Showing 9001 words to 12000 words out of 14403 words
dan da gaske Mymoon na da hannun ƙyauta fiye da misali, komai ita ta ke bai ba tare da ta damu ba tinda ya ce mata da sun kammala karatu zai ne ba babban aiki shike nan.
Haka Shamo da Muheey, ta so ya na da kuɗi a yanzu domin ta fantama amma sai dai tana target da idan sun kammala ya ce mata a Dubai zai fara aiki, hakan yasa ta sake maj sosai, kuma in ta samu kuɗi wajen wasu samarin ta shi take bawa.
Ma'esh da na ta wato Abdul, suma ba ƙyar soyayya suke sha.
Kaf cikin su, su Merry ne suk gina tasu akan gaskiya. Sau da dama takan yi mai ƙyauta amma baya amma saman, dai-dai da katin waya sai ta dawo mata da shi, har sabuwar waya ta siya mai amma yaƙi amsa.
*Merry*
Zaune take tana kallon wani Nigeria Film, take wayarta dage gefe ta yi saƙan saƙo, da ta basar amma jin na biyu yasa ta ɗauka tana kallo. Sauƙon farko na kuɗi ne, 3k sai saƙon Abbasa. “My patner ba yawa, my first gift to you." Murmushi ne ya ƙwace mata sannan ta kira number na sa, sai dai kaman kullum ba yi pecking ba har ya katse, take na sa kiran ya shigo wayan ta amsa. Bayan sun gaisa.
“Nagode sosai.” ta faɗa tana jin wani shauƙi na mamaye ta, ita ko dubu darin da yayanta ya saman tama ɗazu ba ta yi wannan farin cikin ba. Maganar minti uku suka yi katinsa ya ƙare, ajiye wayar ta yi dan tasan ko kira nawa za ta mai bazai ɗaga......
*KANO*
A gurguje ta shirya, ko wani lafiyayyan breakfast ba ta yi ba, bayan ta isa Goodness Tv, sanna in da suka zauna jiya, tambaya ta yi akan c.e.o, aka ce mata yakusa iso wa. Zama ta yi dan gaba ɗaya tin jiya ba wani natsuwa ta samu ba, littafin sirrin ta ne, ba za ta so kowa ya gani ba, fatan dai ɗaya bai karanta ba.
Tana zaune ta ga wuce wansa, da idanunwa dake cikin niƙaf take kallonsa. Shigen dressing ɗin jiya ta yi, sai dai na yau hijabi ɗin dogone har ƙasa, haka kuma ɗaurin niƙaf ɗin a ciki ta yi kafin ta ɗauka hijab.
Yana zama ya runtse idanuwa, tare da kifa kansa jikin desk. Har ga Allah in ya ce ba ya cikin damuwa ya yi ƙarya, Darling na neman kashesa. A ce matarsa, matar aure, haka take yawo cikin maza balagaggun da sunan suna mata aiki, dan ta ƙi yadda da mace ta dinga mata aiki. Shi tunda yake bai taɓa ganinta da kayan mutumci ba sai ranar aurensu, amma a washegari tin da safe ta sanya wasu tsinannun kaya, shi kansa mamaki take basa, domin in ta yi wani abun sai shi ya ji kunya. Yana so ya dinga taka mata burki amma. Baya iyawa sam, yanzu haka ya baro gidan ne tana sanye da wasu sleeping dress, kuma a parlour take zaune, yasan dole Musa mai shara ya shiga cikin.
A karo na ba adadi ya kuma jan tsaki, take ya buɗe idanuna, sai aka yi sa'a suka sauka akan littafin jiya, take ya tuna ya hangenta ɗazu. Bayan ya ba da umarnin da a taura ta. Ta shiga a gabansa ta tsaya tana ɗan tsugunna mai kai, tare da basa wani paper. Amsa ya yi yana mai karantawa.
“Assalamu alaikum, sir good morning, I'm sorry, jiya na yi mistake, ba wannan book ya dace na dauko ba, fatan ba'a duba ba?.” sai ya ɗago ya kalleta yana ɗaga mata kai. Sannan ya ba ta wancan, tare da amsa ɗayan bayan ya duba ya ce.
