Showing 15001 words to 18000 words out of 142577 words

Chapter 6 - Rubutaccen Al'amari Book pdf Complete-.pdf

da Hajjajo kallon Abba sukeyi cikin jin dad'i Daddy sai murmushi yake yi ita kuwa
Hajjajo kai take ta jinjina wa,
gaba d'aya sai farin ciki ya cika zuk'atan su,
Shi kuwa Hamma Umar tunda yaji furucin da Abba yayi,
gaba d'aya yaji jikin shi na rawa gabb'an jikin shi kab kamar an sassare su,
sai zufa yaji yana ketomai tako ina ido ya d'ago ya kalli iyayen nashi sai kuma atake yaji wata

iriyar kunya mai tarin yawa ta rufeshi nauyin Abba yaji gaba d'aya ya kama shi,
cikin tsananin kunya ya sunkuyar da kanshi k'asa yatsun hannushi ya rink'a murzawa tare da
yin shiru sai bugun zuciyar shi da ya tsanan ta,
Daddy ne ya kalli shi cikin kula yace.
"Farouq kaji ta inda Allah ya kawo mana mafita ko?,
tunda dama kai tunanin ka matar da zaka aura ta kasan ce mai tausayawa Usman ta taya ka
kula dashi kar tazo ta rabaka da d'an uwanka,
kaga a sauk'ak'e ita Ummul yar uwarsa ce kuma ko yanzu tana kula dashi."
Shiru yayi bai d'ago ya kalli Daddy ba sai gyad'a mishi kai yakeyi,
haka yasa Abba ya zuba mishi ido cikin kula yace.
"Farouq."
Shiru bai amsa ba sai gyad'a kai ya kumayi alamar amsawa, shima Abba kai ya jinjina tare da
k'ara kiran shi a karo na uku yace.
"Farouq."
Jin Abban nata jerama mishi kiran yasa ya d'ago kanshi kad'an cikin raunin murya yace.
"Na'am Abba."
a hankali Abba yace.
"Farouq d'ago kanka ka kalleni."

Kai ya jinjina a hankali ya d'an kalli k'anin mahaifin nashi,
sai ya kuma yin k'asa da idanun shi,
kafad'an shi Abba ya dafa murya a tausashe yace.
"Farouq kai da banne a cikin yaran mu kowa da halinsa kowa ana fahimtar ina ya dosa amman
kai haka Allah ya halicce ka kana da zurfin ciki ba'a gane abin da kake so da abinda baka so
kuma bakin ka baya furtawa,
toh ka sani duk da haka bazan cutar da kaiba,
dan kafin ka zama maraya mu muka zama marayu kuma d'an uwanmu Abbanka shi ya zame
mana uwa da una bai regemu da komai ba yakan hak'ura da farin cikinsa dan ya sama mana
farin ciki,
haka zaisa Farouq bazan k'untata rayuwar kaba,
yadda Ummul take y'ata haka kaima d'anane jininane ni da maifinka uwa d'aya uba d'aya
Farouq ina sonka son da bana yiwa y'ay'an cikina,
Farouq ni ubane a gareka kuma aboki kuma amini kuma mashawarci,
Farouq bazan yimaka doleba sai da son ranka karkaji kunyar shaida min baka son Ummul in
har baka sonta ka gaya min ,dan bazan yimaka auren cusheba bare na dole,
ka furta min kana son Ummul? ko baka sonta?."

Kai ya rink'a jujjuyawa yana sauk'e numfashi a ranshi yake juya kalaman Abba a fili kuwa cikin
raunin murya yace.
"A,a
A,a Abba a,a ba kaina nake tunawa ba , Abba Ummul bata sona,
ko cikin yayunta ni da ban ta d'aukeni kuma gashi tana da wanda take so,
Abba me za'a cewa Mustapha? Ummul da Mustapha nake tunawa kar sanadi na a cutar dasu

hakan zaisa Ummul ta k'ara tsanata bana son na zama bak'in jakada a Rayuwar Ummul da
Mustapha."

Sai kuma yayi shiru yana murza yatsun sa tare da kamo lips d'in shi na k'asa yana d'an ciza.

Abba da Daddy kuwa ido suka zuba mishi yayin da Hajjajo kuwa gaba d'aya take kallon shi da
suffar maihaifinshi ,
Umar Faruoq shi haka Allah yayi shi baya son shiga hakk'in kowa .

