Showing 51001 words to 54000 words out of 81601 words
Chapter 18 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAH.txt
d'akin ta ga shine, bud'e mata hannu ya yi akan ta je gare shi, kukan ta ne ya qaru, a hankali ta miqe ta je ta fada jikin shi for the first time a rayuwar ta bayan ta girma, kuka take sosai, kamar zata hadiye zuciya, shima kukan yake, baisan yana son ta ba sai yanzu, itama bata zaci wannan yaba shi da zuciyar ta ke yi ba sone sai yanzu, suna tsaye a haka Rasheeda ta banko qofar ta shiga....
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 23:
Hannu ta sa ta damqi damtsen Atiyyaerh ta janye ta daga jikin Yousuf ta kwad'a mata mari, cikin qanqance Ido da d'aga murya ta ce,
"Ai dama na San za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, tinda na ga gilmawar ka kayo nan jikina ya ban akwai Wani abu, a gidan nawa zaki nuna min karuwanci? To ki kwantar da hankalin ki kwana nawa neèe ?daga gobe ne fa za a yi bikin naku, jibi an daura aure an kai ki gidan mijin, kin je can ki ci uwar da zakici a can amma ba a nan ba,"
Ran Atiyyaerh da Yousuf ba qaramin b'aci ya yi ba, musamman kalmar karuwancin nan da ta ambata ta sosa zuqatan su, amma dake Atiyyaerh akwai hakuri, tin kallon farko da ta mata na b'acin rai bata sake ko da kallon ta ba,ta juya ta koma gado ta kwanta ta dora pillo a kanta, sannan ta ja bargo ta rufa, Yousuf ne har yanzu ya ke tsaye ya kuma tsare Umman tashi da ido, yana son ya yi magana amma ya rasa mai zai furta da Allah ba zai fushi da shi ba, tabbas in zai magana ko ashar ya dura ba zai ji sauqin zuciyar shi ba, wannan matar me mummunan halin da be tab'a ji ko gani ba a rayuwar shi mahaifiyar shi ce, kalaman shi dole su zama masu taushi a gare ta in Yana son Rahamar Allah, a wannan gab'ar kuwa bai da kalamai masu wannan taushin, hadiye wani abu ya yi mai mugun d'aci ya sa kai zai fice,
"Ina zaka je kuma?"
"Makaranta zan koma,"
kafin ta furta wani abun ya fice, daidai zai bude qofa Abban su shima ya kama zai shigo, murmushi Abban ya masa amma ya kasa maida masa da martanin Murmushin, dan haushin Abban ma yake ji sosai ai ba kowacce wasiyya ake cikawa ba, wannan akwai cutarwa a cikin ta, ace shi bai isa da gidan shi ba,saboda kawai wasiyya sai kowa ya rufe ido, fadar Allah nawa sike takewa duk da ba zai iya nunawa ba, amma tabbas yasan suna aikata Wani abun mara kyau ko da a b'oye ne, sai wata wasiyya ce zata hana su kyautata wa marainiya, wannan ko uwar ta na da rai ba zata so hakan ba, komai son ta yi mending abubuwa tsakanin ta da Umman su, kafad'ar shi Abban ya dafa ya d'an matsa kad'an,ai kuwa kamar ya matso da kuka, kuka ne ya kwacewa Yousuf, wanda Abban nasu ya ji dad'in zuwan kukan, dan ya kula tin ba yau ba d'an nashi yake son Atiyyaerh, sai dai a wancan zuwan da ya yi ya tabbatar da zargin shi ,se kuma ga wannan mummunan had'in aure da ake son a Yi wa yarinyar, rungume shi ya yi sosai a jikin shi dan ya yi kukan shi ba me hana shi, sun fi minti 5 a tsaye, sannan ya kamo hannun shi suka qarasa shigowa, zaunar da shi ya yi a kujera kusa da Sulaiman da idon shi har yanzu yake kamar gauta, duk da yayi kukan amma har yanzu zuciyar shi na nan da takaicin wannan had'in auren, ji yake kamar yaje ya batar da Ahmad din, in ba a ga ango ba wa zai aure ta d'in? Afrah ce ta je ta debowa Abban nasu ruwa da abinci, zama ya yi yaci tukunna, yaran na mai kallon lallai Abba har abinci kk iya ci? Bayan ya gama ya yi hamdala sannan ya fara magana kamar haka,
