Showing 33001 words to 36000 words out of 81601 words
Chapter 12 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAH.txt
Kawunan ka ka musu sallama kar ka tafi ba tare da sanin su ba"
Kallon Mama suka yi da ta sha majina irin na masu kukan nan,
"Adnan Allah ya maka albarka, ya faranta maka, Allah ya jiqan mahaifan ka da Sakeenaah ya raya abinda kuka haifa Allah ya kare mana Kai a dik inda ka shiga, Allah ya habaka kasuwancin ka Ameen,"
Amsawa suka yi dikan su da "Ameen" sannan sika miqe don raka Adnan zuwa waje, wasiqar da ya ga an rubuta sunan Atiyyaerh ya zaro a aljihun shi ya damqa a hannun Mama sannan ya yi gaba zai fita,Atiyyaerh ce ta riqe shi tana kuka, tana kiran Mummyn ta, Adnan zuciyar shi ta cika fam da quncin rabuwa da mutanen da yafi so a rayuwar shi, bai san sanda ya yakice ta ba ya shige motar ya ja da gudu yana kuka, Mama da ta sunkuya ta d'aga Atiyyaerh dake birgima a qasa, kukan itama take, Abba share kwallar shi ya yi ya taimaka mata sika d'aga ta, dan ji ta yi ta yi mata nauyi, sai tirjewa take, tana kiran Daddy da Mummyn ta, a haka sika shiga,Mama ta goya ta,yar wayar shi Abba ya lalubo ya kira Auwal.
Ba su fi awa biyu a zaune ba Auwal da Rasheedah suka shigo, bayan gaishe2 ne, Abba ya sanar masu da dalilin kiran nasu dika, ya kira su ne dan damqa amanar da marigayiya Sakeenaah ta bar masu, Rasheedah ce ta bata rai sosai, sannan ta ce..........
[01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HERMEEBRAERH
Page 16:
Bakin ta da ta bud'e za ta yi tijara kamar yanda ta Saba ta kulle gam dan ganin yanda kowa ya d'aure fuska dan son ganin qarshen rashin mutunci da qiyayyar da take wa 'yar uwar ta ta, musamman ma Auwal da yake jin in tace zata yi wani gangancin nuna ita fitsararriya ce ba abinda zai hana shi yau a gaban iyayen na ta ya jibge ta ai hukunta ta ya yi tinda Rasheedah dai kamar jakka take sai ta ci bugu take nutsuwa yau kuwa a shirye yake da ya hukunta ta gaban iyayen nata, tana fuskantar hakan daga wajen Auwal sai ta ce,
"Ba sai ka tashi ka dau akwatin mu tafi ba, aiki ma malam kawai ina fama da wasu qananan a gaba na a tashi a wani jonan wata,"
Ta na kaiwa nan ta yunqura ta dau qarama daga jakunkunan Atiyyaerh ta yi waje ta na mita addu'ar shiriya iyayen ta da mijin nata suka bita da shi, Mama sai share hawaye take ta na kukan tausayin marainiyar Allah, da ace Sakeenaah ta yi shawara da ita kafin dasa wannan tunanin a zuciyar ta ai da ta hane ta, ta sauya mata da wata shawarar Mai billewa, domin a iya hangen nesanta na manya bata hangowa Atiyyaerh Jin dad'i wajen Innar tata ba sai wahala, Abba ne ya dinga lallashin ta ya na bata baki ya na nuna mata abinda ya sa Sakeenah yanke wannan hukuncin, fatan su Allah ya sa yarinyar ta yi SANADIN shiryuwar Rasheedah.
Rasheedah na fita waje ta ga mota mai matuqar kyau sosai a fake a harabar gidan, gefen motar kuwa drivern gidan marigayiya ne jingine da ita, drivern ne ya duqa kad'an ya gaishe ta, sannan ya tambaye ta inda mijin ta yake, amsa masa ta yi da,
"Ya na ciki akwai Wani abu ne?"