Kai Abba ya jinjina sannan yace.
"Farouq amsa min tabbaya ta,
shin kana son Ummul ? ko baka sonta?."

Kai ya k'ara sunkuyar wa cikin cushewar tunani a ranshi yake tuna.
"Abba ya zanyi in kalli tsabar idanun ka nace bana son y'arka ta cikin ka?."

A zahiri kuwa kai ya girgiza murya a raunane a hankali yace.
"A,a Abba ya zanyi ink'i y'ar uwata."

Nannauyan ajiyan zuciya Abba ya dire sannan ya kalli Daddy cikin jin k'arfin guiwa da kara
yace.
"Hussaini ina nemawa d'ana Umar Faruoq auren d'iyar mu Ummul."

Murmushi Daddy yayi tare da yin hamdala yace.
"Na bada auren Ummul ga d'ana Umar Faruoq."

Hajjajo ko murmushi tayi da hamdala sannan ta sanya alkhairi a acikin abin,
shi kuwa Hamma Umar kai ya d'ago a hankali yace.
"Abba nagode Daddy Allah ya biyaku."

Da sauri Abba yace .
"A a Farouq godiya kuma a tsakanin mu ai nauyin mu ne mike sauk'e wa."

Kai ya kuma sunkuyar wa murya a raunane yace .
"Abba ya za'ayi da Mustapha? Abba me za'acewa Mustapha? Abba ya Ummul zata d'auke ni?."

Gyara zama Daddy yayi sannan a nitse yace.
"Farouq wannan magana bamu gaya maka itaba har saida mukaje muka samu iyayen
Mustapha mu kayi misu bayanin Ummul zamu bada ita ga d'an uwanta,
Alhamdulillah iyayen Mustapha masu mutun cine sun fahim cemu inda anan take suka kira
Mustapha a gaban mu akayi mishi baya ni,
tabbas Mustapha yana son Ummul kuma ita tana sonshi d'an Mustapha ya san haka d'an tunda
mahaifinshi ya mishi bayani Mustapha kuka yake tamkar yaro,

Amman kuma hakan bai hanashi ya fahimci abinda mik'e nufi ba,
d'an haka yace ,
yaji kuma ya yarda amman don Allah kar a hanashi zuwa gun Ummul tunda ba'asan
Rubutaccen AL'AMARI da zai wakana ba yace zaici gaba da neman ta in ita rebonshi ne zaka
bar mishi ita,
haka yasa yake zuwa gunta har yanzu kuma munce karya gaya mata yakuma yarda munkuma
ce ya rege kiranta da zuwa duk ya yarda."

Allah sarki Umar Faruoq mai sadaukar da farin cikin sa ga wani gaba d'aya sai yaji ya tsani
kanshi dan yanaga ya shiga hurumin wasu ya tsaga soyeyyarsu,
gaba d'aya jikin shi ya mutun a haka suka tashi taron su,
Daddy ya tashi ya koma gidan sa shi kuwa Abba yayi part d'in sa a parlour shi ya samu Nenne
tana zaune rik'e da carbi hankalin ta na kan tv tana kallon tashar sunnah tv,
zama yayi gefen ta cikin sakin fuska da halin girma ya kalleta tare da cewa.
"Khadija rege sautin tv nan akwai maganar da zamuyi."

cikin girmamawa ta rege sautin sannan ta juyo gareshi cikin nitsuwa tace.
"Fatan alkhairi."
kai ya jinjina cikin girma da isa da gidan shi ya shaida mata yadda sukayi da y'an uwanshi kab.
sannan ya d'ora da cewa.
"Kinji hukuncin da muka yanke."
shiru Nenne tayi cikin zulumin abinda zai biyo baya a hankali kamar cikin rashin fahimta tace.
"Umar ko Usman?."
cikin zuba mata ido yace
"Umar dai ba Usman ba ko kina da magana ne?."

Kai ta juya yayin da idanun ta sukayi tab da k'olloh cikin sanyi tace.
"A a me zance ba komai sai fatan Allah ya sanya alkhairi Allah yasa sanadin haka zumunci ya
k'ara k'arko."
sai kuma tayi shiru sannan tace.
"Lallai Mustapha yayi halin kirki,
sai kuma ita Ummul."

