Showing 21001 words to 24000 words out of 42033 words
Chapter 8 - Zumuntar kenan 3 book Hausa Novels by Takori.txt
ada sai ya wuni baiyi magana ba.
Ina kewar Fa'iz ne a bisa dalilai da yawa dani kaina ban san adadinsu ba, ko ba komai ina jin motsinsa cikin gidan da maganganunshi ko a waya ne nasan dai ba ni kadai bace cikin gidan. To amma ya tafi, ya bar min kangon gidan da abin da ke cikinsa, gidan yayi shiru, yayi tsit sam babu dadi kamar babu mahalukin dake rayuwa a cikinsa.
Ina kwance tsakiyar kafet din falona na tada kai da filon kujera kwanaki uku da tafiyar Fa'iz, aka danna kararrawar son shigowa fallon. Daga nan inda nake kwance nake tambaya,
"Waye?"
"Ni ne Shu'aib".
Na bude ina dariya, "Yaya Shu'aib kaida wa?" Shima dariyar yake yi, ya shigo na bashi hanya ya wuce ya zauna a kujera muka soma gaisawa. Sannan ya ce.
"Yaya Fa'iz ya turo ni inzo in karbi ATM dinki in amso miki kudi a bankin UBA ko kina da bukatarsu, in kuma hada miki (tablet) dinki in sanya miki 'Interner data' in dora ki akan 'social networks' akwai 'group' na A.B family a (whatsapp) kowa yana ciki ki dinga hira da 'yan uwa madadin kiyi ta zama shiru".
Ban yi musu ba na mike na dauko masa 'Samsung tablet' din na kawo mishi ko ni zanso hakan. Amma jaganar karbo kudin a UBA na ce.
"Shu'aib bar kudin nan a muhallinsu, me zanyi dasu? Bana bukatar komi sai abinci gashi nan dankare nau'i-nau'i a 'store' da 'freezers, ga Ya'u na kawo katin waya. (I need nothing)".
Ya gyada kai cikin gamsuwa, hannunshi da idanunshi akan tablet din yana ta shiga 'applications' muna ci gaba da hirar mutanen gida da na Giwa.
Na mike na kawo masa lafiyayyen 'yoghurt' din 'L&Z Dairies' dake cike da (fridge) dina da sabon cup-cake din da nayi jiya.
Na ce, "Shu'aib, ina Hajjaty?" Sai bayan da na fada ne kunyar kaina da nadama suka zo suka rufe ni, muryata ma a lokacin tayi kasa sosai.
Dariya yayi, "Hajjah tana nan lafiya ko jiya na je Giwa sun tafi Umrah ita da Baba Na'ibi".
Ya cigaba da shan L&Z Dairy yana lumshe ido saboda gardin madarar ya aje gorar, ya ce.
"Wai kuwa don Allah Aunty Fa'iza yaya kike yi Yaya Fa'iz yayi miki magana?"
Shu'aib kusan sa'a na ne domin bai fi shekaru biyu ya bani ba, tsakaninsa da Fa'iz kuwa shekaru bakwai ne , mukan tattauna matsalolinmu da junanmu tun sanda muka fara hankali.
Nayi murmushi na ce, "Kamar Yaya Shu'aib?"
Ya ce, "Yo mutum ba fara'a kullum fuska kamar bindinga, babu alamar rahama sai muzurai. Duk inda yara suke ya tashe su. Shi ne nake mamakin yadda zai zauna da iyali yayi mu'amala ta dadin rai dasu. Don na tabbata in ba mace mai tsantsar hakuri ba, babu wadda zata iya daukar ginshirar Yaya Fa'iz ...".
Dariya nayi, "Baka da dama Shu'aib! Ni dai toh!! Ba zan ce baya magana ba, amma yafi yi a waya da abokansa!!!:.
Na jawo wata hirar don hirar Fa'iz da yake sani ya na sanyani cikin wani hali, da ni kaina ban san shi ba. Ban san irin shi ba, mai wuyar fassarawa ne.
Har la'asar muna tare da Shu'aib bayan ya hada min 'Whatsapp, wattpad, Facebook, Twitter da Instagram. Sannan ya zuba min duka numbobin 'yan uwa, muka yi sallama na juye duka 'cup cake' dinnan nace ya kaiwa Mama. A ranar na soma (chatting) dasu Ummi nima da (family group) dinmu ta watsapp.
