Showing 39001 words to 42000 words out of 81601 words

Chapter 14 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAH.txt

17 Oct 2025

1489

tara ruwa a robar da ta yi wa Afrah wanka, ta na gamawa ta d'auke ta ta tsumbula ta cikin ruwan sanyi zata yi mata wankan da shi,kara ta sake ta miqe tsaye tana karkarwa, dariyar mugunta Rasheedah ta saki kamar wata qaramar yarinya me mugunta,zare Ido ta yi ta umarci Atiyyaerh da komawa cikin ruwan ta zauna, qi ta yi ta ci gaba da kukan ta a tsaye, da qarfi ta zaunar da ita cikin ruwan , yarinya na kuka ta qarasa mata wankan, daga ranar ruwan sanyi ya koma na wankan Atiyyaerh, se dai idan ruwan zafin wankan yaran ya ragu, tsabar mugunta ce ta sa ba zata kunna tap din ta sake had'a mata me zafi ba, tinda akwai heater a bathroom d'in,ta gwammace ta d'ebi na sanyi ta yi wa yarinyar amfani da shi.

*******************************

Mama  na zaune ta na tinanin ko ya Atiyyaerh take ? Dan ta riga ta San halin Rasheedah bata Jin zata Iya kyale yarinyar ta wataya a gidan su,se kawai ta yanke shawarar zuwa dan ganin ya suke tafi da riqon amanar da aka bar mata, bayan ta sanar da Abba ya bata izini,sannan ya fita shago a unguwar ya siyo abubuwan kwalama na yara yace akaiwa Atiyyaerh da su Afrah, sallama suka yi ta hau abun hawa sai gidan su Atiyyaerh.

Tana isa gidan ta bud'e gate da kan ta ta shige, tinda ba mai gadi yanzu, harabar gidan ta kalla ta ga ba motocin gidan hatta da ta Auwal d'in babu, alamu ne na ya fita kenan, da  sallama ta Isa qofar shiga cikin gidan, ta kama hannun qofar ta murd'a, sai ta ji ta a bud'e, sallama ta ci gaba da yi amma ta ji shiru ba Wanda ya amsa, a can ta hango Atiyyaerh k'wance akan kujera ta takure waje d'aya, ta na rawar sanyi,ga parlour ya d'auki wani duhu saboda kashe fitulu da aka yi Kuma labulaye a sake suke, zuwa ta yi da sauri ta Isa gaban yarinyar ta d'aga ta tana tab'a jikin ta, zafi taji rauu, nan danan ta d'aga ta hankalin ta tashe, kwalawa Rasheedah kira ta hau yi amma shiru, miqewa ta yi ta bubbud'e d'akuna biyu na farko da maibin shi taga wayam, sama ta hau can inda d'akin yaran yake a nan ta gansu, Rasheedah ce a tsakiya yaran sun kwanta a jikin ta sun rufu suna kallo, kwalin popcorn zaune a gaban su suna kallo suna ci, mamaki ne mai tarin yawa a ran Mama,

"Me nake gani haka Rasheedah? kin saka yaran ki a gaba Kuna kallo amma kin bar wannan tahalikar ita daya a waje, da Wani barawo ne ko me mugun abu ya shigo gidan fa? Shikenan sai a cutar da ita ke kina nan Kuna more rayuwa da yaran ki? habaa Rasheedah, a ina ki ka koyi wannan rashin imanin ne haka? Wacce iriyar zuciya ce a qirjin ki? Tinda ki ke da ni Rasheedah baki taba gani koda bera na wulaqanta ba, haka mahaifin ki, me zakice wa Allah randa ya tambaye ki amanar marainiyar da aka bar maki?"

Cike da takaici mama ta bar d'akin, zuwa ta yi tana hawaye ta na tina Sakeenaah baiwar Allah, ta duba kitchen ta d'akko maganin zazzabi na Yara ta had'a tea Mai d'umi ta bawa Atiyyaerh tea d'in da magani, sannan ta dakko towel da ruwa mai rangwamen sanyi ta yi ta goge mata jiki da shi, kafin minti 5 ta fara zufa bacci mai nauyi ya d'auke ta.