Cikin kula Abba yace.
"Ummul kam ai dole tabi umurni na."

Kai Nenne ta gyad'a tare da tarin zulumi.

Daga nan sukaci gaba da hirar yadda bikin zai kasan ce.

Shi kuwa Hamma Umar su Abba na fita ya koma kan 3 str ya konta yayi shiru tafin hannushi
yasa ya rufe fuskar sa,
gaba d'aya zuciyarshi ta cushe ta cika da tausayin Mustapha da Ummul shi kam gani yake

tabbas ba'ayi musu adalci ba,
d'aya rumtse idonshi sai ya rink'a ganin yadda Mustapha ke kallon Ummul zuwanshi na k'arshe,
Hajjajo ce ta matso shi gefen shi ta zauna a hankali tace.
"Umaruh Farouqu farin cikin ka iyayen ka ke bid'a shi yasa suka yanke wannan hukuncin da su
sama maka dad'in rayuwa,
ba k'inka sukeyi ba."

ido ya d'an bud'e sannan yace .
"Na sani basa nufin cutar dani."
daga nan kuma ya mik'e jikin a mace yace.
"sai da safe."

"Allah bamu alkhairi."

Part d'in su ya nufa yana zuwa ya samu Usman yana konce sanyi da 3qtr shi a jikin shi matso
shi yayi a hankali ya kalli B'iyayen nashi ganin yayi bacci ne yajawo blanket ya rufeshi,
sannan yayi addu'a ya shafa mishi sannan yaje yayi wonka yayi al'wala yazo suka konta..


A hankali Abba ya kammala shirye-shiryen auren Ummul da Umar hatta kayan d'akin Ummul
Abba ya had'o mata a saudia ba abin daya rege,
abin mamaki shi kam Hamma Umar daga ranan basu kuma maganar dasu Abban ba,
Abin da ke bashi mamaki kuwa hatta kayan d'akin an kaishi gidan da yake zama a damaturu
cikin gida jen ma'aikatan an shirya komai tsab ba abin da ya rege da bobu a gidan hatta kitchen
d'in an shirya komai tsab.


Ita ko Ummul duk abinda akeyi bata da labari,
shak'uwa tsakanin Hamma Umar da Usman kuwa kullum k'aruwa yake Hamma Umar sam baya
yarda ya kwana a damaturu yana tashi daga office nashi zai kama hanyar potiskum,
Ummul da Mustapha kuwa suna soyewa son ransu shima Mustapha har manta maganar su
Abba yakeyi wasu lokutan.


Yau jumma tun da safe Ummul ta tashi da ciwon cikin da mararta kad'an-kad'an,
haka yasa bata samu tayi aikin da Hamma Umar ya k'indaya mata ba,
shi kuwa Umar Faruoq tun da sassafe ya shirya tsab shida Usman tea kawai suka d'an sha
sannan suka fita a tare Usman ya nufi wurin aikin shi shima Hamma Umar ya nufi cikin
damaturu,
kasan cewar ya jumma'ace aikin ba yawa sosai.

11:00 Am kiran Adam ya shiga woyar Hamma Umar d'in,
yana d'agowa yace.

"Adam ya akayi ne?."

"Yauwa Hamma Umar dama Abba ne ya aikoni da masu gyaran labulaye yace a canza
labulayen toh munzo kuma baka gida gashi gidan a rufe."

"OK gani nan zuwa yanzu ku jirani kad'an bari in k'arisa aikin dan tare zamu koma cikin
potiskum d'in."

"Toh" yace sannan suka koma cikin mota suka zauna.

Jimawa k'adan Hamma Umar d'in ya iso ya bud'e musu gidan nashi suka shiga ,
a take su Abdul suka canza labulayen gidan kab sannan suka kimatsa komai suka shimfid'e
carpet masu lau shi da taushi gaba d'aya gidan ya d'auki k'amshin da shek'i ga k'amshin sabon
penti ga k'amshin sabbin kayan d'akin ga k'amshin kasan cewar Hamma Umar ma abocin
tsabta da k'amshin ne komai yayi ras sai shek'i da k'amshin yake zubawa, shi kam Hamma Umar yana tunanin me Abba yake shirin yi tunda yasan har yau Ummul bata
san da zancen ba haka dai ya bar abin a ranshi tunda shi bashi da yawan magana,
su Abdul na gamawa suka d'auki hanya tare da Hmma Umar..