Sati biyu bayan nan Mama ta sake aiko Yahya ya kawo min wasu jarkoki cike da magani mai zaki wai Mama ta ce in sanya a (fridge) in maida su ruwa sha na (tsumi). Da zuma iri-iri 'yan asali da abubuwa dai daban-daban wani ta ce asha da nono,. wani da peak-milk. Zuciyata tayi ta raya min meye nufin Mama na bani wadannan magunguna? Amma da nayi tunani mai zurfi Mama dai uwata ce wadda ba aurena da Fa'iz ne ya hadamu ba.
Mama uwata ce ta tun fil'azal ba zata bani abinda zai cutar dani ba, sai na dukufa shansu dare da rana yadda tayi 'prescribing' kowanne a rubuce a 'yar takarda har suka kare.
Satin ya kare ta sake aiko da wasu, haka muka yi tayi har watanni biyu.
Rannan a (chatting) nake tambayar Ummi ko tasan magungunan mene ne mama ke dirka min? Ta ce in fasalta mata su. Na fasalta har 'prescription' dinsu. Tayi alamar dariya ta hanyar turo 'emotions' na dariya ta ce.
"Mama nayi mana gatan da Hajjah, Aunty Hawwa da MOmin ABU suke kunyar yi amna. Ke dai kiyi ta sha Fa'izah ba zai cuce ki ba. Nima nan haka take aiko min dasu jarka-jarka kulli-kulli. Kiyi godiya kawai ga Allah da yayi mana baiwar uwar mazaje tagari mai kaunarmu tsakani da Allah.
Daga nan Mama ta koma aiko turaruku iri-iri 'yan Borno. Ni kam karba kawai nake ina faman turara daki. Amma sai Mama tayo waya ta ce.
"Fa'izah! Turarukan dana aiko miki fa ba na turara daki bane, jikinki zaki ke turarawa, kullum da yamma bayan kin fito wanka. Akwai abin turaren wuta na lantarki (burner) cikin lokas din (kitchen) dinki ki dauka kiyi amfani da ita, nasan hankalin ki bai kai wurin ba".
Na ce, "Akwai wata dana samu ne a falo da ita nake amfani, insha-Allah zanyi yadda kika ce. Mama Allah Ya kara girma".
Murmushi tayi ta aje wayar.
Tunda nayi nisa a sha da amfani da magungunan da Mama ke aikowa, sai na soma samun wani irin sauyi a jiki da zuciyata. Na nemi kiyayyar da nake yiwa Fa'iz na rasa tana (decreasing gradually) a kullum. Sai wani irin bege da son ganinsa. Da tsananin son kebewa dashi da son jin koda muryarsa ne amma babu. Tunda ya tafi ko sau daya bai kira ni ba har na soma zargin anya ba asiri Mama ke yi min ba, inso danta in kaunace shi? Nayi saurin kawar da wannan tunanin tare da yin istigfari a zuciyata.
[1/4, 12:23 am] Takori: ***
Na wayi gari ne yau cikin matsanancin nishadi, irin wanda ban taba tsintar kaina a ciki ba. Don haka na share ko'ina na goge lungu-lungu da sako-sako na gidan ya zama tas, sai sheki yake kamar lomarka zata fadi ka sanya baki ka side, duk da gidan ba wani datti yayi ba, don akai-akai nake kula da tsaftarsa. Na samu kaina da son shiga dakin Fa'iz, ko na rage kewar sa data addabe ni. A hankali na murda kofar na shiga dakin ga mamakina a bude ya barshi, sallama dauke a baki na.
Fa'eez ya kawata dakin baccinshi da duk wani nau'in kayan jin dadin rayuwa. Duk da A/c a kashe yake, amma dakin da sanyinsa, wanda ya hadu ya cakude da sassanyan kamshin '212'n da Fa'eez ke amfani dashi (on a regular basis). Babu komi dake cikin dakin da aka saye shi cikin Kadunan, bayan gidan Fa'iz kadai abin kallo ne, wanda bai cika girma ba. Banda katifar ruwa data mamaye gadon shi, karamin 'frame' din dake aje dai-dai santar inda yake sanya kanshi guda biyu kanana su suka dauki hankali na.
Sannu a hankali nake takawa zuwa garesu, yayin da kafata ke nitsewa cikin (center-carpet) mai tsananin taushi dake gaban gadonsa. Wanda ya sha bamban da sauran carpet din dake cikin gidan baki daya.