“Sa'adatu jibreel.. Right?." Sai ta ɗaga mai kai. Bayan ya kuma ɗan ɗau lokaci ya ce.
“Gobe ki dawo akwai interview, wanda da kinci zai fara aiki Monday.” wani irin farin cikin ne ya kamata, take ta kalla gefe guda da yi sujuddur-shukrh, sannan ta ɗago tana mai godiya da hannu har ta fice.
Samun kansa ya yi da murmushi, sannan ya kalla CCTV cameran gidan Tv, sai ya tsinci kansa da bin ta da idanu, duk in da ta yi, har ta bar gidan Tvn. A ransa ya ke aiyana “Yanzu wannan halittan dake naɗe cikin shigar mutum, ta taɓamin zuciya....... Anya matar aure ce ma?." Ganin babu mai bashi amsa, ya sa ya fita dan duba ma'aika.
Ɓangaren masu ɗauko rahoto ya yi, komai na tafiya dai-dai, yanzu abin da yake hari shine, gasar da aka sanar za'a yi a gaba Nigeria, akan ɗauko rahotonni, kuma nan da wata uku ne, sannan Goodness Tv yana ɗaya daga cikin gidan Tv goma da za'a yi wannan gasar da su. Gobe zai tantance masu tafiya dan mutum biyu kawai ya ke so. Yama san dole ya sanya Haidar, dan a kashi 100 na ci gaban gidan tv shi ya samo musu kashi 50, yaron akwai hazaƙa, kuma yana ji da shi, duk in da rahoto take to Haidar na wajen, shi yasa gidan Tvn su ya zama the best a Kaduna state.
“Sir Abubakar, Alhaji Banbo ya iso.” jin an kira sunan sa ya kalla yarinyar da ta yi magana, ita ma ɗaya daga cikin masu aikin gidan ne, dan dukka suna sanye riga mai tambarin gidan Tvn wato wasu na'urori na zamani, sannan an rubuta *GOODNESS TV* _taken mu ƴan cin mu_ .
Bayan ya ga Alhaji Banbo da za su yi hira da shi aka irin nasarorin da yake samu a cikin ɗan shekarau. Wani Senior shine suka gabatar da shirin shi yana gefe ne. Sai misalin 2:30 ya koma office.
Wayarsa ya ciro yana shiga contact gani 10 missed call, kuma dukka na Darling. Bin kiran ya yi, take ta ɗauka ta hau mai faɗa kaman wani yaronta.
“Ina ka ake wayan? Sai ai ta kiranka ba za ka ɗaga ba, kana can kana washe ma ƴamma haƙora koh?.” ji ya yi kaman ya jefar da wayan amma sai ya ce.
“Dear da zan shiga masjeed ne na sanya wayar a mute......”
“Ya isheni, ka dai kula, kuma wallahi in ka kalla wata mace ban yafe ba.” ƙit ta kashe wayan. Dafe kansa ya yi, shi dai kullum wannan Darling ɗin neman haukata sa take. Take kuma ya ɗauki wayan yana shiga Gallery lock, bayan ya fito da shi daga freezer (wani wajen na ɓoye app) take ya cire password ɗin yana kallon hotunan wajen. Murmushi ne ya ƙwace mai, dan jiya da zai wuce sai da ya yi snapping littafin dukka, dan har ga Allah so yake ya karanta komai dake ciki.............
*ABUJA*
Bayan Ukasha ya fito daga wanka, shima Umar ya shiga, ya jima yana gasa jiki sannan ya fito, bayan sun sanya kayan barci, tare suka ci abincin da suka yi order sannan suka kwanta suna hira. Wayan Ukasha ne ya yi ƙara ganin. Amira ya sa ya kira bayan na ta ya katse. Suna gaisawa ta ce.
“Masoyi, wai yaushe burin na ka zai cika ne?, Baba ya ce ka turo gobe, in ya wuce zai ba wa ɗan uwansa ni, kuma ni kai na ke so." Shuru ya yi yana kallon Umar sai ya ce mata.
