Showing 12001 words to 15000 words out of 24658 words

Chapter 5 - AMANAR AURE Book Complete By Rabiatu SK Mashi.doc

17 Sep 2025

59

ya dauko ameelah ya tafito da ita daga cikin motar yamayar da kofar motar ya rufe, yanufi cikin asibin a gigice yake tafiya yana kiran sunanta, amma bata motsaba yana isa cikin asibin likitoci suka karbeta, suka nufi emergency room da ita, hilal yayi kokarin shiga dakin amma suka hanashi, wuri yasamu agefe yazauna ydafe kai yana hawaye tambayar kansa yake "meya faru da ameelah Allah katada kafadunta"
Zufa ya karyo masa yasa hannu ya shafe,...
(Bawan Allah hilal, abin tausayi, matarsa sai ci masa Amana take, da sannu Allah zai saka masa)...

Lalluben aljihunsa yafarayi, yafito da wayarsa ya kira iyayen ameelah,

3:40am
Suka karaso asibitin, yana ganinsu yatashi tsaye suka karaso gurinsa, a gigice momy tace "meya faru da ameelanah.. Hilal meya faru da ita"

hilal ya girgiza kai "momy wlh nima bansanibah kawai nazo naganta akwance ne a falo"

Cike da mamaki momy tace "falo kuma, tokai kana ina" hilal ya bude baki zaiyi magana abba yace "yanzu balokacin wannan tambaye2 ne ba, kuzo muje muji me likitoci zasu fada akan" abba yafice momy ta kalli hilal kallon rashin fahimta sannan tabi bayan abba, hilal ma yabi baynsu...

Sunfi minti 29 a bakin dakin da Ameelah take ciki sannan likita fito, da sauri suka taresa,

abba yace " likita meke damunta "

likita ya dube abba, momy and hilal yace " babu abinda ke damunta sock ne kawai akwai abinda ya firgitata, tasana diyarsa tasamu sock, amma batada wani matsala kowanne lokacin zata iya farkawa, idan ta farka kuma tana bukatar hutu kafin kuwuce da ita gida"

abba yace "alhamdulillah, Allah mungodema, ya juya gurin likitin "yanzu likita zamu iya shiga muganta "

likita yace " a a ba yanzuba kujira harta farka, ko kuma dayanku yashiga domin idan tafarka taga wadda tasani kusa da ita, kota samu natsuwa "

Momy tayi saurin cewa "nizan shiga likita" abba ya juyo ya kalleta, zumudin nan nata bata masa rai yake, ya harareta amma ko a jikinta, bata jira likita yayi maganaba ta tsunduma cikin dakin,
Likita yace " ita kadai ta isa ku sai kuzauna acen kafin tafarka" ya nunawa abba wuri da hannunsa sannan yafice yabar wurin,
Abba da hilal suka samu guri suka zauna suna jirar farkawar ameelah...

Na:- ?Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [4/17, 12:39 AM]

????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??45and46??

A hankali Ameelah ta fara bude idonta, momie na zaune gefenta tayi tagumi, ta miqe da sauri ta qarasa inda take!

Qarema dakin kallo Ameelah tayi kafin abinda ya faru da ita ya fara dawo mata a qwaqwalwa! A firgice ta miqe zaune, tasa hannu ta fizge qarin ruwan da akai matah sannan ta dora hannu akai ta fasa wata razananniyar qara, jikinta sai kyarma yake nan danan taa hada xufa tana wani irin kuka marar dadin saurare!

Su abba da hilal da suke zaune a waje sukaji karar ta da sauri suka nufo dakin..

Can muka hango momie maqale jikin bango ta dafe qirji cike da tsoro, daqyar ta iya bin bango har takai qofa nan suka hado da hilal da Abbah suna shrin shgowa tare da likita!

Momie kam bata bisu ba sai dai ta tsaya riqe da qofa, su Abbah suka qarasa inda take suna tambyarta meya faru? Sai mexai faru? Muryarta ko kadan bata fita! Sai wani zazzare edo take tana kallonsu, saikace bata sansuba, edonuwanta sunyi jajir, Har lokacin jikinta bai daina 6ari ba!

