Showing 9001 words to 12000 words out of 24658 words

Chapter 4 - AMANAR AURE Book Complete By Rabiatu SK Mashi.doc

17 Sep 2025

62

kwata kwata baimunba, ke gabaki daya local ce baki wayeba" yatashi tsaye yana nuna mata dan yatsa kamar zaikai mata duka "dubi yadda kike shigarki saikace yar gafaka, dan Allah Amal ki hakura dani, kinji ance kwarya tabi kwarya kibarni nasamu daidaini kema kije kisamu daidai ke"

Amal hawaye take sosai, tana danasanin zuwa dakinsa datayi, daman tasan wulakancine tukwauicin dazata samu, dolece tasa tazo saboda son datake masa,

Yaja tsaki yanufi hanyar fita, a bakin kofar yaci karo ammi dasauri yaja da baya, ammi takarasa shigowa dakin ta kalli amal sannan tajuya ta kalli afham ta bata rai sosai tace "daman nasan za'a rina, hakan yasa nabiyo bayanta domin nasan halin wannan bakar zuciyar taka, inajin duk irin abubuwan dakake fada mata, ka kyauta mutumen bazan, wadda bayajin maganar iyayensa"
Afham yakara tsuke fuska yana gunguni yace " yanzu ammi saboda amal zaki cemun mutumen banza" cike da hargowa ammi tace "eh nace, maras kunya wadda baya tsoron fushin iyayensa"
"To shikenan, afham yafada cike da bacij rai yanufi hanyar fita da karfi yaja kofar kamar zai karyata, yafita yana huci yabar dakin"....

Na:- ? Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [4/7, 1:00 AM]
????Amanar Aure
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??33 and 34??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

kai tsaye garden ya wuce cike dajin haushin Amal, wayarshi ya fiddo yana addu'ar Allah yasa Ameelah na online ko fira suyi ya samu natsuwar zuciyarshi,

Cikin rashin sa'a kuwah bata online tsaji yaja, ya tura wayar cikin aljihu sannan ya lumshe ido, kamannun ameelah yafara bayyanowa a cikin zuciyar yana murmushi, tunanin ameelah kadai ya isa yasaka shi farin ciki,
*** ***
Sai bayan la'asar lis sannan hilal yafita, bayan duk mai wakana ta auko tsakaninsa da matarsa ameelah, sabon wanka yasake tare sukayi wanka shida ameelah, yaudaikam yasamu farin ciki sosai a gurin ameelah, basu fito daga bandakinba saida sukayi alwala, suna fitowa hilal yajasu sallah, bayan sungama yafita...

Ameelah tafita tarakashi har waje, sannan tadawo cikin Falo yanayin Falon ta kalla yadda yayi kaca kaca, tayi ajiyar zuciyah, sannan tashiga gyara, komai batayi acikin gyaranba taji wayarta tayi karar shigowar text, da sauri ta ajiye aiki tanufi wuri wayar,

Sakon afham tagani, magiya yake mata akan dan Allah ta hau online, yayi miss dinta,

Murmushi kawai ameelah tayi, ta janyo data ta bude tana jiran shigowar massages,
*** ***

Afham yana zaune yaganta online wani dadi ya kama zuciyarshi don yanason chart da Ameelah, nan take ya manta da bacin ranshi cikin nishadi yake mata typng..

Afham "Ina fatan kyakkyawar mace ma mallakiyar zuciyatah tana cikin qoshin lpy.

Murmushi Ameelah tayi cike dajindadi

Ameelah "lpylau kaipa?

Afham " ina cikin Annashuwa dajin dadi, Ameelanah yau babu wanda ya kaini farin ciki, gsky nazo duniya cikin sa'a dana hadu dake??

Ameelah " 'nima nayi sa'a kuma ina cikin farin ciki"

Afham "kinsan me? Inanan zaune nake a garden ganyayyakin itatuwa sai kadawa suke ga daddadan iska mai dadin shaka, ji nake dama muna tare! Don Allah Ameelah yaushe zamuyi aure??

