Showing 18001 words to 21000 words out of 42033 words

Chapter 7 - Zumuntar kenan 3 book Hausa Novels by Takori.txt

tura haushi ya ce.
"UHm! Na ce ba?"
Fa'iz ya dakata amma bai juyo ba.
"Ka nemo motar hawa a kyale min tawa ta huta. Haba, ya za'a ce in hau abu, kaima ka hau, wannan sam ba tsarina bane. Duk kabi ka zage min gari da motar ma bana so, ka je ka rike ka kirgo kudinta ka biya ni, fakat".
Ya ce, "Zan kawo abinda ya samu, shi kenan?"
Baba ya ce, "Wane irin abinda ya samu? Naira miliyan biyar cur na sayi mota ta, haka za'a bani ko Naira biyar ban yarda tayi ciwon kai a ciki ba. Mota ta 'R-Class' ce kaje ko'ina ka tambaya haka kudinta yake".
Takaici a wurin Fa'iz baya faduwa, ya ce.
"Haba Baba, ai babu ciniki tsakaninmu. Yaushe ma na fara aikin da har zan tara abinda kake fadi? Duk ajiyar da nake yi ta kananan ayyukan da nayi kai na turowa aka yi aikin gidan nan da muke ciki".
Baba ya ce, "Kai ka sani. Albarkacin shekara biyu da tayi a hannuna, na shigeta sau bakwai, a kawo min naira miliyan uku, cash ba ta 'credit card' ko 'cheque' ko 'internet banking' ba. Ni nasan bankin da nake mu'amala da abina".
Mama dariya take har da kyakyatawa. Fa'iz bai kara tankawa ba ya fice. Na bi bayanshi nima dariya ta cika min ciki amma na kame kaina tunda ni ke da nasara. Ina shiga motar kafin na kai ga rufewa ya fisgeta kofar ta rufe kanta da kanta, saura kadan ta guntile min 'yan yatsu.
Tunda muka hau titin da zai kaimu Zaria bai ce min komai ba, kazalika bai kalleni ba. Ya maida hankali sosai a tukin da yake yi (at a speedy level).
Momi kurum muka samu a gida muka gaisheta, bai iya yayi hira da ita ba duk kokarin da yake na boye bacin ransa. Daga bisani ya tashi ya barmu ya ce zai je cikin (city) ya dawo sai mu tafi.
Bayan fitarsa Momi ta zuba min ido tana kallo.
"Wato mai hali dai baya fasa halinsa. Ana murna kwana biyu an jiki shiru ashe wata sabuwar tsiyar kike shukawa a inda babu mai ganinki balle ya tsawatar. To in kowa baya ganinki ko Fa'izu bai kawowa kowa kararki ba, Allah da Ya halicci kowa da komai Shi Yana ganinki da duk abinda ki ke aikatawa na zahiri da badini. Daga ganin yadda Abubakar yake kumburi wanda ba halinsa ba, kinyi rashin mutuncin naki ne".
Na ce, "Wallahi Momi banyi masa komai ba, lafiya muke zaune tunda muka bar gidan nan. Tsakanin shi da Mama ne, don kawai ta ce sai ya sake dawowa na bishi inda yake, shi kenan yake fushi".
Momi ta harzuka, ban kai ga direwa ba ta ce.
"Ubanki za ki zauna kiyi eye? Na ce ubanki za ki zauna kiyi, ke ba zakiyi zaman aure irin na kowacce mace ba? Shashasha maras mutunci.
In don ni kike yin wannan dabbancin wallahi kin dauki alhakina don ni babu abinda Abubakar yayi min wanda ban dauka a yarinta da kuruciya ba tunda dai ni dai gaba da gaba bai taba fuskantata ya zagenin ba sai dai inji a bakinki, wanda tun lokacin ba sauraron ki nake ba, bani kuma da tabbacin ko karya kike don bacin ke ban taba jin wani ya ce Fa'iz ya zageni ko baya sona ba.
Akwai abinda baki sani ba wanda in kin sauke iskokin dake kanki kinbi a hankali watakila nan gaba za ki sani. Baka taba jin ZUCIYAR MUTUM... baka kwantar da hankalinka a kanshi ba. Don masu iya magana sunce ZUCIYAR MUTUM.... BIRNINSA!.
