Showing 27001 words to 30000 words out of 42033 words

Chapter 10 - Zumuntar kenan 3 book Hausa Novels by Takori.txt

galla mata harara na ce.
"Inda Walida ta fiki kenan, hankali da sanin ya kamata. Wawuya kawai, kashe talbijin din nan bana son hayaniya".
Kausar ta zumburo baki, "Ni fa hutawa nazo yi ba aikatau ba. Tun ranar da maigidan ya koremu ban kara marmarin zuwa gidanku ba. Yanzun ma ba don Momi ce ta takura min ba da banzo ba".
Na kama baki na ce, "To yi mana rashin kunya ke da aka turo ki taimakeni mu sada zumunci. Tashi maza-maza ki wanke (plates) din da aka yi amfani dasu da tukwanen, kiyi 'mopping' (kitchen) din ko mu raba gari yanzu-yanzun nan har bakin 'gate' a jiyo mu".
Ta mike tana kumburi kamar zata fashe tayi (kitchen) din Walida na yi mata dariya.
Na ce, "Lallai Momi tana fama da wannan yarinyar, Allah Yan shiryeta".
Walida ta ce, "Ai in tana yi Momi cewa take gadon Fa'izah".
Nayi murmushi sosai cikin raina na ce, "Fa'izar da".
Da daddare muna kwance a gado daya, Walida Kausar nata barci abinsu cikin kwanciyar hankali amma ni sai juye-juye nake daga wannan gefen zuwa wancan. Na kasa barcin magan-ganun da muka yi da Momi ke cina ta ko’ina, suna babbaka ni.
A karo na farko nayi tunanin jarraba shawarar Momi na. To amma in kira Fa'iz ince masa me? Ince Fa'izu Abubakar, yanzu ina son ka? Da wane baki? Da wane harshe? Da wacce siga? Na ciza na hura na kasa samo sigar. Ina cikin rukunin mutanen da basa iya fadin abinda ke zuciyarsu a fatar baki, sannan ni mutum ce mai tsananin kunya da kama kaina.
Wata zuciyar ta ce, "Fa'izu ba matsayin miji kadai yake takawa a gareki ba. Dan uwa ne na jini. Ba lallai sai kince sonshi kike ba, 'actions show feelings atimes...".
Da wannan shawarar da wannan tunanin na kira Ummi, cikin barci mai nauyi ta daga bayan wayar ta sha (ringing) ta gode Allah. Har bana jin abinda take fadi sosai sai da na harhada na gane cewa take.
"Waye?"
Ajiyar zuciya na saki mai nauyi, tattare da jin nauyi, na ce.
"Ni ce, kiyi hakuri 'for' damun barcinki. Lambarshi nake so ki bani".
"Shi wa?"
Ta katseni cikin kaguwa.
Sai na kasa bata amsa, don naga alamun rainin hankali cikin tambayartata. To lambar wa zance ta bani ba ta mijina ba? Ko zance ta bani lambar wani kato ne bayan mijin da Allah Ya halatta mini? Sai na kasa ce mata komai.
A fusace ta ce, "Wai lambar wa zan baki? Yaya Bashir yana kirana".
Na tattara sauran karfin halina da guntun kashi na a katara na ce.
"Yaya Fa'iz".
Sai cewa tayi, "Wanne?" Cikin iya shege.
Kamar na fashe da kuka na dai daure na ce.
"Na Hajjah".
Dariya Ummi ta saki mai ban haushi da bakanta zuciyar wanda aka mawa. Sai da tayi ta harda hawaye duk da bana ganinta ina jinta tana share shi, sai da ta mula cikin ginshira irin ta su ta 'ya'yan A.B sannan ta ce.
"Gashi kuma ya gargademu baki dayanmu kada mu sake mu baki lambarshi don gudun kada kisa mai (bomb) a kunnen wayar ya tashi da shi, kin san makiyinka har kullum nesa-nesa kake yi da shi musamman wanda ka sanshi farin sani cewa makiyinka ne dole ka sha masa lahaula".
Cikin tsananin takaici na ce, "Umm!".
Ta ce, "Na'am Fa'izatu!"
"Bana cikin kayan 'yan wulakancin ki. In banda dole banga me zai sa in neme ki ba balle har ki wulakanta ni...".
"To ni na ce ki neme ni?" Ta katse ni.
