Showing 1 words to 3000 words out of 66338 words
Chapter 1 - MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt
*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤
_NA_
*Zee* *MD* ✍🏻
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Dasunan_ _Allah_ _Merahama_ _Mejin_ _K'ai_ _Tsira_ _Da_ _Aminci_ _Sutabbata_ _Ga_ _Shugaban_ _Halitta_ _Annabi_ _Muhammad_ *S.A.W* 🙏🏻🙏🏻
*Wannan* *Littafin* *Banyishi* *Dan* *Wani* *Kowata* *Ba* *Duk* *Wanda* *Yayi* *Dai-Dai* *Rayuwarsa* *Yayi* *Hak'uri* 👏🏻👏🏻 *Allah* *yasa* *Mu* *Amfana* *Ameen*🙏🏻
🅿️ 1.
Zaune take a tsakar gidan su rik'e da littafi da viro tana rubutu , Bakinta kawai zaka kallah kasan wak'a take rubutawa , tayi Nisa cikin Rubutun Wak'ar ta taji Muryar Umman ta tana kiranta " *NABEELA* kina inane ? cikin Sauri ta ajiye littafin da viro tamik'e ta nufi 'Dakin nasu , a Zaune tasamu Umman ta ta tana laluben d'ankwalin ta , da sauri Nabeela ta k'arasa ta d'auko mata d'ankwali tana d'aura mata , Umma tace " Kaini Bayan gida fitsari nakeji , Nabeela ta rik'e hannun Umman tata wacce take da lalura ta rashin gani , Band'aki ta nufa da ita suna tafe a hankali har ta raka ta , sai da Umman ta kammala abinda zatayi sannan tafito ta maida ta cikin d'akin , Umma tace " Nabeela muna da sauran d'umamen tuwon nan kuwa ? Nabeela tace " akwai Ummana bari na zubo miki , cikin jin dad'i Umman tace " Allah yayi miki Albarka Nabeela , Allah ya cika miki burinki nasan zama Mawak'iya , wani murmushi Nabeela tayi najin dad'i tana amsawa da Ameen ya Allah tafita daga d'akin....
Bayan ta zubowa Umman ta tuwon ta kaimata ta dawo ta cigaba da rubuta wak'ar ta , Sallamar Jidda itace ta katseta daga rubutun , tana ganin Jidda tafara Murmushi tace " har nafara tunanin bazaki zoba tunda naga kin wuce lokacin zuwanki , Jidda ta janyo Kujera ta zauna kusa da Nabeela tace " Bari kedai 'Yar Uwa wallahi sai da nagama gyarawa Inna gida sannan tabarni nataho , Nabeela tace Yaya Innar take to ? lafiya lau wallahi Ina Umman take dafatan kuntashi lafiya ? Nabeela tace " Lafiya lau muka tashi Umma tana ciki tana cin Tuwo , Jidda ta dubi littafin dake Hannun Nabeela tace " kice kinfara sana'ar taki kenan ? wallahi Nabeela kina had'a kanki da aiki , kullum kina rik'e da littafi da viro kina aikin Rubutu wak'a , Nabeela ta gallawa Jidda harara sannan tace " Bawani aiki wallahi , kinsan arayuwa ta Babban Burina shine nazama Mawak'iya , kuma a cikin jikina inajin wata rana Allah zai amsa min wannan burin nawa , Jidda ta tab'e baki sannan tace " wallahi da dagewa kikayi da addu'a Allah yasa a d'auke ki aikatau a gidan Alhaji Ghali kidinga d'aukar kud'i har kisamu ki koma makaranta , Nabeela shuru tayi fuskar ta tad'an sauya alamar bataji dad'in maganar Jidda ba , Jidda tana duban Nabeela taga yanayinta dafa kafad'ar ta tayi tace " kiyi hak'uri 'Yar uwa idan maganar ta k'ona ranki , Abinda yasa nace miki haka saboda inason kiyi karatu koyaya ne , suma Mawak'an dakike gani sunyi makaranta , kuma a tunanina inkikayi karatun koya yane nasan zai yimiki amfani ki kai matsayin