Showing 12001 words to 14144 words out of 14144 words

Chapter 5 - MUGUWAR SURUKA PDF Completed.txt

kuma insha Allah duk inda yarinyar nan take sai na sa annemo min ita bai ce mai komai ba yawuce.










Hajiya tana zaune zaman gida babu dad'i komai ita keyi babu mai yimata wanki babu mai share mata d'aki sab'anin da da komai yimata akeyi duk ta rame tayi baki girki sai dai ta kwashi na k'asan tukunya wanda Saiham ta rage shima sai ranar da taga damar ragewa wataran ma bata rage mata, ga Safwan duk ya birkice duk abinda Saiham tace shi akeyi a gidan Hajiya ita takewa Saiham wanki ta share gida tayi wanke wanke babu mai kula ta a gidan wulak'anci kullum da irin salon da suke mata.



Hajiya na zaune a tsakar gida Saiham da Safwan suka fito daga d'aki hannun su rik'e da juna ta kalle su ko kallon inda take basuyi ba ta tashi ta sha gaban su tace "Yanzu kuna ganina amma babu wanda zai iya yimin magana kuna ganin halin da nake ciki amma baza ku kaini asibiti ba, wani bazan kallo Saiham ta watsa mata tare da hankad'e ta ta fad'i gefe tace ki mutum mana ina ruwan mu da zaki zo kina mana hauka a nan Safwan yaji wani iri amma babu yadda zaiyi ko bud'e baki yayi zaiyi magana sai yakama, Rik'o shi tayi tace "Dan Allah sweetheart mu tafi kar ta b'ata min rai suka shige mota suka wuce, ta saki baki tana kallon su wani hawayen bak'in ciki wani na koro wani.
























*✍🏼✍🏼ԹհɑɾԵҽҽʍɑɾհ մʍɑɾ ɑҍժɑӀӀɑհ*
[9/2, 2:46 PM] ɧąʝıყą ცąცცąɧ🙎🏿: 🙎🏿🙎🏿🙎🏿🙎🏿🙎🏿🙎🏿🙎🏿🙎🏿
*MUGUWAR SURUKA*






*♻£EXCLUSIVE WRITERS FORUM*






_Writing by_ *:-pharteemarh*




_Story by_ *:-bebe'ath(yar gatan huda)*




_£dited by d eloquent £ditor_ *:-bebe'ath*




*dєdícαtєd tσ вαíwα wrítєrѕ*💋💋💋








~page~
75to80


🔚






Nadama sosai Hajiya bilki tayi taje tabawa Alhaji hak'uri ya kore ta tare da gargad'in kar tak'ara zuwa masa gida, da kanta taje ta same iyayen Suhaimah take sanar musu cewa duk abinda ya faru k'arya ne kuma ita ta saka Safwan yace ba cikin sa bane ko ta tsine masa duk ta fad'a musu muguntar da ta had'awa Suhaimah, tace "kuma abinda yasa idan na fad'a muku magana kuke yadda wani boka nasa yayi muku asiri amma ku taimaka ku yafen min dan Allah tana kuka tana fad'a.






Shi ko Dady abin mamaki ya bashi ya d'aure masa kai toh ita wannan mata wanne irin k'iyayya take wa 'yarsa haka da tayi mata wannan abu, Momy kuwa kuka take sosai tana Allah ya isa tsakaninmu da ke bilki bazamu yafi miki ba kin cutar da mu kin cutar mana da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba Dady ma kasa daurewa yayi sai da yayi hawaye yace bilki ki tashi ki bar min gida kafin insa a fitar min da ke kije ke da Allah dan cutar da kikai mana bazamu yafe miki ba, ta tashi ta fita tana da nasanin abinda ta aikata.












Suhaima suna zaune cikin kwanciyar hankali duk abinda take buk'ata Adnan yana musu basu da damuwar koma.








A k'ofar gidan su yaga Hajiya bilki a zaune kamar almajira yace "Hajiya lpy kike zaune anan tace "Adnan dan Allah ka taimaka katayani bawa su Alhaji hak'uri akan abinda ya faru sharrin shaid'ane takwashe kaf labarin ta bashi ya jinjina kai yace laila to tashi kije zan basu, ya shige gida ya barta a zaune a gurin.








Yana shiga gida yaga su Dady a zaune yayi tagumi Momy kuwa kuka kawai take guri ya samu ya zauna yace lpy na ganku haka, Dady ne ya d'ago idan sa wanda suka kad'a suka jajir yace "Adnan kaji wannan muguwar matar abinda tayi mana duk abinda take zuwa to fad'a mana akan Suhaima ashe k'arya take kawai k'iyayyace.


