Showing 81001 words to 84000 words out of 142577 words
Chapter 28 - Rubutaccen Al'amari Book pdf Complete-.pdf
k'arfi ya shiga motarshi yana cewa,
"kace ana can anata kashe mutane Ummul kuma na can sannan kuce kar naje".
yana kaiwa nan ya figi motar cikin firgici ya nufi uguwar tasu,
yana zuwa ya samu uguwar a hargitse duk ko ina sai jini da gawarwakin mutane gaba d'aya
jikin shi sai rawa yakeyi cikin tausayawa rayuwar mutan k'asarmu ta Nigeria ya rink'a ratsawa
gefe-gefe yana kaucewa gawakin har ya samu ya isa cikin gidan nashi bai had'u da suba,
parking yayi ya fito da gudu ya nufi kan y'ar barandar da zata sadashi da k'ofar shiga parlour
nasu,
key yasa ya bud'e k'ofar ya shiga hannun shi rik'e da woyarshi yana ta kiran Usman tun a cikin
mota amman har yanzu da yake kiranshi a karona 13 bai d'aga ba har kiran ya katse,
ganin haka ya zira woyar a aljihun shi ya k'arisa bakin k'ofar bedroom d'in
Ummul d'in,
turawa yayi jin k'ofar a rufe yasa cikin tashin hankali ya fara magana da d'an buga k'ofar yana
cewa,
"Ummu ! Ummu! Ummuna ina kike? Ummu na kizo ki bud'e min k'ofa Hamman kine".
ita ko Ummul wacce tun sanda harbe-harben Boko Haram d'in suka tasheta a baccin daya
saceta gaba d'aya jikin ta ya fara b'ari kar-kar d'an cikin ta ya k'ara komawa saman k'irjin ta
numfashin ta ya rink'a korar juna sai wani irin zufa ke tsatstsafo mata tako ina,
ta kasa ko motsi dan fargaba da bugawar zuciya tana jin yadda mak'onta su ke guduwa amman
ta kasa tabuk'a komai,
sai yanzu da taji muryar Hamman nata ne ta yunk'ura cikin rawan jiki taje ta bud'e k'ofar,
yana ganin ta ya bud'e mata hannunshi,
da sauri ta fad'a jikin shi,
wani irin ruggume juna sukayi wanda basu taba jiyawa junan su irin wanan ruggumar ba,
Hamma Umar kam da k'arfi ya matseta a jikinshi kamar wanda yaga mutuwa na biye da ita,
itama da iya k'arfin ta tasa hannunta ta ruggumeshi murya na rawa tace,
"Hamma mu buya".
kai ya jinjina cikin rawan murya ya tallabo konta ido ya tsura mata cikin nata idanun yace,
"Ummu naji tsoro karsu kashe min ke shiyasa na dawo Ummu na ina sonki inajin tsoron rabuwa
dake zomu fita mu tafi asibitinmu yanzu na shigo layin nan basa nan sun gudu bayan sun
kakkashe mana yan uwa musulmai".
sai hawaye car-car a idanu su,
a hakan ya jawo hannun ta ko mayafi basu tuna d'aukaba tunda yanaga mota zasu shiga,
janta yake tana binshi a baya gaba d'aya jikin ta na rawa bata da kuzari ko kad'an
a haka har sunzo k'ofar fita parlour sai kuma duk suka juya suna kallon cikin gidan nasu,
sai ya kuma kamo hannun ta suka fito woje,
taku d'aya sukayi a na biyu suka tsaya cak a tsakiyar barandar tasu,
jikin Ummul rawa yakeyi har d'an cikin ta na yin k'asan maranta kuka ta saki cikin rawan murya
ta nuna zugan Boko Haram da suka cika harabar gidan nasu wanda sunkai su 8 gaba d'ayan su
rik'e da bindigogi da wuk'ak'e cikin tsoro ta k'ara rik'e hannun Hamma Umar d'in murya na rawa
tace, "Wayyo Allah na Hamma na nashiga uku zasu kashemu".
juyowa yayi cikin karfin hali ya kalleta murya a carke yace,
"Ummu na Insha Allah zan kareki bazasu kashe min keba zan kareki keda d'anna Allah yana
tare damu".
suna cikin haka suka k'araso gabansu cikin rashin imani d'aya daga cikin su yace,
"Kai meya dawo da kai?
bayan kana ganin kowa yana guduwa kai kuma yanzu muna ganin ka ka dawo munga
shigowar ka cikin gidan shine muka biyoka muje meya dawo da kai?".