Bayan fitar Mama Yousuf ya qurawa mahaifiyar su ido, domin ta masu qarya, d'aga kafad'a ta yi tace wa yaron da ya kafe ta da kallo,

"Meye kuma kk tsare ni da wannan manyan idon naka,"

" Umma kin ce tana bacci a d'akin mu,"

"Eh mana fitowa ta yi dan munafurci amma ai a can na barta ta na baccin"

Sauka ya yi daga gadon ya fito ya zo wajen Kakar su ya zauna, nasiha ta hau yi masa sosai game da qanwar tashi kamar wani babban mutum haka yake sauraron ta kuma dik abinda take fad'a masa yana shigar shi matuqa, Rasheedah ce ta fito tana hura hanci ta zauna a d'age ta gaishe da Mama, ko kallon ta mama bata yi ba, ta miqawa Yousuf ledar su tace masa shi da qannen shi, wannan kuma na Atiyyaerh ne,Abba ne yace a basu, cikin fushi Rasheedarh ta fara magana,

"To baga shi ba, yaran ma sai kin nuna banbanci, tsakani da Allah ai da hadowa kawai za ai ace gashi a ba yara,ba kiyo ledar kowa daban ba, ta haka ne yara ke tashi kai a rabe,"

Cikin fushi Mama ta fara magana,

"Ai tinda dama zuciyar ki ba mai kyau bace dole ki ji b'acin rai akan hakan, haba ke kuwa, ki dinga sanyawa kan ki salama, ki sawa kan ki tausayi, da soyayya, ko kin mori kyaun da Allah ya miki, domin wannan baqar zuciyar taki ke tauye ki"

Kauda kai Rasheedah ta yi tana qunquni, Mama bata ce komai ba ta aje Atiyyaerh ta miqe zata tafi, sai da taje qofa ta juyo tace,

"Abinda kai a duniyar nan za a maka, wanda bai ba ma an masa balle kayi, kuma Allah ne shaida ban ma iyayena haka ba, mahaifin ku har iyayen shi suka rasu sina saka masa albarka,ki bi duniya a sannu shi haqqin maraya nauyi ne da shi, nauyin shi ya fi dutsen Dala Rasheedah ba Zaki Iya d'aukar nauyin haqqin marainiya ba ki samawa Kan ki salama ki ajiye qiyayyar nan mara tushe, kin Yi wa mahaifiyar ta hassada da zazzafar qiyayya ta bar maki duniyar, yanzu madadin ki yi karatun ta nutsu ki tina kema watarana Zaki inda mahaifiyar yarinyar nan ta tafi amma ki ke toshe kunnen ki ki ka rintse idon ki ki ke wa yarinya azaba, kar ki ce ban fad'a maki ba Rasheedah na fitar da haqqin da ke tsakanin mu na uwa da 'yar ta na fad'a maki gaskiya ruwan ki ne ki bi, ruwan ki ne ki barta kar ki bi"

Tana kaiwa nan a maganar ta ta fice, dan guntun tsaki Rasheedah ta ja sannan ta d'auki ledar Atiyyaerh ta debi kayan ciki ta qara a na su Yousuf, Sulaiman da Yousuf na tsaye suna kallon ta tare da Afrah ta debi biscuits da sweets ta basu, Yousuf qin karba ya yi, sai ita Afrah ce ta karba, Sulaiman kuma da aka bashi, zuwa ya yi ya aje gaban Atiyaerh ya koma ta bashi wani, cikin qara da hargowa ta fara magana,

" 'Yan iskan yara masu halin uban su kar ku ci d'in ku kuka sani,"

Ta kwashe ledojin zata shige d'aki sai ta ji muryar Auwal na fad'in,

" Allah na gode maka da basuyo halin ki ba duk da banji me ya faru ba, da sunyo halayen ki da na shiga uku na lalace da haifar mugun iri,"