" kuyi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri, shine kalmar da zan iya had'a ku da ita, ku sani uwa ta wuce wasa, kar kuce zaku yi fushi da mahaifiyar ku, tabbas uwa ba abar wasa bace, ku yi hakuri da hukuncin da ta yanke, ni kaina zan so hana wa, amma a wannan karon ina son, itama ta ga irin abun da Sakeenaa take son ta gani, na fahimci inda komai yake dosa yanzu haka, ku qara hakuri, zuciyata tafi taku b'aci, badan komai ba sai dan ganin nine mai gidannan, ina da ikon sawa kuma na hana, amma qiriqiri gidana yafi qarfi na, dan haka dole na bamu hakuri dika, Yousuf kai hakuri a daura aure sai ka koma,"
Yana kaiwa nan ya miqe da jakar shi ya wuce ciki, wata qara yousuf ya saki ya koma da baya ya kwantar da jikin shi akan kujerar, sunan Allah kawai ya fara ambato, dan yasan shine kawai mafitar shi a halin da yake ciki cikin iKon Allah kuwa sai ya ji ya fara samun sauqin zuciyar shi, umarni ya ba Afrah akan taje wajen Atiyyaerh, ita kuma bata son zuwa kunyar ta take, wannan zalinci har ina, me zata ce mata? Da wanne idon zata kalle ta to? Amma haka ta miqe ta shiga dakin, tana zuwa ko taga Atiyyaerh na rawar sanyi, tab'a tan da zata yi se ta ji jikin ta rauuuu, kamar wuta, sai karkarwa take, miqewa tai a kid'ime zata fita, ita kuma ta tattare duk qarfin ta da ya rage ta cafko ta,
" Kar ki sanar da kowa, in kk fita raina zai fi haka baci, ki barni wataqila mutuwa tace tazo dan ta sauqaqa min komai dake faruwa dani, ina zan saka kaina, na zama marainiyar qarfi da yaji da ubana, ina mahaifina? Meyasa bai waiwaye ni ba ya nunan ina da uba? Me yasa bai zo ya tsaya min ba? Afrah ba mai jin kukana ko nayi, a banza, ko nai roqon a taimakan a banza, amma ba komai, akwai Allah, kuma baya barci,"
Afrah kuka kawai take ba qaqqautawa, Atiyyaerh ko idon ta yanzu ya bushe, bata jin kukan ma, sai suyar zuciya, a haka aka kira sallar isha'i suka miqe, dan ranar ko magrib ba wanda ya yi,alwala Atiyyaerh ta d'auro da taimakon Afrah, mazan suka yi jam'i suka rama magrib da ke Kan su sannan suka maida isha'i, tinda suka yi sallah Atiyyaerh ke zaune a wajen bata motsa daga wajen ba, domin ta kula sallar da ta yi ta yaye mata wani kaso mai tsoka daga damuwar ta, miqewa ta yi ta ci gaba da jero nawafil, bata samu ta zauna ba sai da taji qafafun ta sun kasa tsaiwa, saida taji idon ta na rufewa sannan ta kwanta a wajen, cikin zuciyar ta addu'a kawai take na neman zabin Allah, tana roqon in laifi ta yi wa Allah ya ke mata wannan horon ya yafe mata, in jarabawar rayuwar ta ce haka tana roqon Allah daya bata ikon ci, kar ya sa ta sab'a masa,a haka bacci ya dauke ta,Afrah ita kuma sai wajen hudu ta tashi ta yi ta nata nawafil din da addu'o'i, kowa a gidan bai rintsa ba banda Rasheedah da ta yi d'aid'ai a gado, tana ta kwasar barci harda saleba.
