Showing 1 words to 3000 words out of 81601 words

Chapter 1 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAH.txt

17 Oct 2025

183

[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼  KAI NE JARUMI💅🏼





WRITTEN BY HAERMEEBRAH



*NOTE*: BA SABON RUBUTU BANE TSOHUWAR AJIYA CE.

*Dan Allah kamar kullum ina kira akan ko bai maki dad'i ba yanzu ki adana saboda gaba wataqila ya miki*


Page 1:








Alhaji Hamza Muhammad Jambulo, d'an asalin garin kano ne gaba da bayan shi ma'ana uwa da uba dika kanawan dabo ne,Allah ya azurta shi da macen aure mai suna Maimounatou,da Yara biyu mata Rashida da Sakeenaa, Maimounatou ta fito daga tsatso na masu akwai, iyayen ta hamshaqan masu arziqi ne, ta na da kyau daidai misali, ta kasance kafin auren su da Hamza tana da masoya da yawa,manyan yaran attajirai,yaran 'yan kasuwa kamar mahaifin ta da yaran 'yan siyasa dik cikin su bata ga Wanda zuciyar ta ta aminta da shi ba dan haka sai ta qi zab'en kowa a cikin su dik da takura da azalzalar ta da iyayen ta suke akan ta fidda mijin aure.

Hamza shi ne saurayi na farko da ta fara so, ta had'u da shi a hanyar ta ta zuwa gidan Goggon ta, shi Kuma ya dawo daga 'yan bige bigen shi na neman kud'i,ya had'a zufa ya gaji liqis, dik da yanayin shigar shi da Kuma ganin yanayin shigar da ta yi ya San ba sa'ar shi bace, amma kyan ta da kamalar ta ya sa shi tsaida ita ya gabatar da Kan shi, Kuma ya Sanar da ita abinda ke zuciyar shi, tare da neman sanin inda take zaune saboda a cewar shi mace mai Kamala kamar ta be Kamata a tsaida ita a hanya ba, tin daga nan Hamza ya sace zuciyar Maimounatou ta ji dik duniya ba Wanda take so ya zama mijin ta sai shi, ta na son namiji da confidence irin nashi,babu b'ata lokaci ta masa kwatancen gidan su, ko a fuska bata ga tsoro da fargabar komai a tattare da shi ba, kamar yanda take gani a fuskokin wasu in ta sanar da su ko ita wace ce.

A hankali soyayya mai tsafta ta yi qarfi a tsakanin su, Iyayen shi sun San wacece Maimounatou a wajen shi, sun sha bashi hakuri akan ya barta ya nemi wata, duba da har a wannan lokacin bashi da tsayayya Kuma kwakkwarar sana'a, amma ya roqi da su ci gaba da Yi masa addu'a in rabon shi ce Allah ya bashi, in ba rabon shi bace Allah ya musanya mashi da Mafi alkhairi.

Bangaren Maimounatou kuwa ba Wanda ya San shi sai mahaifiyar ta, mahaifiyar ta ta yi iyakar qoqarin ta dan ta fahimtar da Maimounatou irin tazarar da ke tsakanin ta da Hamza amma ta kafe sai Hamza,haka ta hakura ta kyale ta sannan ta gabatar da buqatar ta wajen mahaifin Maimounatou, da labari ya riske shi Shima kafewa ya yi ba zai aura mata talaka ba, ya Saida akuya ta dawo ta na ci masa danga, sai dai a cikin yaran abokan shi hamshaqan 'yan kasuwa ya aura mata Wani, Maimounatou da Jin haka ta hau kuka, rashin lafiya kuwa har da kwantawa a asibiti, akan dole iyayen ta suka  hakura suka aura masu junan su.

Tinda Hamza ya auri Maimounatou be tab'a zuwa wajen kowa roqon ko da allura bane, ya jajirce ya tsaya da qafafun shi Kan jiki Kan qarfi,da dad'i da wuya, rana da iska, damina da rani ya nemi kud'i dan rufa wa Kai da iyalin shi asiri,shine dako, shi ne share sharen manyan shagunan 'yan kasuwa, shi ne garuwa shi ne faci shi ne Saida kayan miya, dik wata sana'a da Hamza ya San za ta kawo masa kud'i be zauna ba ya tab'a ta, be dogara da kwalin makaranta ba , su na nan a haka yau da dad'i gobe da d'aci har Allah ya azurta su da yaran su biyu 'yammata kyawawa.

