ya zauna. Idan ka kallesa yadda fuskarsa take a matuƙar kame ga kuma Glass dake idanunsa ba za kayi zaton yasan da zaman wasu mutane ba a restaurant ɗin. Sai dai komai dake faruwa a daidai lokacin kuma cikin restaurant da mutanen ciki yana an kare da kowa kuma idanunsa suna a Kallon ta da kuma lura da abin da take yi tun shigowar sa Wurin.
“Sannu da ƙoƙari Fatiyya wannan kayan maƙulashe haka duk nawa ne ni ɗaya?.”
Ramla ta faɗa a lokacin da ta ɗauki pan pizza ta kai baki tana kallon Fatiyya da ta jide ma ta kayan kwalam da maƙulashen a saman table da take zaune.
Fatiyya tana dariya ta ce. “E mana ai naki ne duka ki cinye ban da wannan dan ba da shi na bada ba ke naɗai ne kawai.” 😌
Ta faɗa tana gallawa Abrad dake zaune gefe yana shafa waya harara kamar yadda ta saba. Kuma ta yi maganar ne tana ƙoƙarin kai lomar pancake a baki. Sai dai wuffff taji an wafce ko kafin ta yi wani yunƙuri ya kai baki ya gutsira tare da bin ta murmushin ƙeta yana kashe ma ta ido.
Dariya Ramla ta yi zatayi magana a daidai lokacin kuma idanunta suka yi tozali da kyakyawar fuskarsa, duk da cewa bata ga kwayar idanunsa ba amma ƙwaƙwalwarta ta iya tuno ma ta a inda ta san shi ko a ce ta taɓa ganin sa.
Ba tare da jiran komai ba ta ɗa ga masa hannu tana Murmushi dan kuwa haka kawai taji ya dace ta yi masa magana kuma ba komai ne ya bata gwarin gwiwa ba sai Murmushi da taga ya yi ma ta alamun shima ɗin ya gane ta.
Da mamakin ta sai gani ta yi ya miƙe tare da ƙari sowa wurin cikin wannan dai kamilalliyar muryar tasa ya ce.
“Zan iya zama kuwa?.”
Ta ɗa ga masa kai ba tare da ta ɗauke idanunta daga kansa ba.
“Wannan kallon fa ko dai kinayi ne domin ganin wurin da kika min rauni a wancan Ranar ya warke ne ko a'a?.”😂
Ya faɗa lokacin da ya zauna ya miƙawa Abrad Hannu suka yi misabaha.
Ramla ta ɗan saita kanta ganin ta ɗan kwafsa ta ce. “Ohmm.” Kawai sannan ta kuma cewa. “Kamar akwai sanayya tsakanin ku?.”
Ta tambaya ganin alamar kamar shi ɗin da Abrad sun san juna. Abrad ne ya bata amsa da faɗin. “E amma sanayyar ba sosai ba, ke fa a'ina kika san sa?.” Ya yi ma ta tambayar yana kallon ta, sai dai tun kafin ita ta bada amsa shi ya riga ta da faɗin. “Waya take yi alhalin tana tuƙi har ta kusa kaɗeni bata sa ni ba, shi ne dalilin haɗuwar tamu.”
“Ai kuwa dai gashi wancan Ranar mun rabu ban san naka sunan ba.”
Ramla ce ta yi maganar yanzu tana duban Fatiyya da ta dawo wurin riƙe da madaidaicin tray mai ɗauke da bottle na ruwa a kai. A je gefen sa tana faɗin. “Ai ni nayi fushi ma Yah Mahabub kwana biyu ka manta damu.”
A yarda ta yi maganar zaka fahimci cewa Akwai shaƙuwa da tafi kama dana Ƙanwa da Yayanta a tsakanin su.
Ramla ta saki baki tana dubansa shi da Fatiyya ɗin. Again ita ma Fatiyya ta san shi ke nan?. “Mahbub...” Ta maimaita sunan da ta ji Fatiyya ta faɗa tana dubansu fuska ɗauke da murmushi da yafi kama dana yaƙe.
“Sorry Ƙanwa ta kwana biyu bana a garin shi ya sa bana zuwa ya kike yasu Umma fatan ana samun customers sosai sosai?.”
