Showing 3001 words to 6000 words out of 14403 words

Chapter 2 - HASASHE KO BURI Hausa Novels by Pretty SK.txt

22 Sep 2025

585

nan ma gida ne mai sunan gida, dan a kwai komai na more rayuwa, kuma ko ina ya ji kuɗi, kana isowa za ka gane gidan sojoji ne dan uku suna gadi ta waje haka ciki akwai mutane biyar, manyan sojoji masu ƙarfi.



*Muheey*

*Kwance take kan kujera tana latsa waya cikin nishaɗi, dan tin bayan da ta shigo daga school ta haye kujera tana chart da wani wanda ba ta san waye ba, murmushi ne kwance a kan fuskarta. Sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa a kallo ɗaya za ka ma gidan ka fahimci akwai rashin wadata kaman na sauran amma akwai rufin asirin Allah, kiran sunanta a ka kuma yi dan haka ta miƙe da nufi ƙaramin tsakar gida amma a ɗan gyare yake.

“Haj. gani.” ta faɗa tana isa gaban matar dake zaune kan tabarma tana yankan kabeji.

“Na faɗa miki ki sha gari ki zo ki amsa girkin nan, kafin ki fice, yau Allah ya yi kin leƙo mu.” wani abu ne ya tsaya mata a rai, amma ta kasa magana, ganin haka bai da amfani shi yasa ta koma ɗaki dan shan gari ta amsa aikin kafin ta bar gidan zuwa in da take ƙwana.



*Mymoon*

Wani haɗaɗɗen place ne mai matukar haɗuwa, yana bene haka kuma ya tsari, stairs Mymoon ta fara takawa zuwa bedroom ɗinta, bayan ya shiga aljannar duniyar ta, ta shiga bayi ta yi wanka sannan ta fito ɗaure da towel tana tsane dogon gashin dake kanta. Zama ta yi tana mai kallon chocolate ɗin da ke kan bed, da sauri ta dauka tare da yaga ledan ta kai baki, dan ita akwai son kayan zaƙi.



*************************************


*KANO*


Bayan ta shiga wajen direct in da jiya ta shiga nan ta nufa tana da maimaita addu'oi a cikin ranta. Ta riga ta saba duk in da ta bi sai an zuba mata saboda irin shigarta, dan a yanzu ko a jikinta dan an bi ta da kallo. Bayan ta shiga wajen da kai ta gaishe su, sannan ta hau layi, in da mutane huɗu ne gabanta. Daga kallon wajen ta fahimci wanda ake jira yana nan. Wayarta ta ciro tare da rubutu sai ta miƙa ma wacce ke gefanta, da yake jiya sun haɗu to tasan ba ta magana dan haka ta amsa ta karanta sai ta ce.

“Hmmmm Sister, wai ce wa ya yi da baki zai mana tambayar kuma mutane biyar zasu ɗauka dan suna da mutane.” da jinjina kai tana kuma wani typing ɗin, bayan ɗayar ta duba ta ce.

“A ƙalla mutane 15, sun shiga kuma gamu mu huɗu.” alaman godiya ta mata tana mai da wayan tare da tsare ƙofan da kallo har wanda ke ciki ta fito, sannan wani ya shiga, haka haka har wacce ke kusa da ita ta fito rai ɓa ce, a kallo ɗaya ta fahimci akwai matsala, dan haka ta dafata tana ɗaga mata kai.

“Na haƙura nikam, ki shiga Allah ya sa ki da ce.” daga haka ta wuce, take jikinta ya yi sanyi, sannan ta nufi ƙafan ta tura a hankali, tana sallama a cikin ranta.

Duk da tana cikin niƙaf amma sai da lafiyyan ƙamshi ya dake ta, lumshe idanunta ta yi, sannan ta kalla officer ɗin, ba laifi ya haɗu, duk da akwai abubuwa da ko ina na da ga na'urori, cameras da dai sauransu. Namiji ne ta hanga tsaye jikin glass yana kallon haraban gidan tvn, matsawa ta yi ta zauna tunda ya ji ya tashi. Tsaye yake cikin manyan kaya, hannusa riƙe da flask tea yana sha a tsaye, juyowa ya yi tare da nufo in da take tsaye sannan ya mata alama da ta zauna, a ɗan daburce ta zauna dan ya mata ƙwarjini. Guy ɗin ya haɗu ma sha Allah, dogo mai cikar kamala. Shima zama ya yi. Yana mai kallonta dan ko ƙyayar idanunta ba ya gani.