Rasheeda itace babba, sannan Sakeenaa, tsakanin su akwai tazarar shekara biyu, Yau da gobe Hamza ya na 'yan bige bigen shi har Allah ya sa ya samu tsayayyar sana'a ta Saida shaddodi manya da qanana da yadi Shima manya da qanana sai jallabiyyu na maza, albarka ta yawaita cikin kasuwancin shi nan da nan sai arziqi ya zauna masa Shima aka fara sharafin duniya na masu akwai da shi, a da ana Kiran shi da Hamza Kai tsaye, yanzu kuwa Alhaji Hamza Muhammad Jambulo da shi aka San shi.

Wata rana suna zaune da matar shi Maimounatou da 'ya'yan su inda  Rasheedah ke da shekara goma Sakeenah kuwa na da shekara takwas, Maimunatou na zaune kusa da mijin ta ta dora qafar ta daya a cinyar shi shi kuma yana matsa mata, a cewar shi ta gaji da aikace2n gida dole ya mata tausa,

" Tawan ki duba fa ki ga yanda Allah ke hukuncin shi, an hana ni ke a baya ba dan komai ba sai dan talauci, amma yanzu daga ni har ke bama qirga zuwan mu qasa mai tsarki nawa  mu da yaran mu, a yanzu kowa dai ya shaida Hamza me buga can buga nan ya zama Alhaji Hamza"

A hankali ta zame qafar ta ta matsa sosai jikin shi, kwantar da kan ta ta yi a kafad'ar shi sannan tace,

" Mijina KAI NE JARUMI NA dogaro da Allah da jajircewar ka ne suka Kai ka matakin da ka ke Kai a yanzu,sannan ka sani tun a  baya na yi alqawarin ko da shi ko bashi kai zan aura Kuma na aure ka d'in a halin baka da shi,amma ba gashi ba yanzu Allah ya dube ni ya sa ka kaima ka zama mai akwai din, dan haka godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, Allah ya raya mana zuri'ar mu,"

"Ameen Jaruma ta"

Sumbatar ta ya yi a  goshin ta suka ci gaba da hira akan samu da rashi, Wanda yake faruwa da izinin Allah, Rasheedah dake gefen su kuwa kyab'e baki ta yi ta tashi ta yi dakin ta.

Rasheedah: Rasheedah Hamzah, ta kasance Fara ce irin farinnan mai matuqar kyau da daukan hankali, sannan akwai ta da kyau daidai misali, ga gashin ta baqi mai cika saidai bai da tsaho sosai, Rasheedah kwata2 ba ta dakko halayyar iyayen ta ba ko kad'an , tana da wasu irin halaye masu wuyar sha'ani,Rasheedah na da tsananin qin talaka, 'yar Qarama da ita se girman Kai, kwata2 ko qawaye ba ta yi sai da yaran masu akwai, da yanda take son kuɗi da abin duniya haka take son ibada da anyi salihar mace.

Sakeenaa: Sakeena sab'anin rashida ce daga halitta har kuma halaye, domin kuwa ita baqa ce irin baqinnan mai matuqar kyau, gashin ta baqqiqirin Mai yalwar tsahi da cika, girar ta kamar an gyara mata ita take a ko da yaushe ka kalla, makaranta bari na taqaita maku akwai kyau wajen Sakeenaa, ta bangaren halayyar ta kuwa tayo halayyar  mahaifan ta sak, kai har za a iya cewa ta d'ara su kyan hali,akwai ta da  son ibada, tin Kan ta Iya sallah take qoqarin gwadawa har ta Iya sallah, a qarancin shekarun ta in ta ga iyayen ta na azumi zata kame bakin ta tace itama yau azumin take kowa nata ne da talaka da mai kudi, bata ware wa, gashi a duniya tana son 'yan uwan ta musamman Rasheedah.