“1mnt." Kafin ta ce wani abu, ya kashe.
“Umar menene abin yi?.”
“Ai tin ba yau ba na ce maka, ka aure su daban-daban, amma kaƙi ji.”
“A'a, na haƙura da ita ɗin."
“Amma......” sai kuma Umar ya yi shuru, dan wallahi ya sha wahala kafin Amira ta amince da kyar domin kuwa yarinya ciwon da samun ta yana wahala gashi kuma a yau zai yi missing na wannan yarinyar, yana ji yana faɗa mata cewa Allah ya haɗa kowa da rabonsa ya gode da kulawar ta a garesa, idanuwansa a kulle take ya faɗa duniyar tunani na rayuwarsa.
_Na faɗa muku nima ina da wani buri wanda a kullum da shi nake kwana nake tashi a kuma ba komai bane burin illa a kan wata yarinya, za ku yi mamaki ku ji na ce wata yarinya!, sai dai nawa ba irin Ukasha ba ne, burina kan lamba kwara ɗaya tak, nake shan wahala, na kasa gano ta bari dai in baku taƙaitaccen labarin shekaru biyu baya, a wata rana laraba bayan na dawo gida sai na koma office saboda na yi mantuwa. Bayan na juyo, ina cikin tafiya bayan na jiyo, ina cikin tafiya sa na faka daga gefen hanya saboda hadari ya haɗu sosai kuma ban son tafiya ana ruwan sama, wata kyakkyawan yarinya na gani daga gefe guda, mayyuwa hadarin ne ya tsai da ita, cikin uniform ɗin islamiyya take, maybe mota take jira amma fa hadari ya haɗu sosai kuma gaba ake da saukar da ruwa yasa na buɗe motan ina mata magana da ta shigo, ta jima tana tunanin shigowan, sai daga baya ta shigo cikin zama dai tana cemin ta gode, ɗaga mata kai kawai nayi take kuwa aka tsuge da wani ruwa mai matuƙar kara da karfi, da iska an jima ana zubga wannan ruwan daga bisani ya dan sassauta sa'an nan na tambayeta ina son narage mata hanya, ta ƙi yadda wai za ta sauka a nan da muka dinga musu har dai ta iya mun kwatancen in da za ta sauka ba musu na ku dauki hanya zuwa in da ta mun kwatance, za ta fita kenan na buɗe bakina na ce mata, baki faɗa mun sunanki ba ƴam mata sai ta yi murmushi sa'an nan ta ce mun sunan mai tsaɗa ne. sai na ce to Dan Allah ban number wayanki ba musu ta dauko pepper ta bani numban tare da ficewa cikin farin ciki da murna na dawo gida na daukefan zan kira number sai naga lambar bai cika ba nai mamaki sosai ganin number guda goma ne kasa kuma ta rubuta ka nemi ɗayan da kanka sai ka kirani to fa in faɗa muku daga wannan ranar nake ta faman haɗa lambobi dan in kira ta sai dai kullum cikin rashin sa'a nake har yau ban samu ba shekara biyu kenan ban santa ba ba za su sunanta ba kuma na koma in da na sauke ta a mota an ce ba wanda ya santa a unguwar. Har na fara fidda rai amma ina ta bincike a kan lambobin, amma har yau jiya i yau.
“ Mun gama magana, Umar ni yanzu a lokaci guda nake son samunsu.” Shiru umar ya yi kamar yana bacci shima ya kwanta yana mai tunanin yaushe wannan burin nasa zai cika, ya haɗa su a lokaci ɗaya kuma har ga Allah ba zai ɓoye ma kowa ba, domin shi auren gaskiya zai yi ba na yaudara ba............
END.
> Tab wannan shine Buri kuwa, ko na ce Hasashen amma agaishe dukkan fa. 🙄
🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny. by *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*
Page1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣
*KANO*
Bayan ta isa gida, ta tadda ƙanwar mahaifiyar ta ta zo, da yake a nan take ita ma, ta yi tafiya ne zuwa Abuja dan kasuwancin ta, business take yi kuma ita ke rufa musu asiri kamar yadda suka rufa mata ita ma, domin mijinta ya rasu, kuma ba ta haihuba, danginsa suna ƙi ba ta komai, shine ta dawo gidan na su.