dakikeso kikai , yanzufa kiduba kigani tunda aka koroki daga makaranta yau ina lissafi wata bakwai kenan har yanzu baki koma ba , gashi yanzu shirye shiryen zana jarrabawa ta komawa Ss 3 . Ake shirinyi . Nabeela kinsan iyayenmu basu da k'arfin dazasu biya mana muyi karatu , Nima badan Mak'ocin mu yana biyamin kud'in ba da yanzu ina zaune a gida , Nabeela taja Numfashi tabbas maganar Jidda haka take , cike da gamsuwa da maganar Jiddar tace " Bank'i maganarki ba 'Yar uwa , kinsan d'an Adam da buri kuma kinsan tun ina yarinya Babban burina nazama *Mawak'iya* , Jidda tace " nasan da hakan 'Yar uwa , kuma nima addu'ata itace Allah yacika miki wannan burin naki , Yanzu dai meye abinyi ? Nabeela tace " tashi zanyi nashirya muje gidan Alhaji Ghalin kozan dace , Tare suka mik'e ita da Jidda suka nufi cikin d'akin nasu , Umma tana jinsu tace " Jidda kinzo kenan ? tund'azu mutuniyar taki take dako zuwanki ya Innar taki ? Jidda zama tayi kusa da Umma sannan tace " Ina kwana Ummana yagidan ya kwana ? Umman Nabeela tace " gida ya kwana lafiya Jidda , Jidda tace " Inna tace tana gaidake itama , Nabeela daman tuni tayi wanka nan tashirya cikin wata atamfar ta da aka kawo musu kwancen kayan , Hijab d'inta tasaka sannan tacewa Jidda nagama shiryawa , Umma tayi musu fatan samun aikin tare da addu'ar Allah yatsaresu , Nabeela duk abinda tasan Umman nata zata nema saida tashigo mata dashi cikin d'akin Sannan suka fito ....
Nabeela da Jidda k'awaye ne sosai tun suna yara , Gidan su Jidda na bayan layin su Nabeela kowa yasan k'awancen su a cikin Unguwar , tamkar 'Yan uwa na jini suke wajen shak'uwa , Suna tafe suna hirar su cikin kwanciyar hankali har duka k'arasa k'ofar gidan Alhaji Ghali , Suna zuwa kuwa sukayi sa'a get d'in gidan Abud'e yake , da sauri suka shiga gudun kar masu gadi su hanasu shiga , Motar Me gidan suka gani shida Matar gidan suna tsaye a jikinta da alamar tafiya zaiyi suke sallama , Hajiya Sara tana ganin su Nabeela ta had'e ranta tamkar ba itace take murmushi ba , Alhaji Ghali yana ganin hakan yakai dubansa ga inda take kallo yaga metagani ta canza haka , Ido biyu yayi dasu Nabeela take yafara had'iyar yawu , su Nabeela k'arasowa sukayi gaban Hajiya Sara suka durk'usa suna gaidata , cike da Yauk'i ta amsa tana dubansu tace " wai bakune masu Neman aiki ba nace muku muna da masu aiki ? Jidda cike da girmamawa tace " Mune Hajiya , dan Allah kitai maka mana ko sharar filin cikin gidannan ne sai mudunga yimiki kina biyan mu , Hajiya Sara ta had'e gira sannan tace " bana buk'atar hakan , ina da masu yimin komai dan haka kuje wani gidan koza kudace dan bamu kad'ai bane madu dashi a cikin unguwar , Cikin Zuciyar ta mugun tsanar yaran ce aranta , gasu kyawawa dasu ga dirin jiki ko ita sunfita , Musamman waccen shegiyar dabata magana Nabeela kenan , cikin Zuciyat ta take wannan zancen , Muryar Alhaji Ghali dataji itace tasa ta dawo daga zancen zucin datake , cewa yayi " yakamata Hajiya ki taimaka ki d'aukesu , tunda ai gidan da girma baza arasa aikin dazasuyi ba , Hajiya Sara bata musu da