Wannan sune 'Yammatan Alhaji Hamzah.

A kwana a tashi a sarar mai rai,Rasheedah da Sakeenah sun zama manyan 'yammata, bayan saukar qur'ani da suka yi tin su na Yara, sun sake yin wata a yau,inda suka samu kyaututtuka masu yawa musamman Sakeena da ta yi haddar ta ba algus, baqin ciki kamar ya kashe Rasheedah dan ganin yanda ake ta ba wa Sakeenah mahimmanci a makarantar, amma ba yanda za ta yi dole ta danne ta bar abun a ran ta.

A hanyar su ta komawa gida ne suka  had'u da wani kyakkyawa Kuma kamilin saurayi,babu b'ata lokaci ya tsaida su,sallama ya yi musu, Sakeenah ce kawai ta amsa, Rasheedah kuwa qa'idar ta ne se ta fara kallon mutum in ta ga ya mata sannan ta amsa Kiran shi ko sallamar shi, in be mata ba ko mutum zai shekara yi mata sallama ko a zuci ba zata amsa shi ba, ta na kuwa juyawa idanun ta suka sauka a saman fuskar shi ta Kai duban ta kowanne bangaren na jikin shi nan da nan  kyaun shi ya yi gaba da ita ta ji ya yi mata, se dai kashhhh a qafa ya zo, dan bata ga alamun Yana tare da wani abun hawa ba, ko da ace machine ne kuwa, kawai sai ta had'e fuskar ta ta juya ta fara sauri dan Isa gida,Sakeenaa ce ta tsaya ta amsa masa sallamar shi sannan suka gaisa, yana kallon yanayin Rasheedah a ranshi yace,

'Gwanda da Allah ya rufan asiri ba ke nake so ba,lallai yau da na san se na wahala wajen neman soyayyar waccan nunar ranan'

A zahiri kuwa gabatar da kan shi ya yi a wajen Sakeenaa in da ta nuna mai gidan su da suke hangowa sannan tace,

" Na gode da soyayyar da ka furta ka na min Adnan, amma zan baka hakuri, ba dan ka na da makusa ba, sai don ina son kabi doka da tsarin mahaifina, shi ya kamata ka fara samu ya baka izinin ganina, domin shi zai aurar da ni, kaga bai kamata na fara kula ka ba da izinin shi ba ko?"

Wata kyakkyawar ajiyar zuciya ya sauke dan a da ya d'age nunfashin shi ne saboda tsoron kar ta yi rejecting d'in shi,se Kuma ya ji magana ta hankali da tarbiyya daga bakin mace Mai daraja murmushi ya sakar mata sannan yace,

"Amma kin matuqar tsorata ni,kar na ja ki da hira yanzu sai nazo gidan na ku,meye sunan malamar na gabatar maki da kaina da suna na amma ke ki na min rowar naki,"

Murmushi ta yi daya qarawa fuskar ta kyau, sannan ta sanar da shi sunan ta, suka yi sallama ta tafi,yana ta kallon ta har ta shige gidan su.

Bakin ta d'auke da sallama ta shiga gidan nasu, bata tarar da kowa a parlour ba har  tsakar gidan, dan haka sai ta wuce d'akin su direct ta tarar har Rasheedah ta cire kayan ta ta saka wasu ba tare da ta yi wanka ba, al'adar ta kenan ita tsafta bata cikin agender din ta, kad'a kai Sakeenaa ta yi ta wuce ta cire kaya ta dau towel din ta na  wankan ta shiga bathroom, tsaki Rasheedah ta yi sannan tace,

"Aikin banza ace wai duk kyaun da Allah ya miki, ki tsaya sauraran wancan abun, da ganin shi ba qaramin matsiyaci bane, me zaki da shi? So kike duk sanda zanje gidan ki na qulle abinci na a leda ko a food flask na je? Me yaci da zai baki? Kin wani tsaya kina ta rangwad'a kina karairaya, ko dai kyaun shi ne ya rude ki? "

