Showing 135001 words to 138000 words out of 142577 words
Chapter 46 - Rubutaccen Al'amari Book pdf Complete-.pdf
baki ta d'an tura ido
na zubda k'olla murya can k'asa dakaji kasan an gajiyar da ita a hankali tace,
"Hummmmm ya Usman kayi hak'uri na gajifa bazan iyaba wallahi jiri nake ji ka wahal dani da
yawa".
Sake kashe mata ido yayi ya laso lips enta yace,
"Kuma in kika bari k'ollah nan ta zubama saina k'ara Ummu na ina sonki yau kin sani farin
ciki kin jiyar dani dad'in rayuwa".
Da haka yawuce ya sata cikin ruwan,
duk yadda taso ya fita yak'i haka nan ta hak'ura sukai wanka tare ya sake ɗagota ya
kwantar da ita kan gado bayan ya goge mata jikinta ya fesheta da turare sa ya samata
rigar bacci shima ya shirya ya hawo gadon ya kwanta ya rungumeta kanta na kan
damtsen hannun shi da haka bacci yayi awon gaba dasu.
Haka nan da wayo da tsokana da barkwanci Usman yake samun nutsuwa sosai da
Ummul a koda yashe yaso sannan yana kula da ita sannan yana k'okarin bata kayan
itace tunda yaji ance suna gyara mace da k'ara mata ni'ima.
Sati uku kenan da Usman yasami damar raɓar matar shi,
koda yaushe yana manne da ita indai ya dawo daga aikin dayaje yana bata kulawa
sosai itama tana jin daɗin yadda yake mata saidai salon shogoɓa kam bata fasaba duk
da dazaran ta fara yake sakata dariya da barkwan cin shi.
Ranar wata juma'a Usman daga gurin aiki suya wuce masallaci yayi sallar juma 'a sai da
akayi magrib sannan ya dawo gida,
makullin hannun shi yasa ya buɗe k'ofar ya shiga yanda yaga palour a yanda yabar
shi yasa ya juya ya kalli kan dining table gani yayi babu komai hakan yasa gaban shi
faɗuwa kirjin shi yafara bugawa ya ajiye jakar hannun shi yayi bedroom ɗin yana shiga
yanda yahango Ummul kwance a nannaɗe cikin bargo tana rawar sanyi yasa yayi
saurin hawa gadon ya janye bargon ya rungumota,
zare ido yayi nan da nan jikin shi yakama rawa jin yanda jikinta yayi zafi ga
numfashinta na fita da kyar,
k'ara matsota yayi ya mannata da kirjin shi cikin rauni da sanyin murya yace,
" Ummuna meya faru Hubby?".
sai kuma yasa hannu ya share mata k'ollah dake zuba daga idonta yace, "Yi hak'uri
Baby na bari mutafi asibiti".
A take kuma sai tayi wani irin yuk'uri jikinta na rawa ta k'ank'ame shi idanuwan ta a rufa
a hankali tace,
" Ya Usman kirjina".
Hannun shi ɗaya yasa ya dafa kirjin yace,
"Kiyi hak'uri zai daina".
Daukan ta yayi yakai cikin mota ya kwantar mata da seat sannan ya dawo yaɗauki
wayoyin shi da nata yaja k'ofar ya rufe sannan ya koma motar ya zauna,
tukin yake yana ɗan kallon ta har suka isa asibiti,
saida aka basu ɗaki aka kwantar da ita sannan likitan yaje yayi gwaje gwajen shi
yakuma ɗibi jininta yaba nurse ta tafi lab dashi dan gwadawa likitan ya juya zai fita ya
dafa kafaɗar Usman dake tsaye yana kallon shi yace,
"i will call you when i got the result".
Dakai Usman ya amsa mai likitan na fita ya matso ya zauna bakin gadon ya rik'e
hannunta ɗaya yana shafa kanta a hankali har bacci ya ɗauketa.
Ba afi mintina 30 ba Nurse ta shigo hannun ta ɗauke da faranti da kayan aiki akai
tace mai likita na kiran shi
fita yayi dasauri ya nufi office din dr,
Ita kuwa ta kama hannun Ummul tafara aikin ta.
