x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - RANAR BIYAN BUKATA Book Complete BY Nainarh KD .txt

  • 57001 words
  • 58146 words
  • Out of 58146 words

Category: Top Hausa Novels 2025

Views 5581

17 Aug 2024
ta kai Shari'a an fafata tsakanin kwararrun lauyoyin da na waɗan da a ke ƙara da kuma lauyoyin gwamnati domin kuwa gwamnati ita ta ɗauki nauyin shari'ar kasancewar Mahbub da Samara jami'ai na gwamnati shi ya sa lamarin ya kasance hakan, Neina tana zaune gefanta kuwa ɗiyarta ce wato Mienal wacca tun a jiyan suka gano gaskiyar zancen a lokacin da Hamraz ya kira Umnia ya sanar da ita abin da yake faruwa a taƙaice dai tun a jiya Neina ta haɗu da ɗiyarta kuma suka gaskata juna sun sha kuka sosai.
Ana tsaka da shari'ar ne kuma wani abin mamaki ya ƙara faruwa ta hanyar bayyanar wata budurwa mai suna Ariana (Ina tunanin kun gane ta ba, wacce suka haɗu da Irshad a lens journey da ya tafi a sri Lanka, bayan dawowarsa kuma yake yawan tunani a kan ta! tofa ita ce wannan.)
Ariana Salis Mamman shi ne cikakken sunanta, mahaifinta Salis Mamman mai muƙamin President of Journalism, shi ne shugaban dukkanin ƴan jarida na ƙasar nan a kwanakin baya wani Babban yaron sa ya fara bincike a kan wani sanannen attajiri nan ne ya gano ainihin true color na Alhaji Umair Ubaydullah a lokacin kuma yana cikin su tsundum kuma sun gane shi ɗin ɗan jarida ne wannan ne ya sa suka yi masa mummunan kisa, sai dai basu sama hujjojin da yake a kan miyagun laifukan Alhaji Umair Ubaydullah ɗin ba domin ya riga da ya turawa shugaban sa P. Salis Mamman wannan dalilin ya sa a wani dare suka afka gidan P. Salis Mamman da yake zaune a Borno State domin asalin ɗan can ne sun sama nasarar kashe shi da matarsa sai dai ɗiyarsu Ariana ta gudu basu samu sun kasheta ba kuma sannan da waɗan nan hujjojin ta gudu.
Sai kuma gata a yau ta bayyana a kotu kuma ta miƙawa kotu waɗan nan hujjoji.
Dama a rayuwa komai ya yi farko tofa ƙarshen sa na zuwa, shi ya sa a ke so a koda yaushe mutum ya kasance cikin aikata abin da ya kasance na daidai kuma Alkhairi kuma komai mutum zai yi ya yi domin Allah ya tuna akwai Ranar hisabi.
Daga ƙarshe dai waɗan nan azzalumai an yanke musu hukuncin kisa ta Hanyar rataya yayin da shi shugaban nasu likitoci suka tabbatar da cewa yana da taɓin hankali domin dama duk mutum mai hankali ba zai aikata abin da ya yi ba, sai dai cutar ta samesa ne sakamakon abin da mahaifin sa ya aikata ta hanyar kashe mahaifiyarsa a gabansa tun daga nan ƙwaƙwalwarsa ta taɓu ga kuma abubuwan da suka biyo baya a Rayuwarsa, har yazo matakin da yake a yanzu.
Wannan dalilin ya sa kotu mai adalci ta yanke masa ɗaurin rai da rai a gidan kaso. Kuma ta raba aure dake tsakaninsa da Annabella ɗiyar Mr Aabdar Dawlah domin ita ta buƙaci hakan.
Alhamdullilah kowa ya yi farin ciki da wannan lamarin ya kasance, Aunty da yaranta sun ci gaba rayuwa mai inganci cikin ƙaunar juna yayin da Samara ta kasance Jami'ar sirri, ita kuma Officer Umnia ta yi matuƙar ƙoƙari yayin da sai da ta tabbatar da Samra wato Queen Lulu ta mu ta zama cikakkiyar Jami'ar DSS.✊
Alhamdullilah ma sha Allah bayan wani lokaci aure ya gudana tsakanin Mahbub da Samara da kuma Samra (Lulu) da Irshad.