Suna zuwa gida sallan jumma'a suka tafi,
Bayan an taso masallacin ne Dr Umar ya wuce chemist d'in shi,
Abba kuwa da sauran gida suka dawo,
Itako Ummul zuwa yanzu ciwon cikin ta ya fara tsananta,
tana zaune a parlour Nenne tana d'an juya kai Aliyu ya shigo parlour kallon ta yayi cikin kula
yace.
"Sannu Anty Ummul ko inje in kira Hamma Umar ne?."
a d'an wahalce ta harareshi tace.
"Barni in mutun."
Dariyan tsokana yayi sannan yace.
"Kije Abba na kiran ki."

Da sauri ta d'an zaro ido gami da dafe k'irji cikin tsoro tace.
"Ni? da gaske Abba na kirana?."

"Ehh wallahi da gaske ne,
toh menene dan Abba ya kiraki ji yadda kike zaro ido."

"A a wallahi Aliyu Abba baya kirana ko batun makaran ta ne Nenne yake gayawa ta gaya min,
ni dai naji tsoron kiran nan nashi."

"Toh koma dai menene kije maji daga baya."
cewar Aliyu kenan.

A bak'in kofar parlour Abban ta tsaya tare da yin sallama ,
Daddy ne ya amsa tare da cewa .
"Ummul na shigo."

Kai ta sunkuyar cikin jin tsoro ta shiga a hankali can gefen Daddy ta zauna yayin da zuciyarta
ke luguje,
a hankali ta gaida su,
sannan tace.
"Abba Aliyu yace kana kirana."

Kallon ta yayi cikin k'aunar y'ar tashi a hankali yace.
'"Ehh ina kiran ki."

Sai kuma duk sukayi shiru,
can dai Abba yayi gyaran murya tare da cewa.
"Ummul ni wayene a gareki?."
Kai ta d'ago cikin k'arin firgici a hankali tace.
"Mahaifina."
Kallon ta ya kumayi sannan yace.
"A duniya bayan mahaifi yarki akwai wanda ya fini sonki?."

Baki na rawa tace.
"A,a babu."

"Na tabbatar kina da sanin cewa shariya ta bani damar zab'a mik'a majin aure ko."

"Ehh."
ta bashi amsa hawaye na bin fuskarta.

Shi kuwa gyaran murya yayi sannan yace .
"Abin da ban saniba ko zaki iya min biyeyya kan zab'in da nayi miki."

Zuwa yanzu kam ta k'asa magana sai kai take gyad'a wa tana wasa da yatsun ta.

Cikin bada umurni Abba yace.
" toh nayi miki miji,
kiyi biyeyya a kanshi ko bana raye shine mijin ki, mahaifiyata da d'an uwana sune shaida,
na bada auren ki ga d'an uwanki Umar Faruoq."

Kalaman Abba sun maida Ummul kurma sun sata wani irin razani da firgici gaba d'aya jikin ta
rawa yakeyi bugun zuciyar ta kuma kamar zai b'allo ya fito woje kunya yayi mata wani irin nauyi
cikin rawan baki tace.

"Hamma Umar Faruoq?."

Kai Abba ya gyad'a mata tare da cewa.
"Ehh shi d'in dai."

Hannu tasa cikin tsoro ta kama kanta ta bud'e baki zatayi magana Abba ya dakatar da ita cikin
tsuke fuska yace.
"Tashi ki tafi bana buk'atar jin komai daga gareni ba shawara bace umurni nane wannan."

Tanaji Abba na cewa tashi Amman ta k'asa ko d'aga yatsarta,
sai da taji ya zuba mata tsawa,
cikin firgici ta mik'e ta fita ,
tana fita kai tsaye part d'in Nenne ta ta nufa ,
tana zuwa a parlour ta samu su Ya Usman su ya Adam ya Sadik da Aliyu kai tsaye cikin
bedroom ta shige,
Usman na binta da kallon ganin yadda take a firgice.