Sai Wani zaro ido take, komawa gefe drivern ya yi yana jiran fitowar Auwal, zuwa ta yi kusa da shi tace,
"Malam ba aiko ka aka yi ba ne? To ka isar min da saqon mana in ya so in ya fito se na Sanar da shi,"
Kallon ta ya yi kawai dan yana da labarin ta tsaff dik Wani kalar wulaqanci da qiyayya da take nuna wa Madam din su ya sani, dan haka cike da jin haushin ta ya kalle ta ya ce,
"Amma ai da na zo kk ga na maki magana hakan na nuna maki cewa na san ko ke wacece,shi ya sa ma na tambaye ki mijin ki, To saurin Jin saqon da yake ba naki ba na mene ne? Ki Jira ya fito mana mtswww"
Cikin tsananin mamaki da shakkar drivern ta ja baya tana qunquni, dan ba qaramin jibgegen mai qarfi bane, fuskar nan baqiqqirin ba wasa a tattare da shi, komawa ta yi ta qame sannan tace,
"Ka gama b'oye2n uwar da zaka b'oye duk uwar da zaka fad'a zai dawo kunne na ne"
Cikin fushi ya matsa daf da ita yace,
"Uwar wa kk nufi?"
Su Abba ne suka fito dan rako Auwal da Atiyyaerh dauke da akwatunan yarinyar, Abba ne zai Kai su tinda Auwal ba shi da abun hawa,kicibus suka yi da abinda ke faruwa tsakanin Rasheedah da driver,kallon Rasheedah suka yi wadda ido ya firfito waje ya mata gulu2 se wara su take cike da tsoro, a firgice take da mutumin kamar ka ce mata kyatt ta saka gudu, hanlalin ta ya yi mugun tashi to dukan ta wannan basamuden ze yi ko me?
"Niiiii....niiii...ni.. ban ce uwarr ka baaa.. ai,"
Ta qarasa maganar tare da damqe bakin ta da ke rawa, tsoro ne ya mamaye ta ta ji kamar ta saki fitsari saboda maimaita kalmar uwar ka da ta yi, tana kyalla ido taga su Auwal na fitowa da gudu ta kwasa ta yi wajen su tana maida hawayen daya taru mata, Auwal na ganin yanayin ta sai ya ji be ji dad'in hakan ba, ko ba komai ya na son matar shi, halayen ta ne baya so ko kad'an, cikin yanayin daure fuska ya ce wa mutumin,
"Malam lafiya zaka sa min mata a gaba kana muzurai? Kai ba drivern Alhaji Adnan bane?"
Cike da girmamawa ya qaraso, ya gaishe su, sannan ya sanar dasu ya kai Adnan Airport ne se ya bashi umarnin ya kawo motar gidan Auwal,ya je gidan nasu ya tarar ba kowa shine tunanin shi ya bashi ya zo nan, ya San ba za su wuce nan d'in ba, godiya su ka yi sosai, Mama hawayen tausayin Adnan da qaramar 'yar su ne kawai ke kwaranya a idanun ta, shikenan yanzu ya tsallake wata qasar dan kawai ya manta da damuwar rashin matar shi,anya kuwa ba za su nemi fatawa wajen malamai ba? Anya ba a cutar da shi ba? ta na wannan tunanin ta ga Suna Saka kayan Atiyyaerh a motar, sannan Auwal ya ce,
"Mu je ka aje mu ka dawo da motar, Dan ka ga dai mu bamu da inda za mu ajiye ta, kar a sace a wannan unguwar tamu, gwanda a barta nan kawai zai fi"
Da Jin haka sai driver ya ce,
"Ai Yallab'ai cewa ya yi na maida ku can gidan shi, in yaso ko in akwai wani abu da kuke buqata a can gidan naku kun je ku dauka daga bay,amma yafi son ku koma gidan nashi da zama tinda ba kowa ciki se masu aiki"
Auwal ya so ya qi karb'ar tayin komawar su wannan katafaren gidan Rasheedah ta hau rantsuwar ba zata koma tsohon gidan su ba ga gida sun samu daga sama su tsaya Wani halin qauyawa, Abba ma tausar shi ya yi akan ai ba komai ya karb'a su koma can d'in zai fi maslaha, da kyar Auwal ya amince za su koma d'in, murna Rasheedah ta hau yi ko kunya bata ji bakin ta har kunne, ashe da rabon ta a cikin wannan makeken gidan,kaiii jama'a daɗi kashe ta, haka suka d'unguma suka yi gidan, suna isa bayan sun fitar da kaya ne ta shiga ciki da Farha da Ayiyyaerh, driver na ganin ta wuce ya zagaya gefen Auwal ya fad'a masa wata magana qasa2, sannan suka yi sallama ya tafi, yana waiwayen gidan yana hawayen kewar iyayen gidan nashi masu son shi, masu karamci, addu'ar samun Rahamar Allah ya yi wa Sakeenaah sannan ya nema wa uban gidan shi sauqi a wajen Allah daga halin quncin da yake ciki,kafin su rabu se da Adnan ya bashi jari mai tsoka da qaramin gida, shida me gadi, su Shamsiyya ma sai da ya musu ihsani sosai kafin ya sallame su, dik da ya basu zab'i in suna so Suna Iya ci gaba da zama idan sabuwar matar gidan bata da matsala da hakan.