Ya faɗa yana shafa kanta. “Ai duk muna Lafiya, fatan kaima ka dawo lafiya?.”
Cewar Fatiyya. “Alhamdulillah Ƙanwa ta amma fa ya kamata ki yiwa Auntyn ki bayani na kinga yadda take binki da kallon tuhuma.”😃
Ya faɗa yana buɗe bottle na ruwan da ta kawo masa dama haka suka saba tun wasu watanni baya yake zuwa restaurant ɗin idan ya zo sai dai ya sha ruwa kawai kuma ya biya kuɗi kamar wanda yaci wani abun, tun basa amsa har dai suka saba da zarar yazo ma sun san mene ne yake buƙata, ruwa kawai sai dai ya yi ta danna waya idan ya gama ya a je kuɗi ya tafi ana hakan har Fatiyya da ta kasance mai saurin sabo da mutane yawan sakin fuskar da yake da shi ga kowa ya sa suka saba yake kiranta da ƙanwarsa ita kuma ta kirasa da Yah Mahabub.
“Ai Bama sai tayimin bayani ba, na gane komai wato dai mai siya da siyarwa ne a ka sama shaƙuwa tsakani.”
“Ai kuwa kin cinka daidai.”
Cewar Fatiyya tana dariya.....
___
*Irshad POV.*
Kamar yadda ya tsara washe gari ƙarfe sha biyu na Rana a Katsina ta yi masa, sai dai yaje a rashin Sa'a tare da samun mummunar labarin da ya Girgiza tunaninsa na cewar wannan gidan marayun ya daɗe da rushewa kuma bayan hakan abubuwa da dama sun faru a taƙaice ma su marayun dake a gidan duk basa nan kowa ya kama kansa. Duk da cewa ya san za'a rina domin tsawon shekaru huɗu ke nan amma bai yi tunanin wannan labari zai samu ba. Hakan bai masa Bama sai da ya bincika iya yadda zai iya a kan ko zai sama bayani na wurin da a ka mayar da marayun, amma bai sami komai ba, gashi abin haushi ko pictures nasu bashi dashi duk ya bar su a gida balle ace za'a iya gane inda suke ta hanyar pictures ɗin. Jiki ba gwari ya dawo Abuja duk ya shiga damuwa da takaicin kansa na watsar dasu tsawon lokaci da ya yi bai tashi tunawa da su ba sai yanzu gashi bai san ma ta inda zai fara da neman su ba, Burin sa bai wuce a ce suna raye ba. Haka dai wannan Ranar ta kasance masa duk babu walwala. Washe gari ma haka ya tashi gajiyar jiya bata sake sa ba.
*10:56 na safe.*
Ya shiga Palon Aunty da ta sama sallama tun jiya da Yamma a ka dawo da ita gida kuma ta warware tas dama damuwa ce silar summa da ta yi.
Tana tsaye ne ta ɗan durƙusa kaɗan tana sakama junior takalmi ta ɗa go tare da dubansa tana amsa sallamar nasa. Yayin da ya ƙari sa shiga ya zauna saman Sofa. Bayan sun gaisa Aunty ta dubesa cike da kulawa ganin idanunsa sun yi jajur alamar bacci bai ishesa ba ta ce.
“Pooh kana lafiya kuwa an ya zaka iya zuwa Mining Company ɗin kuwa naga kamar bakajin daɗi ko dai na kira Dr ya duba ka?.”
Kallon ta yake yana ɗan lumshe ido, a har kullum yana Alfahari da kasancewar sa mata a wurin Mahaifin sa kuma mai nuna kulawa a garesa sam bata gajiya da hidima da shi, kuma duk da cewa ba zata haifesa ba amma a matsayin ɗa ta ɗauke sa kuma yana girmama ta bisa ƙaunar da take masa. Ya ɗan Girgiza kai.
“Nope it's okay, ba sai yazo ba...”
Ya faɗa yana kuma lumshe ido daga ƙarshe ma ya ɓige da kwanciya saman doguwar kujerar.
Aunty ta dubesa tana faɗin. “Tohm shikenan tun da kace hakan amma dai fita Company sai dai idan ka warware.”
Ta faɗa bawai dan ta fasa kiran Dr ɗin ba, a yadda taga yanayin sa tasan daurewa kawai yake yi kasancewar sa mutum mai zurfin ciki...