"Sanda ki ke shuka rashin mutuncin ki wa kike nema? Wane irin zagi da wulakanci ne baki yi min ba a lokacin da kike tsula tsiyarki? Sai yanzu da taki ta kawo ki ne kika san ina da amfani?"
Na ce, "Shi kenan Ummi, zan nemi Zaneerah, nasan ba zata yi min abinda kika yi min din nan ba. Na dauka abokin kuka shi ake gayawa mutuwa, dalilin da yasa na neme ki kenan".
Ta ce, "A'ah ba shi ake gayawa ba, abin dariya ake gaya masa kuma ni abokiyar dariya ce ba ta kuka ba, Allah Ya raba mu da duk abinda zai sa mu kuka...".
Ban tsaya jin karshen iskancin nata ba na kashe wayata. Na kudure a raina ba zan sake neman Ummi a duniya ba. Don haushi sai da hawaye suka zubo min.
Ban yi kasa a gwiwa ba na kira Zaneerah dake Lagos, (with full confidence on her) don kowa yasan Zaneerah 'is nice' kuma yarinya ce mai sanyi da sanyin hali fiye da kowa cikin A.B baki daya.
Bugun farko layin ya shiga, amma har ya katse bata daga ba. Ban hakura ba na sake kira a karo na biyu, ya jima yana ringing shima kafin naji sassanyar muryar Zaneerah ta ce.
"Hello!".
Da sauri na ce, "Kinyi barci ne Zaneerah?"
Ta ce, "Ko nayi barci ko banyi ba ina ruwanki Fa'izah? Kiyayyar Yayana da ta shafe ni... Ba kya nemana balle YAYA ALIYU! In maye na cin kowa baya cin kansa, Yaya Aliyu bai cancanci burus din da kika yi dashi ba in ni na cancanta saboda Yayana Abubakar. Diyata mai sunanki wadda aka sawa sunan domin KAUNAR ki balle wadda na sake haifewa ita ko darajar Allah Ya raya ko da 'text message' ne bata samu ba. A lahira da kallo akan ZUMUNCI da kuke yin wasarere dashi a yanzu akan wasu hujjoji marasa madafa. Yanzu ma zancenki da irin butulcin ki muka gama ni da Yaya Aliyu. Umh! Ina sauraron ki yanzun da wacce kika zo?"
Sai kalamai suka kare a yawun bakina domin na yarda na amince nayi amanna da gaske ni din mai laifi kan laifi ce ga Zaneerah wadanda bazance ban san nayi ba, sai dai a wancan lokacin basu dameni bane domin ina da damuwata ta kashin kaina da ta dame ta kowa, ta mantar dani kowa da komai har da YAYA ALIYUN.
Gaskiyar Zaneerah a LAHIRA da kallo akan zumunci, zamani ya canza al'umma da dama muna wasa da zumunci da hakkokinsa ta yin amfani da uzrorin kanmu da suka sha gabanmu, wadanda in ka bibiya duk na neman duniya ne wadanda ba zasu karemu gaban mahalicinmu ba ranar da yake binciken wannan amana da hakki mai girma mai suna ZUMUNCI da Ya bamu a hannayenmu cikin Alqur'ani da Hadisi.
Zumunci abu ne mai girma. Allah Ya kawo mu wani zamani da baka neman dan uwanka na jini don jin lafiyarsa ko ta iyalinsa da halin dayake ciki, sai kana bukatar amfanuwa dashi 'in any way or the other'. Ina rokon Allah Yasa al'umma MU GYARA mu dawo da zumunci a muhallinsa irin na iyaye da kakanninmu a inda baka bambance dan wa da dan kani ko da shi ne beran masallaci saboda talauci, ko da shi ne karuna saboda arziki ba zaka bambance dan wa da dan kani ba koda da fatar baki ne ba za'a bambance maka ba sai dai ace "DUKA DAYA!"
Na nisa cikin mutuwar jiki da ta zuciya da tunanina yazo nan. Na rantse na manta waya muke ni da Zanira kuma kudin wayata na tafiya.
Zanira bata aje ba haka nima sai dai kawai taji shasshekar kukana.
Allah Sarki Zaneerah, Zanin Hajjah, Zanin Mama, Zanin Yaya Aliyu... Sai ta kama dariya, dariya sosai mai nuna maida komai wasa, kuma ta fada ne don ta huce fushinta ba don ta kullace ni ba 'And she's relieved by expressing it'.