Alhaji Ghali , komai yayi agunta dai dai ne dan haka cike da kissa tace " To Alhajina yadda kace haka za'ayi , zanduba naga wannen aikin za'abasu , cike da jin dad'i su Jidda suka fara Godiya tamkar su kifa , Hajiya Sara ta dubesu tace "kushiga cikin gidan ina zuwa , cike da girmamawa suka ce mata to sannan duka mik'e suna barin gurin , Alhaji Ghali tuni yarakasu da Mayun Idanunsa yana jin sandarsa na harbin iska , cikin zuciyar sa yace " haba Hajiya kinaso kimin k'eta inga abinci har cikin gida sannan kice zaki koran minsu , Hajiya Sara tana hankalce dashi dan tasan waye Alhaji Ghali wajen neman mata tamkar bunsuru , duk iskancin dayakeyi tana sane dashi , dan har k'awayenta take turawa yanemesu in yabasu kud'i suraba tare , dayake itama gwanace wajen iskancin harda mata yi take shiyasa bata damu da halin sa ba...
Zunguran Sandar sa tayi firgigit yadawo daidai yana kashe mata ido , cikin Kissa tace " yaga Abincin cinsa hargida ko ? sosai k'eya Alhajin yayi yana cewa " indai dake agabana ai duk mata maza nake ganinsu , cikin jikinsa tashige tana manna masa hot kiss tace " ninasan dahakan Alhajina , dak'yar yasamu yamata dabara yafita dan sauri yake zasu had'u da wata sabuwar yarinyar sa dayayi, wacce bai san Hajiya Sara ce tahad'a su ba , motar sa na fita tayi wani murmushi na mugunta sannan ta furta " Alhaji Ghali kenan , duk wani arzik'in dakake tak'ama dashi sai yadawo nawa , tunda banhaihu dakai ba dole ne na ci rabona a jikinka , juyawa tayi tana murmushi tashige cikin gidan nata.....
Tunda su Nabeela suka shiga cikin palor suka zama 'yan k'auye , iya had'uwa palor gidan Alhaji Ghali ya had'u , gawani k'amshi dake tashi tamkar anyi b'arin turare , suna nan zaune saiga Hajiya Sara tashigo , Zama tayi akan d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun palor , Dubansu tayi sosai sannan tace musu " kutashi tsaye kuciremin Hijabanku tunda ba gidan mutuwa kuka zoba , jikinsu na rawa duka mik'e suka cire hijaban nasu , k'irjinsu tabi da kallo tamkar tsohuwar mayya , cikin Zuciyar ta tafara cewa " tabbas wannan yaran 'yan baiwane , kalli Nonon su tamkar susuka dasa abinsu , kowacce tana da dukiyar fulani daidai misali gasu atsaye k'yam , kallon datake musu yasa jikinsu yin sanyi suka fara tsarguwa , ganin hakan yasa ta saita kanta cikin Zuciyar ta tana fad'in " bayanzu zan nemeku ba sai na janyoku jikina na gama daku sannan , a fili tace " inaso kudunga yimin aikin gyara gida da yamma , dan haka zaku dunga zuwa duk k'arfe Uku kufara aikinku , sai bayan Magariba zaku dunga tafiya , inkun amince daga gobe kufara zuwa , inkuma baku amince ba to karku sake dawomin gida , cikin girmamawa sukace " sun amince zasu dunga zuwa , Nan tace susaka Hijabansu sutafi , da sauri suka d'auki Hijabansu suka saka sallama sukayi mata zasu wuce , kiransu tayi ta zuge jakar ta tabawa kowacce dubu biyu sukayi mata godiya duka wuce , suna fita tahau dariyar mugunta tana fad'in " zakuzo hannune yara tabbas saina sha zumarku sannan sai mijina yasha shima , sai kundawo yarana sai yadda nayi daku.....
