Showing 39001 words to 42000 words out of 142577 words
Chapter 14 - Rubutaccen Al'amari Book pdf Complete-.pdf
kai k'araba bare ya
kai karanta,
Anty Halima na yawan kiran Hamma Umar tace ya Ummul ta nitsu ko? sai yace mata ehh ba
komai fa,
ita kuwa Anty Halima bata gamsuwa hakan yasa tana yawan zuwa weekend toh hakan yasa
kab ta lura da zaman da suke yi.
ya Usman kuwa tunda akayi auren yak'i zuwa a cewarsa sai Ummul ta dena kuka,
Hamma Umar kuwa rana d'add'aya ne baya zuwa cikin pataskum shida k'anin shi sunyi ta hira
yana kula dashi kamar da sukan je gun Amminsu,
su wuni.
Yau Saturday tun safe Anty Halima da Hajjajo da inna da Aliyu suka shirya zasu je gidan su
Hamma Umar d'in ,
Hajjajo kuwa ta dage sai dai Ya Usman ya kaisu ,
dolen shi a hakan badon yaso ba ya kalli Hajjajo tare da cewa.
"Toh sai ku jirani na shirya ai Hajia Yawo."
murmushi tayi tare da cewa.
"Zamu jira jeka shirya,
dan ni nafi yarfa da tuk'in ka kaida Umaru,
Adam gudune dashi Abubakar ko motarsa kamar zai fire in mutun ya shiga."
Murmushi kawai yayi ya tafi part d'in su,
yana zuwa wonka ya shiga amman ya kasa sai kife kanshi da yayi a jikin gini ya rink'a wani irin
kuka mai cin rai zuciyar shi na harbawa da k'arfi zuwa yanzu Ya Usman shi kad'ai yasan idan
yayi tarin yakan ga jini amman yak'i gayawa kowa dan ya naga shi lokacin sane ya kusa.
Haka yasha kukan shi sannan ya shirya ya fito suka tafi idanun shi na cike da begen ganin
Ummul d'in.
A gidan Hamma Umar kuwa yau kwana yayi cikin takura haka ya wayi gari a buk'ace
bayan ya dawo masallaci d'akin shi ya wuce da niyar ko zai samu yayi bacci amman ina baccin
yak'i zuwa,
dole ya fito ya nufi d'akin nata yana shiga ya haggota tana zaune bakin gado cikin sanyi ya
zauna gefen ta,
shiru yayi yana kallon ta,
ita kuwa tab'e baki tayi tare da harara shi k'asa k'asa dan ta rigada tasan damuwar shi ita kuwa
ta naga ta nan zata cuzguna mishi,
ajiyan zuciya ya sauk'e tare dasa hannun shi ya kamo nata cikin rawan murya yace.
"Ina cikin matsala dan Allah ki taimaka min wallahi na fara cutuwa da rashin kulawar ki Ummul."
cikin ko in kula ta mik'e taje gaban dressing Mirror ta tsaya tana gyara gashin kanta,
mik'ewa yayi tare matsowa bayan ta suna kallon juna ta cikin madubin
hannun shi yasa ya tattara gashin nata a hankali yace.
"Ki tsammin aron lokacin ki da jikin na d'an wani lokacin ta haka zaki ceci lafiya ta."
juyawa tayi a tsiwace zatayi magana kenan ya fizgota jikin shi,
cikin rawan jiki ya had'e bakin su wuri d'aya,
ido Ummul ta zare jin yadda Hamma Umar d'in yake mata wani irin hort kissi ,
cikin zafin nama ta tureshi ta koma jikin mirror ta tsaya tana rawan jiki tare da kallon yadda
Hamma Umar d'in ya birkice gaba d'aya lips d'in shi sunyi jazir sai shek'i suke ida nunshi ma sai
shek'i suke alamun sun ciko da k'ollah,
ido ta kuma zarowa ganin ya zare jallabiyan jikin shi ya nufi kanta yana cewa.
"Zan karb'i hak'k'ina Khairi tunda na lura baki da tausayi so kike ki kashe ni."
kai ta rink'a juya mishi tana cewa.
"Karka matsoni wallahi bana so."
Bai kulata ba sai k'ara matsota yakeyi ganin haka yasa cikin sauri ta lalubo kolban turaren dake
kan mirror,
tana nuna mishi tana cewa.