"Ni fa komai ya wuce kuma har ga Allah nayi miki UZRI dai-dai har saba'in Fa'izah Fa'iz Abubakar...".
Murmushi nayi, wani irin dadi ya ratsani da wannan suna mai sanyi data kirayeni da shi.
"Bani da bakin da zan wanke kaina, sai dai ince KIYI HAKURI, KIYI HAKURI, KIYIHAKURI ZANEERAH...!"
"Kema kiyi hakuri 'for hurting your feeling with my words'. Na fada ne don in huce bacin raina kuma na huce".
"Nayi miki alkawarin zuwa har Lagos in Yaya Fa'iz ya dawo inga 'yata da takwarata, in baiwa Yaya ALiyu hakuri. Yanzu ma ina bashi wani na bin wani, kamar yadda na baki.
Bayan nan ki bani lambar Yaya Fa'iz ko ki tambayo min Yaya Aliyu in baki da".
Sai bayan da na fada ne wata kunya ta rufeni, wai macece take neman lambar mijinta a wurin 'yan uwa da dangi wannan abin kunya har ina! Ai kiyayyah ba hauka bace, sai ko in ta hadu da tabin hankali. Abin kunyar ma kuma ga kanwar mijin uwa daya uba daya. Allah ka agajeni.
Wata irin guda Zaneerah ta sakar min a kunne wadda har saida ta dode min dodon kunne, nayi saurin kauda wayar daga kunena. Sannan na jiyota tana cewa.
"Mafarki nake ko ido na biyu?"
Na amsa da karsashi, "Idonki biyu Zaneerah, don Allah ki bani. Kada kiyi min abinda Ummi tayi min, kada ki hukuntani da laifina bayan na riga na amshe shi, na kuma aikata shi ne bisa kuskure. Don Allah Zaneerah...". Na karasa cikin karkarwar murya da rishin kuka.
"Saurare ni Fa'izah".
Ta fada cikin jin kai da kauna irin ta dan uwa shakiki.
Na rage sautin kukan ina sauraronta.
"Wallahi kinji nayi rantsuwa ta 'yan Musulmi kenan Yaya Fa'iz ya hana kowa ya baki lambarsa. Ya hana ni, ya hana Yaya Aliyu, ya kuma yi rantsuwa duk wanda ya baki ya yanke zumunci dashi har abada! Ki karbi uzurina domin ina daga cikin mutanen da yake mutuntawa, ya kuma yarda da amanarsu".
Sai na zamo 'standstill, wordless, speachless, motionless! Me Fa'iz yake nufi da hakan? Kuma me yake nufi da katse duk wata hanyar sadar dashi gareni? Bani da sani akan hakan, haka itama Zanirar. Don haka tambayar ta ma baya da amfani.
Hawaye ya sake ciko idona. Muka yi sallama kowanne jiki ba kwari. Tana fadin sai sunzo ganin gidan Malali, ko da yake ta gani a hoto wai Mama ta tura mata ta watsapp.
A wannan daren, mai cike da sauyin sabbin al'amura masu dama a gareni, dai-dai da minti daya ban runtsa ba. Kuka nake yi wanda ni kaina ban san dalilin sa ba. Nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. Idanuna suka shiga radadi, da zugi dole na sassauta musu.
Anya ba asiri Fa'iz yayi min ba? Domin ko ga marigayi Nazir S. da Yaya Aliyu dana so a baya, so mai azalzalar zuciya ta, yake azabtar da ruhina bai kama kafar na yanzun akan Fa'iz Bamalli ba.
To ko Mama ce tayi min asirin? Nayi saurin kawo A'uziyyah da Istigfari a bisa wannan mummunan zato da yake darsuwa a zuciyata. Na tabbata Mama, ko wani cikin zuri'armu ta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ba zai taba yi min asiri wai don in so Fa'iz ba. Domin bamu san shi ba, bamu san hanyar nemoshi ba, bamu san inda ake yinsa ba haka bamu san yadda ake yinsa ba.
Abinda muka sani shi ne idan muna da bukata, mu tashi cikin dare mu tsarkake kanmu da tufafinmu mu daura alwala, mu fuskanci alkibla muyi sujjadah ga Ubangiji mu fada mishi bukatar mu. Wannan ce tarbiyyar da aka rainemu da ita yaranmu da manyanmu. Ko da zata yi yunkuri akan inso Fa'iz sai dai tayi addu'a na Allah Ya daidaita tsakaninmu in da ALHERI (sunan wani littafin Takori).