__
*Umnia POV.*
*11:55 na safe.*
Bata jin daɗi amma haka take daurewa kuma ta taho Headquarter kafin ta ƙari so sai da ta biya ta duba jikin Safiyya Aunty sannan ta taho. Yanzu ma tana zaune ne a office ɗin ta, ta kuma ɗa go kanta ta dubi Budurwar dake zaune cikin office ɗin da ta zo wai a kan mutuwar mahaifin ta commissioner domin jin yadda binciken yake wakana. Wannan ne karo na farko da wani daga Ahalin commissioner ya zo musu a kan maganar binciken mutuwar saboda haka sauke ajiyar zuciya ta yi, tare da faɗin. “Har yanzu muna iyakar bakin ƙoƙarin mu a kan binciken kuma muna dab da kama mai laifin a hannu ku bimu da fatan Nasara kawai.”
Ƙarishe maganar nata ya yi daidai da shigowar kira a wayar Tamannah dake zaune tana sauraren ta hakan ya sa bata gama jin abin da take faɗa ba. Ta ɗa ga wayar tana sauraren Mulaika da ta kirata gefe guda kuma tana Murmushi ta tuna abin da ta yi ma Mulaika ɗin a Birthday party da ta shirya.
“Autyn Mannah kina ina ne, jikin Mommy ya tashi yanzu haka muna asibiti kiyi sauri kizo yanzu, jini take zubar wa sosai su kansu Likitocin sun kasa gane mene ne ainihin abin da yake damunta.”
Miƙewa tsaye ta yi hankali a matuƙar tashe take faɗin. “Garin ya ya? Yanzu kuna wani Asibitin ne? Ki turomin address ɗin. I'm on my way...”
Ta ƙari sa maganar tare da katse kiran ta dubi Officer tana faɗin. “Madam zan tafi kawai Mommyna bata jin daɗi idan babu damuwa zan kiraki kawai mu ƙarishe maganar.”
Umnia ta amsa ma ta sannan ta fita sauri sauri....
🔥
*Ko wane ne Mahabub?*
*Mene ne yake faruwa da Mommyn su Tamannah?.*
*Allah Sarki our Pooh (Dimple Perfect) Dole kayi zazzaɓi na rashin ganin selfsame naka....😭*
*Gaskiya Officer ya kama ki yunƙura fa mun ƙosa musan wanene Makashin commissioner da kuma dalilin sa🌚*
*Ko mene ne zai faru gaba????.*
*KU MUJE ZUWA KAWAI SANNAN MU HAƊU A NEXT PAGE JIBI IN SHA ALLAH DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA🔥🔥🔥*
*_Helloooo..! Kwana biyu an jini shiru za'a ce wannan lafiya. Lafiyar ce ta yi ƙaranci shi ya sa kukajini Shiru. Now am back kuma in Allah ya yarda baku ƙara jina shiru. Zaku ci gaba da samun update a kai a kai sai dai ban yi alƙawarin Kullum ba, amma zan dage na dinga yi muku long idan kuna buƙatar long page naga ruwan Comments da zai tabbatar da cewa lallai kunaso._*
*A Daure a yi abin wato comment da like da Share ✊✨🔥 🙌 Domin a ƙara min gwarin gwiwa ta hanyar ci gaba da kawo muku wannan daddaɗan labari....*
# RANAR BIYAN BUKATA
# NAINARH KD NKD'S
# 07079793782
👆👆 Wannan lambar ta ita za'a sameni a halin yanzu. Domin ɗayar lambar tawa mutanen nawa what'sapp sun kuma rufe wa 🥲 sai kuma idan sun buɗe 😃 Ban da kira Dan Allah. Idan ta kama sai an yi kira dole ga wannan lambar ita ce official number tana on duty everyday (08081129487).
