x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - RANAR BIYAN BUKATA Book Complete BY Nainarh KD .txt

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 58146 words

Category: Top Hausa Novels 2025

Views 5582

17 Aug 2024
lokacin ne ya fara haɗuwa da Ramla kuma wani abu da a ke kira da Love at first sight ya faru da shi a game da ita, kasancewar sa Ɗan gayu wayayye kuma mai tarin ilimin boko da addini, bai bar abin a ransa ba ya sama manya da maganar. Kuma a lokacin ne yake sanin ainihin labarin ta da irin uƙubar rayuwar da take fuskanta a gidan su wurin Kishiyar Mamanta. Bayan samun labarin hakan sai yaji cewa ma a lokacin ya kamata ya mallake ta matsayin mata ko dan ceto ta daga hannun waccan muguwar mata, duk da cewa tana da ƙarancin shekaru amma haka ya dage yaji ya gani sai ita, to koda a ka sameta da zancen kuma a ka shirya musu haɗuwa domin fahimtar juna bata ja zancen ba, ta amince da shi domin kuwa Yazan Gwani ne ya haɗu ta ko'ina ta yadda tsantsar kyansa kan sa ya sace zuciyar mace lokaci guda ba tare da ta an kare ba...😍






Kowa ya yi farin ciki da kasancewar wannan lamarin, ai kuwa nan da nan ba tare da wani jinkiri ko ɓata lokaci ba, a ka tsayar da Ranar auren nasu kuma manya suka yanke hukunci a kan cewa bayan auren Yazan zai sakata a makaranta ta ci gaba da karatunta da Bahbah Rihane ta tsayar ma ta da shi tun tana S.s 2 a secondary school. A Lagos can inda yake aiki za su zauna.


A lokacin da Bahbah Rihane taji wannan labarin na auren Ramla da Yazan hankalin ta idan ya kai birnin sin to ya tashi a gigice, domin kuwa ɗiyarta Zahra take ma kwaɗayin ta samesa kasancewar sa daban da sauran samarin Dangi duk ya fisu kyan, dukiyar, daɗi da ƙari gashi kuma ma'aikacin gwamnati da yake samun albashi mai kwaɓi. Duk da cewar Bahbah Rihane ta san da wuya Zahra ta aminta da auren Yazan ganin cewa Ramla yake so domin Zahra ita babu ruwanta sam batayo hali irin na uwanta ba. Amma haka Bahbah Rihane ta yi tsallen Albarka ta ce ita sam bata yarda da wannan Aure ba. Abin dariya fa domin fa ƙananun Malaman nata da ta saba bi suna ma ta aiki a wannan karon abin bai yi aiki sam, domin har kusan sakin ta Mahaifin Ramla wato Malam Yahyah ya yi lokacin da ta tashi bala'i a kan sai dai a fasa auren da Ramla a ɗaura da Zahra. Ta yi matuƙar gigituwa ganin a karo na farko da mijinta Malam Yahyah ya yi musu da umarnin ta. Amma duk da hakan bata karaya ba, domin ita ce ta shiga nan ta shiga can duk dan ganin wannan Aure bai yiwu ba.


Sai dai ƙudirar Allah ne wannan auren domin kuwa duk Malaman nata sun kasa kataɓus. Haka nan tanaji tana gani lokacin da a ka sama ma auren yake ta ƙaratowa kuma ana ta shirya shirye babu kama hannun yaro. Tuni Dangin Mahaifin Ramla sun ɗauke ta sun mayar da ita can hannunsu suna gyara ɗiyarsu ciki da waje domin ba'a san ina ne inda dangin mahaifiyarta suke ba, tun lokacin da ta aura mahaifin Ramla suka gujeta don ba'a son ransu ta aura matsicyaci ba a matsayin ta na ‘yar masu sa arziƙi.
Babu yadda Bahbah Rihane ta iya da nufar Ubangiji domin tana ji tana gani har Allah ya kawo yau da take Talata a ka ɗaura auren Yazan da Ramla bisa sadaki mafi daraja. Ai kuwa a yau ɗin kamar ta zauce haka take jin ta tsaban baƙin ciki da haddasa ƙarin abin takaicin nata ma shi ne yadda Zahra ta yi ma ta halin ko in kula sai ma shiga cikin ƙawayen amarya da ta yi ana damawa da ita...🤸🤣
(Hhhhh wai wai wai Ni kam wannan abu yana matuƙar ɗaure min kai fa 🤔 yadda wasu iyayen namu mata suke ɗaukar karar tsana su ɗaura a kan yaran mazajensu bawai kuma don yaran sun yi musu wani abu ba ko kuma sun tare musu wani abun 🙂 a'a kawai tsaban rashin son a zauna lafiya da kuma bak'ar zuciya, nake ganin yake kawo hakan 🤨 Dan Allah iyaye mata a daure a ja yara koda bana miji ba, a jiki domin ba'a san mene ne gaba zata haifar ba. Rayuwar tana sa tsayi 👏 kayi abin kirki ma ya ka ƙare, balle kuma na tsiya???? To Allah ya sa mu dace kuma ya bamu ikon gyarawa gaba ɗaya 🙏❤️ Nainarh ce. . . 🙌)