Allah sarki Hamma Umar cikin jarumta yace,
"Matata na dawo in d'auka".
harara suka watsa mishi cikin izzati sukace,
"ita bata da k'afane da bazata gudu ba"?.
cikin rashin karaya yace,
"Bata da lafiya ne bazata iya guduba"".
jin haka suka matso gaban su cikin rashin imani suka fizgo Hamma Umar d'in suka shak'e
wuyanshi suna cewa,
"Ai gwara daka dawo kaga zamu samu mu kashe ka mu rege arna".
ita kam Ummul tunda suka fuzgo shi ta saki k'ara mai k'arfi ta matso kusa dasu cikin bushewar
zuciya ta rink'a kaiwa wanda ya shak'eshin duka tana,
"ka sake shi mugaye kawai azzalumai kuku bashi raine da zakuce zaku kasheshi mugaye
Hamma na ba arne bane kune arna kafuran Allah ta ala".
shiko Hamma Umar da k'afafunshi ya rink'a harbin na gabanshi da suketa dariyar mugun ta
naushin su yakeyi sosai har ya kada uku daga cikin su,
ganin hakan wand'a ya shak'enshi ya sakeshi cikin zalumci ya kalli sauran yace,
"Ku kasheshi".
nan sukayi kanshi gaba d'ayan su,
Ummul kuwa kuka ta farayi da burburwa tana neman agajin Allah,
shiko Hamma Umar kamar wasa ya rink'a dambe dasu Allah cikin ukonsa sai gashi ya jikkatasu
duk da taron dengin da sukayi mishi,
bai bar kare kanshi ba,
ganin haka babban nasu yace,
"ku sake shi".
ba musu suka sake shi,
hakan yasa Ummul ta taso da sauri tazo kanshi zata fad'a jikin shi sai babban nasu ya rik'eta ya
bank'are hannayen ta cikin ta ya fito fili,
K'ara ta saki da k'arfi tana cewa,
"Hamma Umar".
shima Umar cikin razani ya taso yayi kanta,
dan sauri babban nasu yace,
"wato Kai jarumi mai k'arfi ko,
toh mun fasa bazamu kasheka ba,
a gaban ka zamu kashe matar taka mu fasa cikin nata mucire abinda yake ciki,
kai kuma zaka zama ganimar yak'inmu zamu musuluntar da kai kaima ka zama mayak'i d'an
Boko Haram ".
yana gama fad'in haka yace kai zo ka farka cikin nata,
da sauri wanda yake bayan Hamma Umar d'in ya zaro wuk'a,
ganin haka
cikin rawan jiki da murya Hamma Umar ya sake guiwawin shi k'asa yana rawan murya yace,
"Kuji tsoron Allah ku sani Allah na ganin ku mutuwa kuma tana matakata ko wanne mai rai sai
ya d'and'ane ta,
ku dena kafurtani *Ni Musulmi ne* karku kashe min mata karku cutar min da d'ana".
dariyar mugunta suka saki baki d'ayan su suna k'ara bank'are Ummul ganin haka Hamma Umar
d'in ya yunk'ura da k'arfi zai jawota,
a dai-dai lokacin wanda yake bayan shi ya zaro wuk'a da nufin farka cikin Ummul,
cikin rashin imani da tsoron Allah yasa wuk'ar a wuyan Hamma Umar a gaban Ummul suka
d'anneshi sukayi mishi yankan rago ν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈ,
Allahu Akbar Hamma Umar Allah sarki Ummul cikin wani irin firgita da gigicewa da fita hankalin
ta tasaki wani irin k'ara mai firgatar da duk wani bani Adam dake wurin,
juyowa tayi da k'arfi ta rink'a dukan wanda ya rik'etan dukanshi take a haukace tana,
"Wayyo Allah na wayyo Hamma na Wayyoni Ummul naga ta kaina mugaye azzalumai Allah ya
isa nima ku kasheni ku kasheni nace ku kasheni ko".