Yana shiga likitan yaimai nuni da kujerar gaban shi ya zauna jikin shi sai rawa yake dan
yanajin tsoron kar zuciyar tace keda matsala bayaso ace wani abu ya taɓa zuciyar ta,
shima likitan ya fahimci halin da yake ciki na firgici dan haka bai tsaya yimai dogon
bayaniba yace, "congratulation mr Shuwa you pregnant your wife last 2 weeks". wani irin
kallo yakema likitan kamar baitaɓa ganin shi ba saikuma ya maida kan shi ya jingina
jikin kujerar da yake zaune ya lumshe idanu yasauke ajiyar zuciya sannan ya ɗago yana
hamdala tare da yiwa likitan godiya ya fita.
Ita Kuwa Ummu bacci take ga drip da Nurse ɗin ta saka mata yana tafiya a hankali,
tsayawa yayi ya tsurata mata ido k'olla na zuba daga idon shi yasa hannu ya shafi
gefen fuskarta yana Al'ajabi da lamarin ubangiji Ummu na d'auke da cikin shi bayan ta haife na
Hamma Umar enshi tabbas lallai wanna shine *Rubutaccen al'amari* gaba d'aya zuciyar shi ta
cika da rauni sai zubda k'ollah yake,
A hakan ya shige bathroom na ɗaki yayo alwala yafito ya shimfiɗa sallaya yayi sallah
isha'i sannan yacigaba da nafilillinshi yana addu'a idanun shi nata fitar da k'ollah, yana
zaune kan sallayar kira ya shigo wayar shi wanda yasan bai wuce Adam ko Sadiq ba
dan sukanyi video call a irin wannan lokaci wato k'arfe 01:30am agogon Kuala lampur
sannan 9:30pm a Nigeria, janyo wayar yayi ya amsa ganin gudan jinin shi d'an d'an
uwanshi Umar Farouq zaune akan cinyar Adam a kan gado da shirin baccin shine yasa
yaji sanyi a ranshi yasaki murmushi shima Farouq dariya yayi yasa hannu ɗaya ya rik'e
airpist ɗin dake kunnen shi cikin gwarancin sa yace,
"Masa'ul khair Abeey". wani sanyi yasake ji a ranshi yana fara'a yace,
"masa'unnur ya bunayya, hw's ur day".
Domin dukkansu haka suke magana da Faruq suna haɗamai hausa, turanci, larabcin
shuwa arab, kanuri,
shiko Aliyu harda indianci yake cakud'a mai dan haka shima Faruq yake fahimtarsu
insunyi,
cikin gwari-gwarin ya kalli Usman yana murmushi yace,
"Abeey bah shadik ayi bacci wau adun bah Adam am fana".
Dariya yayi mai sauti yace,
"OK Baba Sadik yayi bacci yau a gun Baba Adam zaka kwana?".
kai ya gyad'a mai cikin jin dad'in Abeeyn shi ya gane maganar sa,
shima Usman dariya yayi tare da cewa,
"Yau tunda gurin bah Adam za'a kwana ya sunan ka na gaskiya?". gyara zama yayi
sannan yace,
"Uwan Faruoq Adam Cuwa".
Dukkansu dariya sukai yadda ya ke cewa Umar Uwar shuwa kuwa cuwa dariya sosai sukeyi
har Adam da yake mak'ale da kunne ɗaya na airpiest ɗin dan haka Farouq yake ko
fita za ayi dashi tofa duk wanda ya ɗaukeshi a lokacin shine mahaɗin sunan shi kuma
ko abu kabashi a lokacin duk wanda zai tambaye shi sunan shi na gaskiya to dana
me bashi abin zai haɗa,
sake tambayar shi yayi yace,
"Bobo na d'azu nakira ance katafi unguwa to a unguwar da kukaje ya sunan ka na
gaskiya? ".
Saida ya juya ya kalli Adam sannan yasa hannu ya janye airpiest ɗin dake kunnen
Adam ɗin dan kar yaji abinda zaifaɗa yayi k'asa da murya yace,
"Uwan Farouq Abba Daddy cuwa".
