Showing 21001 words to 23611 words out of 23611 words

Chapter 8 - Shaawar Ta Nikeyi Complete Hausa Novel By Zainab Usman.txt

17 Mar 2026

11

yakeyi an gayra komai an saka turaruka ga abinci dinning table a shirye, murmushi suka sakarwa juna Ayma tace Gaksiya wannan fasahar data zo muna ta yanke muna Wahala zama gidan nan kega zuwa banda gobe mu wuce Legas." Anam tace "Wai da gaske Legas zamuje.?"

Ayma tace "Ke d'auka wasa nikeyi ne dole muje mu k'ara bud'e idanun mu." Cikin dare Sukayi Muguwar shiga ta bakaken kaya suka baje sumar kansu yadda ko idanunsu ba'a gani Anam ta sakawa Ayma nel itama ta saka kana suka fita bedroom din Salma suka shiga tana bacci, suka janye bargo,

tare da haske mata fuska ba shiru ta bud'e idanunta ganin su tsaye a kanta saida ta saki fitsari tayi masifar firgita, kuka ta fashe da shi ai kuwa suka shiga sakin dariya kamar mahaukata kana cikin mak'ale murya suka fara wasu magan ganu masu ban tsaro Salma tace "Ai wallahi har abada bazan karya alk'awarin dana d'auka ba ku yafe min da kyar suka fito, kana sukace idan ta gayama wani ko ta fito zasu yanka mata kai,

bedroom din Laure suka shiga itama sun masifar firgita kana suka fito sai bedroom din Alhaji Manir yana kan sallaya addu'a yakeyi jin motsi yasa shi waigawa saida ya zubara ai kuwa suka sakamai dariya, ajiyar zuciya ya sauke kana suka sanar da shi yadda sukayiwa su Laure Ayma tace "Kaga banda gobe zamu bar gidan nan mun kammala aikin mu abinda nike buk'ata kayi muna komai zamu tafi Legas ne a jirgi muke son tafiya."

Yace "An gama wallahi naji dad'i sosai na gode Allah ya saka da Alkhairy." Kana suka fito zuwa bedroom, washegari kuwa koda Alhaji ya sauko sun had'a breakfast an gyara ko ina na gidan sai k'amshi yakeyi Hajiya Salma sanyi da meni siket da riga iya cibiya tayi kyau sosai ta gayra sumar kanta, Hajiya Laure riga da wando ta saka ma sha Allah sunyi kyau dama,

iskanci ne yasa suka mayar da kansu y'an jagaliya, har Mota suka raka Alhaji ya tafi, Office, Alhamdulillahi cikin Kwana uku komai na gidan ya sauya ba kamar da ba yaune su Ayma zasu bar gidan sukayiwa Alhaji tijara sai ya sakesu ai kuwa ya basu takardar saki kamar da gaske suka d'auke akwatin kayansu, Alhaji baya parlon iya su Hajiya Laure ne,

Ayma tace "mun tafi idan muka ga an sauyawa dawowarmu bazatayi muku kyau ba." Tare suka had'a baki wurin fad'in"Ai wallahi mun sauya har abada saboda mun fahimce kuskuren mu." Anam tace"haka ake so suka bar gidan Ayma na cewa Yanzu "Misira zamu nufa ko k'asar faris wurin bikin Aljana Sury.?" Anam tace "Mu fara Misira daga nan mu wuce faris kega ai cikin awa biyu mun je mun dawo."

har suka fice parlon Laure tace "Wani aiki sai Aljani kijifa inda zasuje cikin awa biyu su dawo." Salma tace "wace nan in dai Aljanu ne kega mubar zancen nan karsu dawo."

Writer Bey Pinky Darling Mrs Jay ✍🏼
masu buk'atar More page suje Arewa pen suyi following dina pinkyjay@

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWARTA NIKEYI*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

(Romance love story)

🔞❌
Writer Bey
Pinky Darling Mrs Jay ✍️
✨✨✨✨✨✨✨✨


Following this link to join my WhatsApp channel domin samun zafafan liltafaina sabbi da tsofaffi tare abubuwan k'aruwa

https://whatsapp.com/channel/0029ValAwoOInlqYMwE1dK00


BOOK ONE
PAGE 2️⃣9️⃣⏩3️⃣0️⃣

Bakin get Alhaji ya d'auke su sai filin jirgi ya kammala musu komai na tafiya, har Hotel ya kama musu idan suje akwai yaronsa da zai zo daukarsu, be dawo gida ba saida jirginsu ya tashi, b'angaren su Ayma kuwa k'arfe uku jirginsu ya sauka saiga yaron Alhaji Manir yazo daukarsu da yake an bashi number Ayma, hotel ya kaisu bayan ya karb'e key d'in room don shi yazo ya kama d'akin,