Take wayarsa ta kuma yin ringing sai ya ɗaya.

“Darling still mace ce......” take ta jiyo muryan mace ta cikin wayar tana cewa.

“Ta yi waje, na faɗa maka maza zalla.”

“Wanan matar aure ce fa.” ya faɗa yana kuma kallon yarinyar da ke zaune.

“Juya cameras kanta ya yi.” kafin ya yi magana ta katse, sannan ya yi latse-latse a System, ba'a jin ba ma wayar ta kuma yin ringing.

“Ka mata interview ɗin.”

“Okh my Darling.” daga haka ya sauke ajiyan zuciya yana mai faɗin.

“Takaddu.” da yake ta ciro sai ta miƙa mai ba tare da ta falle rubutun ba, ya amsa yana dubawa.

“Uhmmm your full name.” da sauri ta miƙa mai wani paper ya amsa ya kalla. (My name is Ameeratulkhairi. Sa'adatu Jibril) shine a rubuce sai ya ɗago da ɗan faɗa.

“Ba ki da baki ne, dan kina matar aure, ba za ki yi magana ba?.” da sauri ta kuma miƙa mai wani, kamar ba zai amsa ba sai ya amsa. (Bana magana, Bebiya ce.) Take ya ji wani abu ya tsirga a zuciyar sa. Sannan yaji tausayinta sai ya aje.

“Na fahimta, kinsan kafin na baki aiki dole kiban labarin ki, da dalilin son aikin journalist, da kuma irin gudummawar da za ki ba da sai kuma wani fanni dan na ga ba ki yi zurfi a karatu ba.” ɗaga mai kai ta yi sannna ta cori wani littafi tana miƙa mai. Ya amsa yana mai buɗe wa. ( Buri na shine zama ƴar jarida) shine ya fara cin karo da shi sannan ya ɗago ya kalleta.

“Ki je gobe ki dawo, misalin 1:30pm, in dai labarin ki ya gamsar shike nan.” godiya ta mai da hannu sannna ta yi fara tafiya, sai ya samu kansa da bin bayanta da kallo da sauri ya ɗauke kai yana cewa.

“Ki gaidamin mijinki, bangan shi ba amma ya burgeni da yake sa ki yi wannan shigar.” murmushi ta yi tana mai ɗaga kai tafice. Take ya hasaso Darling cikin shigar nan za ta yi ƙyau amma ko mutuwa zai yi ba za ta sanya ba, yara sa maike yawo a kansa ne, da zarar ya bar gida yakan ta jin wani yanayi akan ta da kuma abubuwan da baya so ta na yi, amma da ya ji muryanta ko ya koma gida shike nan sai ya mance. Kallon rubutun ya yi da ya yi mai mugun ƙyau, ita ce ta ƙarshe dan haka ya buɗe shafin gaba. (Labari na mai ɗauke da darasi da haƙuri.) Sai ya yi murmushi ganin rubutun da yawa ya sa ya miƙe sannan ya hau kan sopa ya hau karatu.............





*ABUJA*


Office ne wanda yake cike da takkadu, zaune yake kan kujera yana latsa system sannan yana kallon screen ɗin, knocking aka yi ya ba da umarnin shigowa. Take aka shigo, wani saurayi ne sa'ar shi, yana rike da laptop ya ce.

“Aboki na kammala.” sai ya kalla abokin na sa ya ce.

“Good job, yau za ka raka ni wani waje.”

“Hmmmm na san yanzu burinka kawai kake so ka cika, amma a ganina Ukasha ka sauya shawara please.” sai ya bar latsa system ɗin ya zuba ma abokin na sa idanun.

“Umar, dole na cimma wannan burin na wa, a yanzu biyu na ƙasa saura biyu, na tambayeka, burina zan fasa? ko na Hussain ɗina?.”