Ita dai amarya bata kulasu ba tanaji suka ci gaba da shaƙiyancin su suna taɓa fira har lokaci ya ɗan ja, sannan ne suka kyale ta bayan shigowar wata Babar mace a Dangin nasu da a ke ɗan shakkar ta dan babu wargi sam a tare da ita, bata san ma mene ne wasa ba, shi ya sa a ke mugu mugun shakkan ta daɗi da ƙari kuma ta kasance tana auren wani sanannen attajiri a garin Kaduna.


A Ranar da a ka ɗaura auren amarya da ango zasu bi jirgi zuwa Lagos gidan su domin kira na gaggawa da ango ya samu shi ya sa abin ya koma hakan domin da fari an tsara sai bayan ɗaura aure da kwanaki biyu sannan za'a zaɓa wasu daga cikin Iyaye da ‘yan mata na dangi su da kansu su Kaita can Lagos ɗin daga nan a ga mazaunin nasu. Amma wannan kira na gaggawa kuma mai muhimmanci da Yazan ya samu shi ya sa a ka dawo da tafiyar nasu a yau.




A lokacin da za'a tafi da ita ne a ka biya da ita wurin Bahbah Rihane domin su gana duk da cewa sun san ba son auren take ba, amma an yi ne dan a fita haƙkinta matsayin ta na mariƙiyar Ramlatu ɗin.


To koda a ka kaita a maimakon Bahbah Rihane ta yi faɗa da nasiha da jan hankali kamar yadda Iyaye na gari keyi ga ƴaƴan su, a'a ita sai ta ɓige da kawo wasu zance dai daban waɗan da basa da alaƙa ma da abin da aka kawo Ramla ɗin domin ta yi ma ta wato nasiha, haka dai a ka yi a ka tashi.
Biki ya yi albarka wuraren takwas da rabi na dare a ka yi ma amarya da ango rakiya har zuwa filin jirgi domin tafiyarsu Lagos. Haka dai a ka rabu cike da kewar juna cikin su har da masu kwalla domin kuwa gani suke kamar bankwana suke yi kamar ba zasu sake ganin su ba, jiki a sanyaye ga kowa dai haka suka gama sallamar amarya da angon ta suka shige jirgi, sai da Dangi suka ga tashin su sannan kowa ya koma gida cike da kewa....🥲








LAGOS STATE!






Wani irin rawar mazari dukkanin sassan jikin ta keyi tsaban firgici da tashin hankali da take ciki wanda ba Komai ne ya yi sanadi ba sai ƙarar harba harbe da ya cike ko'ina na gidan nasu, yasa bata san lokacin da ta dinguro ta ka ba daga saman gadon da take kuma jikinta bai dena rawa ba. Awanni biyu baya idan a ka ce ma ta zata tsinci kanta a cikin matsanancin hali na firgici da tashin hankali da take yanzu ba zata taɓa yarda ba.


Amma kuma walƙiyar ƙaddara! Ya saka yanzu gata cikin wannan mummunan hali.


Da sauri Yazan dake tsaye bakin taga yana leƙen abin da ke faruwa hankali tashe ya dawo gareta tare da rungumo ta yana bubbuga bayan ta cike da son ta kwantar da hankalin ta, duk da yasan ba abu ne mai yiwuwa ba a wannan lokacin dai musamman a gareta.


Ya saka hannunsa yana goge jinin da ta yi haɓo a hancinta sanadiyar faɗowar da ta yi.


