Showing 6001 words to 9000 words out of 14403 words
in ce.” A ƙawataccen parlour suka zauna, take muhibbat ta nufi wani ɗaki in da take ƙwana tana mai cire hijab ɗin ta, sannan ta zauna kan wani gado mai shegen ƙyau. Tana fatan Alhaji Ahmed kar ya dawo nan kusa, dan ko ya dawo baya fin sati ɗaya, yake koma wa aiki, in da a chine yake aiki a wani Company, yakanfi wata biyu a can. Ya auro ƴar uwarsa ce ya aje ta a wannnan layin, in da ya haɗa shegen gida, Mariya ba ta iya zama ita kaɗai a gidan kuma gashi su a salin ƴar Kebbi ne, shine Alhaji Ahmed ya nema da ɗaya daga cikin yaran Malam Yaƙin da a dinga ta ya Mariya kwana shine Muheey ta tare abinta, takan kwana biyu ba ta leƙaba, dan anan tana jin daɗin rayuwar gida kuma take fatan ta samu mijin kamann Alhaji Ahmed.
Parlour ta dawo ta zauna gefen Mariya. Mariya ba wata babba ba ce dan da kaɗan za ta girma Muheey.
“Aunty Mariya ina son na roƙe ki wani abu.” Muheey ta faɗa tana kallon Mariya. Ɗaga mata kai ta yi alaman ta na ji, take da dasa da faɗin.
“Kinsan group ɗina na school M-Ladies koh?.”
“Eh kina ban labarin su.”
“To dukka suna da mota, wallahi suna cinye wankan, kina yawon faɗa min ina da ƙyau da iya jan hankali namiji, to wallahi a school sai kana filawa, hatta wasu daga kayanki in nasa sai na je ina jin nakai sai na ga sun kereni." Ta kai maganar tana mai da idanunta ga tv, hannu Mariya ta sa tana dafe kafaɗarta.
“Wallahi Muheey, kina da ƙyau sosai, kuma insha Allah mai kuɗin dai za ki aura, yanzu dai ki bari zuwa gobe duk yadda muka yi da Alhaji, sai na faɗa miki, sai ki dinga aron motata tunda ni yanzu na bar zuwa aiki saboda ciwona.” takai maganar tana ɗan tari. Take tausayin Mariya ya kamata saboda ita sikila ce, yau lafiya gobe rashin lafiya a haka dai take lallaɓawa shi yasa tabar aikin da ta fara yi anan...........✍️
END.
🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
*Sadaukarwa*
_Na sadaukar da wannan shafin ne ga dukkan my followers 🙏, Allah ya bar ƙauna da soyayya, ina yin ku over 💃💃💃❤️ Kuna ƙarfin gwiwa ta._
*PAID BOOK* 🤭
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny. by *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*
Part 7️⃣⏩8️⃣
*ABUJA*
_____Sun jima suna tafiya a mota kafin Ukasha ya yi parking a gefen wani gida sai a lokacin ya buɗe baki ya ce.
“Common ƴam mata huɗu sun gagara ka samo min, ji bi wadda ka kai ni wajen ta last hmmmm.”
“Ukasha, kai fa kace mace ta kasance da abubuwa biyar na farko mai natsuwa, siririya, mai sakin fuska sannan wacce tsayinta kar ya wuce ƙirjinka, sannan mai addini. Amma ba ya maka duk wacce na kawo maka.”
“Kai ne ba ka iya tsaɓe ba sam, Murja - Bahaushiya, wata ƴar lukuta da ita, sam ba ta min ba.” Fita suka yi yana mai kiran wata number, bayan ya yi magana ya ce ma Umar.
“A facebook muka haɗu, kuma hotonta ya min shine na zo na ganta, Fulani ce.” kai kawai Umar ya ɗaga yana tsanar wanna burin na Ukasha.
