Showing 45001 words to 48000 words out of 81601 words
Chapter 16 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAH.txt
karambanin Afrah ya Kai ta ta saka wa Atiyyaerh tiraren ta a jiki kuma Rasheedah ta ji qamshin ranar Atiyyaerh sai ta daku, Afrah kuwa haka za tai ta kuka tana bada hakuri tare da Yi wa Umman nasu rashin kunya, Auwal ya sha yo musu shopping ya siyo kayan Kwalliya da turare domin Atiyyaerh amma haka Rasheedah zata kwashe, Yana so ya yi magana, ya na gudun ja wa yarinyar duka ko Wani zagin a wajen muguwar Auntyn tata.
Watarana ba da niyya ba Afrah ta dauki hijabin islamiyyar Atiyyaerh ta feshe shi da turare a zaton ta nata ne tinda iri d'aya ne, sai da ta gama shiri zata fita daga d'akin Atiyyah ta fito daga wanka d'aure da towel, ta kula da hijabin ba Wani baqin ruwan biro a jiki, fari ne qal, se ta tsayar da Afrah ta mata bayanin wannan nata ne, Dan kuwa na Afrah ya baci da ruwan biro, hakuri Afrah ta bawa Atiyyaerh ta miqa mata hijabin ta, ta koma ta d'auki nata ta Saka,sannan ta sauka ta ce wa Atiyyaerh Suna jiran ta a qasa, bayan kammala Shirin ta ne tsaf ta Sanya hijabin ta sauka qasa itama Gani ta yi Afrah ce kawai su Yousuf sun yi gaba, ta na zuwa kuwa hancin Rasheedah ya shaqi qamshin turaren Afrah a jikin Atiyyaerh, tini ta kama masifa da bala'i ta na fad'in Atiyyaerh ta raina ta bata Isa ta hana ta abu ta hanu ba, bud'e baki Atiyyaerh ta yi dan ta mata bayani, ta kuwa tashi a fusace ta Kai mata duka, bata kyale yarinyar nan ba se da ta lallasa ta tas sannan ta barta ta haye sama ta na ci gaba da zagin Atiyyaerh, kallon Afrah da ke kuka kamar ita ake duka Atiyyaerh ta yi sannan ta ce,
"Afrah in dai kina so na da gaske baki son ana dukana kamar mara gata ko galihu, ko dake bani da gatan ma ai, Dan Allah da son Annabi ki daina qoqarin sai nayi amfani da kayan ki, na gode da qaunar ki a gare ni yayata, bana fatan Allah ya gajiyar dake a wajen tausaya min keda Yayah Da Yah Sulaiman amma Dan Allah ki dinga taya ni kiyaye abinda za a dinga dukana akwai zafi, ba wai iya zafin jiki ba, Ina Jin zafi a nan d'ina, Ina Jin zafi Afrah a cikin zuciya ta, ba zan iya kwatanta miki ya zafin yake ba, ba na fatan ki ji irin wannan zaf'in Afrah akwai ciwo sosai,na riga na gama yarda Mommy na ta rasu Daddy na Kuma baya so na saboda Mommy na ta rasu shi yasa ya barni anan na sha wahala, na ji na amince zan jure komai, zan shanye komai, amma dan Allah ki taimaka min zamana anan ya min sauqi, ba zan iya ci gaba da jure irin wannan wulaqanci da quncin ba Afrar akwai ciwo sosai,"
Afrah ta kasa magana sai kuka, da gudu ta fad'a jikin Atiyyaerh ta rungume ta sosai kamar zata tsaga jikin ta ta shige ,banda gunjin kukan su baka Jin qarar komai a parlourn, Yousuf da Sulaiman tini sun Isa makaranta saboda a tinanin su Afrah ce ta tsaya kyale kyalen ta da ta Saba zata sa su makara, dan haka basu San wainar da aka toya aka cinye ba,sai da suka yi kuka suka gaji suka tsaya a tap din tsakar gida suka wanke fuskar su sannan suka tafi makarantar.