Rayuwarsu ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da ƙaunar juna, finally mahaifiyar Irshad ta dawo gare sa kuma ta nema yafiya na sharesa da ta yi, kuma ya yafe ma ta bayan tataburza da ta ɗiba da shi, kuma asirin Mummy Abida ya tonu a wata Rana da take shirin sakama mijinta Alhaji Khalil I Khalil guba dan yaci ya mutu, a cewarta dama can saboda dukiyarsa ta auresa sai dai bata taɓa haihuwa da shi ba domin Abdallah da Abrad yaran ƴan uwansa ne suke a hannunsa, shi ya sa take ƙoƙarin kashe sa ta kwace Dukiyarsa, sai kuma gashi asiri ya tonu, ai kuwa a wurin ba tare da jiran komai ba ya rattaɓa ma ta saki har uku kuma ya fattataketa ta bar masa gida dama ƙarshen alawa ƙasa. Ta ɓangaren Ramla ma ta koma ga danginta kuma sun yi farin ciki da komawarta garesu sannan sun dangana na rashin Yazan da suka yi, sai dai ta wani ɓangaren sun ji daɗi sun kuma yi farin ciki tun da azzaluman sun sama hukuncin da ya dace dasu dama zalunci baya taɓa kafuwa na bar abada na ɗan lokaci ne dama kuma daga ƙarshen ƙarshe ko da koda yaushe ƙarshen alawa ƙasa...!



~HAPPY ENDING 👏💯~


ALHAMDULLILAH!




*To duka duka dai anan wannan labarin na RANAR BIYAN BUƘATA wanda hausawa suke cewa Rai ba'a bakin komai ba, yazo ƙarshe.*




*Ina fata gaba ɗaya zamu ɗauki darussan dake ciki sannan mu watsar da mummunan abubuwan da ke ciki, Labarin gaba ɗaya ya ginu ne a kan fansa da kuma neman adalci, sannan kuma da zalunci, kamar dai yadda mahaifin Jaish ya kashe mahaifiyar Jaish ɗin a gaban idanun Jaish ɗin baya da haka kuma matar daya ƙara aura wato Clara ita kuma take gana masa nata salon azabtar war ta hanyar yi masa barazana da wuƙa a kan kawai sai ya kira ta da Mama alhalin saboda a aureta a ka kashe mahaifiyarsa a gaban idon sa ku duba fa, baya da hakan suka ci gaba da yin abubuwan da basu dace ba a gabansa da haka ya yi sanadiyar taɓa ƙwaƙwalwarsa har a ka wayi gari ya kashe su, daga nan kuma mai makon abin ya tsaya iya nan, a'a sai a ka sama a kasi shima Uncle ɗin nasa ba mutum ne mai tsoron Allah ba ya yi amfani da wannan damar ta hanyar mayar da Jaish ɗin ƙasurgumin ɗan ta'adda, kuma abin da zai ƙara baku mamakin shi ne bai fa haɗa Jaish da iyalansa ba duk da cewa Jaish ɗin tamkar ɗa yake a wurinsa. Ta ɓangaren su Lulu ma maraici da kuma fyaɗe da a ka yi ma mahaifiyar su har ta haifesu shi ne abin da ya jefa Rayuwarsu gaba ɗaya a garari har ita ma Samara Prof Bakori ya sama Nasara a kan ta.


Allah ya sa mu amfana da abin da Labarin yake tafe da shi, Allah kuma ya haɗa mu A littafina mai zuwa nan bada jimawa ba mai suna *BA TABBAS.* Ina fata zaku ci gaba da bibiyar alƙamina. Nainarh KD Nkd's.✍️




Salma Ahmad Isah ba zan manta dake ba Tawan ina miƙo gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gareki.🍬💯💘






# RANAR BIYAN BUƘATA
Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba
END
BY
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
# Nainarh KD Nkd's
Thu, Aug, 1, 2024!
Proudly.💪✍️