A tsorace likita ke mata gwaje2..
Tashin hankali na hango muku sosae a fuskar hilal dasu Abbah, momie kam har ta fara kuka tana sambatu abinda ya qara qular da Abbah kenan!

Likita ya dade yana mata gwaje gwaje kafin ya fara musu bayani "gsky wannan aikin bana asibiti bne, rashin lafiyar Ameelah har yanzu mun kasa ganoshi, amma ina baku shawara kuje wuren malamai ku nema mata taimaka!

Momie ta dafe kirji tace "na shiga uku! Wannan wane irin ciwo ne, Allah wannan sammu ne aka mata, ture ne za'a mata, domin mu duk danginmu babu mai jinnu! Koma waye sai Allah ya saka miki!

Abbah ya watsa mata harara yace "don Allah ki shga goma ba uku ba, lafiyar 'yerki zaki nema ko kwasar ma kanki zunubi xaki tsayayi wurin zato?

Daukar Ameelah zamuyi mu koma da ita can gidanmu mu nema mata magani? Ta daga kai tana gurnanin kuka cike da tausayin 'yer tatah!

Na:- ?Rabiatu sk msh da Mr, Smiles??
[4/17, 12:55 AM]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??47and48??

Daga asibitin wurin wani babban malami mai bada taimako suka wuce, sun mishi bayanin abnda ke damunta malam yasa almajirinshi ya kawo mishi ruwa a kofi ya tofa mata addu'o'i a ciki sannan ya watsa mata a fuska, tai wani irin zabura ta fara ihu da kyarmar jikin, nan malam yaci gaba da mata ruqiyya!

Duk yanda yaso Ameela tayi magana ko kadan bata fita, bugu (duka) kam ameelah ta shashi duk ta qara fita hayyacinta! Gata fara fatar jikinta tayi jaa sosai da manyan borarai,
Daqyar aka samu kafaffen Aljanin ya fita, nan ta kwanta ta fara nannauyan barci!

Hilal duk da yana namiji sai da ya zubda mata hawaye, ji yake kamar ya maida ciwon jikinshi saboda tsananin tausayin matarshi, momy ma kuka take cike da tausayi, wani duka akayiwa ameelah shi saita rufe ido, saboda ihun da ameelah keyi,
Abbah ne ke qarfafa musu gwiwan basu haquri yana kwantar musu da hnkali! (Su Ameela kam anji jiki, ko wannan ya isheta darasin cin Amanar Aure??)

Tufafin dake jikin ameelah duk sun lalace,

Abbah ne yace ma hilal yaje ya dauko mata kayanta saboda daga nan idan tafarka gida zasu wuce da ita saita qara samun sauqi! Jikinshi a sanyaye ya tafi cikin tunanin halin daya bar Ameelah!

Sai da yaje gidanne ya iske a bude kamar yadda ya barshi, yananan ynda suka barshi, qafarshi yaji ya daki wani abu akasa, ya duqa wayar Ameelah ne ya dago yana dubawa kusan 9 miss calls.

Bai duba ko na waye ba yana shirin ajewa wani kiran ya qara shgowa! "HMM" yaga an rubuta, ya dauka ya kara a kunnenshi yana shirin magana.. Hmm ya rugashi!

Cikin tattausan murya yake magana "haba! Haba!! Haba!!! My Ameelah ni babu abnda zaki cemun, kinsan yanda na shaqu dake bzanso kimin nisa ba koda na qaramin lokaci ne, ya za'ay ki brni tun jiya ba chat ba waya? Yayi shru yana jiran abnda zatace.

Shikau hilal mutuwar tsaye yayi da waya a hannunshi, ko motsi yaa kasayi! HMM yaci gaba "ya zaki shru ki qyaleni masoyiyah? Kinsan irin son da nake miki ko kin daina sonah ne? Nasan hkanma bzai yiwu ba amma kimin magana ko zanji dadi a raina!