A hankali na russuna na dauki 'frame' din. Wani dadadden hoto na ne mai rungume da (teddy bear) wanda da alama ya kaiwa gwanaye ne sun wanke shi sun adana a cikin 'frame' din ya zama kamar daukar jiya-jiya. A kusa dashi wani hoton nawa ne cikin (swiss-lace) da goggoro, wato ranar partyn 'Indoor-sport hall' na nan Kaduna. Na tsuke giran sama da ta kasa wanda hakan ba karamin kyau ya kara min ba tamkar anyi shi ne 'in-style' ba bacin rai ba.
Na tambayi kaina wannan shi ne 'SO' kenan? Wanda ni bana jin shi? Don ko cikin wayata ba zan iya ajiye hoton Fa'iz ba balle a dakin barci na, inda nake ta da kai da mayarwa, a yayin kwanciya da tashi daga barci.
To me ya hana inso Fa'eez? Babu! Illa shi SO din abu ne wanda ke yin kansa, ko ince yin Allah ne, ko kuma wani hali na mutum ko wasu (personal-attributes) kan zamo sila na samuwarsa, and Fa'iz 'lack any loving attribute to be loved upon'. Wato bashi da wani hali da za'a so shi don su, sai wani sashe na zuciyata ya ce dani.
"A bisa rashin saninki kenan a da, banda yanzu, da kika fara lakantar ainihin waye FA'EEZ BAMALLI?" (And I came to the conclusion that) ba wani abu ne ya hana ni son Fa'iz ba illa tunanin baya... Inada RIKO, bani da mantuwa, sannan inada gudun wulakanci. Ina son momi na, Ina ganin muddin na sake da Fa'iz nan gaba zai koma min Fa'izun Hajja, wato Fa'izunsa na baya, zai sake sanya ni cikin 'problem' sannan zai sake tsanata...
Na cigaba da kallon dakin tare da komi dake cikinsa ba tare da na bude kowacce ma'adanar kaya ba (locker).
Ba don komi ba sai don nasha jin Hajjah na fadin, "Yiwa miji bincike ba ta'ada ce mai kyau ba, duk mai yiwa mijinta bincike wata rana sai ta binciko abinda zai daga mata hankali, ya hana ta bacci, ya sanyata bakin ciki wanda bata da maganinsa. Watarana sai ta binciko abinda ba alkhairi ba!".
Duk da baya dakin amma kamshinsa 'permanent' ne. Turaren '212' tamkar shi kadai aka yiwa. Komi na Fa'iz kamshinsa ne a jiki hatta takardunsa, bedsheet da labulayen dakin nasa. Na kasa fita a dakin Fa'iz, sakamakon wani shauki (emotion) dake dibana, zan so ace a lokacin yana cikin dakin ne ko yana falo yana kwala min kira in kawo masa kaza da 'chips' dinsa.
Shaukin dake dibana ne ya debe ni ya kwantar a gadon Fa'iz, ya janyo tattausan bargonsa ya lullube ni dashi. Da filon shi na tada kai na lumshe ido ina cigaba da shakar daddadan kamshin na '212' (men). Na soma zargin kaina da son Fa'iz a karo na farko. Wadannan (emotions) din (are for real!) YAA SATTAR!!! Ya Sattaru, idan mafarki nake ina rokon ka da ka farkar dani. Na bude dukkan idanuna dake lumshe, da karfi nayi wurgi da filon na zauna dabas a tsakiyar gadon ina wurga ido kamar mara gaskiya.
Eh, mara gaskiya ce (in fact!) Domin son karyata 'emotions' din nawa nake da gangan suna fin karfina. Na sakko daga gadon cikin barin-jiki, amma ga mamakina na kasa fita a dakin Fa'iz! Ina son dakin!! Ina son nayi bacci a dakin ko na samu nutsuwa.
Na koma na kwanta cikin mutuwar jiki da zuciya, naja bargo na rufe har kaina. Bacci mai karfi ya fisgeni.
Tafiya nake cikin wani kungurmin daji, ba gida gaba ba gida baya, na bullo ta gabas aguje nake a dalilin wutar dake bina, wuta bala-bala wadda ke tafe ta hanyar cin busassun kirare na jejin. Ina gudu ina kiran sunan Allah amma wutar nan bata bar bina ba. Gudu nake kamar raina zai fita har na sare, karfina ya kare.