" karka isoni Hamma Umar ka fitan min a d'aki."
bai kulata ba don shi a zaton shi ko buga mishi kolbar zatayi,
ita kuwa yana iso ta cikin tsoro da mugunta ta saiti idanun shi ta dannan bak'in turaren feesssh
sai cikin I....
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 1⃣6⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
*S*ai cikin idanun shi,
da k'arfi ya rumtse idanun tare dasa hannu ya damk'e kanshi da hannu. bibbiyu kai d'in ya rink'a
juyawa tare da yin layi cikin wani irin azaban da bazai misal tuba gaba d'aya jikin shi b'ari yakeyi
duk ta inda hudar gashin jikin sa yake zuface ke tsatstsafowa kwayar idanun shi tamkar zasu
zazzago su fad'o k'asa ji yakeyi tamkar rushin wuta aka cusa mai a cikin idanun, ba abin da jikin shi keyi sai rawa daya bud'e bakinshi zaiyi magana sai ya kasa sai lips d'in shi
suyi ta rawa tamkar maijin sanyi a haka ya rink'a juyu a cikin d'akin har yaje bak'in gado lokaci
d'aya kuma ya rink'a murza kanshi a jikin gadon dan azabar da yakeji,
Ita kuwa Ummul da fari murmushi tayi ganin yadda ya rumtse idanun shi jikin shi na rawa,
amman zuwa yanzu tsoro ya rufeta ganin yadda Hamma Umar d'in yake cikin azaba da gigita
gefe ta tsaya jikin ta na rawa cikin tsoro a hankali ta fara cewa.
"Hamma! Hamma!."
Yana jinta amman bashi da damar amsawa ba abinda yake yi sai murzan kan nashi da yakeyi,
cikin dauriya da k'arfin hali ya d'an bud'e idon
ihu Ummul tayi cikin firgicin ganin yadda kwayar idanun nashi sukayi jazir tamkar zasuyi aman
wuta sun fiffito woje sun hargitse,
shi kuwa Hamma Umar bud'e idon daya d'an yi sai da yaji k'ahon zuciyarshi tamkar zata dare
dan iskar da ta d'an shiga cikin ido
cikin sauri ya sake rumtse idanun ya k'ara danna kanshi a kan gadon,
Ummul kuwa gaba d'aya ta tsinke sai kuka ta saki da iya k'arfin ta tana kiran shi tana,
"Hamma Umar ka tashi! ka tashi mu tafi hospital. "
Ganin yadda gaba d'aya ya fara sakewa ne yasa ta sake sakin wani k'ara mai k'arfi.
Dai-dai lokacin Ya Usman kuwa yayi parking a harabar gidan jin yadda Ummul ke kuka da k'arfi
yasa cikin zafin nama ya fito da sauri ya nufi cikin gidan yayin da Aliyu ke binshi da gudu,
suna shiga parlour Ummul kuwa tana fitowa a nufin ta zata d'ebo mai ruwan sanyi ya woke
idon,
ganin ya Usman d'in ne tayi sauri taje gareshi cikin kuka da tsananin tsoro da firgici ta rik'e
hannu Usman tana buga k'afafun ta da k'arfi tana kuka murya na rawa take cewa.
"Ya Usman Hamma Umar!
ya Usman Hamma Umar."
shi Usman har ga Allah a zaton sa ko laifin tayiwa Umar d'in ya d'an razanata shiyasa take
kuka,
Aliyu kuwa tunda yaga yadda take kukan kawai sai ya nufi d'akin da take ta nunawan,
ya shiga ya haggo Hamma Umar d'in yadda yakeyi da gudu ya juyo parlour cikin tsoro yace.
"Ya Usman Hamma Umar baida lafiya fa zo kaga yadda yake."
dai-dai lokacin kuma su Inna da Anty Halima da Hajjajo suka shigo jin abin da Aliyu ke fad'a
yasa suka nufi cikin d'akin,
suna shiga Usman ya tallabo d'an uwanshi a jikin shi cikin rawan murya da bugawan zuciya
yace.
"Hamma na! Hamma Umar ! d'an uwana ! me yake faruwa da kai Hamma Umar kayi min
magana Hamma Umar meke faruwa?."