Shi kadai yake magana yana qara ma hilal quncin zuciyah! Shi da kanshi ya gaji ya kashe har lokacin hilal yaa kasa cire wayar a kunnenshi yayi tsaye kamar wanda aka dasa!

??kuyi haquri plz da rashin jinmu kwana biyu dabaku yiba, duk muna exam ne???? Masu neman na bayanma su mana uzuri plz??

Na:-?Rabiatu sk mashi, da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [9:49AM, 4/19/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??49 and 50??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

A sandare hilal yakai xaune saman kujira, "innalillahi wa inna ilaihin raju un" itace kalmar dayaketa maimaitawa a bakinsa, Ya tafe qirjinshi da hannu

yana mayar da nunfashi, gumi ya karwo masa, wani irin zafi yakeji a zuciyarsa, saboda tsananin kishi, idanuwansa sukayi jajir,
A hankali ya dora kansa a jikin kujera, ya rufe edo, kalaman dayaji a wayar sukadai ke masa yawa a kwakwalwa,

Cen bayan wasu yan mintuna ya bude idonsa, a lokacin hawaye suka sauka kan kumatunsa, yasa ya share,

Wayar ya dauko yafara duba number, number airtel ce, ya fiddo da wayarsa yayi copy na number, sannan yasaka wayoyin duka biyu aljihunsa, yatashi yanufi dakin ameelah,

wani dinkin atamfa yadauko mata tare da wani katon hijab, sannan yafito,
Saidai ya tsaya ya rufe gidan kam sannan yashiga motarsa, airtel office ya wuce direct yabasu number suduba masa, suka ce masa saiya jira nadan wani lokaci, gudun karsu abba suga yajima baidawowa yasa yabar musu number tare da cemusu zai dawo anjima,

Har a lokacin hilal yakasa dawowa hayyacinsa, jiyakeyi kamar zuciyarsa zasa fashe. Da zaiga wannan mutum da ya kira matarsa daya yayi mummunan saba masa,

Hakadai yakarasa gidan malam mai ruqiyya a bakin kofar gidan kafin yashiga yatsaya ya daidaita kansa domin ba yason su abba sugane yana cikin damuwa, sannan yashiga cikin gidan, ya mikawa momy tunfafin,
Abba da hilal suka fita momy ta chanzawa ameelah kaya, sannan suka dawo suna jiran farkawarta,

Kusan rabin wuni sukayi a gidan, tun cikin dare har safiya ta waye, sai misalin 12:00pm na rana ameelah ta farka, a hankali ta bude ido tana kallon su momy da suke gefe da ita, bakinta na rawa tace "momy ina ne nan meya kawoni nan"

murmushi momy tayi kafin takarsa gurinta tadafa kanta tace "ki kwantar da hankalinki, muna gurin nema miki lafiya ne "

Atsorace ameelah tace "lafiya kuma umma meya faru dani" momy tace " aike yakamata muyiwa wannan tambayar, meya faru dake a daren jiya ?"

Gaban ameelah yafadi domin ita harta mata da abinda yafaru da ita sai yanzu da momy tayi mata wannan maganar,
Bakinta yadau bari, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, abba da hilal suna gefe suna kallonta, ameelah tace "nima bansaniba "

Na:-? Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[9:49AM, 4/19/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??51 and 52??

ViOHW????

Cike da mamaki momy tace "kamarya baki saniba?" Abba yayi gyaran murya momy tajuyo gurinsa, abba yace "kedaina tambayarta kijira ta samu natsuwa daga baya maji sauran zancen a gurin mijinta"

momy taso tayi magana sai kuma tafara domin tasan tana musa masa zai hau masifa, saita kame bakinta,
Suna zaune malam yashigo, yatarar da ameelah ta farka, godiya yayiwa Allah sannan yayiwa abba bayanin zasu iya tafiya da ita, taje cen gida takara samun natsuwa, abba yaciro bandur na kudi yabawa malam sannnan yayi godiya suka dauki ameelah,
Gidan hilal suka wuce da ita, hilal yabude gidan suka shiga momy ta rikata suka karasa har cikin dakinta, saman gado ta ajiyeta sannan sukayi sallama dasu suka tafi,