Tana zuwa ta zauna gefen Nenne dake kan sallaya cikin wani irin yanayin ta kifa kanta kan
k'afafun Nenne cikin cushewar sauti ta saki wani irin galabaicen kuka mai cike da tausayi kuka
takeyi mai tsuma zuciyar mai sauraro kukan take da sauti,
Nenne kam tana ganin haka tasan me yasa ta kukan gaba d'aya sai zuciyarta ta cika da
tausayawa y'ar tata,
su Ya Usman kuma suna jin kukan da takeyi cikin sauri suka shigo d'akin ,
cikin tarin tausayawa Usman ya zauna gefen ta baki na rawa yace.
"Ummul meke faruwa? meya sameki? meke miki ciwon?."

Ba amsa sai kukan da takeyi,
Nenne kuwa tsuke fuska tayi cikin fad'a tace.
"Ke ni tashi a kaina tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina kukan banza bazan kiyi
magana ba."

Cikin kuka mai cushe zuciya ta d'ago kanta baki na rawa tace.
"Wayyo Allah wayyo Nenne kiji abin da Abba yace min Nenne wallahi ina son Mustapha ina
sonshi yana sona dan Allah Nenne ki bawa Abba hak'uri wallahi ina son Mustapha."

Wani irin dogon tsaki ya Adam yaja cikin buga mata tsawa yace.
"Ai Mustapha yafi miki kowa a duniya tunda har kike kuka da umurnin Abban mu,
ni wallahi kin saman na k'ara tsanar sa."

Juyowa tayi cikin kuka tace.
"Ya Adam kasan da waye Abba zai had'a ni?".
A hatsala yace.
" Na sani mana kuma yafi Mustapha da komai."

Cikin kad'uwa da bugawar zuciya Ya Usman ya kalleta tare da cewa.
"Waye za'a had'a ki dashi?."

Kuka ta saki tare da cewa.
"Ya Usman waifa Abba da Hamma Umar zai had'a ni aure."

Ido Usman ya zaro cikin wani irin yanayin yayi wani irin.....


By
*GARKUWAR FULANI*



*RUBUTACCEN AL,AMARI*

page 1⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*








*Zan abbato mutanen sokkoto su y'an kwaraine basu da tsoggoma idan kaje ka sanya fad'a
musu zasu rik'eka da kyau harda lallamah k'warai-k'warai na gane duniya mai sonka shike yi
maka hiddima masoya na na sokkoto kun gaman gata gaisheku �nakeyi domin
kuke raba gardama sokkotawa ina al'fahari daku domin baku da hassada a zuk'atan ku
shiyasa na sadaukar da wannan shafi gareku sokkotawa*

*Ha*nnushi ya tura kasan pillow dake gefen ta da niyar zai jawo laptop d'in shi daya bari a
wurin,
lalubawa yakeyi aman baiji inda laptop d'in yakeba dan d'akin yana da duhu gashi kan gadone
mai rumfa duk yasha gyara da shimfid'a da labulaye sai ya k'ara duhun,
Ita kuwa Ummul tana ganin shi dan ita ta dad'e a d'akin so duhun yabi idonta shi kuma yanzu ya
shigo d'akin shiyasa yake ganin duhun sosai,
tab'e fuska tayi cikin ko in kula tasa hannu ta turo laptop d'in nashi k'asa dai-dai sautin kan
yatsunshi ta turo shi,
shi ko da sauri ya sunkuya da nufin yasa hannu ya taro laptop d'in kar ya kai k'asa gudun karta
lalace,
amman ina cikin rashin sa'a ta fad'o kan yatsunshi tsinin aggil d'in jikin marfinta ya caki kan
farcen babbar yatsarsa,
cakar da a take farcen ya tsage lokaci d'aya jini ya fara zuba a take k'afar ta fara wani irin b'ari
dan azabar daya ratsashi gaba d'aya yatsar kuma sai motsi take kamar zata fice a jikin shi,
cikin wani irin azaba dayaji ya ziyarci k'ahon zuciyarshi ya dafe kanshi da k'arfi hannun shi sai
rawa suke gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka taso ida nunshi sukayi jazir ya kasa magana sai
harshen shi ya d'an zaro ya rink'a d'an kad'awa yana furza numfashi tuni zufa ta keto mai ta
sashoshin jikin sa, harshen yake d'an kad'awa yana fidda sautin.
"Shihhhhhhhh ahhhhshhhhhh."
Sai kuma k'afar tashi daya d'an d'ago yana yarfawa,
Ita kuwa Ummul sai murmushi mugunta ta rink'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login