mahmo yayi aure ba tare da saninmu ba har Babansu Zali ya shige masa gaba duk bamu sani ba? Kawai so ake ashiga tsakaninmu dashi,karki damu gobe kafin bakwai mah na iso gidan sae muje mu binciko kamar yadda tace,amma idan har zancenta ya kasance k'arya ne toh wlh Momi har gida zamuje muci mata mutunci....."



Cike da farin cikin zancen 'yar tata tace"Nagode 'yata nasan ke da Labeebah ne kawai zaku iya goyar min baya..... "



Haka ta k'ira Labeebah,itama din kamar Khairat din tayi,ta lailayowa wani uban ashar ta gundumawa Haj.Rabi,tare da tabbatarwa Momin da cewar itama din kafin bakwai tana family house.



Sae kai komo kawai momi ke tayi adakin baccinta,kallon agogo tayi taga 10:45pm,ji tayi kamar ta sanya hannu ta tura sandar agogon xuwa karfe bakwai na safe............. ??Qd



A/N



Ghen!Ghen!!Ghen!!!.... Nakowa's family fire on the mountain in a bit??_e??_e??_e



Can't wait.



*wait! Karku ce min har kun manta da batunsu mal.Gaddafi? Jinns din Rukky Lema?



*Ina labarin daren Farkon *Suhaileedar?*



*Ina labarin Mubeen mijin Hauwa'u Jiddoh?



step-by-step zamu bisu,ku dai ku cigaba da kasancewa dani.



*IT'S*



*YOUR*

B??0so

*LADY*



*HAFNAN??c*



,

*??
cSHIN SO DAYA NE???c*



*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*



*WATTPAD???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?:HAFNANCY??c*



*IG:Hafsy___mustee*



??\??\



*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*



??2\BABI NA HUDU??2\



*Page 9-12*



Har Baba ya kare jawabinsa da nasiharsa agaremu kan zaman aure da haquri da juna,ban tsinci komai ba don gaba daya hankalina ya tafi ne ga tsananin mamakin yadda akai Engr. Mahmood ya aureni,da kuma sunan k'aryar da yayi amfani da ita wajen aurena wato *'MAHMOOD NAKOWA'*.



Taya mah xan soma tunanin xaman aure da wan saurayina? Taya kuma xan soma tunanin had'a idanuwa da Mubarak axuwan k'anin mijina?shi kuma ya dunga min kallon matar wansa?Sannan wani irin tashin hankali ne xa'ayi idan har Mubarak yasan cewar wansa ya aureni? Nasan tabbas zeyi tunanin cin amanarsa nayi bayan ko kadan bani da masaniya akan faruwar hakan.Wallahi wallahi da'ace nasan cewar Engr. ne wanda mahaifina keta burin aura min da wallahi baxan tab'a bari ayi wannan auran ba,na gwammace koma meh ze faru ya faru amma baxan taba cin amanar Mubarak ba.



Se de kuma hausawa sunce *'RASHIN SANI YAFI DARE DUHU'*.... Aikin gama ya riga da ya gama,baxan iya maida hannun agogo baya ba,amma nasan ta yadda xanyi na raba auran nan bayan na gama jin dalilinsa na aurena.........



Allah-Allah kawai nake wannan munafikin tsohon kilakin ya gama xancen soki burutsunshi sannan mu saka kafa mubar gidan don na samu na aiwatar da kudirin dake cina arai.



"Fadima tunanin meh kike?tashi ku je dare nayi Allah yayi muku albarqa.... "



Maganar Baba ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana Lula.Da hanxari na mik'e donna k'osa mu bar gidan.Su Mami ne suka mana rak'iya.Hafeezah ce rungumeni dani har muka isa waje inda yayi parking motarsa.



"Fadima Allah ya tsare,sae munzo ganin dakin amarya.... " Mami ce ta fadi hakan sanda na daidaita xamana ah kujerar meh xaman banza.Hakan ya bani tabbacin Lallai Zariar zamu tafi da daddaran nan.



(Ni kuwa nace sorry Fadima xakuyi 3weeks agidanki na nan Kanon dake 'court road').



Axuciyata nace"kafin kuzo ganin gida Fadima ta ware don baxan tab'a iya xaman aure da wan saurayina ba..... "



Har muka bar unguwar muka haye saman titi babu maganar data shiga tsakanina dashi.Xuciyata se tafarfasa take tare da min wani mugun zogi.



Shi kuwa Engr. Sam ya kasa sakewa da wannan shirun da Fadimar ta masa,yasan tabbas shirun nata bata banxa bace,dole akwai abinda take shiryawa aranta.Sae daya tsaya kan hanya ya siya musu gasasshiyar kaza,pizza da kuma youghourt masu sanyi na roba.