Anty Halima ce cikin rawan jiki ta kira doctor Abbas abokin Hamma Umar d'in,
sannan ta juya ta kalli Ummul dake ta zare ido jiki na rawa alamun rashin gaskiya cikin tuhuma
Anty Halima ta buga mata tsawa tare da cewa.
"Ki baryi mana kuka ki gaya mana meke damun shi me ya sameshi?."
jikin Usman ta kuma matsowa ta kalli Hajjajo da inna da suke ta kuka,
Aliyu kuwa gaba d'aya jikin shi rawa yake ganin yadda jikin Hamma Umar d'in ke rawa,
tsawa Halima ta kuma buga mata cikin watsa mata harara,
k'ara rik'e hannun Usman tayi,
shi ma Usman da yake rugume da d'an uwanshi cikin rawan murya yace.
"Ummul me ya samu Hamma Umar?
meke matsa ciwon?."
k'ara rik'e hannun Usman d'in tayi cikin rawan murya tace.
"Ya Usman idonshi ne yake mai ciwo."
cikin mamaki da k'arin tuhuma Anty Halima tace.
"Me ya samu idanun nashi? yaushe ya fara mishi ciwo? me a cikin idanun ? nasan dai Hamma
Umar baida ciwon ido,
Amman ji yadda yakeyi kamar Wanda maciciji ya tsirta mishi dafi a cikin idon,
me ya samu idon ina tabbayarki kinyi shiru."
baki na rawa tace.
"Turarene a cikin idon."
gaba d'aya kusan a tare suka zare ido woje cikin tsoro sukace "turaren kuma?."
"Ehh."
ta basu amsa tana rawan murya.
jin haka Usman ya rugumoshi cikin sauri yace .
"Aliyu jeka bud'e min mota mu tafi asbitin su."
Aliyu har ya mik'e Hajjajo ta kalesu cikin sauri tace.
"Usman ajiye shi maza d'auki makullin motarka yanzu kaje laying FULANI ka seyo mana
madarar shanu wanda ba'a tafasa ba daga nan ka biya Islamic kemis ka seyo zam-zam."
cikin juya kai Usman yace.
"Hajjajo wad'an nan abubuwan me zasuyi mu tafi asibiti kar turaren nan ya kashe mai ido."
Inna ce ta kalleshi cikin k'arfin guiwa tace.
"Ajiye shi ka gudu yanzu ka seyosu."
toh yace tare da kontar da Hamma Umar d'in sannan suka fita da sauri shida Aliyu,
kai tsaye layin filoli sukaje sukayi sa'a kuwa suka samu d'anyen madarar shanun daga nan suka
seyo zam-zam sannan suka nufi gidan,
a gidan kuwa doctor Abbas yazo tun bayan fitan su Usman amman Hajjajo ta hana a sa mishi
komai,
dole Dr ya hakura yana jiran dawowan su Usman ,
su Inna da Hajjajo kam gaba d'aya basuyi tunanin ya akayi turaren ya shiga idanun shi ba,
Anty Halima kuwa tun tuni ta zargi k'anwarta bare da taga kolban turaren a tsakiyar d'akin.
Su Usman na dawowa Hajja tace,
a had'a zam-zam d'in da madarar shanu a bashi yasha ,
haka suka had'a suka bashi yasha,
a hankali ya fara jin zogin da zuciyarshi keyi yana raguwa,
sannan ta kamo hannun shi cikin sanyi tace.
"Farouq."
cikin rawan murya yace.
"Na'am."
"Alhamdulillah."
Inna tace sannan cikin jin k'arfin guiwa tace.
"Halima je kitchen nasu ki kawo roba mai d'an girma."
"Toh" tace tare da ficewa da sauri ,
tana kawowa Hajjajo ta ajiye mai robar a gaban shi sannan ta matso da koryar madarar shanun,
cikin kula tace.
"Ga madarar shanu k'asa hannun ka a ciki ka rink'a d'iba kana wonke idanun ka bud'e idon."