A yau ne aka daura auren Atiyyaerh da Ahmad, akan sadakin su da suka bada dubu goma,bakin shi kamar zai tsage dan murna,hakoran nan nashi farare da suka rine da hayaqi sai kyalli suke , ba laifi Ahmad na da dan kyau,daidai misali, but he is not that extremly handsome, abokan shi 'yan ganye kamar ruwa a wajen, haka aka tashi Abban su Rasheedah kamar zuciyar shi ta fashe, ko gidan su Atiyyaerhn bai shiga ba ya sa kai ya tafi gidan shi Mama kuwa dama bata zo wannan auren baqin cikin ba, ta dai Kira Yousuf a waya ya had'a ta da Atiyyaerh, ta mata nasiha sosai Kuma ta bata hakuri akan abinda ke faruwa, su Yousuf da Sulaiman daga wajen suka yi makaranta, dama Sulaiman a shekarar ya shiga first semester yake ya na so ya Maida hankali dan ya samu GP me kyau kamar yanda Yousuf ya ke nuna masa mahimmancin hakan, ba wanda ya dauki ko tsinke a cikin su suka wuce,kafin Sulaiman ya San Kiran da ake musu ya sa ran samun wani abu wajen Abban su amma yanzu ji yake in ba kud'in makarantar da ya zama dole ba bai da buqatar komai wajen su ba qaramin haushin su yake ji ba dikan su, Auwal ne ke ta gaisawa da abokan Ahmad, sai abun qauraye suke masa, a haka taron ya tashi, Auwal ya shige gida, direct d'akin shi ya nufa, dan gidan kamar ba aure ake ba, a dangi ba wanda yazo, sai wasu qawayen Rasheedan su uku, suma d'aya ce halin su ya zo d'aya da ita, sauran biyun ne suka samu suka gyara Ablaerh, suka sa ta ta yi wanka, bata masu musu ba ta yo ta fito, bayan ta dauro alwala, zama ta yi suka shafe ta da mayuka masu kyau da suka zo da shi, masu qamshi, a cikin su wata tayo mata humrah mai qamshi sosai, suka shafe mata da turaruka , suka mata kwalliya daidai yanda kyaun ta zai qara fitowa, mamakin kyaun ta suke, the more suna kallon ta the more suna qara ganin kyaun ta, Afrah kam ko jambaki bata saka ba bare kwalli, haka ta zauna kamar wadda take takaba, fuskar nan ba walwala ko ta sisin kwabo, haushin ma Ablaerh da ta zauna ake mata wannan shirmen take, murmushi ta mata ta dafa ta bayan qawayen Umman su sun fita,
" Bana son damuwar ki, in na tafi ina tinano fuskar ki cikin damuwa hankalina zai dinga tashi ne, ki sassauta wa zuciyar ki, ni yanzu na sallama wa Allah ragamar rayuwata na san ba zai tsaran abinda zai zama cutarwa a gare ni ba, zan shiga gidan aure na da son zaman gidan mijina ba da wata niyya ba, tinda ya zama mijina ba zan masa musu ba, zancen halayen shi da kk tsoro kuma kar ki damu, duk fa wanda yaso zama lfy shi yaso,ki sama min nutsuwa ta ganin kyakkyawar fuskar ki cikin annuri,ta haka ne inna tafi zan dinga jin dad'in tunawa da ke, ki min alqawarin zaki dinga zuwa wajena Ina ganin ki, ta haka ne kewa ta zata ragu,"
Afrah gyada mata kai kawai take cikin kuka,daga qarshe suka rungume junan su, Atiyyaerh ta yi matuqar qoqari wajen maida hawayen ta ta hadiye su, dan bata son ta bawa Afrah qarfin guiwar ci gaba da kuka, bud'e qofar aka yi aka shigo, qawayen Umman su ne da umman tasu, dayar mai halin Ummar tasu ce tace,
" Yar nema mai kan buta meye na kukan? Ke za a aurar ko neman gindin zama a wajen ta? Kar na qara ganin kin zubda hawayen ki a banza,"