Tana isa ta aje Afrah dake hannun ta ta saki hannun Atiyyaerh da ta tattaka ta nufi sama dan dubo Mommyn ta, ta na tafe ta na kiran mommyn nata da Daddyn ta, Rasheedah kuwa juyi ta hau yi tana kallon gidan, wani daɗi ne ya kama ta, yanzu ta zama hajiya kenan, ga sauran suturun Sakeenaa nan, dan da akai rabon gadon Sakeenah surutun ta kaf an bar wa Rasheedahn ne tinda kusan girman su d'aya, murjewar fata kawai Sakeenaah zata nuna wa Rasheedahn saboda banbancin Jin dad'in rayuwa,a lokacin da aka ce an barmata suturun qunci ta dinga yi ta na fad'in ba a bata komai ba, gani take duk uwar dukiyar su ace ba ta da abin gada na qanwar ta ta se sutura? Auwal ta gani ya shige ta ya yi dakin da aka kwatan ta mai direct, bin bayan shi ta yi da azama,daf zai bud'e qofar d'akin dan ya shiga ne ya juyo ya wurga mata wani kallon da yasa ta koma gefe da sauri, shiga ya yi ya saka key, inda aka masa kwatance nan ya leqa,baya ya yi da sauri, dan bai tab'a ganin abinda ya gani ba a rayuwar shi, kud'i ne maqudai masu yawan gaske, a cikin wata jaka qarama, gaba daya ya rud'e se zufa yake samun gefen gado yi ya zauna,yana kallon kudin daga nesa, takardar dake Kai ya dakko ya bude, karantawa ya hau yi a zuciyar shi, idonun shi sai zubar da hawaye suke, nan danan ya saki kuka sosai, tausayin bayin Allahn nan yake ji matuqa,a yau ya tabbata dukiya ba ita ce kad'ai farin cikin rayuwa ba,komai Allah ya baka ko da tsinke ne ya nufa ta SANADIN shi ne za ka yi farin ciki to kuwa za ka yi farin cikin,nan take ya ji duk soyayyar da yake wa Rasheedah a baya ta kau, domin ta dalilin ta ne wannan qunci ya sami wannan mutum na rabuwa da gudan jinin shi, domin ba dan qiyayyar da ta nuna wa Sakeenaah ba da tini yana tare da diyar shi, daure fuska ya yi ya miqe ya adana kud'in ya cire key d'in ya fita daga d'akin a bakin qofa ya gan ta ta na muzurai, Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya Isa d'akin da ya ke Jiyo kukan Atiyyaerh ya d'auke ta suka bar gidan, bin shi ta yi da kallo da son qarin bayani akan me ya Kai shi cikin d'akin Kuma me ya faru ta ga kamar ya yi kuka, Auwal kuwa ya fita ne saboda baya son ganin ya ta yanzu kwatakwata, ji yake kamar ya rufe ta da duka, ya rasa me zai gaya mata ya fidda mata wannan halayyar tata a jikin ta, kyabe baki ta yi ta ci gaba da exploring gidan.