“Na yi kewarki.” ta faɗa amma ta hannuwa, matar ta fahimta sai ta rungume Ameeratulkhairi ɗin tana faɗin.
“Ni ma haka, wallahi duk lokacin da na kalle ki, sai na ji wani tausayinki na taso min, insha Allah maƙiyanki sai dai su mutu, sun rabaki da abin da ya ke na ki, wanda Allah ma ya baki suna so su ƙwace.”
“Ke dai bari, yanzu haka daga gidan Tvn take, wai za ta yi ɓangaren ɗauko rahoto.”
“Mubarta, idan suna tsammanin ta nakasa kenan to akwai wani baiwar ai. Ƴata ko ina ne ni zan tsaya miki sai dai karki kuskura duk rintsi ki bayya wa duniya jikinki, hatta fuskarki bansan ta bayya wa kowa.” Ameeratulkhair ta ɗaga mata kai tana mai ɗauko abinci dan yunwa take ji, farin ciki ne fal ranta dan tana da yaƙinin wannan ƙyakkawan bai karanta littafin ta ba.
“Yanzu wannan ne ake nuna kishinsa haka, tab ni kuma sam bai mun ba......uhm shan koko kwanciyan rai.” ta faɗa a zuciyarta dan tina matar da ta kira C.E.O, shi kuma har da rawar jiki ana ce mata Darling. Murmushi take tana mai bar wannan tunanin a cikin ranta........
Babu page ɗin da ya tsaya sai *Zuciyata* , murmushi ya saki yana mai fara karantawa.
“Ban tsammanin zan yi aure a rayuwata amma idan har zanyi, ina buƙatar don wasu abubuwa akan mijin. Bayan ilimi, nagarta, hali mai ƙyau, akwai wasu abubwan da na ke so. Misali Namiji mai suna Namiji, natsana Mata-maza, ban san namiji ya zama kaman yaro, na juya sa yadda na ke so, a'a na fison namiji mai izza, mai cika ido, mai zafi, mai ƙarfi (ba wai dan mu yi faɗa ba, dan in na taro faɗa ina da shi.)”
Ajiye wayan ya yi yana mai jin abubuwa biyu na taso mai, na farko tamkar da shi take magana, kamar dai yadda Darling ke juyasa.
“Dama ni Mata-maza ne?.” ya tambaya kansa, wani zuciyar nasa ya ce masa 'Eh' tsaki ja yana mai miƙa wa, ta ku biyu ya yi sai ya tsaya cak, yana duban jikinsa, ko zai ga duk abin take faɗa, ya jima a tsaye sannan ya ƙara karanta sauran layikan.
“Ƙyau, sanyi-sanyi, taushin murya, tafiya a natse, fara'a mai yawa, da kuma iya soyayya, *Duk bansan namiji da su* wallahi banso.” daga nan shafin ya ƙare, sai ya kasa motsi, dan da fari komai ta faɗa, sai ya auna kuma yaga yana dashi amma at end wai ta tsana hakan.
“To ya take son Namiji?.” ya tambaya kansa, dan akwai aikin da zai yi da ya zauna karanta shafin gaba, ɗan uwan wannan.
*ABUJA*
Washegari tare suka je office, bayan sun shiga kowa ya shiga nasa office ɗin dan yin aiki, basu suka tashi ba sai misalin 6. Haka suka juyo dan dawowa gida, ta cikin motan ne, Ukasha dake gefe ya hanga wata budurwa tsaye daga tsallake tana siyan abu a sago, da yake utone ne, sai suka zagayo ta gafen da take, take yarinya ya bar shagon tare da shiga wani layi.
“Umar bi wancan yarinya.” ba musu ya karya kwanan motan tare da bin ta a hankali, wani gida ta shiga dan haka suka faka, take wani yaro ɗan saurayi ya fito daga ciki, da sauri Ukasha ya fito yana ma yaron magana. Bayan sun gaisa ya ce.