"Toh."
yace sannan ya sunkuya kan robar ya ciki tafin hannushi da madarar sannan ya sunkuyo da
kanshi idanun shi ya manna cikin ruwan madarar shanun sannan ya bud'e kwayar idanun a
cikin ruwan madarar,
wani irin zafi yaji ya ziyarci ruhinshi da zuciyarshi,
gaba d'aya saida ya rink'a karkarwa hannushi d'aya yasa ya kamo hannun Ummul dake
durk'ushe a gefen shi wanda shi baisan waya rik'e ba,
sannu su Hajjajo suka rink'a jera mishi ya Usman kuma yana zuba mishi madarar shanun a
haka duk wanda yasa idanun a ciki sai ruwan madarar yayi bak'i a hankali har ya fara yin ja har
ya zamo inyasa idanun a cikin ruwan madarar baya canza launi haka kuwa a take idanun nashi
sukayi fari tas, har kaman sunfi da d'in fari,
sannan aka mik'a mishi goran zam-zam ya k'ara woke idanun sai gashi sun fito ras,
Dr Abbas ne ya kalli doctor Umar Farouq cikin kula yace.
"Kana ganina kuwa?."
Murmushi Hamma Umar yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa ganina normal har kamar yafi na da."
ajiyan zuciya dr Abbas yayi tare da cewa.
"Tabbas muna da manyan likitoci a kusa ga magani mai sauk'i gaskiya nayi mamaki tsoffi sun
zama likiticin babban doctor Umar."
dariya sukayi baki d'aya sannan Hajjajo ta kallesu cikin yin k'arin bayani tace.
"Ko maciciji in ya tsirtawa mutun yawunshi a idanun haka akeyi kuma da izinin Allah mutun zaiyi
ras haka kuwa ko turaren ko wani abu mai Carmichael zakaga gubar zatabi jikin nonon."
Dariya Usman yayi cikin jin dad'i yace.
"Aiko munga zahiri."
da haka Dr Abbas ya tafi,
sukuwa parlour suka dawo suka zauna suna ta jira,
Anty Halima kuwa gaba d'aya hankalin ta na kan UMMUL da Hamma Umar ta lura sarai da
yadda Ummul ke yawan satan kallon Hamma Umar d'in shi kuwa kamar baima san da ita a
wurin ba,
hakan yasa ta k'ara zargin Ummul d'in.
Anty Halima ce ta shiga kitchen ta fara yi musu girgi,
Sai daga baya ta kira Ummul dake zaune kan dinning table ita da Aliyu suna lallatsa laptop d'in
ya Usman,
ta shiga kitchen d'in ta kalleta a fakaice tace.
"Sarauniya kece da bak'in nice da shiga kitchen ko kunya babu kin zauna kina danne-danne,
ga maggi ki b'are min,
sannan ki wonke fruits dinnan ki kaiwa su Hamma Umar d'in da su Hajjajo."
"Toh.'
tace cikin sanyi sannan ta fara b'are margin dan ta lura Anty Halima tana tuhumarta gashi sai
harara take watsa mata,
kuma ta sani in Anty Halima ta gane itace ta fesawa Hamma Umar turaren a idanun shi tohfa ta
shiga tara tasan ya Adam zaiji in kuma yaji Abban su zaiji inko sukaji shikenan sai buzunta.
tana gama b'are margin ta mik'a mata sannan ta wonke fruits d'in ta shiryasu a pilet guda biyu
sannan ta nufi parlour dasu,
tana fita Anty Halima ta jawo robar da ta sa mata magin a ciki da niyar zata sa a girkin nata,
sai taji robar tana k'amshin turare,
k'ara shinshinar robar tayi aiko k'amshin kam rasa taji shi,
kai ta jinjina tare da cewa.
" ba shakka zargina ya tabbata Ummul ce ta fesawa Hamma Umar turaren a idanun shi."
kai ta kuma juyawa tare da cewa.
"Ummul banso had'a ki da ya Adam ba amman kin jawa kanki dole in gaya mishi."
Ita kuwa Ummul a parlour tana shiga taji Hajjajo da Inna suna.
"Wai ni abin mamaki Farouq ya akayi ka fesa turaren a idanun ka? kaiba yaroba."
baiyi magana ba sai latsa woyar shi da yakeyi,
Ita kuwa Ummul gaba d'aya jikin ta ya d'auki b'ari tana jin tsoron kar Hamma Umar ya fad'i
abinda ke faruwa a tsakanin su,
Inna ce ta kuma kallon shi cikin tausayawa dan ita tasan Umar da zurfin ciki koma menene ba
fad'a zaiyi ba a hankali tace.
