Showing 12001 words to 14403 words out of 14403 words

Chapter 5 - HASASHE KO BURI Hausa Novels by Pretty SK.txt

22 Sep 2025

589

yana jin daɗi in ya samu, kuma yana fatan nan gaba ya fi haka dan haɗama Merry lefe. Bai manta ba a lokacin da ya faɗan masu Abdul ba, dariya suka sa mai suna ganin wautarsa ƙarara amma ya share su dan shi yasan mai ya taka, kuma ya dogara ga Allah.

“Assalamu Alaikum.” suka haɗa baki suna amsawa. Shamo ne ya kalla kayan jikin Abbas ya yi murmushi yana faɗin.

“Aboki, kana wahalar da kanka wallahi, dan Allah ji yadda ka kamo duk ka yi ɓaki ma........... Ka bar wahala Merry nasan za ta taimaka maka amma kai dan aci da Gumi ka ƙi......”

“Shamo bar ɓata miyanka, kasan Abbas, in ya faɗa abu baya sauyawan mu dai mu tayasa da addu'a. Ga wannan wallahi bansan ganinka cikin kayan nan, kuma wannan aikin.....” da sauri Abbas ya fizge rigar da I.B ke miƙa mai yana faɗin.

“Good da ka san ban sauya ra'ayi. Kuma in addu'a ce ku zan yi ma wa.”

“Abbas wallahi muna sonka, bamu son ganin kana aikin mai wahala, kafimu haske amma jibi yadda ka koma, mukan sai wani fresh muke yi.” sai dai ya kalla Abdul da ƙyau, kaman zai ce abu amma ya fasa tare da shigewa bayi dan yin wanka. Yasani ba sai sun faɗa mai ba, suna sonsa sosai, kuma ba sa son aikin da yake yi, suna yawan faɗa mai, su za su nema amma shi ya wuta sai suba shi amma ya ƙi sam. Kuma ba ƙarya wani fresh suke dan kuwa ba ƙaramin daɗi suke ci ba. Haka zai dawo ya tadda uban leda tsire, balango, drinks, marada kuwa hmmmm, sannan komai suka ci sai sun aje mai, wani lokacin ya ci in sun matsa. Bayan ya fito wanka ya samu suna shirya wa tare da cika ɗakin da ƙamshi.

“Ka shirya mu ajeka a ƙofar gidan su Merry.” I.B ya faɗa yana taje ɗan gemunsa. Dayake yana son zuwa, aikuwa suka shirya dukkansu. Sun yi ƙyau kaman za su wani taro, Abbas ne ya zura wata jallabiyarsa, sun mai tsiya da ya cire amma ya yi banza da su. Mota suka hau, a hanya Abbas ya ce su tsaya bayan Abdul ya faka dan duk sun iya mota hatta Abbas ya iya. Bai jima ba ya dawo riƙe da leda baki.

“Mutumina me aka siyo ne?.”

“Merry na son awara shine na siya mata.” dariya suka kwashe suna kallon Abbas da hankalinsa ƙwance kuma ya yi banza da su. Shamo da ke gefensa ya dafa kafaɗarsa yana faɗin.

“Abbas, da baka siya ba, taya mace kaman Merry ta ci awaran bakin hanya.”

“Hmmmm za ta ci.” ya faɗa da confidence ɗin sa dan yasan duk abin da ya ba ta cike da nishaɗi yake amsa kuma bai ta ɓa ganin sauyin yanayin a fuskarta ba, shiyasa ko ba yawa yake siya mata abu in dai yasan tana so. Yanzu haka awaran dari biyar ya siya mata............✍️
END.

> Tab akwai ƙura fa, hmmmmm mudai na mu ido, 🥱🙄🙄🙄🙄🙄



🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕


https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

PAGE1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣


*ABUJA*


Misalin ƙarfe 8:30pm, Ukasha ya kira wannan numbern, sai da ya yi kira uku tukun aka ɗauka, wani dakakkiyar murya ce da mai amsakuwa a cikin kunnansa, bayan sun gaisa Ukasha da duk da bai ga mutum ya mai ƙwarji ya ce.