Ina gab da faduwa a yayin da muka iso gab da wani tafkeken kogi, na daga kafata da niyyar in fada ruwan kawai ya cinyeni in huta, ya fiye min cinyewar wutar. Sai ji nayi wani sassanyan hannu ya rungume ni. Wannan hannun ya ce.
"QUL YAA NARU KUNI BARDHAN WA SALAMUN ALA IBRAHEEM... (Yaa ke wuta ki zamo mai sanyi da aminci ga Ibrahim)".
"Na yafewa Fa'izah dukkan abinda tayi min wanda na sani da wanda ban sani ba, wanda tayi akan sani da wanda tayi bisa kuskure, daga ranar da aka daura mana aure... har zuwa ranar da zan daina numfashi...!".
Kamin in dago inga wane ne? Wutar nan tabi ruwan. Bata ba dalilinta. Haske ya mamaye duhun dake mamaye dani. Na dago a hankali a lokacin zuciyata tayi fari kal! Babu sauran wani kunci ko wani kullaci a cikinta.
Na dubi wanda nake rike a kirjin nasa, wani kirji ma'abocin tarin ni'ima da sanyi da sanya salama, ba wani bane FA'IZ ne, FA'IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA.
Idona ya bude 'vivid' na tabbatar mafarki ne nake yi. In banda gumi ba abinda nake shirbinawa. Illahirin jikina duka rawa yake, na rasa abinda ke min dadi. Na kifa fuskata cikin tafukana na soma kuka.
Wannan mafarki shi ake kira kukan kurciyaa...! Wani irin sarawa kaina ya shiga yi saboda kuka. A hankali na mike na nufi kofa don fita daga dakin ko na samu sa'ida cikin zuciyata. Sai nayi tuntube da wani abu kamar littafi gab da bakin kofar dakin. Na russuna na dauka, littafi ne na ajiye tarihi da mihimman bayanai (Diary) da alama garin fita ya yarda shi ba tare da ya sani ba.
Anan bakin kofar nayi zaman dirshan ina buda shafukan littafin. Rubutu yayi na abinda ya kunshi tun daga ranakun kuruciyarsa, da tafiyarshi kasar Russia. 'Tittle' din rubutun shi ne;
"ONLY ALLAH KNOWS WHAT FUTURE HAS IN STORE FOR US".
A wani shafi Fa'iz yayi wani rubutu wanda da alama tun tali-talin kuruciyarsa yayi rubutun domin kwanan wata na kalanda wanda aka buga littafin cikinsa ya nuna hakan. Rubutun yayi matukar bani dariya.
"MEYE DALILIN DA YASA NA TSANI FA'IZA? BAN SANI BA! ILLA SAI DON CEWA ITA DIN KYAKKYAWA CE, TA FINI KYAU, A LOKACIN DA NAFI DUK ZURI'AR A.B KYAU SAI TAZO TA DAMENI TA SHANYE, KOWA YA KARKATAR DA KAUNAR DA YAKE YI MIN GARETA; MAIMAKON FA'IZ KOWA SAI FA'IZAH!".
Murmushi nayi na cigaba da buda shafukan. Wannan rubutun na shafi na gaba ga abinda ya rubuta.
"A Giwa ne. Misalin karfe goma na safe. Ina zaune falon Hajjah ina kallon fadan Isra'el a CNN. Wayar falon Hajjah dake ruri a gefena ban dauka ba sakamakon tunanin da yayi min rubdugu a wannan dan tsukin. Wanda bai wuce SON FA'IZAH ba! Fitowarta da daukar wayarta cikin kumfa ya sanyani kai dubana gareta. Duk da kasancewarta yarinya karama a wannan lokacin, 'yar shekaru goma sha hudu amman ta mallaki suffa kyakkyawa irin suffar da nake so ga 'ya macen da nake burin mallaka matsayin matar aurena. Tun daga wannan lokacin son Fa'izah ya ci gaba da ruruwa a zuciyata kamar gobarar daji.
Nayi kuka nayi nadamar da bata da amfani, musamman da na fahimci kakkarfar soyayyar dake tsakaninta da Yaya Aliyu.
Tsananin kishin Aliyu da nake, ya sanya ni hantarar Fa'izah a kullum a duk lokacin da yake zaune. A wauta ta a wancan lokacin Aliyu yaga bakin Fa'izah ya janye daga gareta, ya daina sonta amma ya ki. Asali ma sai kareta yake, yana bin bayanta cikin kowanne hali.