★¡★
Dare ya tsala, shiru kakeji ko'ina, gari shiru, a daidai wannan lokaci da dare ya raba ko wani mutum zaka samesa ne a gidansa cikin iyalan sa, yayin da daren ya kasance lokaci na huta ga wasu, wasu kuma suka mayar da shi lokaci ne da suke Kaɗaita suna ibada domin tanadar ma kansu kyakkyawar masauki Ranar gobe ƙiyama, yayin da kuma ta wani ɓangaren ba haka yake ba a wurin wasu mutanen domin sun mayar da daren lokaci ne da suke Kaɗaita su baje hajarsu tacin kasuwa na neman Duniya kota halin ƙaƙa kuma koda mene ne zai faru su dai kawai su sama Duniya a tafin hannunsu domin a ganin su ai *RANAR BIYAN BUƘATA* _Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba_ shi ya sa suke cin karansu babu babbaka basu san cewa ba, a kowani lokaci na Rayuwa mutuwa tana iya riskarsu. (Allah ya sa mu cika da imani 😭.)
A tsakiyar daren tawagar masu neman ADALCI da suka bada Rayuwar su domin ganin sun sama adalci na abin da a ka yi musu da ma wanda ake ma sauran al'umma, suka yi ma gidan Prof Bakori tsinke.
TAU! kakeji ƙarar fashewar ƙaramin bomp ɗin da ta saka jikin ƙofar, daidai lokacin kuma ƙofar ta faɗi ƙasa a tarwatse sanadiyar bomp ɗin da ya tarwatsa ta, wanda ƙarar fashewar sa ne ya yi sanadiyar tashin Prof Bakori da yake cikin Bacci a Ɗakinsa ya tashi a gigice yana zare ido sai dai kafin ya gama tantance mai ke faruwa wasu mutane dake sanye cikin baƙaƙen kaya da suka fi kama da na patrol suka shigo Ɗakin fuskokinsu a rufe gaba ɗaya. Jikinsa ne ya ɗauki rawa sanadin hancin bindigar da ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ya ɗaura masa a baki. Zare ido kawai yake babu bakin magana gefe guda yana ƙoƙarin tashin Matarsa dake Bacci hankalin ta kwance a gefe domin a ganinsa idan ma kashe sa waɗan nan mutanen masu kama da mala'ikun ɗaukar rai suka zo suyi sai dai su tafi tare da ita don ba zata saɓu ba bingida a ruwa a ce ya mutu shi kaɗai.🤨
Wani gigitaccen mari ɗayan kakkauran mutumin ya kifa masa a gefen kuncinsa, dandanan kuwa fuskar ta kumbura abin ka da jikin hutu, tsananin zafin azaba da ya ziyarce sa ya sa shi wagale gaba ɗaya Muryar sa ya saki wata firgitacciyar ƙara da ta yi sanadin farkawar Matarsa a firgice tana karanto duk addu'ar da ta zo bakinta domin yadda taji ƙarar ta yi tunanin ‘yan fashi ne suka yo musu zuwan bazata cikin dare, ilai kuwa bata gama buɗe ido ba taci karo da mutane tsai tsaye cikin baƙaƙen kaya riƙe bindigu. Ai kuwa nan take cikinta ya yi wani irin hautsinewa tsaban tsoro da tashin hankali har gudawa taji ta kusan yi a wando.😂
Amma a hakan cikin ƙarfin hali tattaro gaba ɗaya jarumtarta ta tattara wuri guda ta buɗe Muryar ta dake a shaƙe tsaban tsoron dake cinta da kyar ta iya faɗin.
“Shshsttssimm mun shiga uku ‘yan fashi ne.”!
Ta ƙari she da kyar kuma da in’ina. Sai dai tun kafin ta ƙari sa taji an fashe da wata uwar dariya a mai firgitarwa sannan mai dariyar wacca da alama mace ce ta ce. ”Just Relax mana Mrs Bakori waɗan nan ubanin ‘yan fashi ne a gaban ku, kin gane ko?.”
Ta faɗa tana ɗan ƙara girman idanunta da suke masifar tsoratar da Mrs Bakori saboda yadda yanayin su suke dole ne ma ta tsorata balle kuma cikin dare a irin wannan lokacin sannan kuma a bazata.
Ai kuwa jiki na rawa Mrs Bakori ta amsa da cewa. “E e e Wallahi na gane ranki shi daɗe.”
Ɗauke idanunta ta yi a kan Mrs Bakori sannan ta dubi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare ta ce.
