Showing 9001 words to 12000 words out of 42033 words

Chapter 4 - Zumuntar kenan 3 book Hausa Novels by Takori.txt

mai nuni da na amshi wa'azinta ko a'ah? Ba zata gane ba, ba zan iya bane, da zata gane ta adana yawun bakinta a gaba zai yi mata amfani, ta barni yadda ta ganni, rayuwata da tata ba zata taba zama daya ba.
[1/4, 12:22 am] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-4
Washegari da safe, mun karya kumallo cikin farin ciki, ni Ummi da ragowar kannen mu. Daga nan muka tare a falon Ummi muna hira muna shan dariya. Na mike na barsu nayi (toilet) din Ummi nayi wanka na sha kwalliya da daya daga cikin lesukan Ummi da ta ci biki dasu. Na dawo falon na cimma su kafin in zauna kararrawar kofar shigowa tayi kara. Sai na fasa zama a raina na ce bari in hutar da kowa. Na karasa a natse na bude kofar.

Fa’iz ne cikin shadda wagambari babbar, ruwan makuba tare da abokinsa Surajo na Central Bank, shi kuwa cikin kananan kaya. Da ganinsu kaga matasan da rayuwa ke garawa tare dasu, suna cikin lokacinsu, kuma ana damawa dasu a fannonin da suke. Muka hada ido da Fa’iz na yi maza na kawar da nawa na wuce ciki na zauna kusa da Ummi ban kara kallon su ba. Na kuma bi na maida fuskata kamar hadari sai ka rantse ba dani ake hira da dariya yanzun nan ba.
Su Ummi suka shiga gayar dasu daya bayan daya, a sannu kuma su Walida duk suka bar falon. Na maida idona kan t.v (Indian movie) ne ake yi mai suna 'Welcome-Back' na John Abraham. Dai-dai lokacin da aka nuno jarumin shirin, wato John Abraham yana magana.
Abin mamaki dana juyo sai naga shi da Fa'iz suna matukar diban kama, illa ace yafi Fa'iz haske sosai da tarin suma. Nayi maza na kawar da wannan tunanin na mike ina kokarin barin falon.
Kallo Fa'iz ya bini dashi shi da Surajo, Suraj ya ce.
"Madam Fa'izah ba gaisuwa?"
Bai san cewa haushinsa nake ji ba tun ranar (Cocktail) ko kallon sa banyi ba na ci gaba da tafiya.
Ya ce, "Ba don ni ba, don Allah don Annabi ki koma ki zauna, wajenki muka zo".
Duk wanda aka hada da Allah da Annabi, indai cikakken Musulmi ne da yayi amanna dasu dole ya aikata abinda aka umarceshin.
To hakan ce ta faru dani. Na koma na zauna don ba yadda zanyi, amma ban kalle su ba. Ummi ta girgiza kai da alama na bata haushi ta harareni ta mike tayi ciki.
Suraj ya ce, "Na dauki Fa'izah a sahun yara nutsatstsu, masu hankali da sanin yakamata. Kowanne irin laifi Fa'iz yayi mata ya kamata ace lokaci da isowar hankali sun shafe shi hakannan. Riko, ba ta'adar dan Musulmin kwarai bane. Allah Ubangijin mu mai afuwa ne, kuma yana son masu afuwa.
Fa'iz dan Adam ne kamar kowa, ajizi kamar kowanne bil'Adama. Babu wanda yake sama da aikata kuskure, sai fiyayyen Halitta. Sai ake son kullum mu kasance cikin Istigfari, domin Allah Ya yafe mana kura-kuranmu, mu fita daga cikin rafkanannu. Laifi kuma na tsakanin dan-Adam da dan uwansa, sai aka ce mu nema daga junanmu.
Mun nema anki yi mana, mun ce a saurare mu, anki sauraron mu. Anyi mana mummunar fahimta, sabanin ta hankali da tunani. Ya kamata a sanya al'amarin mu a mizanin hankali, laifin da muka aikata bisa sani, ko bisa kuskure a bamu dama mu kare kanmu, kafin a cigaba da hukuntamu akanshi, kada ya zamo da daukar hakki".
Idan na ce jikina baiyi sanyi da kalaman Surajo ba, kema kin san karya nake. Amma ba zan iya ba da kai ba, ba duka na yarda dasu ba, (it's not the hightime).
