Showing 1 words to 3000 words out of 14403 words

Chapter 1 - HASASHE KO BURI Hausa Novels by Pretty SK.txt

22 Sep 2025

583

https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t


*_HASASHE KO BURI_*

_SADAUKARWA_
*🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).*
You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍

🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️




Page 1️⃣ ⏩2️⃣


*ABUJA*

_Sardauna crescent City_

________Mota ce ta shiga wani babban gida, wanda kaf layin shine maƙura a haɗuwa, gidan mai bene ne, ya haɗu ma sha Allah, black gate ne wanda desire ɗin sa abin tsayawa ne kallo ko in ce background ne ma musamman. Ciki kuwa hmmmm interlock ne a zube ya malale cikin gidan, ga flawers da aka zagaye haraban gidan da shi, sannan daga can gefe akwai garden wanda ke ɗauke da bishiyoyi na fruits daban-daban, sai wani gefe guda parking lot ne In da motoci uku harda wanda aka shigo yanzu, ƙiran Sport blue da ƙiran BMW ash, sai wanda aka yi parking Rolls-Royce white ƙal, take aka buɗe ƙofan motan tare da fitowo, tsayawa na yi cak dan ganin wa zai fito, sai ga wani haɗaɗaɗdan Handsome guy, a ƙalla ba zai wuce 27yrs ba, saurayi mai jini a jika, ba ƙarya daga sama har ƙasa ƙyakkyawa ne, haka kuma maji ƙarfi, ba fari bane irin choculate colour ne, irin aikin ɗin nan mai garesa da ƙyalli, yana da tsayi haka kuma faɗi ma, sai masha Allah, tafiya ya fara yi cikin gidan cike da natsuwan da ya zama mai abokin rayuwa.

__________Ma sha Allah, ma sha Allah, wani irin gidan ko ina ce aljannar duniya, baban falo ne irin wanda nake gani a finafinan ƙetare, komai na ciki royal blue ne da fari, komai na wal-wal, an zuba kujeru a babban parlour in da ya ci set huɗu, sannan ga wata arniyar tv mai rai da lafiya. Ga wani labulaye masu matuƙar ƙyau. Ba makusa a falon, sannan da ga ba na zaman mutum ɗaya ba ne, domin tsaf family guda za su sauna a wadace.

A hankali saurayin nan ke bin ko ina da kallo, take ya saki wani murmushi mai sanyi, sannan ya buɗe baki cike da taushin murya ya ce.

“Soon buri na zai cika, a wannan gidan” ya faɗa yana zama kan ɗaya daga cikin kujerun parlour.


************** ****************** ************* **********


*_KADUNA_*

_POLYTECHNIC_


_____________ Mota ce ta shigo cikin makarantar ƙiran buggati da uban gudu, wanda ya sanya mutane kaucewa daga hanya, parking lot ta nufa sannan ta ci uban burki, an ɗau kaman minti uku kafin aka buɗe mazaunin driver, ƙafarta ce ta fara saukowa cikin takalmin Snickers black, sannan sai da ta ɗauki ɗan lokaci kafin ta fito gaba ɗayan ta.


_________Wow ma sha Allah, budurwa ce ta sauke cikin shigar Abaya Black sai ta yafa Vail ɗin a kanta, kana iya hangen yadda kashin kanta ya kwanta ya yi kyau sosai, eyes glass ta cire tana danna car key ɗin, tafiya ta fara yi cikin natsuwa da aji, kowa Binta yake da ido dan yadda shigan ya hauta tamkar ba school ta zo ba.


____________Direct department ɗin su ta shiga kai tsaye, tana shiga aka hau ihu sauran students ɗin, ɗaya daga cikin kujerun cikin ajin ta nufa ba tare da ta ce komai ba, ta na zama sauran ƴam matan da ke gun suka ɗan yi murmushi da ganin shugabar su ta iso, ɗaya daga cikin ladies ɗin ce ta ce.

"Mymoon, kina kashemu da wanka fa." sai a lokacin ta kallesu sannan ta buɗe baki a hankali ta ce.

"Hmmm Ladies, a gajiye na zo school, da badan akwai text ba, da ban zo ba, kuma gashi yau na makara sosai." ƴar dariya suka kwashe sannan wata ma ta ce.

"Daɗi na dake Mymoon akwai ɗaukan serious, yanzu fa kika zo, ko gaisuwa ai ma yi." Mymoon ta kalla friends ɗin ta su uku, suma ƴam mata ne masu ji da class - kyau - da ƙuruciya.

"Merry kenan, bansan carryover and kuma level na ƙarshe ne, dole mu mai da hankali."

"Ma'esh ga guy ɗinki can ya iso." wacce ke gefan Merry ta faɗa ta na kallo wani ɗan saurayi da ya shigo.