Cike da rashin kunya ta murgud'a baki ta shige d'aki, Yousuf ne ya labarta masa dik abinda ya faru da baya nan,nan take ya d'ebe su a amota zai Kai Atiyyaerh asibiti, likita ta gani ya duba ta ya rubuta magunguna, sannan ya yi hani akan a rage yawan yi mata amfani da ruwan sanyi Kuma a kiyaye bata ruwan sanyin ta na sha,suna kammalawa da asibiti suka bi suka sai magungunan da aka bata, sai sukaje wajen cin abinci, aiko Atiyyaerh ta kwashi gara, taf ta cika cikin ta, sannan suka dawo gida, direct d'aki ya kaisu, dan basu buqatar abincin dare ranar, cikin Atiyyaerh ne ya motsa, ya yi qara, nan take ta sake wata muguwar tusa mai wari, su Yousuf ne suka toshe hanci suna tsokanar ta, wasa suke suna ta guje2, can kashi ya matse ta,

" Yaya zan yi kashi,"

"To bodara mu je ki gayawa Umma,"

kama hannun ta ya yi ya tafi da ita wajen Rasheedah, suna zuwa tsakiyar carpet din wajen Atiyyaerh riqon kashi ya kwace mata, tako sake shi a wajen, tana kuka, daidai Rasheedah ta fito dauke da kwanon data gama cin farfesun kifin da ta yi da basa nan,wani wari ne ya daki hancin ta,cikin toshe hanci da yatsina fuska ta kalli su Yousuf da ke zare Ido ta ce,

"Meye wannan? Me nake ji haka, Kashi ki ka min a qasa? kan ubancan kayyasa, yau se na ci kut......Uban ki Ina zuwa,...........
[01/07, 8:47 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




Page 19:


Auwal mamakin yanda Rasheedah ke ta hidima da shi a daren yake,ita ce Yi masa girki mai dad'i da ya fi so, had'a masa ruwan wanka har da su zuba kayan wankan da suka tarar a bathroom d'in masu gyara fata na maza, Yana fitowa ya tarar da kayan da zai Saka na jiran shi, ita ta taya shi shiryawa ta feshe shi da turaruka masu dad'in qamshi, ga wata uwar Kwalliya da ta fesa Kai ba zaka ce ta tab'a haihuwa ba ma balle ace ta ajiye Yara har uku,sai Wani yauqi da shisshige masa take, ya gaji da Shan mamaki qarshe dai ya kama ta suka zauna a bakin gado ya zuba mata idanun shi da ke bala'in burge ta, ya ce,

"Fad'a min wannan sauyin halin na menene, domin ke ba abar yadda bace Rasheedah"

Wani abu ta ji ya soki zuciyar ta me zafin gaske, Auwal baya fad'in abinda ba haka ne a zuciyar shi ba, hakan na nufin da gaske mijin ta me son ta da qaunar ta a da yanzu be yarda da ita ba?hakan fa na nufin ya dena son ta,dan se akwai yarda soyayya ke samun wajen zama,laifin waye dika wannan? Laifin Sakeenah da 'yarta ne? Tabbas laifin su ne, saboda da alama ya fi son su sama da ita da take matar shi, qoqarin danne baqin cikin ta tayi sannan ta yanko murmushin yaqe ta ce.

"Haba Abban Yousuf me na yi Maka a rayuwa Mai zafi haka? Ni dai dan Allah ka yi hakuri bana son tone tone, shi mutum in Yana aikata laifi ya gane kuren shi ai se ya gyara tin kafin a nusar da shi ko Kuma lokaci ya qure masa ko? Na gane kuskuren da na ke aikatawa gaba d'aya shi yasa nake so na gyara,ka yi hakuri ka dawo min da soyayyar ka da qaunar da ka ke min a baya"

Kuka ta fashe da shi Wanda ta tabbata sai ya lausasa zuciyar shi, duk fad'a ko dukan da zai mata tana sane da baya son kukan ta, taurin Kai ne irin nashi ke hana shi lallashin ta,a hankali kuwa ya ji ya yarda da neman gafarar da ta yi, amma be San me yasa ba ya kasa sakewa da ita, Yana Jin kamar akwai Wani abu da take qullawa, share mata hawayen ta ya fara tare da rungumar ta a jikin shi Yana lallashin ta.