Ana Kiran sallar azahar Auwal ya dawo da Atiyyaerh ya shige d'aki ya yi alwala zai wuce masallaci, Atiyyaerh da ke Jin yunwa ce ta ke tab'a Rasheedah ta na maimaita mata kalmar,
"Mummy tea, Mummy tea, Mummyyyy"
Jin da ta yi bata amsa mata ba sai ta fashe da kuka sosai, Afrah da ke tsotsar hannu lokaci zuwa lokaci ta tashi zaune tana ta kallon ta tana tsotsar yatsan ta babba, a fusace Rasheedah ta juya ta kalli Atiyyaerh da ke kuka ta ce,
" Wacce irin jaraba ce wannan, ke ba zaki bar mutane su huta ba? Dubi yanda kika tasar min yarinya, kin koma kin zauna a can ko sai kin ci uban ki yanzu,"
Cikin zare ido da d'aga murya take maganar, abinda Atiyyaerh bata tab'a sani ba kenan a rayuwar ta, ai ko ta fashe da wani rikitaccen kuka,ga yunwa na damunta, tin da suka dawo bata ci abinci ba, gashi har azahar ta yi Auwal ya so ya tsaya ya had'a Mata tea d'in amma kawai ya wuce masallaci.
Ko da ya fita ma tinanin halin da ya baro yarinyar yake, kukan ta har cikin ranshi yake jin shi, maqotan su Rasheedah basu tab'a jin kukan Atiyyaerh haka ba,unguwar ta talakawa ce Adnan ya yi gini a ciki domin ya na kwadayin taimakawa marasa shi, ya tabbata in ya yi gini a manyan unguwannin masu kud'i daidai da abincin da za a bayar sadaka ba lallai a samu masu buqata ba, dan haka ya yanke shawarar gina gida anan,Kuma yake taimaka masu sosai, tausayin yarinyar ne ya kama su dan a tinanin su Atiyyaerh na kukan rashen mahaifiyar ta ne,
"Ahhh lallai naga alama zaki fara cin ubanki kuwa,nace ki yi shiru se ki baren baki? Ke baki san menene shiru ba ashe? Tsit nace"
Ta dora yatsan ta a baki tana zaro mata ido, cikin kuka da gigicewa yarinyar ta kwantar da kanta a gadon tana runtse ido, dan a tsorace take da zaro idon da Rasheedah ke mata,amma ta kasa yin shiru, a hasale kuwa Rasheedah ta kaiwa bakin duka tana fad'in,
"Shiii nace kar na sake jin kukan ki"
Damqe bakin ta ta yi tana ci gaba da kukan a hankali, tare da ajiyar zuciya, a haka ta samu ta yi bacci, tana ta ajiyar zuciya, miqewa Rasheedah ta yi ta fice tana banbamin fad'a, Auwal ne ya dawo a gaggauce hannun shi d'auke da biscuits da madarar gwangwani babba da na Ovaltine, sai millo.
"Ki ji tsoron Allah akan amanar da aka baki, Ina jiye maki sanda amana zata ci ki, Marainiya ce fa? Wanne irin hali gare ki? Na yi matuqar danasanin had'a zuri'a da ke, na yi danasanin sanin ki a rayuwa ta, amma bawa baya wuce qaddarar shi, Rasheedah ke ce mummunar qaddara ta a rayuwa ta, Ina roqon Mai dika da ya bani iKon cin jarabawar nan,dana san haka kk da ba zan taba hada zuri'a dake ba?"
Ya na gama magana ya ajiye mata ledar ya wuce d'akin shi dan yin sallah tinda ya San yanzu Kam an riga da an idar a masallaci.
Wani irin haushin Atiyyaerh ne ya qara kamata,yanzu a Kan wannan yarinyar take ganin wutar qiyayya da tsabar tsanar ta a idon Auwal? Ina soyayyar da yake mata ? A Iya sanin ta dik laifin da za ta masa Kuma ko me zai faru tsakanin su Auwal be tab'a dena son ta ba, hawaye ta ji na bin kuncin ta, da sauri ta goge su, ta na ayyana kala kalar muguntar da zata gana wa Atiyyaerh.