“Dan Allah yarinyar da ta shiga yanzu, kasanta?.”
“Eh yayata ce.”
“Ma sha Allah, in ba damuwa ina son na ɗan tambayeka a kanta.” bayan saurayin da ba zai wuce 17yrs ba ya ɗaga mai kai sannan Ukasha ya dasa magana.
“Ya sunanta? Kuma dan Allah an mata miji ne?.”
“Sunanta Fillo, ko ka ce Fatima, da yanzu an yi auren amma aka fasa saboda ko kwanji ne, ko menene.... Na dai manta.” sai ya ɗan yi murmushi, yana maimaita sunanta Fillo, ba ƙyarya daga nesa ya hangi haksenta, kuma ga wannan ƙanin nata shima fari ne.
“Ka mana sallama da ita.” bayan yaron ya shiga sai can ya fito tare da faɗin.
“Ta ce sai ka fara samun Baba am(Baba), in ya ba ku izini sai ta fito.” number Baba am ya amsa tare da wuce wa.
“To Allah ya sa, munyi da cen ɗaya, dan ga alamu, akwai tarbiyya a gidan.” Umar ya faɗa yana fita daga layin, shi kuma Ukasha yana ta maimaita sunan ta *Fillo* .
*****Omo ta siyo, dan haka wanke-wanke ta shiga yi, ko da ƙaninta ya faɗa mata wasu na neman ta sai ta mai magana cikin fillanci.
“Kace su nema Baba am, in ya amince to.” aikinta ta ci gaba da yi, can sai ya dawo yana murna an bashi dubi biyar. Bafullatanar da ke wanke-wanke ta kalla ƙaninta da suke kama da juna sosai, kafin ta ce komai sai ga wata mata ta fito tana magana da fillancin.
“Ban kuɗin.” yaron ya kalleta tare da juyawa ya fice, yana ji tana kiran sunan sa 'Moddi' amma ya shareta. Budurwa da ba za ta wuce shekara 20 ba ta yi murmush. Take ta wani haska, dan a lokacin na mata kallon tsab. Ƙyaƙƙyawace ajin farko, tana haske mai sosai, sannan ga uban hanci ma sha Allah, duk da ta ɗauka ɗan kwalli amma gashin mai uban tsayi ya sauka har gadon baya.
“Dada am (Mama) ya gudu ai, kinsan Moddi da son kuɗi.”
“Zai dawo ai.” matar ta wuja ta koma ciki. Su huɗu suke rayuwa, Ita Fillo, Dada am wato mama amma ba ita ga haifesu, mahaifiyarsu ta rasu, ta haihu amma yaron ya ɓace tin yana ƙarami, sai Baba am.
Alhamdulillah domin suna rayuwa cikin ni'imar Allah, ba sa samun matsala da Dada am, domin Fillo yarinya ce natsatstsa shuru-shuru. Da dai shiga wani hali sosai da aka fasa aurenta da wani da take mutuwar so, saboda ƙwajin jini dukka 'AS' ne, daga lokacin ta ɗaura aniyar ba za ta ƙara soyayya ba sai bayan ta yi aure, da faruwan al'amarin wata na uku kenan, sannan kusan kullum sai anyi sallama da ita amma ba ta fita sam. Sai ta ce su nema Baba am.................
*KADUNA*
Su uku ne suke zaune suna raha kwanin sha'awa, sam babu mai damuwa a cikin, dan a yanzu suka ƙara tabbatar da Allah yana matuƙar ƙyaunarsu. A yanzu I.B ya riga ya rikita Mymoon da zazzafar soyayyarsa. Yadda kasan asiri koma ya ce sai ta yi, domin kuwa ya iya sarrafa mace fiye da lissafi, hatta mota ta mallaka mai. Shi dai yana cikin alheri dumu-dumu. Sun zama wasu manyan mutane, dan ko su Shamo suna jan kuɗi ba wasa suna target ɗin su mallakar mota. A dai-dai lokacin Abbas ya dawo daga garaji dan alhamdulillah yanzu yana samu ba laifi, wata rana dubu uku ko biyu. Kuma