*Tofah* kubiyoni danjin yadda zata kasance ,
*Comment* plss
*'Yar* *Mutan* *kanawa* _Ce_ 🌹😍*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤
_NA_
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rhamanir* *Rahim*
🅿️ 2.
Tunda su Nabeela suka fito daga gidan Alhaji Ghali suke murna , wannan kud'i da Hajiya Sara tabasu ba k'aramin dad'i yayi musu ba , cike da jin dad'i Nabeela tacewa Jidda " wallahi 'Yar uwa naji dad'in wannan kud'in da Hajiyar Nan tabamu , kinsan wallahi bamu da Abincin daza muci yau , jiya ma wannan tuwon sadakar da muka anso wallahi banci dayawa ba saboda Ummana , shine Yau dasafe na d'uma ma mata shi taci , Ni kuwa har yanzu ban karya ba wallahi kinga kuwa dole naji dad'in kud'in nan , Jidda tayi murmushi ita tace " wallahi nima tunjiya bank'ara cin komai ba , tuwon namu ma mu bai kwana ba saboda jiya ina komawa gida naga Yaya Sa'ade tazo wai Mijinta ya saketa , Nabeela tsam ta tsaya tana duban Jidda tace " amman Jidda meyasa baki sanar dani ba sai yanzu , yanzu Yaya Sa'ade ansakota kenan ? Jidda ta tab'e baki tace "to ai wallahi da wannan k'addararran auren nata wanda a sakoka kasan agida kake , kawai dai muyi mata addu'a Allah yakawo mata wani mijin nagari , suna tafe suna hirarsu Hankali kwance har suka k'araso kasuwa , Jidda tace nidai shinkafa zan auna 'yar hausa kwana d'aya , sannan sai nase wake zuwa kwana biyu muga yadda za'ayi , Nabeela ita Shinkafa ta auna rabin kwano , sai ta siya musu fulawa da wake sauran canjin tasiyo maggi da mai da Barkono , haka suka kashe duk kud'in baifi sauran nera d'ari biyu biyu ba sukayo gida ,
Suna zuwa k'ofar gidan su Nabeela sukayi sallama da juna akan sai zuwa gobe tunda yau bazasu je anso tuwon sadaka ba......
Nabeela na shiga gida tasamu Umman ta a zaune a tsakar gida , k'arasawa tayi ta zauna kusa da ita tace " Sannu da hutawa Ummana yagidan yake ? Umma tayi murmushi tace " Sannu 'Yar Albarka Inafatan kundace and'auke ku aikin ? Kwantawa tayi jikin Umman ta ta tace " Addu'arki ta amsu Ummana an d'auke mu aiki a gidan Alhaji Ghali , zamu dunga zuwa kullum duk k'arfe Uku na yamma mu dawo bayan sallar magariba , cike da jin dad'i Umman tata tace " Alhamdulillah Allah yataimaka Yatsareku da dukkan wani sharri , Allah yacika miki burinki 'Yar Albarka kizama Mawak'iya , wani lumshe Ido Nabeela tayi najin dad'i tace Ameen Ummana , indai nazama Mawak'iya sai na biya kud'i ko nawane anyi miki aikin Ido kindawo kina gani tamkar kowa Ummana , Ciki da jin dad'i Umman tace " Allah yasa Nabeela ta 'Ya 'Daya tamkar da dubu , shafa mata kai takeyi tana ta sa mata Albarka , Nabeela tace " Ummana d'azu da mukaje gidan Alhaji Ghali matarsa da zamu taho tabamu dubu bibbiyu nida Jidda , da muka taho na biya kasuwa na siyo mana kayan Abinci wanda zamuyi Amfani dashi , Umma tayi Murmushi tace " wannan Mata Allah yayi mata Albarka , kinga yau ta hutar daku zuwa anso sadakar Tuwo , Nabeela tace " wallahi kuwa , yanzu ma tashi zanyi nasiyo gawayi nazo na d'ora mana Abinci dan nafarajin yunwa , cike da jin dad'i Umman tata tace " tashi kiyi maza 'Yar Albarka , banason ki zauna da yunwa tunda har ansamu yadda za'ayi....