Kin san Allah ki ka sake sako kafarki gidan nan sai nasa Babanku ya kakkaryata, ba dakin Abdallah ba ko cikin kuratandu kika shiga indai a gidan nan ne sai dai ki bi yawon duniyar daga yau babu mai hana ki".
Idanunta suka cicciko da kwalla amma bata bari sun zubo ba don sanin hatsarin da zubar tasu ke tattare dashi a tare dani.
Nayi murmushin da na tabbatar zai kwantar da hankalinta, gaba daya jikina yayi sanyi kalau.
"Ba gidan nan zan dawo ba. Tunda muka tafi ma ai ba a gidan Baban Kaduna muke ba, Walida bata gaya muku ba? Muna gidanshi ne a Malali GRA".
Ta dan zuba min ido kamar bata yarda da abinda na ce ba.
Na ce, "Wallahi Momi da gaske nake, kuma ki tambayi Mama. Ko ya tafi a can zanyi zamana nayi miki alkawari, in kin ganni gidan nan ko gidan Baban Kaduna ko Giwa ko Kano wajen Ya Rabi gaishe ku nazo yi".
Anan ne ta saki fuska ta ce, "Shi kenan. Su Walidar basu dawo bane, daga can suka wuce Lagos wajen su Zanirah".
Dai dai lokacin da muka ji sallamar shi a dakin, abin mamaki ya saki ba kamar yadda muka zo ba.
Ya ce, "Momi zamu wuce, ni kuma gobe zan wuce Wales din kasar England, na samu aiki da 'British-Airline' zan jima ban zo ba sai na samu (break) mai dan tsaho".
Momi ta sanya albarka tayi addu'a da Allah Yasa matakin arziki ne, Ya kara rufa asiri, Ya kiyaye sharrin karfe da na iska, Ya cire haramun daga cikin abinda za'a samu alfarmar Manzo (S.A.W).
Ya fadada murmushinsa cikin jin dadin addu'arta yana fadin.
"Amin Ya Rabbi Maman Walida".
Na mike, ta dubeni ba yabo ba fallasa.
"Akwai garin semo da bushasshiyar kubewa da bushasshen kifi in kuna bukata".
Na ce, "A'ah Momi, ba yanzu ba dai, zan aiko in ina bukata".
Ta ce, "Ke kika sani".
Da muka shigo Kaduna ya tsaya wani babban 'Shopping Mall' bai yi min ko tayin shiga ba shi kadai ya shiga abinsa. Ya jima sosai kafin naga yaran kantin sun biyo shi da manyan ledoji, suka zuba a bayan motar, sai katon-katon na abin sha (ruwa da lemo) kala daban-daban.
Akan hanyarmu ta shigowa Malali ya tsaya ya tsayi gashasshen nama muka karaso gida duk jikina a sanyaye yake.
Muna shiga Ya'u ya taremu, sai na samu kaina da kara jan lullubina na rufe har rabin fuskata ban san dalili ba ko don ya nuna baya so din ne da gaske? Bazan so ya zamo nayi sanadin hanyar abincin wannan bawan Allah ba, wanda ga dukkan alamu ita ce madogararsa kadai.
Ya kwashe komai daga bayan motar ya shigar (kitchen). Yayi mana sallama ya fita.
Ya maida kofar falon ya rufe da (key) ya dawo ya zauna bisa (carpet) ya kunna t.v tashar CNN yana rike da (remote) ya dawo ya zauna, ya janyo ledar namansa yasa a gaba yana ci yana sauraron labaran, bai kara kallo na ba kamar yadda bai nemi 'chips & chicken' ba.
Na mike ba don an sani ba na shiga (kitchen) na soma sarrafa su kamar yadda na saba, amma na yau (with additional aroma and taste) saboda kamar ina neman hanyar shiri ne ko yaya ne dai na kasa gane kaina. Wata zuciyar ta ce tunda ni nayi nasara nawa ra'ayin aka yi masa fin karfi aka bi, bari in dan kyautata.
Dana kammala na aje a (dining) kamar yadda na saba, na ce.
"Ga (dinner) din".