Basu jima ba wata ta fito daga wanna gidan. Budurwa ce amma mai irin garin jikin nan dan za ka sa ci ta haihu ma, bayan sun gaisa, Umar ya shiga mota yana matse dariyarsa, domin kuwa wannna sam ba za ta yi ba, ta na da ƙiba sosai, haka kuma daga ganinta akwai rawar kai. Bai jima ba ya shigo motar tare da figarta da uban gudu.
“Malam ban shirya mutuwa ba.” Umar ya faɗa yana murmushi sai Ukasha ya ce.
“Wallahi ba haka hotan yake ba, gaskiya Umar ka ci gaba da neman min maybe na dace.” Haka suka ɗan yi hira har suka isa, wanda kusan dukkan hirar akan sauran ƴam matan ne.
Wani gida suka nufa, bayan sun isa, a parlour Suka zauna sai ga wata mata ta fito daga ɗaya daga cikin rooms ɗin ciki. A kallo ɗaya za ka ga kamarsu da Umar, gaishe ta suka yi, ta amsa tana mai zama.
“Kun dawo lafiya?.”
“Alhamdulillah Hajja." Ukasha ya faɗa, bayan sun ɗan jima suka bar ɗakin, wani ɓangaren suka nufa, ba laifi gidan ya haɗu, dan wannan ma gidan Ukasha ne ya dawo da abokinsa tare da iyayensu gidan, tare suke rayuwa dan shi kaɗai ke rayuwarsa.
Zama Umar ya yi akan bed ɗin su, shi kuma Ukasha ya nufa toilet dan yin wanka; har lokacin Umar bai bar dariya ba, dan Ukasha ya shaƙa sosai. A hankali ya ce.
“Allah ka nunamin ranar da burin Ukasha zai cika..... Hmmmm akwai drama sosai." Sai ya ɗan haɗe rai tare lumshe idanunsa yana faɗi a cikin ransa.
“Ni kaina ina da wani Buri. Wanda shine ya hanani aure, ya hanani kula kowace mace, hmmmm wani lokacin ni kaina burin nawa na ban dariya, amma ina yawon hasashen lokaci na nan zuwa da zan cimma wannan burin nawa. Za ku yi mamaki idan na faɗa muku nawa burin domin ba sauƙin sam.”..........
*KADUNA*
Su huɗu ke tafiya cikin ƙananun kaya masu ƙyau, duk da na Abbas bai kai na su ba domin shi na sa ne, amma su renting suka yi, daga class suke dan haka suka nufi in da suka tabbar da M-Ladies suna can. A hanya Shamo ya ke faɗin.
“Ku zauna wasa, ni harna shiga ran Muheey, domin jiya munsha love, gashi yau da wata arniyar mota na ga ta shigo.”
“Ba ka da wasa fa, ni kam ina ɗan shakka Mymoon ne, da na kira ta ko ma ta text."
“Ka dai zauna wasa, ai yi ba kai, dan ni ma na yi ma Ma'esh magana, sai dai ba reply amma nasan za ta yi.” dariya suka dan yi Shamo na kallon Abbas ya ce.
“Kai fa?.”
“Tukuna dai.” daga haka suka hangesu zaune suna ɗan hira cikin raha. Ba ƙyarya sun haɗu iya haɗawa, sannan kowacce da irin ƙyauwun da Allah ya yi mata, kuma kowa akwai abin da ta fi wata.
Bayan sun isa suka yi musu sallama, da yake yau Mymoon na cikin farin ciki sai ba ta ce su tashi ba. Amsa sallamar suka yi, tana mai jin annashuwa a cikin ranta domin Ma'esh da Muheey sun yi motoci, kuma har ta tsara class party da zasu yi a yau, dan tasa ansanar da kowa ya ɗan jinkirta.
“In badamuwa zan iya magana da ke, Maryam.” suka tsinkayi Abbas ya faɗa, sai dai ba musu Maryam ta miƙa tana gyara gyalenta, ɗan gefe guda suka zauna sai Abbas ya ce.
“I'm sorry in na dameki......”
“No karka damu.” ta faɗa tana faɗaɗa murmushin da ke kan fuskarta.