A haka Atiyyaerh ta saba da rashin kwalliya,ta Saba da azabar Rasheedah har ta dena wa duk Wani duka ko zagi kuka, sai dai ta yi Murmushi me ciwo ta bata hakuri,bangare guda kuwa duk wanda ya ganta zai rantse bata da damuwa, Atiyyaerh na da natural kyau Mai d'aukan hankalin me kallo, gata da nutsuwa da kamun kai.
*DUBAI*
Kwance yake a makeken gadon shi, yana ta tinani kamar kullum, har wannan lokacin bai yi aure ba, wayar shi ya lalubo ya danna kiran Abba, Abba na gani ya yi murmushi, ya d'aga kiran, bayan sallama da gaishe2, ne yace
"Abba akwai Wani abu da kuke buqata? Ka San bana so a wannan shekarun naka kana wahalar da kan ka, hutu ka ke buqata a yanzu Abbana"
"Alhamdulillah bamu da matsalar komai sai ta kewar ka, satin can na sama Ablaerh tazo mana hutun qarshen mako,kullum tazo zancen ta bai wuce mu bata labarin mahaifan ta ba, ka daure ka dawo ka ganta,domin kwanciyar hankalin ta dan ita gani take kamar baka son ta ,in ka dawo mu ma namu hankalin ya kwanta, gashi kaqi aure, wannan shine matsalar mu Adnan, to a gaskiya zan fad'a Maka bamu da wata matsala a yanzu se wannan, ka daure ka jure ko dan raya sunnar Annabi Muhammad ka yi aure, Kai fa ba ma'asumi bane Adnan, akwai lokacin da dole Dan Adam Yana buqatar mace,dan Allah ka daure ka yi aure,babbar soyayyar da zaka nunawa Sakeenah kenan ka tsare Kan ka daga fad'a wa halaka ta hanyar yin aure,"
Rintse ido Adnan ya yi cike da jin zafin mutuwar matar shi da kullum ke tab'a shi, ga kewar d'iyar shi dake dawainiya da shi, amma baya jin lokaci yayi da zai je ganin ta,
" Abba ka yi hakuri zan zo ne, amma ba yanzu ba, inshaa Allah zan zo ne,Kuma maganar aure zan duba na gani, Abba na kasa dena tuna ranar da ta barmu, Abba wa ka ke ganin zan aura bayan zuciya ta bata da Wani ragowar gurbin da wata zuciyar zata samu mazauni a cikin ta? Ina tsoron na yi aure na zama silar zubar hawayen wata Abba, Abba ku ci gaba da taya ni addu'a Allah ya sauqaqa min ya min zab'in alkhairi"
"To Adnan Allah ya kare mana kai, ya sa da rabon ganawa,Allah ya sauqaqa Maka radad'in da ka ke ji a zuciyar ka, Allah ya Maka zab'in alkhairi, ka kula da kan ka,ka kare kan ka daga zina,da shayen²n matasan yanzu in an ga kud'i da wadata sun samu se a dinga shaye shaye da neman matan banza, in ka ji wani abu na son mace na taso maka ka yi azumin alkhamis da litinin, ko ka samu ka yi auren ka,kar ka jefa kan ka halaka bayan Allah ya rufa maka asiri Adnan,"
Cike da jin dad'in addu'o'i da nasihar Abba Adnan ya yi godiya suka yi sallama ya koma ya kwanta, yana matiqar jin dad'in yanda Abba ke matuqar son shi,yake masa nasiha da take ratsa masa jiki ta dasa masa tsoron Allah.
******************************
Shirin tafiya kitso Atiyyaerh take ita d'aya, gobe akwai makaranta, Afrah ta riga da ta yi nata tin jiya, tana cikin tafiya ta kusa shiga gidan ne ta ji ana kiran ta, cike da b'acin rai ta d'aure fuskar ta, dan bata qaunar ko da jin muryar shi ne balle ganin shi..
.
.
.