A mota momy tafara masifa anhata taji matsalar yarta wlh ba ai mata adalciba, abba shiru yayi ko kulata baiba yaci gaba da tukinsa, harsuka kasa gida masifa take, suna shiga harabar gidan abba yakashe motar ya rigata fitowa zuciyarsa cike da takaici ya nufi cikin gidan,
*** **** ***
Hilal kuwa kamar jira yake su momy sufita, suna fita ya shigo dakin ameelah, tsaye yayi akanta yana kallonta, cike da bacin rai, fuskarsa a murtuke,

Yana yinsa kadai ameelah ta kalla tagane cewa akwai matsala, taja jiki takarasa bakin gado, "mijina meya matsalar"
Hilal ya tsuke fuska daman jiran yake tafar magana wayarta ya dauko yanuna mata, nan yafara fada cike da hargowa "daman abubuwan da kike aikatawa kenan a cikin wayarki, daman cin amanata kike.. Ehhh ameelah kifada mana?" yakarasa maganar cike da hargowa, da kuma zafin zuciya,

Ameelah tayi rau rau da edo, tsoro yakamata matuka, kaku yasoma kubuce mata, muryarta na rawa tace "daman .... Ehmm..ehmm... "

" daman me Kifada mana, kifada.... Ya nuna kansa da dan yatsa "me kika rasa a gurina, kulawa, soyayyah, addini , ko kuma me, menai miki kike cin amanar aure na" yayi shiru yana jiran ameelah tayi magana amma takasa kuka kawai take,
Hilal yadaga wayar cike da zafin rai "babu matakin dazan iya dauka akanki domin bazan iya sakin kiba amma nasan wannan ce koh, wannan ce matsalarmu koh, to daga yau babu ke babu kara rike waya"

Da karfi ya narka wayar a kasa, saida ta tarwatse gabaki daya,
Ko uffan bai kara cewa ba ya juya yabar dakin yana huci,

Yana fita ameelah ta share hawayenta daman na munafincine, dukawa tayi tadauko fasanshiyar wayarta, taduba sim dinta taga yana nan, ajiyar zuciya tayi, tace "alhamdulillah, daman ni saki kawai nake tsoro, amma tunda baka sake niba, da sauki" tayi murmushi takara kallon wayar kafin tace " hilal kenan kaida kanka zaka kara siyomin wata nasan yadda zanyi dakai"

Nan ta kwashe sauran fila2 wayarta ta ajiye gefe, sannan ta koma kan gado ta kwanta,
*** ***
A gefen afham kuwa, tun lokacin dayayi yiwa amal wulakanci momy tai masa magana, tun daga ranar yake gaba da momy, ya daina mata magana, koya ganta saidai ya sunkuyar dakai ya wuce, duk abinda yakeso saidai yasa aneesah ta kawo masa, (hmm kunji yayan zamani masu gaba da iyayensu, yanzu hakan wasun suke, da zaran iyayen sun sun musu fada to shikenan gaba ta shiga tsakaninsu, su ala dole ba a musu fada, hmm Allah dai ya kyauta)

Momy ce zaune a bakin gadon dakin abba tana kallonsa yana shiri, hulla yake sakawa yana duban mirror,
Damuwa ce tattare a fuskar momy tace "maganafa nake maka amma kayi banza dani, abubuwan yaron nanfa sunfara yimun yawa" tana karasa maganar tayi shiru,
Saida abba ya kammala saka hularsa sannan yajuyo gurin momy fuskarsa a daure yace " afham yana ina" momy tace "yana dakinsa mana " abba yafara taku "zomuje " yanufi hanyar fita, momy uffan baka kara cewaba tabi bayan sa,