_Awanni Biyu Baya!_


Bayan saukar jirgin su ba tare da ɓata lokaci ba drivern Yazan da already yake a airport ɗin yana jiran ƙari sowarsu, ya ɗauke su direct sai gidan Yazan dake a Victoria Island. Bayan ƙari sawarsu kasancewar a gajiye suke kuma ta ce masa yunwa takeji wannan dalilin ya sa suna isa shi da kansa ya bata abincin da tun suna hanya ya saka driver ya yi musu order, sai dai taci shima ta saka yaci dama kuma tsawon Ranar bai ci komai ba saboda hidima da jama'a. Sannan ne ya kai ta wani ɗaki ya nuna ma ta bathroom, ta shiga domin wanke baki, a lokacin da take ƙoƙarin fitowa daga bayin ne ta jiyo Muryar sa yana waya kuma kamar hankali a tashe yake sai dai bata iya jin abin da yake faɗa kasancewar da turanci yake maganar ita kuma ba sosai takejin turanci ba, shi ya sa bata gane komai ba, amma hankalin ta ya ɗan tashi fahimtar shima nashi hankalin a tashe yake, sai dai koda ta fito bata nuna masa komai ba, shima kuma kasancewar baya cikin nutsuwa bai kula da yanayin ta ba.


Ta ƙari sa bakin gado tare da zama kaɗan tana dubansa da ɗan murmushi ba tare da ta ce komai ba.


Shima ɗan murmushi ya yi ma ta ya ce.


“Amaryata!.”


Ta rufe fuska tana dariya, da hakan ya saka shi darawa shima.


“Ki bari kawai wato kunya ta a ke ji, ai ba komai very soon zan cire kunyar gaba ɗaya.”


Bata buɗe fuskar ba sai ma ƙara cusa hannayenta da ta yi tana rufe fuskar.


“Kwanta ki huta kinji abar ƙauna.”




“To Kaifa?.”


Ta tambaya cikin zazzaƙar muryarta.


“Nima ina kammala abin da nake yi zan zo na kwanta.”


Ya bata amsa. Ta turɓune fuska. “Ni dai zan jira ka.”
Ta faɗa cikin shagwaɓar da batasan ta iya ba, don kuwa a ganinta muddun ta kwanta ta yi bacci, tofa wani abu zai faru da shi, ita kuma ta gummace koma mene ne ya samesu su biyun.


“Banason gardama Abar ƙauna, ki kwanta kawai.”


Ya faɗa in serious daga zaunen da yake saman wani dogon stool laptop saman laps nasa.


Kwanciyar ta yi badan ranta ya so ba, sai dan fahimtar kamar dai ransa ne ya ɓaci, ita kuma bataso ta yi abin da zai ɓata masa rai ba.


Ya yi murmushi kaɗan yana rayawa a ransa yana kammala abin da yake yi zai je ya lallaɓa ‘yar kayansa.


Ya ci gaba da abin da yake yi ita kuma tana daga kwancen ta zuba masa ido tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ita ɗaya sai sakin murmushi take yi. Ƙwatsam!!


Lokaci guda wani irin ƙara tare da harba harbe na bindigu ya karaɗe gidan gaba ɗaya da anguwar.


A razane ta tashi zaune daga saman gadon tana zare ido, yayin da shi kuma Yazan ya miƙe a zafafe tare da ƙari sawa bakin taga na Ɗakin yana leƙen mutanen da suka shigo gidan da muggan makamai, kuma wurin sa suka zo.


_Now!_


Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da a ka harba ƙofar sannan a ka buɗe tare da shigowa. Wasu kalan baƙaƙen samudawan maza ne ɗauke gaggan makamai, wurin su shida suka yi ma Ɗakin ƙawanya. Kafin daga bisani wasu manyan mutane alhazzai masu sanye da babban riga su biyu sai kuma wani mai sanye cikin coat da wando suka shigo suma da alama sune shugabannin waɗan nan masu kama da samu dawan.




Wani irin rumtse ido Yazan ya yi yana duban mutanen ransa a matuƙar ɓace domin ya riga da yasan mene ne abin da ya kawo su garesa a daidai lokacin, sai dai kuma shi ya yi imani da ko kashe sa zasu yi tofa sai dai su kashe dan ba zai basu abin da suka zo nema ba. (An ya kuwa Yazan ? 🤔)




“Yallaɓai Yazan Muhammad Mai gaskiya nasan kasan mu ka kuma san su waye mu sannan kasan abin da zamu iya kana kuma kasan mene ne ya kawo mu wurin ka, saboda haka Bama buƙatar ɓata lokaci ka Bamu waɗan nan takardun na hannunka da kake barazanar shigar damu ƙara saboda kana taƙama suna hannun ka, idan kuma ba haka ba ina tunanin kasan mene ne zai faru ba sai na tsaya dogon bayani ba...”


Wata iriyar kakkausar murya ce take wannan maganar ɗaya daga cikin waɗan nan mutanen su uku shi ya yi maganar lokacin da ya ƙari sa gaban Yazan dake rungume da Ramla ya ɗan durƙusa sannan ya yi maganar.