*Thank u guys for ur comments ina jin dadi sosai, kuma yana sa na qara sambada maku typing ba tare da naji gajiya ba. ME LOVE U DA YAWA❤*[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERHMEEBRAERH
Page 21:
Tsayawa ta yi cak a inda take, dan bata son ya bita cikin gidan yana mata surutai marasa tushe da ma'ana a cewar ta,su Kuma matan gidan na biye masa ana cewa budurwar sa ce ita, da fuskar ta mai d'auke da gajeren Murmushi na ba yabo ba fallasa ta juyo, yana tozali da fuskar ta ya ji wani sanyi a ranshi,ba kadan yake son Atiyyaerh ba,shi in za a taimaka mishi yanda baya makarantar nan ba wata uwar yake tsinanawa ba sana'a se d'aukan magana to a bashi auren ta kawai,cikin washe dikkan haqoran shi ya ce,
" Hajiya Atiyyaerh, meye na sauri kawai dan kin ji ina kiran ki, ki kwantar da hankalin ki, in Allah ya nufa nine mijin ki ko ba dad'e ko ba jima sai na aure ki,"
Cikin jin haushin kalaman shi ta gyara tsayuwar ta ta kalle shi Ido cikin ido, amma dake bata son ya gane meye a zuciyar ta sai ta sake fuskar ta ta, ta shanye b'acin ran ta sannan ta ce,
"Haba Ahmad yaushe ka ga Ina sauri ni? Sannan a gani na tinda ka san da haka me zai sa mu yi ta bata lokacin mu mu dika muna tsayuwa hira a titi? Mu Jira mu gani in har akwai qaddarar aure a tsakanin mu, sannan dika dika ma nawa nake? Kai Kan ka shekarun ka nawa har da ka ke hango aure? To gwanda gwanda ma ni mace ce tinda ana wa mata aure da wuri kafin maza, ballantana ma ni yanzu karatu nake, bana buqatar soyayya yanzu,ka bari inna gama makaranta munyi maganar soyayya da auren ma gaba d'aya dan Allah, ka dena bina kana surutan da ka ke please"
"Da gaske kin amince za mu yi magana in kin gama karatun ki? Hakan fa na nufin zaki ban dama na shiga neman auren ki?"
D'aga masa kai ta yi da murmushi, suka yi sallama ta shige gidan nasu.
A tiyyaerh na da samari a wadannan shekarun nata, dan kowa ya ganta zata yake tafi ainahin shekarun ta, duk sanda manyan motocin masu hannu da shuni suka tsaida ta a hanyar islamiyya ta kanyi murmushi ne kawai ta ci gaba da tafiyar ta, a haka ne ta samu wani, Hassan, ba qaramin son ta yake ba,iyayen shi manyan masu kudi ne, ba zai wuce shekara 25 ba, ya takura ta matuqa, Afrah kan ce mata
"ki bashi dama, ko da secondary ne ki ka gama a aurar dake ki huta, wannan rayuwar gidan in baki barta ba zaki samu ciwon zuciya wata rana,"
Takan yi murmushi tace,
"Afrah nawa muke ne da muke tinanin aure ne, we are still young,getting married at young age will not solve my problems, kawai zan ta addu'a Allah ya zaban mafi alkairi,"
Afra kan amsa da " Ameen" amma tana matuqar tausayawa qanwar ta ta, ta wani bangaren kuwa Yousuf ba qaramin tausaya mata yake ba, ya qudurta inshaa Allahu zai jiyar da Ablaer daɗi fiye da yanda take tinanin samun sauqi a rayuwar ta, to taya zai samu wannan damar?