kallon tsana suka bi ta da shi, ba wanda ta tanka ta a cikin su,
" To Ablaerh kin ji dai abubuwan da muka fada maki d'azu, aure ibada ne, ki jaddadawa zuciyar ki haka kar ki saka mata wani tinani bayan wannan Allah ya albarkaci rayuwar auren ki ya kare ki daga dikkan Sharrin da ke cikin ta ya had'a ki da alkhairin da ke cikin ta,"
Daga nan suka miqar da ita dan raka ta gidan auren ta dake maqotaka da su, d'an tsayawa ta yi sannan ta tafi wajen Umman su ta durqusa,
" Ummana na gode da kulawar ku Allah ya qara girma ya biya maku buqatun ku na alkairi, Ummana ki yafen dukkan bacin ran dana kasance ina saka ki a ciki a dik sanda ki ka kalle ni, ki yafe min dan na tafi da albarkar ku,"
Sheqe2 ta kalle ta tace,
" Na yafe maki Allah ya maki albarka, ai wa miji biyayya a zauna lfy dan nasan halayen ki kaf na taurin kai,"
kallon ta Afrah ta yi ta kauda kai, sannan ta fice, miqar da ita qawayen Umman suka yi sai gidan su Ahmad, ba laifi, an masu tarbar mutunci, an girmamasu, d'akin Atiyyaerh kam ya sha kaya,Auwal ba qaramin qoqari ya yi ba wajen cika d'an madaidaicin d'akin da kaya masu tsada, dakin ciki da parlor ne,sai wani d'an kewayayyen waje nan ne toilet, sannan kitchen din su na kwano ne waje ne na had'aka dika matan gidan nan suke girki, a haka kowa ya fara watsewa, dan atiyyaerh bama ta san sanda Afrah ta zame ta tafi ba, tana komawa gidan dakin su ta tafi ta fada gado ta yi ta kukan baqin ciki, kukan tausayin halin da 'yar uwar ta zata shiga anan gaba.
Ango ne ya shigo da ledar shi a hannu, ya ajiye, direct wanka fad'a ya na gamawa ya fito daga makewayin nasu,ya saka wasu kayan, ledar da ya shiga da ita ya janyo ya kuma kamo hannun Atiyyaerh ya zaunar da ita a gaban ledar dake daf da shi, budewa ya yi se ga qatuwar kaza ta bayyana,
" Amarya kin sha qamshi , amar ya baki laifi ko kin kashe dan masu gida,"
Murmushin yaqe ta d'an yi masa, dan gaba daya tsoron shi ma take ji,
"To bismillah amarya mu ci kazar amarci dan ni dai yunwa nake ji"
Yankowa ya yi ya miqa mata a baki cikin Jin kunya ta d'an kauda Kan ta gefe, dariya ya yi yace,
" Yarinya gwanda ma ki ci dan ga qarar da cikin ki yake yi nan kema,alamar kin bar kan ki da yunwa, na riga Kuma da nasan gidan ku ba yunwa, in baki ci bama ni ba fasa wa zan ba atoh,"
"Menene ba zaka fasa ba? Ni fa bana Jin yunwa ne kawai na qoshi"
"Lallai yarinya yarinya ce, wato baki san ma me za a yi ba, tabdijam, to ke dai ci ko ba Kya Jin yunwa ci Dan Allah ba Dan ni ba"
karb'a ta yi a kunyace ta fara ci, murmushi ya mata, ta mayar masa itama, a haka suka gama ci, bayan sun gama ne, ta tashi ta d'aga komai ta goge qasan da aka saka maiqo, ta je ta yi alwala ta wanke bakin ta, shima wanke bakin ya yi ya zo ya kwanta, sallah ta yi ta zauna ta jira ta ji ko zai ce zasu yi nafila tare, kaya taga yana cirewa, daga shi sai gajeren wando, duk halittar jikin shi tana gani, wani wawan faduwar gaba ne ya kamata, cikn in ina tace,
"Ammmm naaa zaci....zaaa mu yi nafila neee, irin na sabon aure da ake yi?"