“Baba am, ɗazu ne na ga Fillo, shine na nemi ta fito na gabatar da kaina gareta, sai ta aiko sai na fara magana da kai, shine na ke neman izini.” yana ji mutum ya ja dogon numfashi.


Shigowarsa kenan ya zauna a parlour, Kallon Fillo ya yi take ci abinci tana kallo, shi ya ƙosa ya aurar da ita, saboda ya gaji, a ƙalla a yau wannan shine na shida a kiransa.

“Gobe ka zo na ganka.” take ya mai kwantance tare kashe bayan dan ko godiyan Ukashan bai amsa ba. Shuru ya yi dan a yanzu Fillo ce damuwansa akan wanda zai aura mata, ba wai ba ta masu bin ta bane, sai dai da yawa sha'awarta ke kawo su, kuma yana gane haka, so yake Allah ya haɗa shi da wanda zai ya amsa da ya mai da amanar Allah zuwa garesa. Babban abin farin cikin shine Fillo duk abin da suka za ɓa mata ba musu shi take accepting.

“Bingel am ( Ƴata ko ɗana) waye aka kuma ba wa numberta?.” da ya faɗa da Hausa dan shi ya ƙware da Hausa sosai.

“Baba am, bansan shi ba nikam.” ta mai da mai da fillanci.

“Voɗi ( yayi kyau).” take Dada an ta fito dan ba tasan ya shigo ba.

“Jabɓama ( sannu dazuwa), Awarti?( Ka dawo?).” ya ɗaga mata kai. Sai ta nufa kitchen Dan haɗo mai abinci.



*Barcin ya ɗauke da da wuri, shi kam Umar ya dage, sai haɗa numbers yake amma number ɗaya yake so ya kuma jarrabawa sai dai daga kira an ɗaga ya yi magana an kuma kashewa, yanzu ya yi kira na huɗu kenan, take na biyar na shiga aka ɗauka.

“Assalamu Alaikum”

“Uban wa ke magana." Muryan gardi ya dakeesa. Sai ya ma ze dan ba yau ya saba kiran maza ba a haɗe-haɗen number.

“Ka ya ƙuri, mistake ne, wata nake nema.”

“Ka kira number mata ta kace mistake ne, dama zargi ta na ke yi, to Allah ya tona muku asiriiiii.” ƙit Umar ya kashe kiran tare da sanya wayar a fightmood tare da kwanciya yana faɗin.

“Zargin uban me, ka mannamin hauka.” daga haka ya shafa addu'ar barcin yana rufa da duvet................





*KADUNA*



A bakin get ɗin gidan su Muheey suka faka, wannan shine karo na biyu da ya zo, bayan sun ɗan jima sai ga ta tafito cikin wata arniyar less maroon, ta yi mugun ƙyau haka kuma sai wal-wal take yi, tana isowa ta sakar mai murmushi tana mai bismillah da ya shiga. A cikin motan suke hanke yadda ake kallon love, sannan suka riga mota, a ɗayan layin suka sauke Abbas, dan ko kusa da gidan ba su ƙarasa ba saboda hango masu bindiga. Dariya Abbas ya musu sanan ya sauka, su kuma suka bar area dan a ɗan kwai nisa tsakanin su da Mymoon.

Mymoon duk ta fi nisa dan haka still, Abdul ya fara sauka sannan I.B ya amsa tuƙin motarsa ya nufi gidan su Mymoon.


A waje ya faka, sannan ya ɗan ɗau lokaci sai ga ta tafito cikin wasu riga ta da wando Pakistan, sai babban gyalen da ta yafa. Ta haɗe rai sosai. Take ya sausauta nishaɗinsa, amma ya danne bai tambayeta ba. Shiga babban gidan ya yi, a wannan Gazibon ta kuma saukansa, ba ƙarya ko ina cike yake da abinci iri-iri, tare suka zauna tana mai ce mai tana zuwa, sannan ta fice.




*Shamo*

A falo ta sauke, yana ta bin ko ina da kallon dan yau ya fara shiga ciki, fatansa shima Allah ya ba shi ikon mallakan irin gidan nan. Abinci ta jera mai sannan ta zauna suna hira, abincin ya ci kaɗan yana so ya tambayeke ina sauran ƴan gidan amma ya yi shuru. Hira suka sha sosai, hankalin su a kwance.