"Muheey ina yawan faɗa miki ki dena haɗani da waccan yaron. Uhmmmm ladies ku tashi muɗan zagaya mana, tunda an sanar Sir Kashim ba lafiya." ba musu suka miƙe kowa cikin shigar da ta hau ta, suna fara tafiya kowa na class ɗin ya na binsu da idanu, dan suna burge jama'a da yawa hatta lecturers ma in sun ga wanna tawagan sai sun bi su da idanuwa.


_________Sune ake ma take da M - Ladies, domin dukka su huɗu sunan su da letter M suka fara. Mymoon - wato Maimuna Tahir ƴar shekara 22, yarinya mai ji da dukiya - kyau - da ilimi, kyakkyawa ce ta ta gaban kwatance, ita kaɗai iyayenta suka haifa, shi yasa take wadaƙa da dukiya yadda ya taso dan Babanta baban attajiri ne wanda ke sahun gaba a masu kuɗin Nigeria gaba ɗaya. Ta ɗauki ƙawayenta da daraja dan haka take sakar musu kuɗi dan su fito gari kamar Ita.

Ita kuma Merry wato Maryam Nuraddeen mai kimanin shekara 21, ita kuma ita ce kaɗai mace a gidan su, Babanta babban soja ne ya mutu tun tana ƙarama, tana da yayyani maza huɗu wanda suka maye mata gurbin mahaifinsu, ita ce ƙarama kuma dukkan su sojoji ne su ma, duk suna ji da ita hakan ya sa take wadaƙa da abin da suke ba ta, haka kuma Mahaifarta babba likita ce.

Ma'esh wato Ma'ishat Muhammad Sani, shekarunta 21, yarinya mai ji da ƙwalisa da ƙyau, iyayenta sun rasu tana zaune ne a gidan yayarta wacce ta yi aure, mijin yayar ne ya ke ɗaukan ɗawainiyar karatunta, akwai dai rufin asiri na Ubangiji, amma rayuwar Ma'isha daban ne tana son ƙarya da harkar manya.

Sai Muheey wato Muhibbat Yaƙub mai shekara 22, yarinya ce ita mai son duniya da shiga cikin manya, mahaifinta malamin islamiyya ne, haka dukkan yaran gidan duk sun yi saukan alƙurani kuma suna koyarwa a islamiyya, ita ma ba baya ba wajen ƙyua da wanka, ita ce kaɗai a gidan ta dage sai ta yi karatu mai zufi, da taimakon mahaifiyarta ta shiga daga nan kuma Mymoon take biya mata, kusan koda yaushe cikin aro sutura take dan ita ma ta cinye wankan, ba tai musu ƙarya ba ta nuna musu ita talakace, sai suke bata kuɗaɗe dan maganar kuɗi ba damuwar su ba ne jiƙakƙune sosai balle Mymoon, dan ita ma Ma'isha tana ji da Naira. Mymoon da Merry sun mallaka motoci manya-manyan dan haka suma Ma'isha da Muhibbat ke neman su mallaka ko ta wani fanni ne.




*Tafiya suke kaman ba zasu taka ƙasa ba, tsayin kusan ɗaya, kuma dukkan su ma sha Allah ƙyawawa ne na bugawa a jarida, Mymoon - Muheey da Ma'esh farare ne sosai, duk da hasken kowa da ban ne, Merry ce mai duhu amma duhun mai ɗaukan ido, choculate ce mai sheƙi. Sannan suna da body shape mai kyau na ɗaukar hankali, ko wacce ɗauke take da babban wayarta, gaba ɗayan su I-phone 16 ne suka riƙe wa.



* Zama suka yi a wani ƙawattacan waje da hutawa.

"Nan da 25mnt Sir Umar zai mana text ɗin Sir Kashim, fatan kun yi karatu, kun san ba sauƙi cost ɗin shi." Mymoon ta faɗa tana bin su da kallo.

"Ba ki da case, wai ya maganar........." Muhibbat ta katse maganar sakamakon tsayawan samari huɗu a kansu.

"M-Ladies, Amicin Allah su tabbata agareku." Ba wanda ya amsa duk da Shamo ya yi maganar cikin sanyin murya da natsuwa.

"Ladies muje class." Mymoon ta furta tana miƙa wa, a cikin rai Muheey ta ɗan yi ƙwafa dan tana jin haushi yadda suke share zafafan gayu kamar su Shamo. suna barin gun, sai mazan suka zauna a gun suna ɗan dariya ƙasa-ƙasa.

"Shamo wallahi a wanna rayuwa kar kasha wiya, kawai kayi wuff da ɗaya daga cikin wa'incan shike nan, ka huta da komai ka zama mijin Hajiya mai capacity." Dariya suka sanya sai ɗaya shima ya ce.