Ameelah tazare ido, kafin tayi ajiyar zuciya

Ameelah "da wuri haka? Duka yaushe na sanka? ko soyayya bmu fara bapa"

Afham yayi murmushi, yana kallon text din ameelah azuci yake fadan, da ameelah tasan yadda yadamu dasuyi aure da wuri dabata fadi hakanba, kodan yabakan tawa amal zai nemi auren ameelah da wuri, bayan yadawo duniyar tunanin daya shiga yafara typng...

Afham "miye a cikin soyayyah Ameelah? Zamu dinga chart ne ko waya, kullum tambyr bazata wuce ya kke? Kinyi mafarkina? Gsky hotannan kinyi kyau sosae! Hmm wannan bashine soyayyaba, ni Kullum burina in kasance tare dake, amma sai dai ayita musayar kalamai ana bayyana shauqi, mezai hana muyi aurenmu kawai?

Gaban Ameelah ya fadi, lallai Akwai rigima, tana cikin tunanin text dn Afham ya kara shigowa
Yace "son gaskiya nake miki Ameelah sona aure, idan kina ganin biki sanni ba ko banyi miki ba zan miki bayanin komi a kaina ga hotunanah nan, don Allah Ameelah ki zamo tawah karki gujemin!

Ajiyar zuciah tayi bayan ta gama karantawa duk ta hada zufa, hotunanshi ne take kallo ta jinjina kai a fili tace gaskia Afham kyakkyawan gaskene!

Yayi matuqar burgeta, nan tafara saqe saqe a zuci, ji take daman Afham ta fara haduwa dashi kafin ta auri hilal,

Na:- ?Rabiatu sk mashi da Mr, Smiles??
[4/7, 1:18 AM]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??35 and 36??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Ranar sunyi chatn sosae da Afham ana shirin yin sallar magrib yasauka yace itama taje tayi sallah, amma taji har akayi sallar magrib tana zaune, sai bayan angama sannan tatashi tayi sallar, bayan tagama tana tatashi tadauki wayarta tasaka chaji amma ta gagara ajiye wayar sai duban DP din frds dinta take har lokacin da hilal ya dawo babu Abnda Ameelah tayi, sai da taji tsayuwan motarshi ta ajiye wayan da sauri ta fara gyaran dakin...

Da leda ya shigo a hannushi ta amsa ta mishi sannu da zuwa ya qarema dakin kallo yanda ya barshi haka ya iskeshi, tana shafar kai tace "tunda ka tafi nake bacci ban samu nayi komai ba gidan!

Hilal yiyi murmushi
Yace "ay kara ki dinga hutawa, bari in fito in tayaki shara! Tayi murmushinta ya shge bedroom dinshi shima babu abnda ta gyara, haka ya shga toilet watsa ruwah shima ko wanki babu (sis rabi'at itama datake macce saida tace wannan wane irin jarabar chatn ne? Wasu matan zasuyi chatn bzasu gyara gdansu ba, babu ruwansu da tsaftar yaransu ko girkin mai gida! Sun gwammace su hau chatn suna cin Amanar aure, ko kuma chatn da qawayensu yaafi musu, nace "gsky ne ba duka matan ke da wannan tunanin ba)

Cikin sauri tashiga gyara gidan kafin ya fito, bayan yafito yazo yatayata suna aikin suna fira babu jimawa suka gama, ana kiran salar isha, hilal yafita yaje masallaci,

Yana fita, kamar tana jira, dasauri takoma gurin wayarta, daman datarta abude take, sakon ni taga sunshigo da yawa, harda wata bakuwar number, ta tsaya tana kallon number, number kamar bata Nigeria ba, saidai kuma hello kawai akace acikin number, saida ameelah takarewa number kallo sannan tafito, lambar hmm tagani ya auko mata sako, tayi sauri tashiga taduba, yace "beauty nayi miss din kalamanki dan Allah muhadu shabiyun dare akwai wani kyankyawan albishir dazan miki, plx kihau karki cemun kin manta saimun hadu" tayi ajiyar zuciya, kafin tafara zancen zuci "yanzu yazaayi muhadu, inason naji albishirin nan nasa" saikuma ta kada kai tace yes natuna,(na kalli rabi at nace "sis mekuma ameelah ta tuna ", tace "oho.. Musa ido mugani" nace "tomh)