Sun kusa da 'court road' yaga shi de ya kasa haquri da wannan shirun nata,yana son ko 'yar zagi ce ta masa ko ze dan sami sassaucin abinda ke damunsa aransa.



Ahankali yace"Fadima pls speak for Allah's sake,kiyi magana don tabbas na b'ata miki,ki zageni,ki mareni idan hakan ze saka ki huce kan abinda aka miki..... Zahra'u cry out loud idan har hakan ze saka ki samu sassauci na abinda kike ji agame da cin amanar da nayi muku....... "



Ni kuwa kamar dama jira nake abani umarni,kawai sae ji nayi na rushe da wani irin kuka meh tsuma xuciya.



Cike da rawar murya yace"Fadima weep weep,ki kara da dukana wallahi I won't stop you idan har hakan ze saka ki yafe min abinda nayi miki............"



K'ara volume din kukan nayi,amma K'ala bance masa ba.Shi kuwa har cikin ransa yake jin wannan kukan nata,ji yake kamar ana caccaka masa allura adaidai saitin xuciyarsa na wannan kukan da takeyi,sae ayanxu yake jin haushin kansa na kuntata mata da yayi.



Beyi yunk'urin hanata kukan ba har suka iso gidan.



Mamaki ne ya kusan kasheni ganin ya shigo damu wata unguwa instead of Zaria da nake ta saka ran can muka nufa.Ban gama shanye mamakina ba kawai naga yana xuba uban horn awani tangamemen gida.Ba'a dau wani tsawon lokaci ba naga an wangame mana gate din gidan,da hanzari naga ya danna hancin motar ciki.



Tsaida kukana nayi ina dubarsa cike da mamaki,ahankali nace"Ina ne nan kuma ka kawo ni? Ina aza ko Zaria muka nufa ah daran nan? "



"Nan din mah gidanki ne,kuma aciki zaki xauna harna tsawon sati uku kafin mu koma can Zariar...... Kuma kada ki samu wata damuwa akan kayar sawarki don komai da zaki buqata yana nan gidan already....."



Ad'an tsiwace nace"What?? Ka dauka cewar xanyi xaman aurene dakai? toh idan mah hakan kake tunani toh tun wuri ka canza tunaninka,idan kuwa mafarkin hakan kake toh tun wuri mah ka farka don Fadima Sa'ad bazata tab'a xaman cin amana ba da wan saurayinta,bazan tab'a goya maka baya muyi kazamar rayuwar nan ba,abin tirr! da kuma Allah ya wadai...!!!....... "



Kuka yaci k'arfina.Ji kake kiiiiiiii!!! yaci wani wawan birki awurin parking lot.



Idanuwansa sun kada sunyi jajur dasu kamar jan gauta,maganganun Fadima sun sosa masa rai ba kadan ba.



Axuciye ya nunata da 'yar yatsa"Karki sake bakinki ya kuma gangancin kazanta aurena dake,zan iya juren komai da xaki min amma bazan juri tsaya kallonki kina kazanta aure sunnar ma'aiki ba...idan ke baki yadda da kaddara ba,toh ni as a good Muslim na yadda da ita,shi de aure nufi ne na ubangiji,matar wani bata tab'a auran mijin wata,haka zalika mijin wata baya tab'a auren matar wani..... Kenan 'matar mutum kabarinsa',dama can Allah ya riga ya kaddara cewar dole sae kinyi soyayya da 'kani' kafin daga baya ki auri 'Wansa'......."



Axuciye nima nace"Amma hanyar daka bi ka samu aurena sam bata dace ba,wannan sam ban yadda wai kaddara bace,kawai son xuciyace aka bi...... "



Baki bud'e yake kallona,kana yace"Subhanallah! Fadima kada b'acin rai ya saka kiyi babban sab'o! kada ki bari ki tauna maganganun da zaki saka Allah SWT yayi fushi dake... "



Sabon kuka na fashe dashi nace"Mahmood idan hakan ta faru waya jawo?........ "



Da hanzari naga ya katseni ta hanyar sanyar 'yar yatsarsa akan lips dinsa"Shhhh! My all pls ki addana duka kalamanki,idan muka shiga ciki kina da damar amayo min da duk abinda ke ranki,amma for now pls juz pretend as if everything is alryt,bana son baba Maigadi yayi zargin wani abin...... "



K'ok'arin magana nake sae ji kawai nayi ya sanya hannunsa ya rufe min baki,cikin wata sassanyar murya wanda aganina ta yaudara ce yace"pls *My all* juz do diz for ur dear husband...... "



Sanya hannu nayi na saukar da hannun nasa da k'arfi tare da furta"Karka sake ka kuma tab'a min jiki....... "



Murnushi naga yayi kafin yace"U are my wife,halal dita,infact! U are all dat I hav got,kinga kuwa dole ne nayi duk yadda naso dake...... "



Ji nayi kamar na kwasheshi da mari ko zan samu dan sassaucin abinda nakeji axuciyata agame dashi.Alokaci d'aya muka fito daga motar,na hangi Maigadi ta b'angaren Mahmood din yana masa barka da zuwa.