Nabeela tana siyo gawayi ta d'ora musu d'anwake da wannan fulawar da tasiyo , dan tasan Umman ta nasan d'an wake sosai , bayan ta kammala musu tashiga wanka , tana fitowa ta d'auro arwala lokacin itama Umman tayi arwalar , sallah suka tayar bayan sun idar ta mik'e ta zubo musu Abincin , tare suke cin Abinci wani lokaci yanzuma tare ta zubo musu suna ci , suna ci suna hira wacce rabinta akan samun aikin nan da sukayi ne , har suka kammala ta d'ebo musu ruwa suka sha , Bayan ta kwashe kwanunkan tadawo ta zauna kusa da Umman ta ta tace " Kinsan wani Abu kuwa Umma ? Girgiza kai Umman tayi alamun bata saniba , Nabeela tace " wai ansako Yaya Sa'ade d'azu Jidda take gayamin , salati Umman tayi sannan tace " wannan aure na Sa'ade sai data fito dai hankali ya kwanta , to Allah yasa hakan yazamar mata Alkairi , Nabeela tace " Ameen , Umman tace tashi zakiyi muje gidan su Jiddar inyi musu Jaje tunda daman kwana biyu bamu had'u da Innar tasu ba , kuma kinga gobe kince zaku fara zuwa aiki bamai rakani , Nabeela tace " to Ummana tashi mutafi bari na d'auko mana Mukulli ....
Suna tafe suna hirar su tsakanin Uwa da 'Ya hannun Nabeela rik'e dana Ummanta , kana ganinsu kaga wanda basu damu da wani k'yalek'yalen duniya ba , a haka har suka iso gidan su Jidda , dayake daman ba nisa tsakaninsu , da sallama suka shiga cikin gidan su Jiddar , Innar Jidda ta ansa cike da jin dad'i tana fad'in " Marhabun da Umman Nabeela , shimfid'a tayi musu suka zauna , Nan Suka shiga gaisawa da juna , Nabeela ta gaida Innar su Jidda sannan ta mik'e tashige cikin d'akin tabar su anan zaune suna hira..
Jidda na kan katifa a kwance Nabeela ta fad'o itama kusa da Jiddar , Jidda tace " nasan kin fad'awa Ummana sakin da akayiwa Sa'ade shiya tazo ? Murmushi Nabeela tayi tace " taya bazan fad'a mata ba , aikinsan dole taji kuma ai jaje zatayiwa Inna , Murmushi itama Jiddar tayi tace " kinsan d'azu da muka rabu dake nataho hanya nayi karo da Ayuba me kanti , kinsan meya cemin kuwa ? Nabeela ta girgiza kai tace saikin fad'a , Jidda tace " Hmm wai d'an iskan Mutumin nan wai cewa yayi nazo nasameshi a shagonsa ko nawa nakeso zai bani , tunda yaga wai karuwancin Namu nida ke k'ara gaba yake , Nabeela tuni ranta ya b'aci tace " ke kuma sai kika ce masa me ? wata iska Jiddar ta furzar sannan tace " wallahi takaici bai bari nabashi amsaba , juyowa nayi na nufo gida shine najishi yana cewa " wai gashinan naje anyi iskanci dani anbani abinci d'anye , wallahi abin yamin ciwo sosai 'Yar uwa , mik'ewa tsaye Nabeela tayi a fusace tana huci , da sauri itama Jiddar ta mik'e tana rik'e Hannun Nabeela tace " Ina zakije 'Yar uwa ? Nabeela tace " taya zai gaya miki irin wannan magana amman kikasa d'aukar mataki , wallahi bakiji yadda zuciyata