"Haka ne Abdul, ni Muheey ta fi tafiya da imani na, ina ma ta amince min, na aureta kaga shike nan naja ƴan canji sosai."

"Uhmmm narasa mai ya shiga tinanin ku, ni wallahi da gaske na ke son Maryam, badan kuɗin ta ba, sannan ina son na mallaka nawa kuɗin da inganta rayuwar ta."

"Abbas kenan, ana maganar capacity, kana shirme, wani inganta rayuwarta bayan a ingance take, rayuwar yanzu sai a hankali, Nigeria ba aikin yi, ni ba zan tsaya ɓata ma kaina lokaci ba gurin neman aiki, to mu matasa ya za mu yi?, Wallahi mace irin su kawai nake nema mai dukita.” dariya suka kuma yi dan Shamo akwai son duniya da son hutu gashi ɗan talaka.

" Wait........ Abbas kai Merry - Shamo kai Muheey - Abdul kai kuma Ma'esh, ni kuma jagaba, shugabar tawaga (Mymoon).”

"I.b shegen ƙura, kaine ai ka kwashe duka ganimar, kowa yasan irin dukiyar mahaifin Mymoon, gashi ita kaɗai ce, kana aurenta kai za ka maye dukiyar sannan ka yi karatu ba maganar raini mutuminaaaaa." Shamo yakai maganar yana imagine wannan lokacin ya zo musu.

"Ba ƙarya wallahi, yanzu muje class, zuwa gobe za mu fara takun ɗana soyaya, dan babban tarko za muyi musu." Abdul ya faɗa suna tafawa da Shamo, jerawa suka yi suna tsara yadda salon tafiyar zai kama, shi dai Abbas sai jinsu yake kawai.


__________ Samari ne su, irin handsome guys ɗin nan, suna ɗaya daga cikin matasa masu ji da wanka a kaf school ɗin, abokai ne tin secondary school, kuma layin su ɗaya, dukkan su shekarun su 26 ne, abota mai tsafta suke yi, gasu da brain, idan suna speaking English sai ka za ci ba a Nigeria suke karatu ba, hakan ya sa suka ɗauka ka, dan kusan komai suna kan gaba.


________Babu wanda yake sana'ar annu a cikin su duk dun dogara ne da karatu, amma a yanzu Shamo - Abdul da I.b sun can za kota yayane so suke su aura mace mai dukiya domin su huta, Abbas ne ya ƙi biye musu amma duk da haka suna tare, ba tawagar da Shamo yaga sun cancanta da su sai M- ladies, duba da yadda suke ji da dukiya..........


****************************************

*KANO*


* Wani madaidaicin gida ne a cikin wani gajeren layi, ba laifi gidan ko ina a gyare yake tsaf duk da na masu ƙaramin ƙarfi ne, wata budurwa na hanga tsaye a tsakar gidan, tana sanye ne doguwar riga ban iya tantance yanayin ɗinkin dan ta sanya hijab wanda yake dai-dai gwiwarta, ma sha Allah, yarinya ce ƙara ma wacce ba za ta wuce 20yrs ba, fara ce ƙal dan ko tabo babu a fuskarta, niƙaf din dake kan igiya ta ɗauka tare da ɗaurawa. wow babu abin da ake gani a jikinta, dan ƙafarta sanye cikin safa haka hannunta ma, hatta ƙwayen idanunta a baka tantance ya suke dan niƙaf ɗin ma ɗinkinsa daban ne.

Jakkarta wanda yana kan kujera ta ɗauka tare da riƙewa sannan ta haɗa hannu ta tafa da ƙarfi, jin shuru yasa ta kaɗa kai dan ta tina mahaifiyar ta na barci, fita ta yi tana mai addu'a fita daga gida. Tafiya take a hankali cikin takatsantsan, har ta isa bakin titi, hannu ta sa ta tari nepep ɗin da ya tawo, take ya tsaya dai-dai ita, sai ta buɗe jakkatar sannan ta bashi wani paper, amma ya yi ya duba, sai ɗan Dattijon ya ce.

“Kurma ce ke?.” sai ta ɗaga mai kai.

“Babban titi, dari biyu da hamsin ne, amma ko ban dari biyu.” ya faɗa yana miƙa mata parper, ta amsa tana mai alaman godiya sannan ta shiga cikin, bayan sun hau titi da ƙyau, ta lumshe idanunta tana magana a cikin ranta har suka isa wajen, kuɗin ta bashi ya ba ta canji, sannan ta kalla babban wajen da ya ajiye ta, a hankali ta sauke ajiyan zuciya sannan ta fara tafiya cikin wajen. Driver ne ya bita da idanu dan ta bashi tausayi.


A tsakiyar cikin filin gidan TV na GOODNESS TV, gidan Tv ne da yake taka babbar rawa a hajar Kaduna. Ta tsaya tana mai bin mutane da kallo, dan akwai mutane ba laifi kowa na harkokinsa. A cikin ranta ne ta furta.