ya fita abinci da abin sha ya kawo musu kana yace "Madam Ogah yace na kula daku duk inda kuke son zuwa na kaiku saboda haka idan kun tashi fita ki sanar dani." To kawai Ayma tace ya fita kana sukaci abinci bayan sun huta wanka sukayi tare da shiryawa, cikin k'ananan kaya, idan ka gansu zaka d'auka y'an Legas d'in ne, suka fita,

tafiya suka d'an yi mai tsayi kafin suka hau napep sukace a kaisu kasuwa zasu d'an zagaya bayan an saukesu Ayma taja hannun Anam suka fara zagaye kasuwar kamar y'an gari Wani b'angare ne suka fito, y'an jagaliya ne kawai a gurin suna shaye shaye, Anam taja da baya tace "Sis mu juya kawai, kafin suyo kanmu." Ayma" tace kan Uba Wallahi bazan koma ba ai saboda su nazo Legas shaiyasa ban zame ko ina ba sai kasuwa inaso na fara da y'an jagaliyar kasuwa kafin na had'u da sauran,

saboda haka kiyimin shiru." Dole Anam tayi shiru saboda tasan tinda tace bazasu juya ba to kome zai faru bazasu juya ba cigaba da tafiya sukayi har suka kawo tsakiyar su ai kuwa kamar jira sukeyi suka zagaye su Ayma d'aya daga cikin su ne yace "Tsageran yara me ya kawoku layin nan ne.?" Ayma tace "Kaine tsagera Wannan layin na ubanka ne da baza'a biyo ta nan ba.?"

"Hyhyhy Waye sa'arki a nan yau saikeyi nadamar zagina da kikayi kai Bado zoka chaskale min y'ar iska ka karb'e duk abinda ke hannunsa." Wani murmushin mugunta Ayma tayi kana ta janyo jakarta dake rataye a gaba tace "Wallahi duk d'an iskan daya dakeni saina rama an gayamuku ni sa'ar yara ce k'ananan y'an iska masu siyar da daga ni uban abinda kuke saida nike bayarwa."

ta fad'a tana d'auko wata farar leda cikin jaka kamar gishiri ne a ciki Chak suka tsaya suna kallonta Bado yace "Ogah kamar fa kokin ce a hannunta." Ayma tace " Ba kama bace kokin d'in ne." Ta mayar cikin jaka." Wanda aka kira da me suna Jams yace "Kaga kuyi mata duka ku karb'e komai." Ai kuwa Bado ya yi kan Ayma zai kai mata duka cikin zafin nama ta guce tare da kai mai naushi a fuska take hanncinsa da baki ya fashe da jini,


kafin ya d'ago ta k'ara kaimasa duka Wani yayo kanta tare da damke sumar kanta dake baya sakin Bado tayi tare kamo hannunwan gayen ta baya tayi wani juya ta dawo gabansa da k'arfi ta juya hannunsa baya ta dawo da shi gaba sai k'arar kashin hannunsa kaji ta k'arya shi, wani ihu ya saka tare da zubewa wurin yana neman agaji, takeyi,

wani katako d'auka jikinsa duk k'ososhi ne yaran da sukayo kanta ta fara kai musu duka da shi gaba d'aya ta zame musu d'an kunama kowa duka takeyi amma babu wanda ya samu nasarar tab'a jikinta, Anam kuwa y'ar kallo ta zama abu kamar a Film sai dukan maza takeyi wai ko dai Ayma jami'ar tsaro ce wannan abin ya daure mata kai,

Jams ne ya tashi ransa a b'ace ya kaiwa Ayma mugun duka saida ta kefe k'asa kafin ta d'ago ya k'ara kai mata naushi, yana dariya, wani juyin azaba takeyi kafin ta mik'e tsaye da kyar, kai mata duka yaje yi ai kuwa ta saka k'afa ta kaimasa wawan shuri gabansa inda Bananarsa take ina wawan Ihu ya saka tare da zubewa wurin yana neman taimako,

inda taga suna dauren daga da wuiwui taje ta kwashe ta gaba ta saka cikin leda har kud'ad'en dake wurin kana tace "Anam mutafi." Suka bar wurin suna fitowa napep suka hau yace Madam ina zuwa tace "Gada zaka kaini." Beyi magana ba har suka k'arasa ta biyasa kud'insa kana suka fita k'arewa wurin kallo tayi kana tace "Lallai wurin nan yaci sunansa k'ark'ashin gada ai kuwa yau sai sun san da zuwana.