Hakan na nufin da Abba da Daddy sukaje unguwa haka Usman yayita mai tambayoyi
yana amsamai suna dariya sannan yace, "Abeey Ummiena". tashi yayi daga kan sallayar
yaje ya nunamai fuskar ta yace, "tayi bacci,
inta tashi da safe zata kiraka ku gaisa ko Bobona,
yanzu kabawa bah Adam saika kwanta kai bacci, i love u".
Shima a gwarance yace , "i wov u Abeey".
ya fad'a yana ɗaga hannu ya cire abin daga kunnen shi ya mik'awa Adam ya juya yayi
kwanciyar shi shiko Adam saida ya gyara mai lulluɓa sannan yaɗau wayar yafita palour.
Saida ya zauna a kujera sannam yace,
"Meya faru? naganku a asibiti haryanzu bata daina kukanba ko?". Cikin damuwa yake
maganar,
"Ba kuka tayiba Adam nadawo na sameta kwance da zazzaɓi sai kuma tacemin kirjinta
nima naɗauka ciwon zuciyar ne amma da mukazo sai akace ba shi bane".
Ajiyar zuciya Adam yayi sannan yace,
"meke damunta to?". yana sosa kai da wata y'ar dariya yace,
"Abee zaka zama kaima".
"yes that's my bro, dan Allah karka faɗawa kowa nizan faɗa". Murmushi yayi a zuciyar
shi yace,
"Kai kaɗai zan iya faɗawa wannan ".
Da haka sukayi sallama ya mata fatan samun sauk'i sannan ya katse wayar.
Sai da safe aka sallamesu dan jikin yayi kwari sosai sai shogoɓa da raki,
haka suka koma gida tanata narke mashi shikuma yasamu aikin yi sai lallaɓata yake
yana rarrashi a cikin ranshi kuwa yana tuna randa yaganta da cikin farouq da yanda
yake lura da Hamman shi da duk motsin da zatayi akan idonshi sai sannu yake mata,
yakanyi k'ollah yana gogewa a ɓoye dan karta gani, Itama kuma hakan ne a ɓangarenta da Usman da yaɗan kauce zata goge k'ollah tana
tuna burin zuciyar Hamma Umar d'inta.
Yau da Asuban fari Usman ya kira Adam wanda shima dai-dai shigowarshi daga masallaci
sallah asuba kenan yace,
"Adam ka haɗamu video call dasu Abba kuma inaso ka tabbatar kowa yana gurin har
Daddy".
Bai tsaya jin abinda Adam zaice ba ya ajiye wayar yakoma bedroom ya ɗauko dogowar
rigar Ummul da ɗan k'aramin mayafin rigar yafito palour itako Ummul tana kwance kan
3seater ya ɗagota ya jinginata jikin kujera ya saka mata doguwar rigar daya ɗauko ya
lulluɓa mata ɗankwalin daman y'ar shimi ce a jikinta da wando 3quater itako kallon shi
kawai take,
Adam ko yasami su Abba da Daddy a palour Hajjajo ya sanar dasu sakon Usman
nason magana da kowa a guri guda kiran kowa na gidan akai Ammi kuwa kawai a
zaune take amma jikinta sai rawa yake kirjinta na bugawa da k'arfi. bugu ɗaya Adam
yayi Usman ya ɗauka ya jingina wayar da kujerar dake kallon su shima Adam jingina
tashi wayar k'irar samsung tab E yayi yanda kowa zai gani sannan ya koma ya zauna.
Shiko Usman komawa yayi ya zauna gaban Ummul a k'asa ya tonk'oshe k'afafun shi
ganin haka jikin Ummul da Abba dake kallon su yafara rawa Nanne ma k'irjinta na
bugawa tai k'arfin hali tace,
"Usman meza kai haka kul karkayi wannan alk'?". Ammi ce ta ɗagawa Nanne hannu
alamar ta kyale shi kanshi a k'asa yakamo k'afafun Ummul wacce tuni tasa mai kuka tana
girgiza mai kai tana k'ok'arin janye k'afarta,
da k'arfi ya rik'e k'afar ya ɗora kan cinyar shi batare daya ɗago kaiba cikin sanyi da
k'auna da begen tuno Hamman shi