Ji nayi shi Mahmood din yace"Mal.Bello gaka ga *'MATAR MAHMOOD*',, Fadima Sa'ad Mainasara....... "



Washe baki Mal.Bello yayi yace"Ikon! Allah ashe de uban gidana ne ya auri baiwar Allahn nan,ai naji sanarwar auransu ita da k'anwarta ah radio,amma se de ba'a fadi sunayen mazajen ba shiyasa ban san cewa uban gidan nawa ne ze aureta ba,amarya ina miki maraba da xuwa Allah ya sanya albarqa awannan auran naku,ina meh tabbatar miki da cewar insha Allahu zakiji dadin xama da boss dina idan har kika bishi ahankali...... "



Duk da uban duhu daya k'arade wurin amma hakan be hanani wurga masa uban harara da murgud'e murgud'en baki ba.Wai mah xanji dadin xama dashi idan na bishi ahankali,an gaya maka ni xaman aure nazo yi?toka sani ayau ba gobe ba Zaria zata ganni. (Duk acikin xuciya ta fadi wannan maganar).



Da alamu akwai shi da xuba,don sake cewa yayi"Amma yallabai aure babu gayyata?ko de ban kai matsayin da za'a gayyaceni xuwa bikin babban mutum bane? "



Ji nayi kamar nace"Ya kuwa ze gayyaceka?bayan shi kadai da iyayen daya hayo ne kawai suka san da munafikin kudirinsu? "



Shi kuwa uban gayyar adaidai lokacin ya karashe fito da abubuwan daya tsaya kan hanya ya siya tare da rufe k'ofar motar.Ni duk azatona baze tankashi ba,don daga ni har Mal.Bello din mun fidda rai.



"Yi haquri yallabai na cikaka da surutu sae da safe... " haka naji Mal.Bello ya fada cike da sanyin murya wanda har ya saka naji dan tausayinsa,har ya juya ze tafi,sae asannan ne muka ji yace"Mal.Bello kaima kayi haquri hayaniyarka ce tayi yawa,auren ne yaxo ba wani shiri shiyasa banyi wata gayyata ba.... "



"Ba damuwa yallabai Allah ya sanya alheri.... " ya fada tare da juyawa ya koma bakin aikinsa.



Mahmood ya rakashi da"Ameen mungode,ka rufe gate din babu inda zani kuma.... "



Wuceni yayi abinsa ba tare da ya min tayin binsa ba,ba k'aramin shaka nayi da hakan ba,amma se kawai na cije don tunowa da kudirina da nayi.Da hanxari nabi bayansa,hadda hadawa da d'an gudu-gudu donna cin masa don tuni yayi min nisa kamar wanda ake jansa da igiya.



Yana gama bud'e entrance door din,ya juyo yana kallona dauke da murmushin yaudara akan fuskarsa,yace"Welcome to your matrimonial home *'Matar Mahmood Nakowa'*.......bismillah kina iya shigowa..... "



Be jira ta cewata ba ya shige abinsa,nima take masa baya nayi kamar wata jela.Wurin yayi duhu sosae,can naga ya kunna hasken lantarki,nan da nan kuwa sae ga haske ya gauraye tafkeken falon.Hakan ya bani damar k'arewa dukkan ilahirin falon kallo cikin dakikun da basu wuce goma ba.Duk wani kayan alatu na more rayuwa babu wanda wannan makeken falon be mallaka ba,tsaya kwatanta muku tsaruwar wannan falon baya daya daga cikin kudirin dake raina,xan de barku da kissima haduwarsa aranku.



Cike da zafin rai na isa inda yake tsaye,babu zato babu tsammani yaga kawai na cakumo kwalar rigarsa.Nace"Brother inlaw can u pls tell me dalilinka na cin amanar dan'uwanka?meyasa ka rabani da farin cikina? Kuma wani suna ne *'NAKOWA'* da kayi amfani dashi wajen aurena?? Huh?? Kayi magana......... "



Da mamaki yace"Subhanallah!! Fadima kin kuwa san girman laifin dake shirin sauka akanki da kika cakumi kwalar rigar mijinki da niyyar ci masa mutunci?pls baby doll take ur hands off me don sam bana son Allah ya kamaki da wannan laifin.... "