“Bubba a fito min da waɗan nan ƙana nun alhakin waje domin zamufi jin daɗin yayyanka namominsu a can...”🌚
Ta faɗa tana nufar wajen. Yayin da wannan kakkauran da ta yi ma maganar ya cika aiki ta Hanyar taso ƙeyar Prof Bakori da Matarsa har zuwa katafaren palon gidan nasa da za'a iya kiransa da aljannar Duniya domin ba ƙananun kuɗaɗe a ka narkar ba wurin tsara sa. (Kuɗaɗen Talakawa ba...🌚)
Haɗe su a ka yi da yaransu mata biyu namiji daya da shi ne babba wuri guda kamar kayan wanki kafin daga bisani ita dai wannan da kallon ta kaɗai yake firgita ‘yan hanjin Mrs Bakori ta kuma bada umarni a ka matsa da Prof Bakori gefe guda domin mission ɗin nasu a kan sa ne shi kaɗai ban da iyalansa.
Palon ya yi tsit bakajin komai sai koke koken yaran Prof Bakori da na matarsa da kuma hucin fitar numfashin tsoro. Hannayensa a ƙulle suke haka ma bakinsa domin kafin Bubba ya fito da shi sai da ya kulle masa hannaye da ƙafafu.
Ta ja kujerar da Bubba ya a je ma ta a gaban Prof Bakori tare da zama idanunta a kan sa tana masa wani irin kallo yayin da zuciyarta take shawartarta a kan kawai ta ɗirkesa da bingidar dake hannunta domin idan ta yi hakan ba laifi ba ne sai ma rage mugun iri daga doron Duniya.... Amma ta daure ta cije dan a ganinta idan ya yi wannan mutuwar da zuciyarta take shawartarta ai yaci bulus kuwa, ya kamata ya ɗanɗani tsananin azaba makamancin wanda wasu mutanen suka ɗanɗana ta dalilin sa kafin ya zo ga mutuwa mara kyawu domin ta yi alƙawarin ɗai ɗai ta rayuwarsa sai ya zama abin tausayi ta yadda mabaraci ma sai ya fisa gata. Bama shi kaɗai ba har da sauran azzalumam da lokaci shi ne zai bayyana su....🩸
“Ku su waye kuma mene ne kuke nema a wurina mene dalilin ku na zuwa gidana cikin dare kuɗi kuke so ku faɗa min nawa kuke so zan baku ni dai ku kyale Ni na rayu...”
Prof Bakori ne yake wannan maganar a galaɓaice lokacin da a ka cire abin da a ka rufe masa baki da shi. Ai kuwa a matuƙar fusace ɗaya daga cikin mutanen ta buka masa wani gigitaccen naushi a haɓa bata haƙura ba ta ƙara da harbin sa a damtse. Ai kuwa ta yi ma sa ɓarna da jini kace kace. Tsananin azaba kasa koda motsi ya yi.
“Good Job Marh Ji..”
Wacca take zaune a kujerar ta faɗa tana murmushi duk da cewa fuskarta rufe take cikin face mask haka ma sauran mutanen da suke a tare. Ta miƙe tsaye tare da ƙari sawa ta ɗan durƙusa gaban sa tana taɓe baki tare da girgiza kai ta dubesa jin abin da ya kuma faɗa.
“Wace ce ke?.”
Tambayar da ya yi, ta fito da kyar. Domin sai da ta ɗan nutsu sannan ta gane abin da ya faɗa.
“Good Question. Wato kanaso kasan wace ce ni ko?, dama nan wurin nake da muradin muzo da kai a yanzu, tabbas sanin ni wacece ba zai maka wahala ba idan kayi duba da wasu shekaru huɗu baya ina tunanin ƙaramar kwakwalwarka bata manta zunubin daka aikata ba da zalunci mafi muni da ka yi ga ƙaramar yarinya wacca batasan komai ba a rayuwar ta sai tarin ƙuruciya duk da hakan kuma tana da buri a tattare da ita, amma ka tarwatsa komai saboda son zuciya, ka lalata Rayuwar yarinya ta hanyar ƙeta alfarmarta. Dabbobin mutane irin ka bai kamata da su ci gaba da Rayuwa ba. Ina tunanin ka tuna wacece nake nufi ba. _‘SAMARA’_ ‘Yar uwata ta mutu ta dalilin ka bazan taɓa yafe maka ba a kan hakan dole ne ka biya abin ka aikata ma ta dole! dole!! Dole!!!”