“Maryam, bansani ko za ki fahimci ni, domin ni ba maye ɗin ki bane, kuma ta yu kimin wata fassara, a gaskiya tun dana shigo school ɗin nan na ganki, na ji kin shiga rai na. Hmmmmm ina ta so na bayya na miki duk da ina da numbers ɗin ki amma ina jin nauyi, yanzu haka na faɗa miki ne saboda ki bayyani eh ko a'a duk da nasan a'a ne, in na ji daga gunki zan maybe na shiga hankalina........” dafiyar da Maryam ta yi shine ya katse mai maganar.
“Abbas, ci gaba ina jinka.” daga haka ya dasa yana ji a ransa harya haƙura ma.
“Idan maganata ba ta miki ba, to dan Allah ki ya ƙuri.” sai ya miƙe take ta ce.
“Zauna ka ji.” ba musu ya zauna sannan ta dasa da ce.
“Nasan kana sona tin ba yauba, nakan gane mai ƙyauta daga cikin idanun mutum. Hulaƙanta mutum baya tsarani na, sai dai zan ma albishir da cewa kana birge Merry tin ba yau ba, amma ka dage dan samun soyyayarta, kuma na zallar gaskiya.” daga haka ta barshi zaune baki buɗe, wajen Ladies ta koma in da ta tarda suna hira ne da su Shamo. Zama ta yi aka da sa da ita.
Su da suke da confidence sai yau suka musu kwarjini, amma Abbas gashi har ya isar da na sa saƙon zuciyar zuwa ga burin ransa.
Da misalin 2:30pm suka sha shagali, Maymoon ta yi wasan kuɗin, domin musamman aka yi order abinci mai rai da lafiya, aka kawo drinks da wasu abubuwan. A na cikin shagalin a filin ball in da aka musu decorating ya yi ƙyau. Hatta case Muheey da Ma'esh sun yanka, Wayar Mymoon ne ya hau ringing, ganin mahaifiyarta sai ta amsa tana fara tafiya saboda hayaniya. Kusa da department ɗin su ta tsaya tana faɗin.
“Alright, thank you so much my dear.” ta faɗa tana kissing wayar, tana juyowa ta ga I.B tsaye ya haɗa hannaye waje ɗaya.
“Lafiya?.” sai ya kalleta tare da faɗin.
“Wannan adalci ne?, A ce ina kiyon abin da ya zama mallakina sai na fahimci wani yana so ya siya.” cikin rashin gane maganarsa ta ce.
“Ka ce mai ba na siyarwa ba ne, ko ya jira ina zaka siyar sai ya siya.”
“Bazan ta ɓa sai da wa ba.” sai ta fara tafiya, da yake ta gefe ne ba wani mutane sai ya shamma ce ta ya tsugunna gabanta tare da miƙa mata flawerr mai launin ja da green.
“Wannan ba iya flawers ba ce, zuciya ta ce, dan Allah ki amsa tare da mai muhalli a cikin zuciyaki.” amsa ta yi sai ta ce.
“Da gaske wannan zuciyar ka ne?.” ya ɗaga mata kai, sai ta saki murmushin mugunta sannan ta saki flawers take ta sanya ƙafarsa ta murje a jikin korayen ƙananan abubuwa dake tsirowa.
Take I.B ya dafe zuciyarsa bai damu ba zuɓe ƙasa, dan shi a rayuwarsa yana son fina-finan soyayya to ya ƙare ta wannan fannin. Sai dai me faɗin da ya yi yana dafe zuciya, ya sa ci za ta yo kansa ne yana da gudu tana mai cillar da komai da ke hannunsa tare da ɗagoshi tana mai kalamai masu daɗi. Sai dai mai da ƙasan idanunsa ya ke kallon fuskarta, dariya ta yi sannan ta kaɗa kai ta yi gaba, ta barshi ƙwace dafe da zuciya................
*KANO*
* Shafi na gaba ya buɗe tare da bin zanen da aka rubuta da *SIRRI* , mamaki ne ya kamasa sannan ya kulle littafin yana faɗin.