Tsabar mamakin kalaman yayar ta ta ne yasa ko juyawa ma ba ta yi ba ta tsaya cak can Kuma ta fice ta bar Rasheedah na ta zagin ta akan tsayawa da Adnan,abubuwan da ta fada mata sun matuqar qona ranta, amma dake itan ba mai ruqo bace kan ta fito wanka ta manta, haka suka shirya suka ci abinci, kome suke sai ta mata mita akan ta rabu da wannan talakan tin kan abun ya kai kunnen mahaifin su, bata ganin nata saurayin Auwal mai kuɗi ne, dan ma yace ba zai na b'ata ta da kudi ba yanzu har sai sun yi aure kar iyayen ta masu ra'ayi su ce ba son Allah yake mata ba,a haka har dare ya yi Abban su ya dawo.

Suna zaune a babban parlorn su, as usual ana ta hira bayan sunyi sallar isha'i, sun ci abinci, sallama aka yi , wanda take Sakeenaa ta gane mai muryar amma ta dake, Abban su ne ya miqe ya yi waje dan ganin waye, Sakeenaa ma tashi ta yi tai ma maman ta sallama akan sai da safe yau ta gaji bacci take son yi da wuri, miqewa itama Rasheedah ta yi tabi bayan ta, ba ko sallama ma maman su  ta yi daki kai tsaye, addu'ar shiriya Maman su ta mata a ranta, ganin halayen yaran nata sun banbanta kamar ruwa da wuta sai ta yi tasbihi ga Allah ta nema musu shiriya baki daya, bayan jimawa kadan Abban su ya dawo, ya na murmushi.

" Maimunatou na barkan mu , da  dikkan alamu bana zan aurar da yaran nan, da izinin Allah, "

Cikin farin ciki da zumud'i take tambayar shi me ya faru,

" Abban Rasheedah me yasa kace haka, wanene ya shigo Kai tsaye cikin gida?"

Dariya ya danyi sannan ya bata labarin zuwan Adnan, kuma ya shaida mata cewar, ya masa izinin ya ci gaba da  zuwa  in sun daidaita Kan su to, in yarinya ta ga be mata ba ba zai wa 'yar shi auren dole ba, ya sanar da shi qa'idar zuwa zancen shi a sati sau d'aya ne, sannan kuma daga bayan la'asar ne zuwa kafin magrib, kuma a cikin parlourn shi babban nan zasu na hirar ba a waje ko farfajiyar gidan ba, kuma baya son saurayi yana kashe wa d'iyar shi kud'i, in ya aure ta ko kantin kwari ne ya sai mata, Adnan ya ji dad'in hakan sosai ba kad'an ba, hakan ya qara masa so da qaunar Sakeenaa, ya tabbata zai yi aure gidan mutunci, Adnan maraya ne, dan haka yake son ya samu macen da zata riqe shi da gaskiya da amana.

Bayan wata shida da haduwar wadannan masoyanne akai auren su, inda gidan Rasheedah ke a kabuga, ita kuma Sakeenaa take a can cikin Jambulon tsakanin ta da gidan su akwai tafiya sosai, anyi aure cikin rufin asiri da kwanciyar hankali, wanda wannan aure ba qaramin dagawa Rasheedah hankali ya yi ba, ta gano Auwal ba wani mai kud'i bane, dan daga gidan da take ma ya nuna mata hakan, gidane irin na qasar nan amma yasha siminti da fenti,daki biyu ne a gidan,sai band'aki ko arziqin kitchen babu, da alama da murhu za ta na amfani.

Gidan Sakeena kuwa ya sha banban da na Rasheedah, gida ne makeke na masu hannu da shuni, kowa ya yi mamakin ganin irin gidan da Adnan ya ajiye Sakeenah duba da yanda ya zo kamar bai da komai.