"Shiiiii ya Isa haka, ki dena b'ata hawayen ki, kin San bana son kukan ki ko?"

Shessheqar kukan ta ne ya ragu, ta sake shigewa jikin shi, ta na Wani abu kamar qaramar yarinya, Auwal ya yi kewar ta da yawa, ya yi kewar shagwabar ta da soyayyar ta, tinda suka zo gidan komai yi yake cikin qunci da Kuma cewar ya zame masa dole ya mata abinda take so kar ta masa haukan ta, amma ba Dan Yana so ba, a hankali suka fara wasannin su, Rasheedah ta sake masa jikin ta sosai ya na yanda ya ga dama da shi, cikin wata iriyar muryar da ke rikita Auwal ta fara magana,

"Abban Yousuf da gaske kenan gobe za ka Kai Atiyyaerh da Afrah makaranta?"

Auwal na Jin haka ya rintse Ido,ya fara qoqarin janye jikin shi da ya mata rumfa da shi Yana wasa da ita, Jan shi ta sake yi jikin ta ta na Masa wasanni masu rikitar wa, ta tabbata a yau ba zai iya fushi da ita ba saboda yanda ta sashi yake ji, ci gaba ta yi da magana daya gefen kuwa ta na Masa wasannin da ya sa maganganun ta ma basu wani shigar shi sosai,

"Abban Yousuf kar ka fahimce ni ba daidai ba, na tambaye ka ne saboda ni nake zaune da yaran nan a gida, na San me kowa ke so, Ita fa yarinyar nan Auwal ba ta son makaranta,na sha jin maganar su da yara tana fad'in ita tafi son yayan ta yana koya mata a gida, dan haka ni shawarata da ka barta a gida....in su Yousuf suka je suka dawo daga makarantar kaga sai yana mata karatun a gida,ta haka ne shima zai samu kwarewa sosai,"

wani kallon baki da hankali kuma ke bama ki iya makircin ba ma Auwal ya mata ba tare da ta sani ba, domin yanda yake Jin ta birkita shi ba zai iya jurewa ya yi fushi da ita ba, gurnani kawai ya mata da "Uhmmmmm" Jin hakan da Rasheedah ta yi se ta qara qaimi wajen rud'a Auwal, ni dai tattarawa na yi na basu waje, na koma d'akin Yara muka kwana.

Washe garin ranar kuwa Rasheedah na can na baccin gajiyar da Auwal ya tara mata, ya farka ya yi wanka ya yi sallah ya shirya sannan ya nufi d'akin yaran, da kan shi ya tada su suka yi brush suka yi alwala Yousuf ya ja su sallah Auwal na murmushin Jin dad'in yanda Yousuf ke da hankali,da kan shi ya shiga bathroom ya had'a ruwan wanka yayi wa yaran wanka har da Atiyyaerh da Afrah, qasa ya tarkata su suka sauka ya soya masu kwai ya had'a musu tea suka sha da bread, sai cake da ya siyo na tafiya makarantar yara da ya dibar wa kowa da juice da suke had'awa da shi, ya d'auke su sai makaranta, suna zuwa ya yi duk wani cuku2 na Saka Afrah da Atiyyaerh makaranta ya gama komai, sannan ya damqa su a hannun hukumar makaranta ya ja ya tsaya dan ganin ajin da za a Saka su, Atiyyaerh direct primary one aka saka ta, Afrah kuma suka bashi hakuri sai dai ta fara daga nursery saboda ita komai bata Iya ba Banda A zuwa F, Atiyyaerh kuwa har sunan ta da na Daddyn ta ta Iya rubutawa Yousuf duk ya koya mata, tana Jin turanci already, ta Iya had'a wasu kalmolin dik da ba dika ba,dan haka Auwal be Wani damu ba yace ba komai, don yasan qoqarin kowa a cikin su, zai tafi Afrah ta dinga kuka, da kyar aka bambare ta akai aji da ita, Atiyyaerh kuwa sai murna take sosai, tinda dama abun nema ne ya samu, dad'in dad'awa an aje ta aji d'aya da Sulaiman, hankalin ta kwance ta samu malamin ajin ya mata wajen zama kusa da wata yarinya mai kyau  itama mai suna Amal wadda ba zata wuce sa'a da Atiyyaerh ba,murmushi suka yi wa juna, sannan Atiyyaerh ta maida hankalin ta in da malamin ke tambayar sunan ta, nan ta fad'a masu sannan ta qara da