Tashi ya yi zaune yace,
" ke ni kyale ni, yau dai saboda na aure ki Allah ya ban iko har isha'i na yi,amma ni kam ba wata nafila da zan yi gaskiya"
Wani baqin ciki ne ya kama ta,da ace Ahmad ba jahili bane haka, da wataqila har son shi zata daure ta koya wa zuciyar ta bayan biyayyar auren, amma inaaa ba zata iya son shi ba samm, cikin kwantar da kai ta miqe ta je gaban shi ta durqusa, ta kamo hannayen shi,sannan ta ce,
"Haba miji na, kai da ka yi raka'a har hudu wannan kuma biyu ne fa kacal, kuma godewa Allah zamu yi akan baiwar da ya mana ta aurar da mu ga junan mu da ya yi, ka ga ai ya Kamata mu nuna godiya da farin cikin mu ta hanyar bauta masa tinda ka ga dai ba za mu yi rawa da waqa ba, magana ake ta Allah,ba Wani ba"
Da Jin haka sai ga Ahmad ya miqe ya zura riga ya je ya yo alwala, yazo ya jasu sallah tayi mamakin yanda ya dan iya ba haka ta zata ba ma sam,a zaton ta komai be Iya ba,
"To yanzu munyi sallah sai gado ko?"
Ya fada yana kamo ta jikin shi ya na qoqarin cire mata hijabin ta,Wani mummunar fad'uwar gaba ne ya kama ta Jin ta a jikin shi da ta yi,a hankali ta saki jikin ta ta kwanta a nashi tace,
"To ai baka min addu'ar da na ji ance angwaye na wa amaren su ba na neman tsarin Allah daga sharrin matar da suka aura da neman Allah ya hada su da alkairan da ta ke da shi, ko so kk na dinga ma rashin kunya ko qin bin umarnin ka?"
Kad'a kai Ahmad ya yi, sannan yace
"Nan da d'aya Atiyyaerh ke kin San da ya na iya karatun sallah ma? Ni ai ban wani iya addu'ar ba, se dai in ke Zaki koya min"
Ba musu kuwa ta koyar da shi, nan take ya dafa Kan ta ya yi mata sannan ya fara mata wasanni, cike da tsoro cikin zuciyar ta, amma ta dake, dan bata son ta yi zaman k'unci a gidan Ahmad, koma me zai je yazo so take kar ta walaka a wajen shi, taurin kan da zata mai shi zai nuna yanda ta zab'i ta zauna a gidan tinda aure dai an riga da an d'aura shi ba Kuma fasa kusantar ta zai yi ba, ko ba jima ko ba dad'e se anyi, to gwanda ma ta hakura ta sawa zuciyar ta salama,ji yake kamar zai had'iye ta, ko ina tabawa yake, yau wai shine da wannan zuqeqiyar a matsayin mata, dole a tanadi addu'a ta godiyar Allah, tun suna wasanni a qasa ya miqar da ita ya kaita gado, ina ganin yazare masu komai na jikin su na basu waje,nace a ci amarci lfy🤭
Ablaerh ta wahala ba kadan ba wajen Ahmad, ta yi kuka ta gode Allah, kukan takaicin rasa budurcin ta ga wanda ba ta taba zata ba shine yake dawainiya da ita, rarrashin ta yake sosai, yace,
"Ashe ku da ku ka yi boko ake cewa yan iska duk qarya ne, wanda basu yi makarantar ba sune yan iskan, dan kinga fiddausin bayan layi gaba daya a bude take,"
zaro ido Atiyyaerh ta yi waje, cikin razana da tsananin tsoro ta kalle shi ashe har neman mata yake bayan shaye shaye????????
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Makaranta ku