*******************************
A kwana a tashi asarar mai rai, yau su Ablaerh ke rubuta jarabawar su ta qarshe a makarantar sakandire ta Al'ansar, Atiyyaerh da Amal na hango sun had'e kai tare da rungume juna suna ta kukan rabuwa da junan su,sun bala'in ba wa qawayen su tausayi, dan kowa ya san yanda suka shaqu, babban abinda ya sasu kukan dama shine an saka ranar bikin Amal, kuma ba a qasar nan zata zauna ba ma, Ghana za a kaita, can dangin mahaifin ta, biki ma a ta can zasu yi shi na al'adun su ba anan ba balle ta samu damar zuwa, da kyar aka raba tsakanin su kowa ta tafi cike da kewar 'yar uwar ta, sun iso gida kan Atiyyaerh na matuqar ciwo, ta rasa ina zata saka kanta ta ji dad'i, dan ko magani tasan ba ta da arziqin da za a bata a gidan, shigewa d'akin su ta yi bayan ta gaida Abban su da Umma dake zaune, Abban su ya taya su murnar kammala secondary school da suka yi, sannan ya na burin saka su a makarantar gaba da sakandire in har results din su ya yi kyau dik da bashi da tantama akan yaran nashi musamman Atiyyaerh, sai dai bai fad'a masu hakan ba, ya bar abun a ran shi, yanayin yarinyar yasa yana son ya je ya ji me ke damun ta, amma yana tsoron iya masifa tace yana banbanci, addu'ar samun sauqin koma meke damun ta ya yi mata a ran shi.
Tana shiga ta fara cire kayan ta, ta ninke ta saka a basket din wankin su, daga ita sai pant da brah, da dogon skirt, a hankali ta warware gashin ta ko zata samu sauqi daga daurin da ta masa, ya zubo a bayan ta, ta sa hannu a can qasa ta buda shi sosai,dan ta sha iska, tana cikin haka aka bude aka shigo, a zaton ta Afrah ce,
" Ban San me yasa ki ke son shigo wa waje ke ba sallama ba kullum, sai kin tsorata mutum kizo kina Wani yi hakuri my sister,"
Tana nuna yanda Afrahn take mata, juyowar da zata yi idon ta ya shiga cikin na Yousuf, cikin in ina tace,
" Yah....yah..yayah?"
Daga mata kai ya yi, cike da murna ta tafi da gudu da niyyar rungume shi kamar yanda ta Saba da tana yarinya,sai kuma ta tsaya agaban shi, tana ta dariyar farin cikin ganin shi, yau wata shida kenan daya koma makaranta, a zariya,
" Yayah yaushe ka zo, ba ko sanarwa?"
Shiru ta ga yayi har lokacin bai motsa ba, bai kuma kifta ido ba, sannan kuma bai ce mata komai ba, kallon inda ya qurawa ido ta yi ta ga ya hadiyi wani yawu , daidai qirjin ta ta ga yana kallo, wata siririyar qara ta saki, ta juya tare da dafe wajen,tana zare ido, gashin ta ta barbaza a jikin ta ya rufe mata kafadu , cikin tafiyar sauri ta sunkuya tana jan bedshit din su, sun irin cusa shi can cikin nan, ya qi fita, kawai sai ta duqa a wajen cike da kunya ba kadan ba, dariya yake sosai, harda kama ciki,
"Yayah go out pleaseeeee,"
" No, i can not just go out,In kuwa na fita sai dai na koma zariya kin yarda?"
Cike da tsokana ya fad'i hakan,
" Yayahhhhh pleaseeee manaaa"
Ta qara fad'a cike da shagwaba da muryar dake nuna alamun gaf take da Saka masa kuka, dariya ya yi sannan ya ja qofar ya fice,kan ya qarasa fita yace mata,
"In kin shirya ki samen a dakin mu na baki tsarabar ki,"
Bayan ta amsa shi da "To" ne ta ji dariya ta kama ta, nan da nan ta nemi azababben ciwon Kan ta rasa se sama sama take Jin shi,ta na Saka kaya ta na tinanin irin kyaun da yayan nasu ya qara kamar ba shi ba, dafe qirjin ta ta yi, data tina wani kallo daya mata, sannan ta tina inda ya kalla, buga qafar ta ta yi a qasa, tana tirje2, tana kukan shagwaba, jikin ta na ta motsawa,Afrah ce ta bude qofar zata shigo, tana shigowa ta ga Atiyyaerh na hakan,
"Ke kuma lfy, me yake damun ki?"