Tana zaune tatuna da sallah dasauri tatashi tanufi bandaki bayan tafito tafara sallah, kamar wadda aka saka yin dole shaf shaf takarasa, tatashi ta nade sallayar sannan tafara shirin bacci kafin hilal yadawo,

Bayan ta kammala shirinta tafesa turare, sannan takoma kan gado ta kwanta, tanajiran dawowar hilal,

Kusan mintinta ashirin a kwance tana jiran dawowarsa, jitayi anturo kofar dakin, tunkafin yakarsa shigowa tayi saurin gyara kwancinta, sannan tarufe ido, tafara jan minshari.....

Na:- ? Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [4/10, 11:44 AM]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??37 and 38??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Hilal yashigo dakin yayi tsaye yana kallonta, yanayin yadda tayi kwanciya yasa yaji aransa kamar tanada gajiya a tattare da ita hakan yasa bai tada taba,
Wurin cire kayansa yanufa ya cire tufafinsa, jallabiya ya janyo yasaka, sannan yanufi gado, har alokcin saida yayita kallon ameelah, yau cike yake da sha'awarta amma bazai takura mata ba, murmushi kawai yayi, ya kwanta ya janyo bargo, a hankali ya karanta addu oinsa na bacci sannan ya rufe idonsa,
Duk abinda ykeyi ameelah najinsa amma saita basar, kamar bacci take
Kusan awa daya tana kwance amma bacci take ba,
Sannan tatashi tayi mika tana kallon hilal, amma duk da hakn bata tashiba, sunansa tarika kira a hankali, taga ko motsawa baiba hakan ya tabbatar mata da cewa yayi bacci, sannan tatashi a hankali, tana tafiya cikin sanda harta fita daga cikin dakin,
Daman wayarta na falo tana chaji, wurin wayar tanufa ta dauko wayar tadawo saman kujera tazauna, agogon wayar ta duba 11:30, wani irin dadi taji domin bata saba alkawarin datayiwa Hmm ba,
Data ta bude cike dajindadi, massages suka fara shigowa, saida tajira suka gama shigowa kaf sannan tafara shiga whtsapp, bunbude sakonan takeyi ahankali tana yin reapply, hartakai ga number hajna beauty,
Dubawa tayi taganta tana online, ai kuwa nan suka fara chart hajna tayi mamaki sosai ta yadda taga ameelah tana matsayin matar aure amma tana chart din dare, har kusan 12..


11:56 Hmm ya shigo online, tana cikin charting da hajna taga text dinshi yashigo, da sauri tafito daga cikin hajna tadawo cikin hmm sakone yaturo

Hmm "Gaskiya beauty ina matukar jinki a raina, ta yadda kike cika mini alkawari"

Ameelah "hmm bakomai ai danna faran ta maka nake",

Hmm "?? thnx i love yhu, ina jinsonki harcikin zuciyata, gaskiya bazan iya hakura dake ba, sonake kizamo mallakina"

Murmushi ameelah tayi kafin tafara typing

Ameelah "??toh meyasa kakeson nazamo taka"

Hmm "hmm beauty kenan saboda ina sonki mana, wai kinkosan yadda nakesonki, bana iya minti talatin batare da ka kalli pic dinki ba"

Ameelah "?? toh lallai kana sona sosai to idan nazamo mallakin wani fa"

Hmm " ?? aikuwa wlh dasai nakashesa, kuma kisa hallahira"

Ameelah "?? kisa kuma, kana nufin zaka iya kisa akaina kenan"

Hmm "sosai ma kuwa wlh idn har akace za a rabani dake to baa nemi zaman lafiyaba"