Don haka ban basu amsa ba, kamar yadda ban dube su ba. In iskar da ta debo su ta isheni kallo, to suma hakan. Sai ma na dauki (remote) na karo sautin t.v kamar banji me yake fadi ba.
Fa'iz ya mike a fusace yayi waje, Suraj ya mara masa baya cikin tsananin mutuwar jiki da sarewa da al'amari na.
Ni da kaina nasan ban kyauta ba, duk abinda zanyiwa Fa'iz a dalilin kiyayyarsa, bai dace inyi a gaban abokinsa irin Surajo ba, da suke matukar martaba juna da girmama juna.
Yadda Fa'iz yayi fushi, na tabbata akwai abinda zai biyo baya na daukar mataki na karshe don kawo karshen rashin da'a ta. Don na lura bai iya daukar mataki ba idan ranshi ya baci, idan na tuna karon mu a 'river-niger'.
Don haka wunin ranar zungur nayi shi ne sululu! Cikin rashin kuzari, Ummi dai bata ce min komai ba don itama haushina take ji, tana kuma tsoron ta shiga maganar ince zan bar mata gidanta. Don haka sai ta bini da ido tun safe har dare bata shiga shirgina ba. Nima kuma sai banji dadin hakan da tayi min ba.

***
Karfe takwas na dare muna cin abincin daren da Ummi ta girka mana muka ji kararrawa (door-bell).
Kasancewar na riga kowa gamawa ni na doshi kofar na bude, ina kwance ne da fari cikin kujera duk abin duniya ya isheni na rasa abinda ke min dadi.
Duk da rashin wadataccen haske a wurin hakan bai hana ni gane fuskarsa ba, ma'abociyar zati da kamala. Hannunshi duka biyu zube cikin aljihun bakin wandon 'ARMANI' dake jikinsa. A jikin sa t-shirt ce ruwan bula mai haske (Tommy Hilfiger) ya saya idanunshi cikin bakin 'prada' mai duhu ainun ta yadda ba zaka iya tantance halin da kwayar idanunshi ke ciki ba.
"Ki dauko mayafi ki wuce muje, Baba ke kiranki".
Cikina ya hautsina ya ba da wani irin sauti kulululu! Idona ya yi rau-rau gab da rushewa da kuka. Na saki kofar na fito har gabanshi na durkusa na soma kuka. Idan ubana ya tsine min albarka wacce irin rayuwa nake tsammatarwa kaina? Wace irin rayuwa zan ci gaba da yi? Mene ne makomar rayuwata?
Ya daga kai sama, kamar mai irga taurari, Allah kadai yasan me yake tunani. Sautin kukana na karuwa, yana tafiya da bacin ransa. Na tabbata na kawo shi bango ne bashi da sauran dabara akaina shi yasa ya sake maida al'amarin ga mahaifina. Amma ganin irin kukan da nake sai ya ce.
"Is o.k, ba Baban ABU ne ke kiranki ba, Baban Kaduna ne".
Anan ne naji dan sanyi, na mike na dauko mayafi da takalmin Ummi ko sallama ban musu ba don hankalina ya dugunzuma ya tashi, bana so ko kankani wata magana akan Fa'iz ta sake hadani da iyayena, nafi son mu ci gaba da ci muna sidewa a tsakanin mu. Har aga wanda zai shanye miyar. Tunda Baba ya fara ikirarin zai tsine min, na fara shiga taitayina.
Na bude kofar gaban motar na shiga, Ummi ta biyo bayana da shirgina a leda, abin mamaki kayayyakina dake gidanmu da akwatinan da ya kawo min da sunan lefe da tsaraba su na gani a bayan motar-baki dayansu wasu ko a leda ba'a zuba su ba. Ga takalmana da jakunkuna na Giwa da na Zaria da takarduna na makaranta. Hakan ya tabbatar mini tafiyar dani ta tabbata.
Hawaye suka cicciko idona. Ya je Giwa kenan ya kwaso kayana duka, haka wadanda suke Zaria.
Ummi na daga min hannu muka bar harabar gidanta, sai na samu kaina da daga mata nima, don watakila rabuwar kenan. Tunda muka hau titi babu wanda ya ce uffan, babu kuma wanda ya kalli dan uwansa.