Yana hawaye yace "Me yarinyar nan tayi mata haka? wannan k'iyayyar tayi yawa




Shima Adnan hawaye yake amma na farin ciki da Allah ya bayyana gaskiya Suhaima tafi ta daga fushin iyayen ta yace "toh Dady yanzu sai muyi hak'uri tunda tanemi yafiyar mu ita kuma Suhaima sai muyi ta addu'a Allah ya bayyana mana ita aduk inda take.




Yace ameen amma in kaga na yafewa wannan muguwar matar toh sai naga Suhaima.




Tashi Adnan yayi yafita yace Allah ya bayyana ta bai wuce ko ina ba sai k'ofar nasarawa gidan kakar su da murna ya shiga Suhaima tana zaune tana gyarawa Ayman gashi suna hira da kaka sukaji sallamar Adnan yana zuwa suka gaisa ake sanar dasu abinda ya faru dukkansu sukayi murna, Adnan yace yanzu bazaki koma da wuri ba sai nan da wasu lokuta dama Dady ne mai matsala amma ita Momy nasan kukan farin ciki take, suka ce "haka ne kaka "tace kai amma gaskiya bilki ba k'aramar azzalumar mata bace kai ni ko a zamanin da ban tab'ajin *MUGUWAR SURUKA* irin bilki ba, tashi Adnan yayi yai musu sallama tare da basu kud'i suk'ara suyi amfani dashi ya tafi.












Dady abu kamar wasa ya ta da hankali neman Suhaima abu har yakaishi ga kwanciya a asibiti lamarin da ya d'agawa kowa hankali musamman Momy takira Adnan tace gaskiya yakawo Suhaima haka, kwanan shi biyu a asibiti bayacin komai yana kwance Momy tana zaune a gefen gadon Sukaji sallamar Suhaima kamar a a mafarki Momy batayi wani mamaki ba sai dai murnar ganin 'yarta da tayi, tayi kyau ta murje kamar wata balarabiya ga Ayman yarinya kyakykyawa, Shiko Dady basan lokacin da ya tashi ba yaje yarik'eta ya kura mata ido kamar wanda yaga sabuwar halitta yana hawaye yace Suhaima kice Allah nagode maka da ka bayyana min 'yarta cikin kwanciyar hankali.










A ranar suka koma gida Dady yayi ta bata hak'uri tace ita basuyi mata komai ba kuma ko sunyi ta yafe musu.







Rayuwa ta koma mai dad'i Ayman tana samun kulawa sosai gurin kakannin ta ga kud'i Allah ya bud'a musu suna shigowa suka k'era gida na gani nafad'a.









Alhaji mahaifin Safwan taje yaji labari yayi murna sosai yaga jikar sa yana k'aunar ta yana kula da ita sosai yana zuwa yana gani ta.







Bayan barin Hajiya daga gidan su Suhaima ta koma gida tunda tashiga d'aki bata fito kuma ba wanda yane me ta acikin gidan ashe bata da lpy baci ba sha tunda ta dawo sai da ta ga ba sarki sai Allah ta rarrafo ta fito parlor lokacin Safwan yana zaune gani halin da take ciki yasa hankalin sa ya tashi ganin mahaifiyar sa haka d'aukan ta yayi yakai ta asibiti sukai mata taimakon gaggawa yaje yasami mahaifin sa yake fad'a masa halin da take ciki ya rufe shi da fad'a yace kar yak'ara zuwa masa da zancen ta, hak'uri yayi ta bashi sai da k'yar ya shawo kansa ya hak'ura sukaje asibiti yaga halin da take ciki ya tausaya mata sosai Safwan ne ke kula da ita saboda Saiham batanan bai san inda ta tafi ba, satin su biyu aka sallame ta taji sauk'i sosai ta koma gidan Safwan taje ta bawa Alhaji hak'uri sai da ya tabbatar da tayi nadama ya mai da ita sannan suka fara neman mafita yadda a subi su nemawa Safwan magani sauka suka sa akayi masa suma suka dage da addu'a suna karb'o masa rubutu yana sha cikin ikon Allah yaji kamar bashi ba kamar wanda yayi bacci ya tashi hankalin sa ya dawo jikinsa ya tuna da Suhaima da cikin shi da yake tare da ita koda yaje gidan su na da aka sanar masa sun tashi hankali a tashi ya koma gida yake tambayar Alhaji ko ina suka koma yace bai sani ba hankalin shi ya tashi sosai kuka yake yana bawa mahaifina sa hak'uri sai da yagama yace toh gobe ku shirya muje sannan yaji hankalin sa ya kwanta.