“Ya Allah badan ni ba, badan halina ba, dan soyayyar da kake ma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ❤️, kasa a yau na haɗu da CEO, ya min interview sannan na ci tare da fara aikin nan. Ya Allah ka cika min burina.” ta kai nan tana jin hawaye a cikin idanunta sai ci gaba da tafiya ta na mai ta ambaton Allah..........✍️


> Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰



🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖


[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t
🌹 *DEDICATION* 🌹
I dedicate this page to *Habibah, my beloved* —
the one who owns my heart and inspires my words.
*May Allah preserve our love and bless us with understanding and peace.*

❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._



Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!*
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_


🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟

*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍



Page3️⃣⏩4️⃣



*KADUNA*


*Bayan an kammala text, suka aka yi lecture sannna aka tashi, a parking lot suka tsaya suna ɗan tattauna daga baya Mymoon da Ma'ishat suka hau motan Mymoon suka bar school ɗin, sannna ita ma Muhibbat ta shiga motar Maryam dan sunfi kusa suka bar school ɗin.

Da idanuwa suka bi motan Maryam da ya bar makaranta, wani ɗan sanyi ne ke ratsa zuciyar Abbas in dai a ga wani abu na Maryam balle da ya hangi fuskantar ta. Trekking suka sha har gida duk da akwai nisa sosai, bayan sun shiga layin nasu, wani gida suka shiga ina da ba za ka yi tsammanin ganin su ba, ɗakin dake zaunen gidan suka zazzuna kan katifa. Gidan su Abbas ne da Shamo dan su gidansu ɗaya imfact yaran kishiyoyine amma babu mai ganewa dan wata muguwar shakuwace tsakaninsu, Ibrahim da Abdul kuma duk maƙotane amma ana suke ƙwana in da suka yi ƙofa ta waje, da yake ɗakin ba laifi akwai girma, katifar biyu suke amfani da shi sannan ga tsohuwar wardrobe ɗin su, wanda ana suka sanya kayansu, sai kuma renting da suke yi wajen Ado mai wanki.

“Na samo Numbers ɗin M-Ladies, na tura muku ta whatsApp.” Shamo ya faɗa tare da ciro arniyar wayansa.

“Wow mutumina, a gun Zubaida ka samu ko?.”

“Eh mana, sai ku fara gina love tin yanzu, balle kai I.B kasan Mymoon akwai ji da kai.” dariya suka yi sannna Abbas ya ce.

“Hmmmm Allah ya ganar da ku, dan wannna hanyar akwai matsala.....”

“Kul, kar ka mana mugun baki, yadda kake son Maryam haka muke son namu.”

“Dena tada jijiyan wuya, ni kunga na fita dan yau zan fara zuwa gareji.” dariya suka kwashe suna mai a dawo lafiya. Shikam ko a jikinsa ya yi waje tare da nufan gajeri dan fara aikin da ya sha wuya aka bashi dan wai ya girma sosai.



*Ma'esh*

A ƙofar gidan su Ma'esh ta faka, sannan suka yi sallama tare da rabuwa, ba ƙwarya, gidan su Ma'esh ya haɗu sosai, ciki ta shiga a in da ta hangi mota baƙa a harban gidan tana mai cin burin ta fara zuwa school da ita. Wani parlour ta shiga wanda ya gaji da haɗuwa, a kujera ta zauna tana kallon TVn dake aiki, ta jima babu motsin kowa sai daga bisani wata mata ta fito daga ɗaki.

“Ma'esh kin dawo?.” matar da a kallo ɗaya za ka ga mugun kaman da suke yi, sai dai shekaru su banbance.

“Aunty na dawo.” ta faɗa da kyar.

“Lafiya!? Me aka miki?.” wacce ta kira da Aunty ta nufeta da sauri, dafata ta yi tare da sanya hannu ta share mata hawayen idanunta.

“Faɗa min, what's wrong?.” Aunty ta faɗa.

“Na faɗa miki I need my own car but.....” sai wasu hawayen, da sauri ta miƙe tare da barin parlour, da idanu Aunty ta bi ta, tana mai jin zafi a ranta, dan idan kana so ka kanta a wani hali ka taɓa mata Ma'ishat.

“Bara Alhaji ya dawo dole yasan abin yi, domin buri na shine faranta miki rai.”


Tana shiga ɗakin ta kulle tare da hawa kan gadonta, wanda ya gaji da tsaruwa. Tasan dole Aunty ta ɗau mataki.


*Merry*

Merry tana yin horn aka buɗe mata, sannan ta shiga, tana yin parkinga ta nufi cikin parlour su, masu aiki ne kawai ta tadda dan har lokacin Mom ɗin ta ba ta dawo ba. Ba laifi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login