Ga mamakina ba Jabi Road muka nufa ba, haka ba filin jirgin sama ba, Fa'iz ya karya kan motar ne zuwa anguwar Malali G.R.A anguwa mai kyawun tsari. Na ciro kaina daga kallon gefen hanya na zube su a kanshi ban san yaushe furucin ya subuto daga bakina ba.
"Ina zamu je?" Fa'iz bai kula ni ba. Ya mika hannu ne ya karo karfin na'urar sanyaya mota. A hankali kuma ya rage gudun motar yana tafiya (slow-slow) kamar baya son mu kai inda zamu. Cikin sanyi ya soma magana.
"Fa'izah, bana so in rika hadaki da iyayenmu, a bisa dalilai da dama. Na farko za'a dake ki ne, duka kuma ba zai taba sawa ki so ni ba. Na biyu za'a tsaneki, kasancewar kowa na son ki tare dani. Amma ke har yanzu kin ki saduda ki zubar da makaman yakin da kika diba, ki fahimci aurenmu na har abada ne. Tunda baki tashi kinga an taba yin saki a cikin gidanmu da kewayenmu ba.
Na san kiyayya halitta ce, kamar yadda soyayya take halitta mai zaman kanta. To amma komai na duniya mai canzawa ne ke naki al'amarin yaki ya canza, yinsa kike tamkar cin kwan makauniya babu azanci babu tunani balle tsoron Ubangiji.
Nasan zafin kiyayya to amma kada ki manta ni dan uwanki ne na jini wanda jininku ke gauraye da na juna. Idan babu so na soyayya akwai so na 'yan uwantaka. Me zai hana ki ture wancan matsayin da ba zaki iya bani ba ki bani wanda Allah Ya umarceki ki bani? (Na 'yan uwantaka da na darajar aure). Kina amfani da abinda ya wuce a sabuwar rayuwar ki wanda ba zai amfane ki da komai ba, da zaki saurare ni ma da kin gane (you are totally mistaken!).
(For how long) kiyayyar taki gareni zata kare? Tunda ni tawa ta kare? Kina kwasarwa kanki zunubai iri-iri wurin Ubangiji akan sanin ki, don ba zan ce cikin rashin sani ba tunda akan idona kika sauke Alqur'ani da sauran littattafan addini.
Bana jin zafin duk abinda kike mini ko kadan, illah tausaya miki azabar Allah.
A dalilin bacin ran da kika sanyani dazu, naji dole in kawo karshen tatsuniyarmu ta zama kurunkus! Daga yau yawon gidajen 'yan uwa da iyaye ya kare mana baki dayanmu. Za muyi rayuwa ne (on our own) kowa yayi irin wadda yake ganin zata fisshe shi. Ba zan kuma hanaki ba, ki ci gaba da abinda kike yi tunda kinga shi zai fisshe ki. Na daina rokon SO sai rashinsa, na daina rokon zaman lafiya sai akasinsa, na daina rokon kwanciyar hankali sai tashinsa, na daina rokon yafiya sai rashinta, na daina rokon a daina ki na sai a cigaba da kina.
Wannan shi ne hukunci na karshe, kuma rayuwa mafi kyau da na zaba mana, don ba zan kwashe ki in kaiki inda ake ganin mutuncina ki ci gaba da zubar min dashi ba".

A dai dai lokacin da ya tsaya gaban wani karamin (flat) mai jan get, yayi (horn) wani buzu yazo da sauri ya bude. Gidan karami ne, amma fa wanda akayi amfani da hikima da fasaha wajen gininsa da tsarinsa tamkar (European-building). Rufinsa ja ne, fentinsa ciki da bai fari da ruwan madara. Ainihin ginin gidan a tsakiyar gidan aka yishi fili fetal ya zagaye shi ya sanya shi a tsakiya. Gini ne na hawa daya (flat).