Kamar ba da shi nake ba kallon t.v kawai yake duk da na tabbatar ya ji ni saboda ba wai yasa muryar t.v din da yawa bane, a'a dai-dai jinsa, raina ya dan baci na wuce na shige daki na sayo kofa amma ban sa mukulli ba. Can naji motsin kwanuka a (kitchen_, na daga labule ta taga ta wadda kana hango duk abinda ke faruwa a (kitchen) sai na hango shi ya dora 'yar tukunya akan (cooker) ya saka indomie guda biyu bai ko cire ledar maggi da chili din dake ciki ba ya kawo ruwan zafi wajen kofi uku wanda ya sha kan indomin har baka hango ta ya zuba, ya rufe. Ya fita daga kicin din ya koma ya ci gaba da sauraron labaransa.
Kamar inje in duba wannan lamari wata zuciyar ta kwabeni abinda ba ruwan ka ance dadin kallo gare shi, na koma nayi kwanciyata. Anfi minti talatin kafin inji shi ya koma (kitchen) din, ban san abinda ya faru kuma ba bayan nan.
Bayan kamar minti biyar naji fitarsa a mota, tsegumi har tsunkuli na yake nayi (kitchen). Na bude tukunyar daya dora a wuta. Indomin ta hadu ta dame ta zama kunu zance ko koko ko tuwo, gatan nan dai ba suna ba fasali. Na tabbata ba zai iya ko tabawa ba balle ya sanya a bakinsa shi ne ya fita yaje ya sayo.
A raina na ce, "Ashe dai girkin banza na da amfani tunda sai da shi ake rayuwa".
Na kara duban dabgen da yayi nayi dariya na mayar na rufe na koma daki.
Nayi zaton zan kuma jin duriyarshi kafin nayi barci, amma har garin Allah ya waye banji ba. Haka dana tashi yin sallar asubahi na fita falon ko zan ganshi sai abincina na daren jiya (chips and chicken) kadai na tarar akan (dining table) inda na ajiye shi ko matsar da shi ba'ayi ba.
Daga nan nayi brush na koma daki, ban tashi ba sai karfe tara na safe. Da hanzari na nufi (kitchen) na soma aikin hada masa karin kumallo, amma na yau 'is special' kamar na daren jiya duk da raina ya sosu da rashin cin da bai yi ba.
Cikin dan lokaci na kammala 'scottish egg, plantain with syrup, bread with jubnah' da ruwan na'a-na'a. Cikin dan lokaci kalilan na kwashe na jiya na shirya su a inda ya saba karyawa a kwanaki goma sha ukun da muka yi tare.
Na koma daki nayi wanka nayi shiri cikin atamfa sufa ja mai ratsin kore da baki wanda dinkin ya zauna a jikina sosai, zanin ya bude daga kasa. Na fesa turare 'escada sentiment' na kalmasa dauri sassauka, na dubi kaina a mudubin dogon yaro na yi wani irin 'fresh' (looking takeaway) ko ni kaina na baiwa kaina sha'awa. Sai na samu kaina da tambayar kaina kwalliyar ta mece ce? Mene ne dalilinta?
[1/4, 12:23 am] Takori: Dana gaza samarwa kaina wadannan amsoshin guda biyu, sai kawai na fita, ina juyowa muka hada ido yana kokarin fitowa daga nashi dakin janye da (travelling bag) mai matsakaicin girma 'troller' ruwan zuma.
Dammm! Naji kirjina ya buga, bugawar da ba'a kirjin kadai ta tsaya ba ta hudo ne har cikin zuciyata. Sanye yake da riga fara anyi rubutu da shudin zare 'TOMMY HILFIGER' da shudin wandon (jeans) turrare, sumar nan ta kwanta tayi luf a saman kansa sai sheki take, inda duk ya motsa sassanyan kamshin '212' ke tashi.. Ya saya kwayar idanunshi cikin gilashi 'porsche' mai duhu ainun, don haka kai tsaye ba zan iya cewa ga halin da kwayar idanunshi ke ciki ba.
Ya ajiye jakar a kusa dashi ya zauna a kujera sosai ya zage zip dinta, ya ciro katin ATM ya dago ido ya dubeni ina tsaye a inda nake ban ko motsa ba.
"Ko zaki iya zama?" Abinda ya ce dani kenan.
Tamkar wata rakuma da akala na bi umarnin furucin nasa, na zauna a kujerar dake fuskantarsa.