Direct dakin afham suka shiga, abba ya turo kofar da karfi yana kiran sunansa, yanajin shigowarsu ya mike tsaye, abba yatsaya yana kallonsa, afham ya sunkuyar da kai, abba yafara masifa "ka kyauta, kuma kayi daidai, wato kai dan zamani koh, kana gaba da mahaifiyarka saboda tayi maka magana akan Amal, to shikenan nima saika shirya yin gabar dani domin wlh bazan janye maganar aurenka da amal ba, idan zaka shirya kashirya domin munsaka ranar aurenku nan da sati daya, marar mutunci kawai " abba yakarasa maganar cike da bacin rai, yajuya yabar dakin,
Kafin momy tafita saida ta dallawa afham harara, sannna tafita,

Afham ya duke kai yana kuka, sai bayan sunfita sannnan yazauna yafara masifa "Allah dai yasani nidai banason amal, auren dole saikace wata macce, wlh bazai yuyuba saidai nabar musu gidan su zauna sukadai, kuma suje su samo wani dan su aura masa amal, wlh gidan zan bari...

Na:- ? Rabi'atu sk mash da Mr, Similes??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [1:12PM, 4/24/2016] ????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??53and54??

Kaya afham yashiga hadawa, saida yacika akwatinsa kaf, sannan ya tsaya yana tunanin idan yafita ina zai dosa, ina zaije,
Kofar dakinsa yaji anturo, yakurawa kofar ido yana jiran yaga wazai shigo,
Aneesah ce tayi tsaye tana kallon yana yinsa, akwatin data gani a gefensa ta kurawa ido cike mamaki tace "yaya afham mekake shirin aikatawa ne, naga kahada kaya"

Afham yakauda kai daga kallon datake masa yaci gaba da rufe zip din akwatinsa, saida ya kammala rufewa yadaga kai yasake kallon aneesah "gidan nan zan bari, kuma idan natafi kigayawa su abba karsu nemeni, domin nabar gidan nan har abada, domin nayi shawara da zuciyata barin gidan nan shine kadai katangata agareni akan auren amal "

Mamaki yacika aneesah sosai, tarike kugu tana kallon afham "hmm yaya afham zuciyarka bata baka shawarar kwaraiba, domin tanema maka saukankiyar hanya wadda zata saka mahalincinka (Allah) Fushi dakai, domin yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye, yaya afham kayi gaggawar chanza wannan gurguwar shawarar taka, mezaka cewa Allah yanzu idan katafi kaddara takiraka kasamu matsala atafiyarka, zakacene kayi fushi da iyayenka shine kabar musu gida, mafi aka sarin irin wannan tafiyar bata zama alkhairi, yaya afham karkaje, kazauna cikin ahalinka shine mafi alkhairi agareka "

edon afham yayi jajir cike da masifa yace "yakikeson nayi kenan natsaya a auramun wacca bana so, nifa kwata2 bana son amal, wlh matukar ba'a rabani da amal ba to wallahi zanbar gidan nan"

Aneesah tayi ajiyar zuciyar, tana mamakin irin zuciyar afham shi baya daukar nasiha, a duk lokacin da kake masa nasiha shi a lokacin yake kara zafi,

Aneesah tasaukar da murya tace " Bana son katafi, kazauna ni zanyi abba da momy magana, zan fahimtar dasu cewa bakason amal, kuma insha Allah zasu saurareni, kabani nan da kwana biyar"

Afham yaja numfashi sannan ya ajiye akwatin akan gado yace "kwanar biyar kikace, nabaki, amma kisani cewa matukar ya wuce kwana biyar to tabbas zanbar gidan nan" yana karasa maganar yanufi hanyar bandaki,

Aneesah tana murmushi, takarasa kusa ga akwatin, tadauketa takaita cikin drowar tasaka, koda tajuyo yashige bandaki,

Kida kai tayi tana murmushi tabar dakin...
*** ***
Bayan hilal yabar daki ameelah cike da zafin zuciya, airtel office yakoma, koda yaje sunkarasa komai, an rubuta duk wani detail akan number,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login