Korran shuke-shuke sunyi kyakkyawan layi a gefe sun bi katangar gidan har wajenta, haka akwai wayar lantarki ta (security) akan katangar gidan. Grass carpet ne lullube da harabar gidan korra sharr sunyi lub-lub alamun suna samun matukar kulawa. Wannan shi ne ainahin gidan da Pilot Fa'iz Mukhtar ya kwashe shekaru biyu kacal yana ginawa cikin garin Kaduna, ba da sanin kowa ba sai mahaifinsa Baba Muntari wanda shi yake turowa da komai ake masa ginin daga Ukraine, hatta zanen gidan shi ya turo masa ko kwabon Baban Kaduna babu a cikin ginin Fa'iz, cikin tsararriyar unguwar Malali GRA.
Ya bude motar zai fita, sai kuma ya juyo ya dube ni. Bani da alamar fitowa illa kuka da nake yi a hankali wanda yafi kama da kukan amarya mara gata, wadda iyaye da 'yan uwa basu rako gidan miji ba. Me na yiwa A.B haka da zafi? Wane irin rashin so ake min cikin zuri'armu? Me Fa'iz yake musu wanda ni bana musu? Daga can kololuwar zuciyata naji wata murya tayi (whisphering) rada cikin kunnuwana, "BIYAYYAH".
Wannan ya tabbatar min na dai tabbata matar FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR tunda har yau gani cikin gidanshi matsayin matar gidan.
Na karbi kaddarar Ubangiji wanda Shi Ya nufi Fa'iz da zama miji a gareni. Bani da inda zani, bani da yadda zanyi, mu zauna a hakan, zaman dolen da ya zaba mana. Sai dai bana jin har illah masha-Allahu zan so shi, soyayya guda daya ce kuma na tabbata na yita na gama. Na karbi Fa'iz a matsayin mijin kaddara, na kuma ci alwashin ba zan kuma yi masa musu ko rashin kunya ba tunda ina kwadayin rahamar Ubangiji kamar yadda na yarda da tunasarwarsa gaskiya ce tsagwaro. Sai dai SO daga gareni bana jin har abada Fa'iz zai samu haka har in koma ga Ubangiji na Fa'iz ba zai samu dariya ta ba balle walwalata. Biyayya ita ce wajibina nayi alkawarin yinta da dukkan iyawata.
Na bude murfin mota na fita ba tare da na dauki komai ba, na doshi kofar da na tabbatar ita ce ta shiga falon gidan.
Ya karaso yasa (key) yana budewa. Wani saurayi ya bullo daga bayan gidan ya fadi yana gaishe shi yana amsawa, sannan ya juyo yana min sannu da zuwa. Ban amsa ba sai daga kai nayi.
Fa'iz ya ce da shi, "Yaya suke yau? Ince ko an basu abinci sosai?"
Ya ce, "Ranka ya dade an basu sunci sun koshi sun sha ruwa tun yamma yau suka kwanta".
Ya yi murmushi ya ce, "Sai da safe to Malam Ya'u. Ka zo da wuri don Allah don zan aike ka kayowa Madam cefane".
Ya ce, "An gama Yallabai. Mu kwana lafiya".
Na rasa suwa ake magana akan su.
Bai sake dubana ba ya bude kofar ya wuce ciki ya janye (curtains) ya sarkafe su a masarkafinsu. Na tube takalmana na shiga, duhu dindim, naji kafafuna bisa wani sassanyan (marbles) mai sulbi kamar bayan tarwada.
Yasa hannu ya kunna fitila daga bayan labule haske ya gauraye falon, kamar rana, sai dana runtse ido, sai ya rage fitilun ta hanyar kashe wadda tafi kowacce haske ta tsakiyar falon, hasken ya koma dai-dai.
Ya yi murmushi ya ce, "Ga dakinki Fa'izah, ga dakinki, bayan shi a ko'ina na gidan nan baki da shamaki. Wannan falon saukar baki ne, naki yana hade da dakin barcin ki, nima haka. A falonki (kitchen) yake, ba abinda su Yaya Rabi basu zuba miki ba irin na 'yan uwanki, amma sunce in gaya miki ba zasu rakoki ba, saboda halin ki ba irin na 'yan uwanki bane. Haka ba zasu ziyarce ki ba sai ranar da suka ganki da ciki irin na Ummi. Suna yi miki fatan ALHERI".
Wata harara na zabga masa, shima ya mayar min da wadda ta fita zafi, ya ce.
"Daga fadar sako? Allah Ya huci zuciyar ki; O.K?"