ATM card din ya aje mani gabana, ya yagi takarda yayi rubutu itama ya turo mini.
"Ga PIN dinsa nan na rubuta a jikin takardar na bankin UBA ne, in kina da bukatarsu sai ki kira Shu'aib a waya ki turashi ya debo miki adadin da kike bukata.
Anjima Surajo zai kawo miki waya ni na tafi ban san kuma ranar da zan dawo ba. In kina da matsala ki kira Mama ki gaya mata, Ya'u zai ke kawo miki (recharge-card) duk sati, ban yarda da fita ko bakin (gate) ba in ba lalura ta rashin lafiya ba tunda rayuwar da kika zaba kenan". Ya mike yana zuge jakarsa.
Idona ya cicciko da kwallah. Ba zan ce bai yi min dai-dai ba, kuma bazance yayi min dai-dai ba. Na san akwai hakkokin shi da yawa akaina, wadanda na sanya kafa na shure na take akan sanina, wadanda hujjojina babu ruwan Allah dasu. Auren Fa'iz dake kaina kadai ya sani dole in bude baki yau inyi magana saboda halin rai, yau yake da tabbatas gobe babu shi. Sannan sha'ani na tafiya wanda bana fatan hakan.
Muryata na rawa na ce, "Ga abincinka fa ka karya mana sai ka tafi".
Ya dubemu duka ni da abincin ya hararemu duk da ance aikin banza wai harara cikin duhu don kuwa bakin gilashi ne a idonsa, ya ce.
"Ki rike kayanki, na gode. Akanshi dai kike yi min tsaki in na saki, to insha-Allahu ba zan sake cewa ki dafa min wani abu ba, sai kin ganni ma balle ince ki bani abincin. Zan tafi inda ba sai nace a bani za'a bani ba, balle aje ga goranta min ko yi min tsaki".
"Kayi hakuri don Allah...". Na fadi cikin kuka.
Ya dubeni cikin mamaki, nasan bai zata ba. Ni kuma harga Allah banyi hakan ko fadi hakan don wata manufa ba, sai don kar ya tafi da fushina in kasance cikin fushin Ubangiji da tsinuwar Mala'iku har yaje ya dawo, wanda ban san ranar dawowar tasa ba.
Ya koma ya zauna, sannu a hankali yake zare gilashin idonshi, ni kuma ina ta sharbe. Ya kirani da wata irin kankanuwar murya.
"Fa'izah!".
Na cira jajayen idanuna na dube shi, ban amsa ba amma idanuna sun nuna ina sauraron sa ne.
"Komi ya wuce?"
Ya tambaya.
Na sunkuyar da kai ina jan zaren carpet bance komai ba, amma na daina kukan sai ajiyar zuciya. Ya baro kujerar shi ya iso gabana yayi zaman dirshan, ya kamo hannuna na dama ya sarke cikin nashi. Na dago kai na dubeshi kana nayi sauri na maryar na sunkuyar. Ko da can bama iya hada ido da wadannan 'sexy' idanun balle yanzu? Da aka samu karin ilhamomi masu yawa a cikinsu?
Ya sumbaci goshina, idanuna, karan hanci da bakin da yakan ce rashin mutuncin dake cikinshi ya fishi girma, mun dade cikin wannan halin, da dukkannin mu bamu taba tsintar kanmu cikinsa ba, zuciyoyi da ruhinmu sun hade sun cure wuri guda, muka samu kanmu cikin mantawa da duk abubuwan da suka faru cikin rayuwarmu. Dai dai lokacin da kararrawar shigowa falon ta soma kara.
Mikewa nayi cikin sanyin jiki, don dama neman hanyar mikewar nake yi na rasa, saboda gangar jikina da zuciyata sun gaza karbar sababbin al’amura masu girma irin wadannan da Fa'iz ke bijirowa dasu a wannan lokacin, wadanda bazan ce ban sani ba ko ban san sune suke wanzuwa a cikin aure ba. Sai dai ban taba yi ba ko kusantar yi ba a kulliyar rayuwata, daga yarinta har zuwa girma, sai ko yanzu da Fa'iz ke son tabbatar min da cewa, lokacin yin nasu ya zo. Goyon bayana da hadin kaina kadai yake jira, domin tabbatuwarsu, 'and I lack such a courage!' (Na rasa wannan kwarin gwiwar). A ganina ‘it’s not the hightime. ..... (lokaci bai yi ba).