Bayan wata daya da kwanaki ne Rasheeda ta matsawa mijin ta akan se ta je ta ga gidan 'yar uwar ta dan ta ga shin abinda ake fad'a gaskiya ne? Daga nan ta je gida gaida iyayen ta, sanda ta fara bi ta gidan iyayen su mahaifiyar su ta bata tabbacin irin daular da aka Kai Sakeenah kasa boye baqin cikin ta ta yi, dan takaici da baqin ciki har kuka ta je tsohon dakin su ta sha ta gode Allah, kafin ta shirya ba ko sallama ta wuce gidan da aka mata kwatance shi ne na Sakeenah, ba tare da ta shiga gidan ba ta tsaya ta na kallon shi daga nesa ta na hawayen danasanin auren Auwal hawayen ta ta share ta samu adaidaita sahu ta yi gida, tin daga ranar ta yanke masu zaman jin dad'i da nishad'i ita da mijin ta Auwal....
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼  KAI NE JARUMI💅🏼





WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





Page 2:



A hankali Sakeenaa ta fuskanci irin qiyayyar da 'yar uwar ta ke mata, ba qaramin baqin ciki ta yi da ta gano hakan ba,ta yi kuka sosai akan baqin ciki, ita dai ta san tana matuqar son yayar ta ta, bata son duk wani b'acin ranta, a baya ta zaci kawai haka halin ta yake yawan kushe abun wasu da son ta burge mutane, ta zaci kowa ma haka take masa, bata tab'a tunanin wai hassada take mata ba me qarfi haka.

Duk sanda Sakeenah  zata kai mata ziyara kuwa sai ta debi abubuwa sosai ta kai mata, kama daga dangin abinci, sutura ,abin sha,da dai sauran su ta Kai ta na Mai nuna wa yayar tata abinda ta mallaka nata ne ba banbanci dik dan ta sa ta dena nuna mata qiyayya a zahiri, amma inaaa sam basa burge Rasheedah ita dai so take ta zama Sakeenah, Sakeenan ta koma ita, dan haka ta na kawo mata kayayyakin nan za ta mata tatas, ta yi mata rashin mutunci,Kuma ta karb'e tare da fad'in raba arne da makami ai ibada ne, kalmar nan na matuqar qona ran Sakeenah wato ma ita ce arniyar.

Abinda ya faru kenan a yau da Sakeenah ta kawowa 'yar uwar tata ziyara, domin a cewar ta Bata son zumuncin su ya lalace koma mene ne ita ce qarama dole ta bi yayar ta Dan sada zumunci, sannan Allah da Manzon sa ba su son duk bawan da yake yanke zumunci, ta na kwadayin ladan da Allah ke ba wa masu Sada zumunci ranar gobe kiyama.

Sanye ta ke da wani leshi Mai sauqin kud'i saboda gudun kar ta saka Mai tsada 'yar uwar ta ta ce ta je nuna mata azziqin tufafi, haka zalika takalmi da jakar da ta d'auka dik masu sauqin kud'i ne Wanda ta siya na musamman saboda zuwa wajen Rasheedah, Adnan ya Kai ta da Kan shi har qofar gidan ya ajiye ta, ya fitar mata da kayayyakin da zata Kai wa Rasheeda, kudi ya qara mata ya ce ta Kai wa Rasheedah, sannan ta gaishe su in ta gama ta kira shi ya Maida ta gida.

Dubu goma ne ya bata ya ce ta ja jari, sallama su ka yi ya wuce, shigar ta ke da wuya ta tarar da Raheedah tana hura murhu zata dora abincin rana, aje maficin ta yi tana yatsina fuska ta ce,

" A'a kaga matan alhazawa matan da suka ci suka tada kai,ku ne a tafe cikin rana haka?"

Murmushi Sakeenaa ta yi sannan ta shige parlour dan ta san sarai magana ta faɗa mata, zama ta yi tare da cire hijab din ta da niqab, sallama Rasheedah tayi ciki ciki ta shiga, tare da dage labulen sakamakon duhun da wajen ke da shi in ba wuta, gaishe da ita Sakeena ta yi cike da farin ciki tace,

" Rasheedah ga Apple na kawo maki dan na kula mun samu dan baba, na san zaki so shi Allah ya raba ku lafiya ya bada mai albarka," tana maganar ta na bud'e ledar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login