"Mummyna na ce man Ablaerh, Daddy na na ce min Atiyyaerh, a gidan mu ma Atiyyaerh su Yaya ke kirana,"

Malamin su Murmushi ya yi, sannan ya ce,ta maimaita maganar da ta yi da turanci, tinda ta iya, nan da nan kuwa ta maimaita da turancin ta na Jin dad'i yau gata a makaranta,murmushi malamin su ya sake yi, yaran aji kuwa suka saka dariya, karatu suka fara, ta yi matuqar maida hankali akan abinda ake koya musu Dan sai ta ji kamar karatun makaranta da na Yousuf akwai banbanci wannan na da wahala, na Yousuf kuwa babu wahala Sam Sam,nan da nan take gane nashi, dan haka duk abinda bata gane ba bata bari a wuce wajen se ta yi ta tambayar malamin su, shi kuwa haka zai dawo baya ya mata bayani daidai fahimtar ta a haka ne ma wasu da basu gane ba suke shiru suke fahimta,a haka suka gama karatun su na wunin ranar har aka tashe su,iya malaman da dik suka shiga ajin shi Atiyyaerh sai da suka san anyi baquwar daliba.

Ban garen Afrah kuwa, da ta gama kukan sai ta saka hannu a baki ta hau tsotsa abunta har baccin ya d'auke ta,an tada ta yafi sau nawa, qarshe in suka dame ta ta saka kuka, haka suka barta ta sha baccin ta.

*******************************

Rasheedah bata tashi farkawa ba sai qarfe tara na safe, agaggauce ta gama wanka ta yi sallah ta sauka qasa, ji tayi gidan ba kowa shiruuu, d'akin Yaran ta nufa ta ga wayam ba kowa, wajen kayan Atiyyaerh ta duba ta ga alamun an tab'a kayan, Murmushi ta yi ta zauna bakin gado tana Jin Wani b'acin rai na yunquro mata, wato ita Auwal zai yaudara? Ya gama more ta jiya ya qi bin maganar ta? Lallai za a yi tashin hankali kuwa, Cike da b'acin rai ta hau watsar da kayan Atiyyaerh qasa ta na tattakawa, ta na gamawa ta fita daga d'akin cikin fushi, zata sauka qasa ta ji alamun bud'e qofa, tsayawa ta yi ta hard'e hannayen ta a qirji ta na kallon qofar, idanun ta sun kad'a sun yi jawur dan b'acin rai,Auwal da ya shigo ya Maida qofa ya rufe, ya ajiye key din motar a center table sannan ya kalli yanda take Wani cika tana batsewa, Murmushi ya yi a ran shi a fuska kuwa ya kalle ta da kulawa ya ce,

"Ah ah Rasheedah lafiya na ga fuskar ki ta sauya haka? Ko dai Kashi ki ke ji ne? Dan na San ki ke da shiga toilet kamar akwai amana kamar wata quda haka ki ke dan shegen yawan kashin ki"

"Kan uban can, ni ce ma me yawan Kashi? To malami dakata ka ji,idan ma ka d'akko wannan shirmen ne Dan na manta me ka yi to wasan ka be karb'u ba, ni zaka yaudara? Ni zaka ci wa amana?"

"Amana Kuma? Rayuwar auratayyar mu ki ka ji na yayata a duniya ko me? Ko so ki ke na Sanar da duniya yanda mugun abun ki be tsaya a Iya fatar baki ba har se kin Yi amfani da jikin ki kamar wata wadda bata San ciwon Kan ta ba? Ke Rasheedah ki kiyaye ni ni ba banzan namiji bane,ba Kuma soko bane ni, sarai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login