Idan kuwa har ta yin to ta tabbata an amsa addu'arta, ina sozn Fa'iz a yau, wani irin so da bazan iya fassarawa ba!!!
Abinda na yarda da shi a tsayin daren baki dayansa shi ne. NA SOMA SON FA'IZ A DAN ZAMAN DA MUKA YI TARE na gajeren lokaci wanda yayi tsayin dare dubu da goma sha hudu a idanu da zuciyata. Dabi'unsa, saukin kansa, barkwancinsa, rayuwarshi gaba daya, addininsa, nutsuwarsa, ‘his unique personal attributes’ da tsananin KISHINSA akaina a fili da boye su suka ja ni ga kaunarsa.
[1/4, 12:24 am] Takori: ***
Cikin wannan mawuyacin hali da sabuwar rayuwa mai wahalar da dan Adam a zuci da gangar JIKI da RUHI, duk da tarin jndadi da daular da ke zagaye dani, na cigaba da gurgurawa har tsayin wata guda. Ya zamanto ba abinda ke burgeni, ba abinda zan ci inji dandanonsa sai dai inci don in zauna da hanjin cikina lafiya, ba abinda nake son ji da gani sai FA'EEZ da MURYARSA... Wadanda ya haramta min haihata-haihata ya kuma toshe duk wata kafa da zan same su daga iyaye da 'yan uwa.
Hutunsu Walida tuni ya kare amma nayi tsalle na dire na hana su komawa gida balle su koma makarantar, in sun bar gidan ban san makomar rayuwata cikin wannan fankacecen gida ba. Domin dai komai na gidan tun zuwansu su suke tafiyar dashi, girki da tsaftace shi.
Abinda nasan ina iyawa kawai shi ne jefawa Dawisu kwayoyin dawa da sake musu ruwan sha idan yayi kura. Na daina ado, na daina wannan kwalisar. Hana rantsuwa nasan ina wanka, wannan kullum ne insha-Allahu. To sai dai bayan shi fa ko Vaseline baya ganin tattausar fatar jikina. Don ma Allah Ya so ni lokaci ne na zafi, da ban san yaya fatata zata koma ba, saboda rashin kula da hakkinta.
Ina yin burushi sau biyu a rana, da safe kafin inci komai, da daddare in zan kwanta. Ina sauya kayan jikina bayan kowacce kwana uku, shima idan na gaji da mitar Walida ta cewa bana fesa deo-spray kayana suna tashi.
Na zama wata irin Fa'izatu mara sanin inda rayuwarta ta dosa. Na zama mara lissafi ko tunanin wasu hanyoyi na inganta rayuwa. A ganina duk wani jin dadin, walwalar da ingancin rayuwar zai samu ne idan naji muryar Abubakar Mukhtar, na kuma ganshi da idanuna. Ko da bai sake cewa yana sona ba 'atleast' in nemi gafararsa, inyi zaman aure dashi irin na iyaye da kakanninmu. Wanda babu I LOVE YOU din sai tarin mutunta juna da darajja juna da sauke hakkin juna da Allah Ya dora a tsakani. Tunda na riga na bar damar ta kubuce min. Dama na sha jin ana cewa, tana zuwa ne sau daya a rayuwa.
Hatta Yaya Rabi na tambaya lambar Fa'iz, na daure duk wani dizgi, shagube da izgilancin ta. Amma 'yar tahalikar nan bata bani ba. Ta rantse ta maya idan na sake tambayarta sai ta kwankwatsa wayarta in daina damunta.
Mutum daya ya rage in tambaya ban tambaya ba, wato MAMA, don ita Hajjah bata rike waya, ko tana rikewa 'issue' dina da Hajjah a yanzu yafi karfin in nemeta a waya, ko in nemi lambar Fa'iz daga gareta. Ina jin bayan hauka da suka manna min a baya, idan nayi hakan zasu manna min fitowa daga turu. Kafin nan kafin in doshi Hajjaty a halin yanzu wani 'issue' ne na musamman mai zaman kansa, ban san da wane kalami, da wace fuska, da wane harshe zan doshi Hajjah in nemi gafararta ba, a bisa rashin kyautawar da nayi ta yi mata har da kauracewa. Anya Hajjar ta cancanci hakan?