dariya sukasa a mugunce wanda take dukan ya tureta ta zauna k'asa dirsham yace,
"ai bama kashe mata sai maza".
shi kuma wanda ya yanka Hamma Umar d'in yana rik'e da kafad'un Hamma Umar d'in k'ara sa
wuk'an yayi a kan wuyan nashi zai k'ara yan kawan a dai-dai lokacin kuma jiragen helkobta na
sojoji dake shawag'i a fad'in garin damaturun suka gilma ta kan gidan su Hamma Umar d'in
kuma sun ga halin da suke ciki ganin haka boka Haram d'in suka hankad'o matashi a kanta
sannan suka juya a guje suna fita,
a gigice ta matsoshi cikin tsananin ihu da rud'ewa,
shiko Hamma Umar cikin azaba da fizge-fizge dan jinin shi dake ta zuba amman da yake basu
iso mak'ok'oron maganarshi ba a hakan yasa hannu cikin wahala murya can k'asa numfashi in
ya fita baya dawowa yace,
"Ummu na ki dena kuka matso matso in mutu a jikin ki Ummu na na yafe miki duk abinda kikayi
min".
sai kuma ya rink'a mimmik'e k'afafunshi jikin shi duk na rawa jinin shi nata zuba,
ita kuwa Ummul matsoshin ta kumayi kanshi ta d'ago ta d'ora kan cikin ta cikin kuka tace,
"Baza ka mutuba Hamma karka mutu ka rufamin asiri".
a wahalce cikin magagin fitar rai murya na caccarkewa can k'asa yake,
"Ummu karki sha komai kibar cikina ki haifamin shi,
Ummu na kice kina sona".
K'ara ruggume shi tayi a gigice tace,
"Hamma bazan sha komai ba Hamma na ina sonka ina sonka Hamma na".
sai kuma tayi shiru jin yadda ya had'a tafin hannun ta da nashi ya damk'e da k'arfe sai kuma
yayi murmushi cikin sanyi da tafiyar numfashi da kyer take jin abin da yake fad'a,
"Alhamdulillah Ummu".
sai ya kuma saketa a hankali yace,
"Am..! Amm...! Ammina Us...! U,,, Usman".
sai kuma yayi mik'a a hankali yace,
"LA'ilaha'illahu MuhammadS'A'W".
daga nan sai Ummul ta jishi yayi shiru ya sake ko ina,
nauyin shi ya k'aru fuskarshi tayi haske sai d'umin jininshi da takeji yana ratsa fatar cikin ta har
zuwa cinyoyin ta,
Daga nan lokacin rayuwar Ummul ko ta shiga wani yanayi kukan da takeyi ya tsaya cak,
sai ta k'ara ruggumoshi a jikinta ta rik'eshi gam,
ta kasa kukan sai tayi zuru da idanun ta,
tana cikin haka taji motocin sojoji kai tsaye gidan suka shiga dan sojojin dake cikin jiragen ne
sukayi musu umarni su shiga,
suna shiga kai tsaye gaban ta suka je,
babban sun ne ya durk'usa gabanta a hankali yace,
"Sannu baiwar Allah me sunan ki".
shiru batayi magana ba bata kalleshi ba idonta na kan wuyan Hamman ta da fuskarshi,
a karo na uku sojan yace,
"baiwar Allah kiyi magana mana musan taimakon da zamuyi miki me sunan ki? me sunan
mamacin? ku yan inane ina za, a samu yan uwanku? ".
duk bata amsa mishi ba,
ganin haka yasa hannu zai jawo gawar Hamma Umar dake jikinta sai ta k'amk'ameshi da k'arfi,
abu kamar wasa da kyer suka kwaceshi a jikinta,
yana karbar shin ne I'd card ν ½ν²³ d'in Hamma Umar d'in ya fad'o daga aljihun sa,
ganin I'd card d'in ne yasa ya d'agoshi ya duba cikin mamaki yace,
"Dr Umar Ibrahim Umar shine doctor Alhj Ibrahim Gaidam govnor jihar nan".
jin haka yasa da sauri ya ruggume gawar Hamma Umar d'in cikin sanyin jiki yacewa sauran,
" ku taho da ita mu tafi gidan govnr dasu".