Axuciye na cikashi ina huci,nace"Da fari dai....._Sister inlaw komai naki sun min,k'yawunki,halayyarki,kamun kanki,uwa-uba da kuma nagartacciyar tarbiyar dana lura ya gama ratsaki,bilhaqqi dan'uwana yayi dace da mace ta gari,xanyi kokari na shawo kan mahaifiyarmu don baxan tab'a bari kanina yayi losing mace ta gari ba....._Brother inlaw ina fatar duk ka tuna da wannan Kalaman naka? "



Fesar da wata iska naga yayi,kana yace"I could still remember everything my baby doll..... "



"Ashe duk kanka kake tayi wa campaign ban sani ba,ni kuwa shashashar sae na dad'a sake jiki dakai har ina gaya maka komai nawa wanda wani abin mah sam be kamata ace na gaya maka ba,amma yadda ce ta haifar da hakan,ni aganina dole na k'yautatawa duk meh sona da Mubeen,balle kana mah dan'uwansa wanda mah yaci alwashin taimaka mana don cimma burinmu ta mallakar juna,kaga kuwa dole na k'yautatamakar,ashe abinda ban sani ba shine,kana da naka mak'arkashiyar akasan kafirar xuciyarka,ashe kana nan kana gina wani dogon buri ne aranka..... Brother inlaw ka yadda dani wallahi ban tab'a ganin maci amana ta lamba d'aya kamarka ba..............."



Da k'arfi yace"Fadima enough..... "



Sannu ahankali ya tako har xuwa inda nake tsaye,yanayinsa ya saka har na soma tsorata don ban taba ganinsa yayi fushi kamar haka ba,gani yayi kamar ina shirin soma taka rawar mazari,se naga ya dan sassauta,ya shimfid'a min pretty smile asaman fuskarsa,hakan da yayi ya saka na saki 'yar ajiyar xuciya araina don atunanina so yayi ya lakada min na jaki.



Ahankali yace"Matar Mahmood ki dena jefan mijinki da munanan kalamai haka,nasan nayi laifi amma ban cancanci kiyi amfani da wannan munanan kalaman agareni ba,kiyi haquri ki saurari abinda xance....... "



"Pls have a sit,sannan ki natsu ki bani hankalinki anan..... " Alokaci daya kowannenmu ya sami wuri ya zauna.



Ahankali ya soma da"Zaynab Abdulmaleek 'ya ce ga wani tsohon comissioner of land & housing tanan Kanon,ni da ita mun had'e ne ah *'Federal University of Nigeria,Nsukka,Enugu state'*,, ah inda nake karantar 'computer engineering' ita kuma take karantar 'pharmacy'.Mun dau tsawon lokaci muna soyayya nida ita wanda ashe mah gari daya muke da ita,soyayyarmu abar kwatance ne da sha'awa acikin campus,bamu dau tsawon lokaci ba mukai aure bayan mun k'are karatunmu da bautar kasa duka,nima kuma alokacin na samu aiki awata shahararriyar 'Electronic company' anan Kanon.shekarunmu daya cif-cif Zaynab ta koma ga mahallicinta bayan tayi wata 'yar gajeriyar jinya ta typhoid...... "



Kuka yaci k'arfinsa wanda har hakan ya jawo na dan ji birbishin tausayinsa araina,amma dana tuna laifinsa agareni,sae kuma nan da nan nasha mur!! nace"Ba labarin soyayyarka da tsohuwar matarka nake son ji ba,labarin yadda akai ka samu aurena nake son ji,we are talking about the presence,so pls stop taking us back Mr.young man................... ??Qd"



A/N

Pls kuyi manage nayi busy ne,buh next episode will be ready tmrrw Insha Allah.



*HAFNAN*??c

*??
cSHIN SO DAYA NE???c



*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION??IdA???*



*{Onward together}*

*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*

'''THE PEN OF LOVE???i HEART TOUCHING B??? TEARS OF SORROWS ???i CURDLES ???i GIGGLES ???i AND MARRIAGE THINK ???b'''

*JUST GIVE US FOLLOW.....*A???



*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*



*WATPADD:HAFNANCY??c*



*IG:Hafsy____mustee*



A?"1jnA???



_*wannan page din taki ce ke daya my Janaf??c,don haka kiyi yadda kike so da ita,Allah yabar qauna da zumunci*_



??c??c



*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*



??2\BABI NA TARA??2\



*page 23-26*



Wuraren 7:10 Fadima ta farka daga nannauyar baccinta,k'arar ruwan wankan Mahmood dake zuba ak'asa ne ya tasheta.Ahankali nake bin dakin da kallo,dakin namiji kenan babu ruwansa da tara kayan k'warmasai,komai tsaf-tsaf dashi,dakin dan gayu kenan,sae wani daddad'ar kamshin turaren daki ne ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login