Akwai ranar da suka amso takardun jarrabawar firamare, don Aliyu yaji haushi kawai nace takardun Fa'izah basu yi kyau ba, komi 'fail' 'poor'!
To Aliyu yaji haushin, amma ba irin wanda nake so ya ji ba. A ranar ne yaga "love colour" na matsananciyar soyayyar Fa'izah cikin kwayar idanuna.
Hankalin Aliyu ya tashi kwarai domin yana gudun abinda duk zai kawo mishi matsala a soyayyar shi da Fa'izah. Musamman ni dana kasance dan gatan Hajjah, wanda dana furta sai aikatawa.
Aliyu ya dubeni cike da masifa, cikin harshen Turanci ya ce.
"Ina gargadinka Fa'iz! 'Don't dare say it'... wato kada ka taba furtawa sai kayi nadama anan gaba".
Na yiwa Aliyu kallon ko ni ko kai har su Fa'izan suka zargi wani abu. A ranar munyi musayarta ba dadi nida Aliyu da muka fito waje, har saida maganar ta hada da manya. Inda naji dadi shi ne inda Baba Barau ya ce babu wanda zai kuma yin auren soyayya cikin A.B tun daga kan Baban ABU wanda shima yayi ne ba bisa sanin mahaifinshi marigayi Abubakar Giwa ba. Ya kara da cewa.
"Fa'izah ta mai rabo ce. Don haka kada wanda ya sake ya furta mata yana sonta cikin mu duka".
Akwai ranar da na sanya Fa'izah cikin bacin ran da ya rudata har ta rungume Yaya Aliyu. A ranar ni kadai nasan abinda naji. 'In fact' kishi ne matsananci . Abinda tayi min bai bani haushi ba illa haushin Aliyu. A ranar ne nasan na fara kuka 'for sake of Fa'izah's love' (saboda son Fa'izah).
Fa'izah in tana kuka sha'awa take bani, in tana tsiwarta burgeni take, (I drive pleasure in making her cry). In tana kuka kyau take mini, sha’awa take bani. Shi yasa na kasance kullum cikin kirkirar abinda nasan zai sata kuka.
Bakin cikin tafiya ta Russia? Ba na komai bane ba don komi ba illa tsoron kada Aliyu ya aure Fa'izah kafin na dawo.
Na karyata kaina a wurin Hajjah da su Baban ABU, Baban Kaduna da Baba Na'ibi ranar da suka kawo min ziyara ta farko kasar Russia, na gaya musu cewa dukkan abinda nake cewa Fa'izah tayi, don inga hawayenta ne wadanda ke sanya ni nishadi, su kuma sanyani MURMUSHI.
Komai na Fa'izah ina son shi, sannan 'is special' agareni. Duk abinda nayi mata nayi ne domin KAUNARTA da 'pretending' kaunar, 'as I have no option' banda yin hakan. Na farko ban isa in furta ba, na biyu kishin yadda Aliyu ya kankane komai nata, na uku ita kanta Fa'izar ta dauke ni makiyinta ne na a buga a jarida, ba abinda zanyi ya goge hakan daga zuciyarta. A zahiri, na soma son Fa'izah ne daga ranar data dawo Giwa. Ta cinye min naman miya.
Babu abinda na tsana irin inga Baban ABU na dukan Fa'izah. A duk lokacin da naga hakan kukan zuci nake da azabta a zuci da gangar jiki. In shige daki inyi ta kuka.
Akwai ranar da Aliyu ya kamani ina kukan ni kadai a daki bayan na yiwa Fa'izah sharrin da ya sanya Baban yi mata dukan kawo wuka, ya tuhume ni amma sai na ce masa bani da lafiya ne.
Ranar da naji Hajjah ta ce mu tafi da su Ummi Kaduna (party) babu tunanin hanyar da zan bi in soke zuwanta da banyi ba amma na rasa. Cikin ikon Allah ta nemi da inzo rabon fada, anan ne na samu hanya ba don komai ba sai don KISHIN KADA WANI YA SO TA CIKIN A.B saboda yadda tayi kyau.
Duk da kasancewar ta yarinya karama a wancan lokacin, tafi duk 'yan matan A.B iya tsara kwalliya, tafi su kyau mai daukar hankali. Sau da yawa nakan ji samarin cikinmu na fadin DAMA A BASU FA'IZAH!
Na kan ji kishi kamar in kashe su, amma sai inga bari kawai in batata a wurinsu ta yadda zata yi bakin