“Haka ne, shike nan, Allah ya cika maka burin na ka.”

“Ameen Umar, nan da watan biyu nake so na yi auren.” sai Umar ya ja numfashi yana kallon Ukasha take magana a cikin ransa.....

'Shin kunsan waye Ukasha?, Kunsan labarin rayuwarsa? Kusan ya halinsa? Kunsan ya nake haƙuri da rayuwa da shi? Kunsan ya yake ɗaukan Burinsa? Wai ma kunsan menene Burin? To Bara na baku labarin a kan Ukasha da kuma Burinsa...........✍️

> To Umar za mu haɗu next page. Still C.E.O muna jiran labarin Ameeratulkhairi. Sai jama'ata kunsan ina yin Ladies kuwa, haka su Abbas ma..........hmmmmm......akwai aiki...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️🥰🤗.










🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
[9/15, 18:34] PRETTY SK NOVERLIST: https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.




💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny. by *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*

PAGE 5️⃣⏩6️⃣

*KANO*


______Bayan ta koma gida, a parlour ta iske mahaifiyarta zaune tana kallon TV, zama ta yi kusa da ita tana mai cire niƙaf ɗin. Mahaifiyar da ke zaune, wanda babu abin da suka haɗa face hancin su da ke yanayi, duk hasken ta ba ta kama ƙafar Ameeratulkhair ba saboda hasken ta daban ne, tana cire niƙaf ni ƙyakyawan fuskarta ta bayya. Hmmmmm haske har kashe ido yake yi, murmushi ta saki wanda fararen haƙora ta suka bayya tare da dimple ɗin ta da suka lotsa, kusa da ita ta zauna tana magana da hannu wanda mahaifiyar ta gane sannan nima na gane saboda Allah ya min baiwar hakan.

“Insha Allah komai zai yi dai-dai, ance gobe na koma, ki ta ya ni da addu'a.” shine abin da ta furta sai mahaifiyar ta ɗaga mata kai. Sun jima a nan suna kallo dan shirin da ake haskawa akwai daɗi. Su biyu suke rayuwa a gidan wanda shine kaɗai suka mallaka daga uban dukiyar mahaifinta wanda ya rasu. Kuma Alhamdulillah suna cikin godiyan ubangiji.

Ɗan ƙaramin ɗakin ta shiga in da ta ga wani littafi akan ƙaramin gadonta, ta sauri ta ƙara da tana ɗauka, take da dafe ƙirji tana fita riƙe da littafin, maihifiyar ta juyi da sauri dan jin yadda Ameeratulkhairi ta buƙa ƙofa , kai ta ɗaga mata alaman tamabaya (Lafiya). Ƙwatance ta shiga yi wa Mamar tana haɗawa da hannun tare da nuna littafin. Da sauri Maman ta waro ido tana wani irin salo da hannunta. ( Sai da na jima kafin na gane mai ta ce)

“Garin ya?.” sai naga Ameeratulkhairi ta zauna daɓas.

“Kar ki damu, insha Allah ba zai karanta wancan ba, ko kuma alhaki na ne, nai ta ki ban na karanta littafi sirrinki mai suna SIRRI ki hanani. Hmmm ai shike nan ga wani ya samu a sama.” Mahaifiyar ta buɗi baki ta koro wannan zancen da hausarta wacce ba ta wani zauna ba.

Take hawaye suka gangaro a cikin idanunta, a yau ta yi dana sanin rubuta gajeren labarinta a irin littafin SIRRI, littafin iri ɗaya ne, dan na Sirrin ya cika shine take so ga fara a sabo, sai ta rubuta gajeran labarin a shafin farko, saboda kar ya ɓaci shine ta bari idan ga je can ta falle, to gaba ɗaya hankalinta ya yi gaba. Kuma jiya duk ta yi rubutu a ciki, hasali ma a gu ɗaya suke, yanzu idan ya karanta wannan shike nan ya gama sanin komai aka ta. Ta sha ainiyin ko wanda za ta aura ba za ta so ya gani ba. Akwai abubuwa da ita kaɗai take son gani, wani ta rubuta dan nishaɗi, wani tana kuka tana rubutawa, wani kuwa duk wanda ya karanta dole ya ta ya ta kukan. Ji take kaman ta fita ta koma sai dai tasan Amma ba za ta barta ba.........