“Anya wannan matar ba ta yi mistake ba, oho dai ni kam ina son na karanta ko dan handwriting ɗin ciki.” sai ya kuma buɗe wa, tare da fara karantawa.
_Wannan littafin nawa ne Ni kaɗai, sirrina ne a ciki. Sunana Ameeratulkhairi, wato Fatima Abdullahi, na ta so cikin gata da jin daɗi, sai dai rayuwar bai min tsayi ba, haka kuma ban karaya ba na dage na jure. Hmmmm ni ina mamaki da wannan duniyar amma ina alfahari da cewa gidan biyu, akwai nan akwai can. Ina ma kaina nasiha da na dinga tina wa da wannan, gaskiya ina son kai na, kalla-kalla, uhmmm Bara na yi shafi-shafi dan sauyaƙe ma kaina_
Ƙarshen shafin kenan, sai ya furzar da iskan baki yana faɗin.
“Anya ba mistake ba ne!.” buɗe gana ɗaya shafin ya yi kowanne da Tittle, Amma akan samu shafi huɗu-biyar kafin wani heading ɗin. na farko *Matsalata* , *Damuwata* , *Mafarkina* , *Burina* *Hashashena* *Farin cikina* sai na ƙarshe *Zuciyata* . Tashi ya yi ya zauna yana mai mamakin ko dan ita ba ta magana ne take rubuce-rubuce haka. Take ya buɗe sannna ya nufa *Burina*.
*BURINA*
_Zama ƴar jarida mai ɗaukan rahotonni, na so a ce mai jawabi ce sai dai matsalata ta rashin magana. Sai na sauya burin da zama mai ɗaukan rahotonni guri-guri, na dage sosai na yi karatu duk dan haka. Allah ka cika min burina, dana dinga yawo a duniya ina ɗauko rahotonni_ sai ta yi zanen hannu. Bai san murmushi ya ƙwace mai sai ya kulle yana ajiyewa akan desk tare da nufan cikin Tv station ɗin.....
Sai yamma ya ta nufi gidansa dake G.R.A, Wani tsararren gida ya shiga, sannna ya fama motarsa Ferari ya nufa aljanar duniyarsa. Ƙofar mai numfashi ne, yana kusanto ta buɗe dan haka ya shiga ƙawataccen parlour wanda ya haɗu iya haɗuwa. Tsayawa muku bayanin zuɓin parlour ɓa ta lokaci ne. Tsayawa ya yi daga in da yake yana kallo macen dake saukowa daga stairs tana taƙu tare da girgiza, ba laifi ƴarinyar akwai ƙyau, a ƙalla ba za ta wuce 23yrs ba, ba fara ba ce tana da duhu, sannan tsiririya ce, sai dai akwai shape, dan rigar da ta sanya ya kamata sosai, tafiya take har ta ido gabansa yana kallonsa, ya fita tsayi sosai duk da tana sanye heal shoe ne. Akwai ta ƙananun ido amma akwai hanci mai tsini. Hancin ta kai jikin rigarsa ta shinahina sannan ta ɗago hannusa ta kalla sai kuma ta sanya yatsanta mai shengen ƙumba ta danna saitin zuciyarsa tana faɗin.
“Fatan babu wata ƴar iskan da ta shiga nan?.” shikan wanna tambaya ya ishesa a ƙalla daga aurensu 1ye kenan amma kullum ya dawo sai an gaba duba shi da tambayarsa.
“Darling Ni na kine ke kaɗai, har abada.” sai a lokacin ta saki murmushi sannan ta rungumesa ta na faɗin.
“Your welcome Baby.” hannunsa cikin nata suka jera har bedroom ɗin sa sannna ta fita tabar mai ɗakin dan ya yi wanka, dafe kansa ya yi yana zama gefan bed, yana mai dafe kansa. A hankali ya nufa restroom, sai da ya sakan ma kansa ruwan zafi tukun ya furta abin da ke mai yawo a cikin zuciyarsa.