Da wannan dumbin tunani marar madafa ko zabi ta kowanne bangare na hada komai na tattara wuri guda na mikawa Subhana, Sarkin da babu abinda ya gagare shi. Ni na raunana, al'amarin ya gagareni iyawa da sarrafawa don haka na mika masa dukkan al'amarin yayi min iko da iyawarsa, bani da tsimi bani da dabara, duk suna ga Sarki ALLAH!
Walida da Kausar suka kasa gane kaina, na farko bana zama dasu muyi hira, kamar yadda muka saba a baya. Bana sanya kaina cikin komai na al'amarin gidan, kullum ina daki nade cikin bargo kamar daddawa, bana umh bana uhm-uhm, sai gululun ido. Wadanda suka fada ciki suka zurma. Fa'iz kawai suka mace da son gani, ko son jin wani abu da ya dangance shi. Bazan iya kwatanta rayuwar da nake yi ba da halin da nake ciki, sai dai ince sunana FA'IZATU!!! Wadda son FA'IZU ke neman hallakarwa!!!

***
Mun wayi gari yau da gingimemen hadari, mai dauke da sassanyar iska, wadda ke kadawa tare da yayyafin ruwa kadan-kadan yaf-yaf akan rufunan gidajen unguwar Malali GRA, wanda hakan ya tada kamshin kasa mai dadi da dadin shaka a hancin kowanne bil'adama.
Dai dai lokacin da nayi wani juyi akan gadona domin gyara kwanciya don karin jin dadin kwanciyar tawa, naji ban zunguri Kausar ko Walida ba wadanda suke kwance gefe da gefe na. Hakan ya sanya ni bude ido sosai tare da tashi zaune. Can na hango su jikin gado suna shirya kayansu kaf a cikin (troller) din da suka zo da ita.
Sosai na wartsake na dube su cikin mamaki, a lokacin da suka gama kintsa kayan suka ja zip suka zuge jakar. Na tashi zaune sosai na ture bargon na ce.
"Ku, lafiya? Ina zaku je?" Walida ta mike tsaye tana gyara lullubin da tayi da mayafin Abaya baka.
"Lafiyar kenan, tafiya zamuyi".
Na ce, "AMma ba haka muka yi da Momi ba, munyi da ita zaku kara sati daya, na rantse daga shi ko kwana daya ba zan ce ku kara ba. Kuji tausayina Walida, kuyi hakuri mu zauna".
Idona ya raina fata, ya kuma cicciko da kwallah.
Kausar ta ce, "Allah ko minti daya ba zamu kara ba, balle yaya Fa'iz yazo ya taddamu a gidan nan ya sake korarmu. Tunda yau zai dawo zaman me zamu yi?"
Da farko ban fahimci me Kausar take nufi ba, abinda na fahimta shi ne Kausar yarinya ce mai riko kamar ni, har yau haushin korar Yayan nata take ji. Don haka cikin lissafina ban lissafa da abinda ta ambata ba sai fahimta nayi kawai bata so ta ci gaba da zaman. Ina wannan harhaden ma'anar ne, Walida ta dora da bayanin da ya warware maganar Kausar.
"Tun karfe bakwai ya kira wayarki, ni lokacin na tashi sai na dauka, Ya tambaye ni yaushe muka zo na ce da shi yau watanmu guda a gidan nan. Ya ce in sanar dake yana bisa hanyar dawowa karfe hudu na yammacin yau. A gayawa Yaya Bashir yaje filin jirgin saman Kano ya dauko shi ta can zai sauka.
Ya ce ina kike? Na ce baki tashi ba, ko in tashe ki in baki? Ya ce in kyaleki kiyi baccinki, amma in gaya miki sakon".
Jina nayi kamar ina yawo akan gajimare, cikin wata alkarya ta madara da zuma saboda dadi, farin ciki, godiyar Ubangiji, murna. Sauran abinda naji a cikin zuciyata a lokacin (unexpressable) ne. Ciki kuwa har da faduwar gaba da bugun zuciya. Wanda suka fito a tare da farin cikin, murna da godiyar Ubangijin suka saukar da wata irin nutsuwa da salama cikin zuciyata.
Na lumshe ido a hankali. Ina rokon Allah a zuci idan mafarki nake kada Yasa na farka sai nayi tozali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login