*ABUJA*

Umar ne ya lumshe idanunsa tare da fara karanto min waye Ukasha?.

*Ukash wato Hassan Muhammad, haifaffen Abuja ne, Mahaifinsa baban attajiri ne, maihifiyarsa kuwa baturiya ce, a America Alhaji Muhammad ya auro ta, bayan sun yi ɗan rayuwa a can sai suka dawo Nigeria saboda business ɗin sa. Alhamdulillah yana samun kuɗi fiye da tinin mai tunani, sannan yana da alheri sosai, shi kaɗai ne ya yi rai a wani gobara ta ta cinye ƴan gidan su, sannna ba wani zumunci ake ba da ɗangiba dan wasu ko saninsa bai yi ba, Kasuwanci ya baro da shi daga ƙasarsa, ya gina sabuwar rayuwa. Bayan ya yi kuɗi mai sunan kuɗi, shine wasu daga danginsa ke waiwayansa, ba laifi yana ƙyautata musu fiye da misali. Sun ɗau lokaci shi da Rose kafin ta samu ciki, a gun haihuwa ta mutu, dan ko musulunta ba tai ba ya yi iya yinsa Alhaji ganin ta musulunta amma ta ƙi.

Tweens ta haifa masu matuƙar kama da shi. Ya ƙi wani auren dan haka ya neman musu wata tana rainan mai su, har zuwa fara tafiyan su, Hassan - Ukasha da kuma Hussain - Sadik, sun taso kansu ɗaya matasa masu jini a jika ga wayau da fasaha, ba yadda za ka yi ka banbance dan komai na su iri ɗaya ne, hatta mood ɗin su sauyawa yake, in yau wannan ne yake da fara'a ko gobe ɗayan ne, abu ɗaya zaka banbance su shima sai kuna tare shine idan suka yi magana domin Hassan ya fi taushin murya shi kuma Hussain muryansa na da sauti. Haka rayuwa taita tafiya har suka kai shekara 24, a wata rana kuwa aka wayi gari babu Alhaji Muhammad, wanda hakan ya yi sanadiyar bugawa zuciyar Hassan dan akwai shi da rauni sosai. Tabbas a lokacin saura kaɗan Hassan shima ya mutu dan har ƙasar waje aka kaisa, ya jima yana jinya kafin ya dawo dai-dai, Ni Umar nine abokinsa na layi, dan haka ni ya mayar ɗan uwana, komai da ni yake tattauan. Sai dai me Ukasha wani irin mutum ne wanda mai tsatsauran ra'ayi, in ya ce abu to babu fashi.

Yakan zo min da tambaya na bashi shawara, haka zan zauna na jero mai sai da ƙarshe ya ce nasa ya fi. Yana da halaye masu ƙyau shi yasa har yanzu nake tare da shi, akwai mutumci, sai dai baya ɗaukan raini da wasa, haka baya son yawan magana, shi dai a yi shuru kawai ayi shuru, ba ya yawan magana, hmmmmm karna jaku da yawa, bara dai na faɗa muku burin sa. Yana da buri biyu haka marigayi Hussain ma, burin na su ko na ce hasashensu suna ɗan kama sai dai akwai banbanci.


Ukasa Burinsa na farko shine cimma wannan matsayin da yake kai yanzu kenan, ya sha wiya sosai amma sai da ya ga ya cimma mallakan kamfanonin da ya yi niyya, baya damuwa da ko nawa ne zai ɓatar in dai ya cimma Burinsa, Sai na biyu shine Aure, yana son ya aure mata biyu a rana ɗaya, Bahaushiya da Bafullatana.

Hussain ma ya cimma Burinsa na farko, wanda sai da ya zageye ƙasashe 15 na duniya, na biyun kuma shine auren Yoruba da Igala, domin yana son al'adar yare.

In da abun yake shine; Ukasha ya ƙulla aniyar cika ma Hussain *Burinsa* dan haka ya yi *Hasashen* auren mata huɗu a rana ɗaya kuma kowacce da na ta yaren.........