dubawa tayi ina ne yafi y'an jagaliya ai kuwa ta hango wani layi mata da Maza ne a gurin kowa sha'anin gabansa kawai yakeyi, k'are chan suka nufa Anam tace "Wallahi bazamu sha ba a nan mutuwa zamuyi." Ayma tace zamanki a Legas na banza ne be tsinana miki komai ba bari kiga yadda ake jagaliyanci da isarsu wurin ta fisge dagar dake hannun Wani yana zuk'a wata budurwa na gefensa tana tsotsar mai Banana,


tana karb'a a baki ta zura tana zuk'ar tabar tana hura hayak'i yana fitowa harta hanci, dai dai kan wani gardi ta tsaya ga dukan alama shine Ogah a wurin ledar hannunta ta dire mai kana tayi mai alamar ya duba ya bata kud'i." Sa hannu ya yima d'aya daga cikin yaransa a duba ledar Wani zare idanu yaron ya yi kana yace "Ogah Wannan fa babbar harka ce saboda har uwar tafiya datayi wahala kusan wata uku an samu,


kaga shikenan yau zamuci dad'i." Kallon tuhuma Ogan keyiwa Ayma ita kuwa ta wayance kamar ta saba har kallar tace "Idan baza'a bani citta ba na k'ara gaba a matse nike." Tana fadar tana zuk'ar tabar tana busa mai hayak'i a fuska, wata dirowa ya janyo tare da d'auko mata Dollar 💵 rafa d'aya ya aje mata yanaso ya Gani idan har y'ar harkalla ce bazata karb'a ba,

d'auka tayi tana juya kud'in kana ta jefar da tabar cikin muryar y'an jagaliya tace "Wai mahaukaciya ka dauke ni ko yaya inaga baka buk'atar kayan ne." Tana gama fad'ar haka taja ledar ya dakatar da ita ragowar ya bata kana tace"Yanzu naji magana." Ta d'auke sigari guda d'aya tace "Dan cinna min ita." Ya kunna mata yace "Amma fa ban tab'a ganin ki a nan fa ko wuraren da nike harkalla daga ina kike.?"

Murmushi tayi kana tace "Ai bana harkalla yara ne ta manya nikeyi ko yanzu dole ce tasa haka akwai wasu kayan yaji da nikeson karb'owa abin kud'i yake ci shine na fito da kayan idan kana buk'atar wasu zan dinga aiko ma yarana suna kawo ma naga kamar nan abar wahala takeyi." Gyara zama ya yi kana yace " Eh muna buk'ata amma me zai hana mu k'ulla harkalla dake saboda wannan farar citta tafi wahala yanzu."

Ayma tace " to Yanzu babu ta a k'asa kud'i neke had'awa na karb'o idan kana buk'ata zaka iya saka rabin kud'in idan na kawo ma saika bayarda ragowar amma fa dole nima ka bani kasona da ban." Yace "Na yarda yanzu nawa zan bada.?" Wani yare tayi mai da hannu ai kuwa ya zubo kud'i a leda ya bata tare da karb'ar number ta kana ta bar wurin, suka hau napep,


Washegari suka shirya suka fita suka zagaye gari kana ta shiga kasuwa duk inda taga yara mata masu tallah marasa gata kud'i take raba musu saida ta rabar da kud'in gaba d'aya data karb'o k'ark'ashin gada da kasuwa, kana suka dawo ta kira yaron Alhaji Manir ta sanar da shi ya ta nadar musu jirgi zuwa k'arfe hud'u zasu koma ai kuwa haka akayi saida tazo filin jirgi ta cire sim card din data baiwa guy d'in nan ta yada shi,


K'ark'ashin gada kuwa sai yau Oga ya samu wanda zai siyarwa Kokin d'in, sai bayan ciniki ya fad'a kana ya duba abar zai shak'a ai kuwa yaji ba komai bud'ewa ya yi me zai Gani idan ba garin fulawa ba ai kuwa nan masifa ta kacame, ya shiga kirani layin Ayma amma a kashe, nan fa ya baza yaransa neman Ayma shiru kake ji,


Ayma kuwa da yamma jirginsu ya sauka suka hau napep zuwa gida, da mamaki take kallon gidan, sabbin motaci ne zube ga bodyguard d'in Ayman na zube a gidan kallon Anam tayi tace "Wai Yallab'ai ya dawo ne.?" Anam tace ga zahiri nan ke Gani." Suka shiga ciki wanka sukayi kana ta saka kaya ta fita Sumy ta gani, tace "Sumy yaushe "Yallab'ai ya dawo ne.?" Sumy tace "Tin jiya ya dawo."

dam k'irjinta ya buga haka ta haura sama tana norking, ta jima kafin k'ofar ta bud'e ta shiga zaune yake kan kujera ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya, yana tab'a wayarsa, Ayma tace "Yallab'ai barka da hutawa banza ya yi mata shiru tayi tasan dole ta fuskance wannan hukunci kallonta sama da k'asa kana ya daka mata tsawa yace "Ke ina kika tafi.?"

saida ta zabura kamar zata kife bakinta na rawa tace "am dama am uhm." Wata tsawa ya daka mata kawai ta fashe da kuka tace "Naje Legas ne." "Legas ya mai maita damk'o ta ya yi tare da kama sumar kanta idanunsa har sun sauya launi saboda b'acin rai yace "Da Auren nawa kika tafi Legas.?"