“Waye Ni? Meyasa na ke ji kaman ba dai-dai ba! Kaman na manta abubuwa a cikin kaina, to ina dangi na suke?.” take ya ji yadda yake jin kaman an buga mai guduma, sai ya dafe kansa, yarasa da ya fara tunanin waye shi sai ya ji haka tare da ciwon kai. Da ƙyar ya kammala ya fito tare da sanya P.J-mask yana mai kallon kansa a mirrow ...............✍️
END.
> Ko a iya haka kunsan tafiyar akwai ƙura, shin su waye burinsu ko na ce hasahsensu zai cika. Yanzu muka soma, domin har yanzu wasu burin ba su gama bayyana mana ba. Still na ƙaƙu na ji na Umar😜.
🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
*DEDICATION*
I dedicate this page to my father, Malam Abdullahi Saleh. I pray that Allah fulfills all his needs, protects him for me, and grants him the fulfillment of his dreams.
*Allahumma Ameen.*
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny. by *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny. by *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*
Page9️⃣⏩🔟..
*KADUNA*
Misalin karfe huɗu suka kammala sa'an nan sukari loads tafiya suke suna yi ga tsakaninsu cikin raha da nishaɗi a bakin mota mai musu ka tsaya gaba dayansu suna tattaunawa r basu jinha ba kowa ya hau motansa tare da barin makaranta mai murna isa gidansu ka tadda mahaifinta ya zo tare da wani dansa na cikinsa bane amma kamar dansa yake domin a wajen sa yake rayuwa bayan ta zauna a falo suka gaisa sa'an nan ta nufi dakin ta na shiga ta watsa ruwa tare da gabatar da sallah dama tayi alwala kwanciya tayi akan gadon tana mai fidda wayanta da su ba adadi a kan screen din wayau murmushi kawai ya saki tana mai latsa massage din ner ce wa tasan na waye don haka shekarar ta saƙonnin soyayya da ta gani birjik wani tai dariya wani tai mamaki kira numban ya shiga wayanta ba musu ta ɗaga
Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu allah ya tabbata a garekiya ki kyakkyawa da ke haska taurari cikin dare, ina ji a cikin raina cikin koshin lafiya sai dai ni da masoyanki na nan kwance ina fama da ciwon zuciyar soyayyakin amsa soyayyata a gare ki don allah kin ji na san kina sauraro na nge laifinki ba don kinki furta komai domin wannan zazzaka muryar jaki bai kamata in jita-jita a alha kawai ba yanzu ki faɗa min nawa zan biya domin in saurari wannan dadin muryan naki ne kama da busassarewa
Ba shi da kyalkyali da dariya domin ya matukar bata dariya bata so yin magana ba amma dole ta amsa mai
Wannan iya zance haka to sannunka daga kokari tom ni kwanciya zanyi sai anjima da sauri ya katseta da cewar shin baki a kauna na ne don allah ki tausayawa marayan allah zuciya na kona yake min zaka da zaki taba saitin zuciya nakiji jwe tamkar ana yakin badalme na biyu tamkar kuma gidan mai ya ƙone da wuta wani gadadi da zafi duka nakeji a guri daya bawan allah kar ya mutu maraya
Ibrahim kenan ni ba komai yasa ban sakamaka fuska ba sabida inaji son ginamijiya da colleges guda biyu suke burge ni so kai naga kana da guda daya tana da maida hankali a karatu kuma gaskiya kina da interesting akan ka so na biyu ne gaskiya baka da shi inda ace kana da shi to gaskiya zamu iya bari ka so ni
Shine menene wannan?
Ina son ya zamana saurayi na ya dinga sanya manyan kaya kullum.”
An gama My Love ” dariya ta yi daga kuma I.b ya shiga jera mata kalaman soyayya masu narka zuciya, aikam babu ɓata lokaci ta yi accepting soyayarsa.
Bayan sati uku kuwa, gaba ɗaya M-Ladies sun faɗa soyayya da su Abbas, sai dai soyayyar Abbas da Maryam ita ce kaɗai aka gina akan gaskiya saɓanin na sauran.
A yanzu I.b ya fara jiƙa da kuɗi,