Cike da shagwaba ta bud'e baki ta fara magana da cewar,
" Ba yayah bane ya shigo mana daki ba ko sallama kuma ban maida kaya a jikina ba,"
Dariya ce ta kama Afrah sosai, cikin dariyar ta ce,
" Ayyaa so sorry love, kuma gashi ya gama gane maki wannan tula tulan naki, kaiiii sorry u,"
Zaro ido Atiyyaerh ta yi dan ta tabbata ba da jimami qaramar yayar ta ta tayi maganar ba, ( in baku manta ba Afrah ta ba Ablaerh kwanaki ne) cike da shagwaba ta miqe ta maka mata pillon dake hannun ta, ta wuce wajen kayan ta,dake cikin wata jaka , dan Rasheedah ta hana ta saka kayan ta a wajen na Afrah,duba doguwar riga ta yi, a kayan ta aje a gefen gado,ta dauki duk abinda take buqata in ta yi wanka zata saka ta aje, sannan ta wuce Afrah da har yanzu bata daina dariya ba tana tsokanar ta, dan ta san yanda Atiyyaerh ta tsani a ga jikin ta,musamman qirjin ta, dan Allah ya hore mata su, sannan ga shi wai Yayahn su da take tsananin jin kunya tin da suka fara girma,yanzu kuma shi ya ga qirjin ta da wanne Ido zata sake kallon shi?
" Kin ji da shi dai ki ta tsokana nan ki ka fi kauri dama ai, laifina ne ma da qaiqayin baki na na fada maki,"
Cikin tura baki tai shigewar ta bathroom d'in, wanka ta yi ta d'aura alwala sannan ta fito, ta shafa Vassilin din ta, da yar farar powdern ta, sai kwalli data zizara, ba qaramin kyau ta yi ba. Afarah ta gani itan
ma ta cire kayan ta ta sa wasu ba tare da ta yi wanka ba,cikin jimanta lamarin Atiyyaerh ta ce,
"Wai ke meyasa baki son wanka ne? Munje mun dawo daga makaranta, mun gama shan qura a hanya mun dawo ga zufa amma ke baki san ki qara wanka ba,"
"Ke ni banni da shegen son wankan nan irin naki kamar agwagwa ba zan iya ba,"
Ta rausaya jikin ta mai kama da na Ablaerh, jerawa suka yi suka fita parlour kamar wasu tagwaye, direct dakin Yousuf da Sulaiman suka nufa, Sulaiman na kwance yana bacci, Yousuf yana zaune alamar tinda ya baro dakin su Afrah yake zaune a wajen, ya yi zurfi a tinanin Atiyyaerh Afrah ta taba shi,
" Yah gamu mun zo a bamu tsarabar,"
Murmushi ya yi ya sauke idon shi kan Atiyyaerh, ita kuma ta yi saurin juya baya tare da sunkuyar da kan ta qasa,dariya suka saka mata baki d'ayan su, miqewa ya yi yana tambayar su ya jarabawar ta yi sauqi kuwa? Haka dai suka yi ta hirar yaushe gamo, ya dakko tsarabar kowa ya damqa mata, Ablaerh yaa bata wata doguwar riga ne mai kyau baqa da ratsin pink a jiki, sai Afrah itama diguwar riga ce da rastin red a jiki, sai tsallen murna suke kamar wasu yara, dakko chocolate ya yi da tarkacen sweets ya ba Ablaerh, dan ya matuqar saba mata da shan su a boye, in baya nan tai kwadayin su har kuka take, ba mai bata, cikin murna sosai ta zube gaban shi, tana godiya,a nan ta bud'e ta fara sha ta rufe ido tana taunawa, tana wani girgiza kai, ba Yousuf ba dake namiji,har Afrah sai da ta yaba da kyaun ta, a hankali ta bude idon ta ta ga suna kallon ta,ta miqe ta fita cike da jin kunya, Sulaiman ne ya farka shima sai murna da ganin dan uwan shi yake, haka suka ci gaba da hira bayan ya amshi nashi tsarabar.
Yauce rana mafi muni a wajen Atiyyaerh, ranar da ta yi kukan rashin uwa da uba , kukan maraici, kukan Ina zata Saka ran ta da abinda ke tinkarar rayuwar ta ta gode Allah,😭😭........
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Yesterday was our 15 years wedding anniversary my beautiful fifulll please say a prayer