Don haka wanda ya danna kararrawar nan in banyi masa addu'ar alheri ba hakika ya cancanci inyi masa fatan ALHERI. Na bude kofar ba tare da tambayar ko waye ba haka ba tare da waiwayar halin da Fa'iz ke ciki ba, Surajo ne.
Nayi murmushi na bashi hanya ya wuce amma kallo daya zai yi min ya tabbatar a rikice nake, kuma hankalina a tashe yake domin na tabbata ya zo ne domin ya dauki Fa'iz ya kaishi filin jirgi.
"Madam rikici, ke kika rike Pilot ko? Kina sane da cewa karfe goma sha daya zai tashi? Don Allah a ringa lura da lokacin aiki cikin lokutan ayyukan soyayyar kada a koro ko ku koma direban tashar da kuka saba".
Fa'iz ya harare shi yana gyara zaman gilashin sa a kyawawan idanunsa, bisa doron karan hancin sa. Ya kwalawa Ya'u kira, ya shigo da sauri, ya dauki jakar suka fita. Surajo ya aje min kwalin waya (Samsung-tablet) ya janyo kofar falon. Na bisu da kallo cikin shatatowar hawaye dana kasa maida su ko rage gudun zubarsu akan kundukukina. Ko hawayen menene? Bazan iya cewa ba.
*****



BAYAN TAFIYAR FA'IZ
Wani ikon Allah ko abin mamaki tun tafiyar Fa'iz sai naji sam bana jin dadin gidan. Kewa da kadaici suka yi min sallama. Da yana nan, ko banyi masa magana ba shi zai mani, zanji motsin dan Adam cikin gidan ta hanyar karakainarsa, a falo da (kitchen) da nasa dakin. Amma yanzu gidan ya zame min kamar makabarta ko motsin kyankyaso babu.
Kusan kullum ina baya wajen Dawisu ina jefa musu abinci, har kujera nake kafawa in zauna. Yanzu har sun saba dani har kofar falo suke biyoni in na haura lokacin da nake fitowa basu abinci. Sai suzo kofar falo su tsaya su bude bindinansu abin ban sha'awa suna juya su gabas da yamma, kudu da arewa cikin nuna baiwar kyan da Ubangiji Ya yi musu da bai yiwa wani tsuntsu a duniya ba.
Yaran gidanmu duka an hana su zuwar mana dagani har Ummi. Haka 'yan uwa ba mai zuwa don kamar yadda na fada a baya sunce sai ranar da suka ganni da ciki irin na Ummi ko 'ya'ya irin na Zaneerah. (In fact) ina kewar Fa'iz duk da bana so na yardarwa zuciyata cewa kewar tasa nake yi.
Duk da bamu dade tare ba, sati biyu kacal muka yi tare, abubuwan dake cikin sati biyun masu yawa ne (it seems like a journey of two year full of blissful adventures) da suka kasa goguwa a zuciya da kwakwalwata. Fadansa na bani dariya, haka kishinsa na babu gaira babu dalili.
In ka debe wadannan na fahimci wasu abubuwa wadanda ada ban sani ba, wato Fa'izu Abubakar, mutum ne mai saukin kai, barkwanci, dadin mu'amala da dadin zama amma fa ga wanda yake so kadai, shi yasa iyaye da dangi duka kowa ke sonsa. Idan baya yi da kai ko ya tsaneka zaka dauka ne cewa babu wanda ya kaishi rashin kirki da rashin dadin mu'amala a duniya.
Hakazalika yawan kiran sunana da yake yi cikin gidan Fa'izah-Fa'izah-Fa'izah kai kace shi ya rada min suna Fa'izah ko Aunty Fa'izah.
(I also missed his regular sayings) "O.K?" Wannan ban san me take nufi ba har ya zamanto nima ta zauna min a baki ko magana na yiwa Ya'u na gama sai na ce "o.k?"
A da kam nasan ba haka Fa'iz yake ba sam, magana ma wuya take masa balle mu'amala da mutane, ban san sanda bakinshi ya bude ba domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login