Haka kuwa akayi kai tsaye suka wuce g Government house dasu,
ana shiga dasu kai tsaye har parlour Alhj Ibrahim gaidam suka wuce,
mutuwar da ta girgiza illahirin mutanen gidan domin ko kwana biyu baiyi ba da zuwanshi,
kuka cur-cur suka rink'ayi anan cikin gidan govnr kuwa akwai abokin Mustapha ganin Ummul
yasa ya kira Mustapha ya shaida mishi,
suna nan a zaune Ummul bata gane komai tasa gawan Hamman ta a gaba bata kallon kowa,
Shi kuwa Mustapha lokacin da aka gaya mishi rasuwar yana gidan mahaifinshi dake bayan
government house d'in cikin kid'ima ya d'auko Umman shi suka taho tare,
suna shiga parlour Umman Mustapha ta matso jikin Ummul a hankali ta kamota,
ita kuwa Ummul bata kalleta ba sai k'ara rik'e hannu Hamman nata tayi,
a hakan taji muryar Mustapha tabbas taji muryarsa amman bata gane me yake fad'i ba,
daga gidan govnr Alhj Ibrahim Gaidam d'in ya bada umarni a d'auki gawar Umar d'in a kaita
gidan sarkin garin nasu wato Mai martaba Alhj Umar Bubaram ibin Wuriwa Bauya,
haka kuwa akayi aka kwashesu aka nufi gidan sarkin dasu inda suna zuwa aka shigar da gawar
sannan aka d'auki motacin sojoji guda 5 aka had'asu da motor Mustapha wanda Umman shi ke
zaune a baya tana ruggume da Ummul wacce ta zazzaro ido tun sanda aka kwace gawar a
hannun ta, a haka suka nufi patiskum bayan sun biya asibiti sun sanar nan ma Dr bashir da sauran
abokansu suka mara musu baya a zaton su a can za, a sallaceshi, suna isa cikin pataskum d'in
kai tsaye gidan su Abba suka nufa.
A gidan kuwa tunda gari ya waye basu da wani nitsuwa kowa jiki a mace,
har zuwa 11 na rana Adam dake konce a parlour Hajjajo cikin kasala ya mik'e ya fita ba tare da
yayi mata magana ba,
itama Hajjajo tana ganin shi amman batayi mishi magana ba,
shiko Adam parlour Nenne ya lek'a inda ya samu Sadik na konce kan 3str Aliyu na zaune gefen
Nenne amman su duk sunyi shiru,
koda ya l'ek'a sun ganshi ya gansu amman ba wanda yayi magana,
parlour su ya wuce yana zuwa ya samu Usman na zaune a tsakiyar parlour sai rawan sanyi
yake,
da sauri ya matso gaban shi baki na rawa yace,
"Hah Usman baka tafi damaturun bane? baka da lafiya ne?".
cikin rawan sanyi da mutuwar jiki yace,
"Adam ban tafiba Adam bazan iya tuk'iba sanyi nakeji har cikin hanjina zuciyata na bugawa".
cikin fargaba yace,
"Usman baka da lafiya ne?".
kai ya rink'a juya mishi a hankali yace,
"Lafiyata lau amman bana jin dad'in yanayin yau kuma sanyi nakeji ina son inje gum Hamma na
dan Allah Adam muje ka tuk'a motor muje gun Hamma".
ba musu yace,
" toh biri in d'auko hula mu tafi".
"Yauwa to kayi sauri mu tafi".
"To" yace sannan ya shiga cikin d'akin da nufin d'auko hular,
A dai-dai lokacin kuma motacin sojojin suka tsaya a k'ofar gidan,
suna tsayuwa Umman Mustapha ta kamo Ummul sukayi cikin gida,
suma sojojin sukabi bayan su amman su sai suka tsaya a harabar gidan gamida cewa Ummun
Mustapha in sun shiga tace ana sallama da mai gidan,
shiko Mustapha gidan Ammin su Hamma Umar ya wuce dan yasan gidan nata.