*Abdul*

Kuwa yaga ƙauna, domin Yayar Ma'esh da kanta ta haɗa mai lafiyayyen abinci, sannan ya ci, ya ji daɗin yadda suka ƙarɓe sa, hatta Ruma ta dinga hira dashi kaman ta san sa. Bayan sun gama, a falon suka zauna, su biyu sai soyayya suke sha, ga Ma'esh akwai iya narka mutu, dan ta iya soyayya balle ta so mutum da zuciya ɗaya.


*Abbas*

Wayanta ya kira sannan ta fito tare da tarensa. Tsayawa ya yi yana bin ta da kallo, hijab ne ta sanya har ƙasa, fuskarta babu komai sai wani ƙwarji da sheƙi da suke mai. A tsakar gidan ya tsaya dan ya ƙi yadda su shiga ciki, har sai da ranta ya soma ɓa ci sai ya ce.

“Ki bari idan zan wuce.” daga haka suka zauna daga gefan gafan garden ɗin. Ledan hannunsa ya miƙa mata, ba musu ta amsa tana mai buɗe wa. Sai kuma ta miƙa mai tana barin wajen da sauri. Da idanu ya bi ta dan bai fahimci yanayin ta ba. Har ya miƙa sai ga ta ta dawo, fuskarta ya kalla sai yaga tana murmushi hakan ya sa ya ɗan saki ransa.

“Na za ci amai kika je yi, ai sai kice min kina zuwa, da wucewa zan yi.”

“Ayya My Ƙwanƙwaso.” murmushi ya ɗanyi sai ta ce.

“Ga abin da na je ɗaukowa nan.” sai ya hannunta da ta fito da shi daga hijab. Plate ne da sai goran ruwa da wani ɗan roba.

“Zuba min, wallahi yunwa nake ji, yau na kasa cin komai, gaskiya na gode sosai da sosai." Ta faɗa, yana gama juye mata awaran, sannan ta zazzaga yaji akai dan shine a roban.

“Malam ɗan kalla can zan ci abinci, kuma sai dai kai haƙuri dan ko bismillah bazan yi ma ba.” dariya ya yi yana mai kallon gefe ita kam ta hau ci tana ta santi. Wani farin ciki ne ya kamashi tare da mamaye zuciyarsa. Har ga Allah ba zai iya misalta yadda Merry take a cikin zuciyarsa dan ita ta daban ce......



*KANO*


Ita ka ɗai ce zaune a wannan ƙaton parlour tana kallon tv, take wayarta ta fara ringing, ganin yayarta ya sanya ta ɗauka tana kai kunni. Bayan sun gaisa sai ta cikin wayar ta ce.

“Mama ta ce tana son ganin ki, yaushe za ki zo, ina so samune ki zo gobe idan Abubakar zai barki.”

“Hmmmm yama isa ya hanani zuwa!, Ko a yanzu na so sai ki ganni a Abuja......”

“Rahma ke sam ba kisan haƙƙin aure ba ko? Ina raba ki da azabar Allah......” ita ta yi saurin katse ta.

“Aunty Aisha kenan, me na yi? Mallaka mijina ya yi, sannan na yi mai iyaka da duk mai son shiga tsakanin mu.”

“Har da danginsa?.”

“Ƙwarai da gaske, nifa duk wanda yake cikin zuciyarsa dole na rabasu, zuciyarsa danni kaɗai take bugawa.” take yayar ta kashe kiran, murmushi Darling ta yi tana gyara zaman. Sanye take cikin wani matsiyacin riga, dan da ita da babu duk ɗaya, sharashara ce, kuma iya gwiwa, gaba ɗaya dai rigar ba ta yi ba. A dai-dai lokacin Abubakar ya shigo. Gaba ɗaya hankalinta ta mai da a kansa, har ya iso in da take.

“Darling wannan kallo fa?.” sai ta miƙe tsaye tana girgiza kai tare da faɗin.

“Da zarar ka ci wannan gasar, za ka bar zuwa aiki, sai dai a sati ka leƙa sau ɗaya, amma daga nan za ka dinga aikin.” ta kai maganar da dukka gaskiyar ta.