Na samu daya daga cikin tausasan kujerun (leather) da suka yiwa falon kawanya na luntsume. Ina kallon yadda aka shirya dakin abin sha'awa, na tabbatar aikin Aunty Rabi ne da Aunty Hauwa, sai na lalace ina kallo kamar a talbijin. Komai (orange) da (lemon green) kamar ka lashe, sannan babu tarkace amma kaya ne masu daraja baki daya tun daga kan (dining table) na tsurar bakin gilashi a can gefen falon ga na'urar sanyaya daki ta girke, doguwa (split) tana ta buso sanyi mai dadi, kayan lantarkin 'Samsung' kaloli ne kawai suka bambanta da na Ummi, ita nata komi (milk and brown) ne.
Ya dauko wayarsa yayi magana, ashe buzu mai gadi ya kira. Ya zo bakin kofa da sauri yana sallama.
Ya ce, "Kaga na manta Ya'u ya wuce, ungu mukullin mota ka kwaso duk kayan dake bayan motar da wadanda ke cikin (boot) ka kawo mata. Ka shigar dasu dakin can".
Ya karba yana fadin, "An gama Yallabai". Da buzuwar Hausarsa.
Ya dubeni kasa-kasa kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce.
"Ki tashi ki shiga nawa dakin har ya gama, ko zama za kiyi sai ya gama kalle ki cikin falon nan?"
Nayi mamakin dalilin fusatar shi haka bayan banyi wani abu da zai fusata shin ba. Na zambura baki, sannan na mike, kada inje ya faska min marin da ya saba faska mini. Don na lura yana matukar son tada hankalin fuskata da tafukansa.
Dakin daya kira nashi nan na shiga ina shan kallo. (INa ruwan 'yar kauyen Giwa).
Ina jin Baba Buzu yana ta shiga da su, sai da ya gama tas ya rufo motar ya kawo masa mukullin. Suka yi sallama shi kuma ya rufo kofar falon da (keys) ya ce.
"Malama fito min daga daki kada ki shafa min najasa a gado".
Kamar wata rakumi da akala sai na fito nayi wanda aka bani, babu musu, ba busa ba daga hannu. Ni kaina har mamakin (silence) dina nake yi. Ko da yake shaidan ne kadai za'a ce masa ga allah Ya kautar da ido.
Ganin bana jin barci, na ce bari kawai in shirya kayana a (wardrove). Ina jinshi ya kunna t.v a (main) falo yana sauraron labaran ALJAZEERAH na soma ninke kayana ina tsara su ina adanawa. Na cikin akwatunan da dinki suke bukata na barsu a ciki na jera akawatunan haka cikin (wardrove).
Ina tsaka da aikin nawa ya shigo, ya tsaya daga bakin kofa, ya canza zuwa pyjamas farare sol, hannunshi daya cikin aljihun 'pjs' din daya rike da kofar.
"Yunwa nake ji, ya za'ayi?"
A raina na ce, "Wannan wace irin tambaya ce? Ban biyo shi don in yi sana'ar kuku ba ko zaman aure irin na mata da miji, sai don amsa kiran Baban da yace min, ashe wayo yayi mani duka na hakura na fauwalawa Allah na mika wuya ga hukincinsa, yanzu kuma yazo yana son dora mini abinda ba dole na ba. Wanda ko kusa ba zan karba ba. Ai ita wannan din (girki) ba fadar Allah bace, al'ada ce, don haka ba zan karbeta ba. Allah cewa yayi su kawo a dafe su ciyar damu, babu ayar da ta ce a sayo mu girka, ni kuma da fadar Allah kawai nake amfani.
Don haka nayi masa shiru, ya gaji da jiran jin ta bakina, ya tabbatar ba zan tanka ba, sai ya ce.
"To a gasa min kaza da (chips) (favourite food) dina kenan. Don naga alamar ke a koshe kike. Akwai kajin a (freezer) din (kitchen), dankalin ma akwai a (kitchen). Duka Ya'u ya sayo, kayan gwari (su tattasai da tumatir) ne kawai babu gobe zai sayo miki, dazu da yaje sun tashi".
Ya juya ya fice. Ban amsa ba, amma a zuciyata na yanke shawarar zanyi, tunda sawa da hanawar duk a cikin umarnin Ubangiji suke.
Sai na saki aikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login