Ummun Mustapha na tallab'e da Ummul suka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan ta tsaya a
hankali tace,
"Assalamu alaikum ".
sai kuma tayi shiru
a parlour Nenne Kuwa cikin bugawar zuciya Nenne ta amsa mata tare da cewa,
" ku iso".
Sadik Kuma da Aliyu mik'ewa sukayi da nufin zasu fita su basu wuri,
Aliyu ne a gaba yana fita Sadik na binshi a baya,
Umman Mustaphan kuwa kallon Ummul tayi a hankali tace,
"Mu shiga ko Ummul".
jin sunan Ummul ne Aliyu ya juyo da sauri,
sai kuma ya zaro ido cikin rawan jiki ganin gaba d'aya rigar jikin Ummul d'in tana jik'e jilak da jini
,
a razane yayi wani irin k'ara,
sai gashi ya fad'a k'asa a sume,
k'aran da Aliyu yayi ne yaja hankalin mutanen gidan baki d'aya a guje suka firfito,
Abba na fitowa ya kalli Aliyu a sume sannan yaga Ummul a tsaye jini na d'iga shima sai ya fad'i
k'asa a sume,
Adam kuwa yana fitowa Abban yaje ya kamoshi dan shi baima lura da Ummul d'in ba,
Nenne Kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake kar-kar kamar mazari sai zufa ke zubo mata,
Ya Sadik kuwa tsayuwa yayi tamkar an dasashi,
ita kuwa Ummul sai yanzu ta d'ago kanta ta kalli ya Sadik d'in nata a hankali tayi taku taje
gaban shi tana zuwa ta fad'a jikin shi,
Sadik daya gama sakewa shima sai zamewa yayi ya zauna k'asa dirsham yana tallabe da ita,
ita kuwa Ummul kifuwa tayi jikin ya Sadik din tana jizon lips d'inta da zuwa yanzu sun kuburo
sintim sintim,
cikin karfin hali Nenne tace,
"Baiwar Allah make faruwa ina Umar?".
shiru Umman tayi sannan ta kamo hannun Nenne suka zauna a kan kujerun dake wurin sannan
ta kalli Sadik a hankali tace,
"Sadik kawo Ummul nan".
kai ya juya cikin kuka yace,
"bazan iya ba".
kukan Sadik yasa Nenne ma ta kife Kai ta fara kuka Adam ma kukan ya fara cikin tashin hankali
yace,
"Dan Allah ki gaya mana meke faruwa Ummul ina Hamma Umar ?".
cikin sanyi Umman Mustapha tace,
"Kullu nafsin za'ikatil maut".
sannan ta dafa kafad'un Nenne taci gaba da cewa,
"Lallai Umar namune amman Allah ne ya bamushi kuma ya fimu sonshi yau kuma ya kira Umar,
Umar ya amsa kiran mahaliccin mu".
gaba d'aya a tare suka mik'e cikin razani da kad'uwa,
Usman kuma dake tsaye gefen Adam,
kai ya rink'a juyawa da k'arfi sai kuma ya kalli Ummul dake jik'e da jini gabanta yaje ya durk'usa
cikin razani yace,
"Ummul gaya min inji a bakinki shi zaisa na yarda Ummul jinin waye a jikin ki?
Ummul gaya min ina kika barmi d'an Uwana Ummul wannan jinin waye a jikin ki? ".
Ba magana sai zamowa tayi daga jikin Ya Sadik ta fad'a jikin Usman d'in a hankali tasa hannu
ta shafo jinin a hankali ta gyada mishi kai,
cikin wani irin yanayi Usman ya mik'e tsaye sai kuma ya,........
*By*
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 3β£0β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Wannan littafi nawa gaba d'ayan shi sadaukarwane wa Hamma Umar, Dr Umar Ibrahim Umar
shuwa Allah ya jik'anka da rahamaν ½νΈν ½νΈν ½νΈ*
*Alhamdulillah Da forko zanyi amfani da wannan damar na mik'a sak'on godiya ta a gareku yan
uwana Musulmai bayan na godewa mahaliccina tabbas lallai musulmi dan uwan musulmi ne
kuma akwai soyayya da tausayin juna da k'auna a tsakanin mu musulmai hak'ik'a naga hakan
kuma lallai in