“To shike nan, Allah ya sa mu ci.”

“Ameen, na ce ma ka rage yawan murmushi, banso yanzu Allah ka ɗai yasan matan da suka kalleka.” ta faɗa tana jan tsaki sannan ta zare wayarsa dake ajiyu.

“In ka gama wankan ka zo ka amsa.” sai ya rintse idanusa yana mai dannar zuciyar sa, haka ya bar parlourn ta bi bayansa da ido. Tana maƙutar don Abubakar fiye da misali, kuma tana ji dan ita kaɗai aka yi sa har abada. Wayar babu password, haka ta gama bincike ta tsab sannan ta ajiye.

Wanka ya yi sannan ya sauya shiga yana sai sakin murmushi dan yasan ba za ta taɓa ganin in da ya ɓoye hoton littafin nan ba, kuma zumuɗi yake an jima ya ɗan duba ko shafi ɗaya ne.




*** Facebook take in da take kallon wata budurwa dake zaune tana koro rahoto, akan nan da wata uku za'a yi wannan gasar na gidan tv, yarinyar kawai take kallo cike da burgewa, take wasu hawaye suka gangaro daga idanunta, ta sanya hannu ta share, abubuwa da yawa suke mata yawo a ciki, da sauri ta ɗauki biri tare da buɗe littafin amma sai ta rufe saboda ta rubuta shi. A cikin zuciyarta take faɗin.

“Allah ka sakamin, Allah ka isar min, kamin sakayya.....” sai kuka ya ƙwace mata amma babu sauti. Haka ta shafa tsawon dare gaban Allah tana kuka. Akan daddumar barcin ya yi gaba da ita.



**Barci ne ya yi gaba da Darling, sai a lokacin ya samu ya janye jikinsa a na ta, sannan ya miƙa yana mai da maɓallen rigarsa, sauka ya yi daga gadon yana barin ɗakin, ɗakinsa ya koma tare da ƙwanciya, yasan dole shi zai tashe ta, dan ta iya uban barci, kashe hasken ɗakin ya yi yana mai ƙwanciya tare da kunna wayar, har ga Allah in bai ga ragowar ɗaya shafin ba, bai jin zai iya barci, tsabar sa wa rai.

“Ina son naga Namiji mai cikan haiba, mai ɗan haɗe fuska, ba wai ba ya dariya ba amma ya zama mai tsaɗa ga kowa, sannan in yana tafiya ya zama ƙasa na amsawa, wato mai ƙarfi, bansan ya dinga slow ko wani tafiya a natse, no cike da izza da ƙarfi, sai kuma ya zama mai faɗin girji mai ɗauke da yalwaccen gashi, Ina son gemu mai yawa, sannan ko da yaushe cikin manyan kaya yake. Eh to irin wannan na ke so, amma Allah duk wanda kaban, sai dai nasan babu mai auren bebeyi duk da ba'a haka ka yi ni ba, mugunta ne irin na wasu ɗan Adam.” daga haka shafin ya ƙare, shuru ya yi yana mai kuma karantawa sannan ya furzar da iska daga bakinsa. Wani yanayi yake ji a cikin zuciyarsa na daban haka, sai ya ajiye wayan yana kulle idanun, take ya buɗe dan yarinyar nan yake hange cikin wannan shigar, murmushi ya saki yana mai jan duvet..............✍️
END.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕

📢 *ANNOUNCEMENT!*

Alhamdulillah! An kammala *FREE PAGE* na littafin *HASASHE KO BURI* ✅

Ga masu son ci gaba da karanta cikakken labarin, yanzu *complete book* yana nan akan *₦300 kacal*!

⏳ Kada ku bari a ba ku labari – ku mallaki naku yau!

_Taku kullum, PRETTYN JAJIRTATTU ✍️🦋_

Ga yadda zaku biya ku samu littafin *HASASHE KO BURI* cikakke:

*Farashi:* ₦300
*Account:*
*Opay – Sakina Abdullahi*
*08126151523*

*Bayan biyan ku:*
Turo *screenshot* ko *shedar biyan ku* zuwa wannan lambar:
*07038436703 whatsApp*

_PRETTY SK CE_

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login