“Umar! Umar!! Umar!!!.” take ya buɗe idanunsa ya zuba ma Ukasha yana faɗin.

“Na'am.”

“Tinanin me kake yi?.”

“Babu komai, Bara na koma office ɗina.” ɗaga haka Umar ya miƙa tare da fice, da idanu ya bi abokinsa har ya fice.

Yana fita ya shiga nasa office ɗin sannan ya zauna yana mai faɗin.

“Yau ko wani duniyar Ukasha zai kaimu neman yarinya oho........” sai ya lumshe idanunsa yana faɗi a cikin zuciyarsa “Ni yake sanya na bincika mai mace, sai na sha wiya na nemo irin macen da yake so, da munje sai ya ce ba tai ba, a ƙalla mun kai wata biyu amma mace ɗaya ce ta yi mai wata Bahaushiya, saura mata ukun...........





*KADUNA*


_Ma'esh_ haka ta hora kanta da ƙin cin abinci badan komai ba sai dan Aunty ta fahimci irin son da take ma mota, sam ta ƙi fitowa ma, har dare, tana jin lokacin da Uncle ya shigo wato mijin yayarta, aikam da shigorwa ko minti 10 ba'a yi ba yarinyar Aunty Rumaisa ta shigo ɗakin na ta.

“Aunty Ma'eh, Momyna tana kiranki.” daga haka ta yi waje, hijab ta zura sanna ta yi waje, babu kowa a babban parlour sai ta nufa ƙaramin, bayan ta shiga ta zauna daga gefe tana gaida Uncle cikin ladabi.

“Lafiya lau, Alhamdulillah, zauna a sama.” sai ta zauna tana facing Aunty, take Aunty ta sakar mata murmushi.

“Maman Ruma na ji ta ce, kina son mota dan zuwa school.... To ai ba ki iya mota ba kuma kinga ita nake so na fara siya ma wa dan ta dinga kai Ruma school. Ki bari da na fara siya mata sai ke kuma duk a cikin shekarar nan insha Allah.” ya kai maganar yana kallon Aunty, sai ya ga ta haɗe rai, tare da miƙe wa ta nufi babban parlour. Ma'isha tasan yau dole a baka carkey, ba a jima ba Uncle shima ya miƙe ya barsu.

A tsaye ya tadda da jikin fridge.

“Hayathy......”

“Dan Allah ka yi shuru Habiby, yanzu a ce Ruma ta girma ta nema abu kuma akwai amma a hanata."

“Haba Hayathy, wallahi ba haka bane, yanzu kinsan banda wani kuɗi, shike nan zan fara siya mata.”

“A'a ni banso, na haƙura." Sai ta fara tafiya da sauri ya riƙo hannunta yana zagayawa gabanta ya ce.

“Kinsan na tsana na ganki cikin wani hali. Me kike so?." Murmushi ta saki tana mai cewa.

“Kaba Ma'isha aron prado kafin ka siya mata."

“Shike nan.” sai ta ɗaga mai kai. Tare suka koma ɗayan parlour, a idan Ma'esh ta saki wani murmushi dan ta san a yau dole burinta ya cika.

“Na bar miki motata prado.” Uncle ya faɗa yana miƙa ma Ma'esh car key, da uban tsalle ta isa gabansa ta na amsa tare da mai godiya kaman za ta shige ƙasa, da yake ta iya mota sosai, da gudu ta bar ɗakin, Aunty da Uncle suka tintsire da dariya.



*Muheey*

* Misalin 4:12pm na rana ta zura hijab ɗin ta sannan ta fita a gidan, sai da ta ɗan yi tafiya mai tsayi domin kuwa layin na su akwai tsayo, wani gidane me gate black ta shiga, ba laifi gidan mai ƙyau ne, knocking ta yi ba'a jima ba aka buɗe, matar da ke tsaye ta kalla Muheey tana faɗaɗa murmushi tare da faɗin.

“Na kira wayanki not reachable.” sai bayan da ta shiga harabn gidan tukun Muheey ta ce.

“Network, na leƙa gida ne.”

“Ni dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login