Bata ba wa yarinyar nan komai ba kuwa na ci sai dare da suka zo cin abincin dare, ai kuwa ta na gama cin abincin ta hau amai, saboda yunwar da ta mata yawa a cikin ta, masifa da bala'i Rasheedah ta fara yi ta na dungure mata Kai, a haka ta gyara wajen ta na zage zage, tea ta had'o mata ta dangwara mata a pida ta haye sama, dan ta riga ta qudurta yau sai ta gwangwaje a sabon gidan nan halin da Atiyyaerh ke ciki kuwa ba zai hana ta hakan ba,
Auwal kuwa tinda ya fuskanci take taken ta ya wuce d'akin yaran shi maza ya yi kwanciyar shi da su bayan ya gama nuna masu su dinga kula da qanwar su, duk abinda take so Suna yi mata daidai Wanda za su iya, Wanda ba za su iya ba su na barin Maman su ta yi, budar bakin Yusuf kuwa sai cewa ya yi,
"Abbah ai na ga Mama bata son Ablaerh dukan ta kawai take da zagin ta ko da yaushe"
Auwal rasa amsar da zai bawa yaron ya yi Dan haka sai ya hau basu tarihin Annabawa har bacci ya d'auke su, su na nan kwance ya ji an bud'e qofa, Rasheedah ya gani sanye da wasu fitinannun kaya, sun bala'in mata kyau, da dane ba abinda zai hana shi zuwa gare ta, amma yanzu Wani irin kyankyamin sake kusantar ta yake gani yake tsabar munin halin ta duk ya manne a jikin ta ba zai so ya kwashi halin ta ba kuwa, Gani ta yi ko kallon azziqi bata ishe shi ba balle na tsiya, cikin shagwaba da tura baki ta ce,
" ko ka tashi mu koma mu yi abun mu can dakin mu ko kuma muyi anan,"
Kallon baki isa ba ya mata,in Kuma ki na iyawa zo ki yi na gani, murmushin mugunta ta yi ta fara cire rigar saman Yousuf da be bacci ba ya kalle ta,zata cire zanin ta kenan Auwal ya yi sufa ya cafke cikin rad'a mata magana a kunne ya ce,
"Baki da hankali ne? Meye haka kk yi a gaban yara? Muje can jarababbiya kawai mahaukaciyar banza wadda bata bawa abun kunya mahimmanci ba a rayuwar ta,"
Sallama ya wa yaran ya rufe su tare da dafa Kan su ya musu addu'o'i ya kashe fitila ya tura qeyar ta sika tafi, dariyar mugunta ce fal ranta,tin kan su isa ta qarasa cire zanin daga ita sai wata yaloluwar riga ciki babu komai, kallon ta ya yi cikin tsananin Jin haushin ta, kenan da a gaban yaran zata cire ta tsaya a haka? Lallai be tab'a sanin ya auri mahaukaciya ba sai yau,ita kuwa ko a jikin ta sai wani juyi take a gaban shi,kasa jure kallon ta ya yi ya fizge ta da mugunta ya wurga ta d'akin nasu ya banko qofa a ran shi ya na ayyana irin muguntar da zai mata tinda ta d'age se an yi🙊
Auwal tin Yana mata na mugunta har zuciyar shi ta yi laushi ta saki dan kuwa Rasheedah na da matuqar tasiri a wajen shi ta nan bangaren in dai zai kusance ta to damuwar shi na raguwa, halayen ta ya tsana matuqa dan se ka kwana tinani baka gano wanne ne na gari a halayen ta ba, da misalin qarfe uku na dare ya tashi ya zauna bakin gado ya na kallon ta ya na tinani kala kala akan halayen ta, ita kuwa tana ta kwasar baccin ta, a hankali ya tashi ya nufi bathroom Dan yin wanka, ya na fitowa ya Sanya