Ameelah tayi dariya a zuce take fadan wannan baida hankali, inajin ya zauce, nadi nake matar aure taya zaiyi wannan ikirarin akaina, ni wannan soyayyar tamu a whtsapp kadai nadauketa amma banda zahiri,
Murmushi tayi sannan tafara reapply

Ameelah "???? toh idan nice nace bana sonka fah, yaza kayi "

Hmm "?????? kidainamin irin wannan wasar, babu abinda natsana a duniya irin yaudara, budurwa ukku nayi kuma kowacce nina kasheta da hannuna saboda ta yaudareni, beauty idan kema kika yaudareni, kasheki zanyi sannan kuma nakashe kaina, domin nasan dacewa nazo duniya da rashin saa, bantaba jin nakamu dason macce kamar ydda nakamu dasonki ba, Dan Allah beauty karki yaudareni,.domin bana bashin yaudarah"

Tun bata gama karanta text dinba tasoma jin jiri, wani zafi taji yafara fita daga jikinta, dukda fankar datake cikin falon, amma bata hana zufa yakaryi ta jikin ameelah bah,

Wani iri tsoro taji yakamata, ayya kuwa wannan mutum ne, hannunta tadaga tana dan fifitawa jikinta,...
(A zuci nace su ameelah angamu da ...????)

N:- ? Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[4/10, 12:03 PM]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??39 and 40??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Cike dajin tsoro tafara typing

Ameelah " Dan Allah da gaske kake kataba kisa akan yaudara, kodai wasa kakemun"

Hmm "?? beauty kenan ai babu wasa a cikin maganata, ni makashi matane masu yaudara, amma idan kina tattama jirani kigani"

Gaban ameelah yafadi sosai tace nashiga ukku, motsi tajiyo a bakin kofar dakin da hilal yke kwnce,
Cike da jin tsoro ta juya gurin, bakomai bane kofar dakin ne tayi kuka, domin ta manta dazata fito bata rufe kofarba, a hankali tayi ajiyar zuciya sannan tatashi taje ta rufe kofar tadawo tazauna, tadauki wayarta..
Images tagani guda ukku sunshigo, a hankali tasaka download dinsu, nafarko wata kyankyawar maccece, a kasan pic din an rubuta "wannan itace SAJIDA itace budurwata ta farko, ta yaudareni kuma na kasheta" kuma babu abinda kayi..

Ameelah ta zare ido a zuci take fadan innalillahi wa inna ilaihi raju un",

Pic nabiyu yabude a hankali tasa hannu ta dannan cikin pic din yabude, shima photon maccece amma bata kai kyau ta farin ba, a kasan photon an rubuta "wannan sunanta FARIDA, munhadu da ita ne ta Facebook, munkusan share wata biyu muna soyayya hartakaimu gamun hadu a fili, data ganni shine tace bata sona, a take gurin zuciyata tahau na kasheta halla hira"

Cab jekaga zufa a jikin ameelah, idanuwanta sunfito bulla2, jikin ta har wani rawa yake,
( nace " ameelah tahadu da jafa i, hmm farawace idan har bata daina cin AMANAR AURE ba, )

Hannunta narawa ta danna cikin photon na ukku, tashin hankali ?? Gawar maccece anyanka mata wuya gata akwace cikin jini, ameelah jitayi kamar ta burma ihu, (koni da nake gefe saida nakasa tsayuwa, saida bro Abdul yacemun "be a man plx" sannan na tsada hankalina naci gaba da rubutu)

Ameelah takasa tsayawa ta duba abin aka rubuta a kasan photon, domin tataba ganin photon a wani grp nata na whtsapp akace wani yakashe budurwarsa saboda ta yaudareshi,

Zuciyarta duka takeyi sama sama, a akan photo nan text ne kusan guda shida, a tsorace tafara karantasu,

1, wadan nan sune matan da suka yaudareni,

2, a yanzu haka babu ko daya a duniya

3, beauty karki yaudareni domin bazan iya hakurin rashin kiba

4, koda yake ai nasan kina sona bazaki yaudareniba

5, ina fatar kinfahimci maganata ko beauty, karfa kiji tsoron halina niba mugu bane, kuma bana cutawa kowa sai wadda ya cuceni,..