"Ko garin fese-fesen turaren nan shine yaje ya fesa a idanun shi,
tunda shi mutun ne ko yaushe ka jishi da turaren a jikin shi."
Usman ne ya girgiza kai cikin kula yace.
"A a kam ba yadda za'ayi ya fesawa kanshi turaren a cikin idanun shi ai ba yau ya fara
mu'amalan tuwa da turaren ba ."
ido Ummul ta kuma zarowa dan ganin kamar duk sun ganeta,
sai kallon Hamma Umar d'in take cikin yanayin ya rufamata asiri,
stool ta jawo gaban shi shida ya Usman ta ajiye musu pilet d'in fruits d'in sannan ta d'an dago
cikin rawan ido da suka ciki da k'olloh alamar ka rufamin asiri,
shi kuwa fuska ya tsuke cikin kauda idanun shi a kanta,
gaban su Hajjajo taje ta ajiye musu nasu sannan ta zauna tana fuskantar Hamma Umar d'in da
alamun neman al'farma,
Hajjajo ta kalleshi tare da cewa.
"Farouq ana maka magana kayi shiru ya akayi ka fesa turaren a idanun ka."
Kai ya juyo cikin sanyi yace.
"Ummul ce....!"
ido Ummul ta zaro woje cikin rawan jiki sai hawaye car-car a idanun ta,
Su Hajjajo kuwa suma ido suka zaro cikin kallon shi sukace Ummul ta fesema turaren?. "
Fuska ya tsuke tare da cewa.
"Ni kam bance ba kaji tsohuwa fa ki tsaya kiji me zance mana."
Usman ne ya tsura mishi ido sannan ya kalli Ummul dake ta rawan jiki ya kuma kalli Hamma
Umar d'in da yake kallon ta sai yace.
"Toh Hamma Umar muna jinka."
Tsuke fuska ya kumayi sannan yace.
"Cewa zanyi Ummul ce zata gaya muku yadda akayi na fesa turaren a idanuna."
Ummul d'in suka kallah cikin son jin zance sukace .
"Ummul garin Yaya akayi ya fesa turaren a idanun shi?."
Tsuru-tsuru tayi da ido shi kuwa kallon ta yake yana d'an murmushi yana jiran me zata ce musu,
abin mamaki sai yaga Ummul ta gyara zama ta tokk'oshe k'afafun ta ta d'auki apply ta fara ci a
hankali sannan tace.
"Hajjajo waifa yaje yayi wonka ne ya fito ya zauna gaban mirror toh sai nazo ina taje mishi
sumar kanshi ina d'an goge mishi sumar da towel,
shine shi kuma yana ta kallona ta cikin madubin ya d'auki turaren wai zai fesa a sumar kan
nashi ,
ya kuma zuba min ido ta cikin madubin a haka ya fesa turare kam cikin manyan idanun shi."
Gaba d'aya su Hajjajo kam dariya sukeyi Aliyu ma sai dariya yakeyi,
Usman kuwa anan take ya gano akwai wani abu a k'asa,
shi kuwa Hamma Umar mamaki ne ya rufeshi sosai yake kallon fuskar Ummul yana mamakin
yadda ta zame kanta a abin ta kuma maida abin da salon so
lallai mace bata kad'an,
Ita kuwa Ummul kallon shi tayi tare da d'aga mai girma d'aya sannan ta tab'e baki.
Anty Halima kuwa baki ta cije tare da juyawa ta koma kitchen d'in ta kwaso abinci ta kawo
sukayi suka sha sunata jira da dariya.
Haka suka wuni har yamma sannan suka shirya suka fito,
a harabar gidan Ummul ta kalli ya Usman d'in cikin zubda k'olloh tace.
"Ayyah ya Usman nima zan koma gida."
lumshe ido Usman yayi yana maijin wani irin yanayi a ranshi a hankali yace.
"Toh ai bani zaki tabbaya ba ki tabbaya mijin ki."
Aliyu ne yayi maza ya karb'e maganar cikin tsokana yace.
"Ba inda zakije Hajia zauna a gidan ki haka kawai ki koma gida kiyi ta takurani,
mu yanzu gidan mu ba wurin zaman ki ehe,
Allah ko Hamma Umar karka barta."
hararan shi tayi tare da kai mishi duka,
shi kuwa sai zillewa yayi ya