Tashi yayi yaje gidan sa wanda baya son yaje kwakwata baya son ganinshi amma kawai yaje yana zuwa yaga mota a cikin gidan yana shiga parlor yaga Saiham tana kwance akan kujera da wani tsohon saurayin ta yana zaune tayi filo da cinyar sa suna kallo daga shi sa T-shirt da gajeran wando ai baisan lokacin da ya fara dukan sa ba ko ta ina suka tashi sukayi waje da gude Saiham bata tsaya ko ina ba sai gidan su Momy tana ganinta tace ke lpy na ganki haka baki kayan dake jikinki ba sai a yanzu ta lura dan mini skirt ne ajikin ta da vest suna tsaye a parlor sukaji sallama dan ake ne ya basu takadda yace wani ne a k'ofar gida ya aiko su suka ansa ta bude takadda saki uku daga Safwan masifa Hajiya lami ta fara ita bilki zatawa haka suma zasu sani kiran yayan Saiham tayi wanda yake auren Nusaiba 'yar k'anwar Hajiya bilki yana zuwa ta sanar mai tare da cewa tana so yasaki Nusaiba ta koma gidan su yace "Ni Hajiya bazan saki matata ba wallahi dan babu abinda tayi min itama ai laifi tayi aka sake ta ba haka kawai aka sake ta ba ya tashi yayi tafiyar sa.












Koma gida yayi yake sanar wa Hajiya abinda yafaru tace "kai amma yarinyar nan ko tsinanniya yarinya kayi m dai dai da kayi musu haka Allah yayi maka albarka Safwan tana hawaye tace Safwan kayafe min duk ni naja maka wannan abun yace babu komai Hajiya komai ya wuce.


















Washe gari k'arfe 11:00 suka tafi gidan su Suhaima sun same su suna nan dukkan su cikin kwanciyar hankali bayan sun gaggaisa Alhaji yayi gyaran murya yace toh Alhaji zuwa mukayi muk'ara baku hak'uri akan abinda ya faru dan Allah Alhaji a yi hak'uri yace babu komai ya wuce a yayyafi juna, shidai Safwan wurga ido yake ta ina zai ga b'ullowar Suhaimah amma shiru babu ita sai can Alhaji yace wai nikuwa ina 'ya tane? yace "tana ciki bata san kunzo ba bari a kira ta Momy ce ta kirata tafita tare da Ayman a hannun ta ta nemi gefe ta zauna ta gaishe su Ayman tana ganin kakan ta ta tafi gurin shi da guru tana masa gwaranci, Hajiya tana ganin ta fara murna bare kuma Safwan wanda hawaye suka wankewa fuska lokaci guda Hajiya takai hannu zata d'auki Ayman amma yarinyar tak'i zuwa gurin ta amma Safwan yana mika hannu taje ya rungume ta yana hawaye nan dai Hajiya da Safwan suka nemi gafarar Suhaima tace "babu komai Allah ya yafe mana anan take basu labarin yadda sukayi da Chachasko.








Bayan wasu watani Mahaifin Safwan yaje yasame Mahaifin Suhaima Sukayi maganar mai da auren su amma sai idan Suhaima ta amince, Yasami Momy da maganar da k'yar ta amince sannan suka sami Suhaimah sukayi mata nasiha tare da fad'a mata kudirin su a karo na biyu tace babu komai Dady nasan bazaku had'ani da abinda zai cutar da ni ba na amince suka ce "Allah yayi miki albarka.




















Bayan sati biyu aka mayar da auren Safwan da Suhaima sannan aka d'aura auren Adnan da Yasmeen aka kai amare gidajen su aka bar Ayman gurin Momy gida Safwan yayi had'adde na gani na fad'a gida ya tsaru sosai suna zaune cikin kwanciyar hankali da soyayar juna Hajiya kulawa sosai take bawa Suhaimah suna zaune cikin mutunta juna rayuwa mai dad'i


















Tammat bi hamdih
*DA HAKA NAKAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA MUGUWAR SURUKA ABINDA MUKAYI DAI DAI ALLAH YA BA MU LADAN SA WANDA MUKA YI KUSKURE ALLAH YA YAFE MANA DA FATAN ZUMUYI BABBAR SALLAH LPY*














*✍🏼✍🏼ԹհɑɾԵҽҽʍɑɾհ մʍɑɾ ɑҍժɑӀӀɑհ*

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login