Kafin tagama karanta text 5 t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aji karar shigowar wani sakon a waje, bakuwar number data gani dazuce akayi mata text da ita,

A hankali ta duba agogon dayake saman screen na wayarta karfe 2:31 tagani, duk tsoro yakamata
Sannan takaranta text nashida

6, nasan yanzu kin tsorata dani. Dan haka zanbarki kije kiyi bacci kisamu natsuwa, Saida safe. Nyt swt drm my beauty???? "

Saman sunansa taduba taga last seen dinsa kusan minti biyu da saukarsa, bata masa reapply ba tafito, bakuwar number data gani wadda akayi mata text kuma number bata nageriya bace sakon takai hannu ta danna sakon ya bude, sakone kamar haka " ke dan kutumar banki ya inai miki magana kin wani shareni, bana son iskanci fa" .....
(To wata sabuwa inji yan chacha)

Na:- ?Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: ????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??41 and 42??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Ameelah tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tafara typing

Ameelah "waye dan Allah, menai maka na zagi"

New no " ni bawan Allah ne kamarki amma ba irin jinsin kiba, ni aljanine, yanzu haka duk abinda kike yi ina kallonki, watar Allah ukubar Allah tana tattare da macce mai hali irin naki, yanzu haka ina kusa dake, la'ananna wacce bata san darajar Amanar aure ba"

Bashiri ameelah ta fara duba gefe gefen ta cike da tsoro tatashi tsaye, tana kallon falon,

Saida Ta tabbatar da komai aciki sannan tamayar da edonta ga wayar tana duba sakon daya turo, tsaki taja a zuci take fadan "wannan yama rainamin hankali, ni zaicewa ba mutum bane,
Cike da bacin rai da kuma raini tafara masa reapply

Ameelah "to idan kai ba mutum bane kafito naganka, ko angaya maka ni matsoraciyace "

New no " hahaha ai bazan fito kigan niba domin ku bil adam bakuda karfin halin ganin tsarin halintarmu amma zan taba kyankyawan gashin nan naki ki tabbatar da cewa ina kusa dake "

Ameelah "?? eh nayarda kataba din...mtsw"

Taja tsaki tana kokarin rufe data taje ta kwanta domin taga karfe 3:10,
Ta rufe Datar tayi tsaye tana tunanin mutumen,

Jitayi an fizge gashinta da karfin tsiya, wata irin mahaukaciyar ihu tasaka, ko juyowoba bata yiba tafadi kasa somammiya,
( nida nake gefe saida birona yafadi, saboda tsoro, koda naduba gefen abdul shiharyakai bakin kofar fita daga falon, lolllx ...nayi kamar nabisa amma sainace to idan nabisa yazaayi nasan halin da ameelah zata shiga saina tsaya)

Kamar daga sama hilal yajiyo ihunta a cikin baccinsa, a gigice ya farka da sunan ameelah a bakinsa, yaduba bata kusa dashi, a gigice yatashi ya nufi bandaki, yaga bata ciki da gudu yafito yanufi falo,
A kwance yasame kasan cafet, da gudu yakarasa gurinta ya daga kanta yana girgizata yana kiran sunanta amma shiru, ya daura hannunsa a akan hancinta yaji bata numashi, a gigice yatashi yakoma daki yadauko makullan mota, yafito ya tallabota, ko takalmi babu a kafarsa, yafita waje a mota yasakata gidan baya, sannan yayi sauri yaje ya bude gete yadawo yashiga motar ya tada motar yafita, bai tsaya kulle gidan ba adu ar fita daga gida yayi yabarwa Allah sarkin iko... Domin yayi ikonsa akan gidan nasa,

Na:- ?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??

????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??43 and 44??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Wata karamar asibiti ta tabayan layinsu nan ya dosa, a manne yakarasa asibitin, ya kashe motar ko cire keys bai tsayaba yazagaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login