Wani dukan uku uku zuciyarta ta shiga yi kallon rashin fahimta tayi mai aurensa kuma kodai ya fara shaye shaye ne kallonta yakeyi a matsayin Saudat, ai bata ankare ba sai da ya buge mata baki saida ta saki kara yace "Yaushe kika tafi Legas kuma gurin waye kika je.?" Ayma bata iya k'arya ba ta sanar da shi Alhaji Manir ne ya yi mata komai har Hotel d'in da suka sauka ta sanar da shi

Wayarsa ya d'auka yana tab'a tare da karawa a kunne yace "Saj ka message nan na turoma inaso ka turomin bayanin komai yanzu ina jira." Ya kashe wayar yace "idan naji akasin abinda kika fad'a hamm." Banko k'ofar parlou akayi da k'arfin tsiya, Saudat ce ta diro kamar mahaukaciya tayo kan Ayma tana shak'o wuyanta tana fad'in "Wallahi saina kasheki na kashe banza,

ni za'a yaudara wallahi bazan yarda kamar ni ace zan had'a miji da wannan banza y'ar matsiyata, jaka jahila y'ar kyauye wacce batasan komai ba na rayuwa nice nan na koyar dake komai amma zaki ci amanata ki aure min Miji na rantse da Allah duk Uban da ya d'aura wannan aure saina naci Kutumar ubansa don.....Tas Tas kakeyi Ayman ya kife Saudat da wani wawan mari cikin b'acin rai yace,

"Uwar tawa zaki zaga tu wallahi bari kiji aure ya dauru doke ki zauna da ita matsayin kishiya abokiyar zama ke har Mace ce da kika tak'amar bazaki zauna da kishiya ba." Duk da marin ya shige ta amma bakinta be mutu ba sai cewa tayi "duk abinda kayi banga laifinka ba amma Wallahi dole saika saketa don bazan tab'a zama da ita a matsayin kishiya ba,

Ke kuma Wallahi ajalinki ne kika aura banza sake har matsiyatan iyayen naki duk saina yi maganinsu." Ta bar parlon Ayma kuwa gaba d'aya sun sakata cikin rudani sai zancen aure akeyi ita da Ayman addu'a takeyi idan mafarki ne takeyi Allah ya falkar da ita, Ayma ne ya katse mata tunani yana fad'in jeki shirya Mumma na son ganinki karki bata min lokaci."

haka ta fita tana son tamabaya amma ba fuska haka taje ta sauya kaya doguwar rigar les ta saka da mayafi me kyau ta saka turare sai kwalli data shafa da man baki, tace "Anam zamu fita da Yallab'ai." Tace "adawo lafiya bayan ta fito parlon k'asa ta gansa yace "koma ku fito keda kawarki." Ciki ta koma tace Anam ta shirya tare zasu tafi." Mayafi kawai ta saka riga da siket ne a jikinta na atamfa,

ta fito yana gaba suna bayansa har suka k'arasa Mota suka shiga bodyguard d'insa suka marasa baya, basu zame ko ina ba sai gidansu, parlon sama suka haura nan ya ajesu, ya shiga bedroom din Mamma ya sanar da ita Ayma na parloun cike da farin ciki ta fito,


cikin mutunci da girmamawa ta gaida Mumma ta karb'a cikin sakin fuska tace "Y'ata kiyi hak'uri da abinda zakiji nasan ban kyauta miki ba sai labarin aure kika samu bayan ke dawo an d'aura aurenki da Ayman ne jiya."!!!!!!!!!

Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahi a nan na kammala book one sai mun had'u a book 2 wanda Inda zaku samu amsar tambayoyin ku ya akayi aka d'aura auren Ayma da Ayman ya akayi Mumma ta samu dangin Ayma shin dama tana da a hali me ya kawota Katsina shin ya zamansu da Ayman da Saudat zai kasance , shin zai kamu da sonta kuwa

Ko iya SHA'AWARTA Kawai yakeyi,

Masu buk'atar payment ga account number 7060577995 Zainab Abdullahi Opay bank shaidar biya 07060577995
Writer Bey Pinky Darling Mrs


6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login