Tsananin tsoro ne da firgici a tattare da Ramla dake rungume jikinsa. Zuciyar sa na tafarfasa ya dubi tsohon da aƙalla ya ba shekaru Hamsin da biyar baya, tare da tsitta masa yawu ya ce.


“Alhaji Umair Ubaydullah na rantse da Allah mai girma sai dai idan zaku kasheni amma ba zan taɓa bada waɗan nan takardun ba, burina ayi muku hukunci daidai da abin da kuke aikata, kunyi sanadiyyar mutuwar yara ƙana na da babu ruwansu ta hanyar gina gidaje masu matuƙar tsayin da ya zarce lissafi kuma ba bisa ƙa'ida ba, Wannan dalilin ya sa ginin bai ɗauke dogon lokaci ba ya rushe kuma bayan mutane sun tare a ciki da hakan ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama, kuma baku tsaya iya nan ba ku ɗin manyan azzaluman mutane ne zaku iya aikata komai saboda cikar muradin ku tabbas lokaci ya yi da zaku girba abin da kuka daɗe kuna aikatawa, nayi alƙawarin komai nene zaku min sai dai kuyi bazan bada waɗan nan takardun ba...”


Ya ƙari sa maganar cikin zafin zuciya ba kuma tare da tsoro a tattare da shi ba.


Alhaji Umair Ubaydullah ya saki wata firgitacciyar dariya yana juya kai tare da yiwa ɗaya daga cikin baƙaƙen samudawan nan inkiya da ido.


Ai kuwa ya ƙari so wurin tare da bugawa Yazan wani abu mai kama da guduma dake hannunsa a kai, da hakan ya yi sanadiyar ɗauke war jinsa da ganinsa na wucin gadi. Ya kai hannu tare da riƙe kansa da ya fara fitar da jini. Ihu Ramla ta kurma tana kiran sunansa gunin ban tausayi ganin yana rumtse ido.


“Mr Aabdar Dawlah da alama fa wannan ɗan taurin kai ne mene ne ya kamata a yi masa?.”


Alhaji Umair Ubaydullah ya tambaya yana duban ɗayan mutumin dake sanye cikin coat da wando.


“Hhhh ka bar min komai a hannuna.”


Wanda a ka kira da Mr Aabdar Dawlah ya faɗa yana sakin wata dariya mai firgitarwa sannan ya ƙari sa wurin da Yazan ke kwance dafe da kansa. Ya fizgo Ramla dake saman ƙirjin Yazan ɗin tana kuka.


Kifa ma ta wani wawan mari ya yi tare da cizgar gashin kanta ya dubi Yazan yana faɗin.


“Ina takardun suke kokuwa sai na kashe ta.”


Ya faɗa a zafafe. Sai dai tun kafin Yazan ya yi magana. Ramla ta riga sa da faɗin.


“A'a Yayana karka basu domin koda ka basu nasan ba zasu kyale mu ba kashemu zasu yi.”


Jin abin da ta faɗa yasa Mr Aabdar Dawlah ya kuma kifa mata mari da har sai da bakinta ya fitar da jini, sannan ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta still bai dena kifa ma ta mari ba tuni ta fita hayyacinta saboda tsananin azaba.


“Ashsha Alhaji Haashir kana dai kallon abin tausayi da gaske fa ba zai bayar ba sai mun saka yara sun ƙeta ta tukunna..”


Alhaji Umair Ubaydullah ne ya faɗa hakan yana taɓe baki tare da duban ɗayan mutumin da ya kira da Alhaji Haashir. . . Sai dai tun kafin Alhaji Haashir ɗin ya kai ga yin magana. Suka tsinkayi Muryar Yazan yana faɗin.


“Ka dena! karkayi mata komai na amince zan baku takardun.”


Ya faɗa cikin zafin zuciya dana rai.


Cakk Mr Aabdar Dawlah ya dakata daga abin da yake ma Ramla tare da sakin ta ta faɗa jikin Yazan. Ta taimaka masa ya tashi da kyar tana girgiza masa kai amma haka nan ya ƙari sa wani wuri cikin Ɗakin ya buɗe locker dake wurin sannan ya ciro takardun ya miƙa wa Mr Aabdar Dawlah.


“Gashi nan na baku ku taimaka ku kyale min matata yarinya ce bata da laifin komai kuma batasan komai ba.”


Mr Aabdar Dawlah ya karɓi takardun yana ma le baki ya dubi sauran abokin neman Duniyan nasa yana wata shegiyar dariya ya miƙa musu takardun ai kuwa take a wurin suka yayyaga ta gutsire gutsire gaba ɗaya suna sakin dariyar Nasara.


Yazan ya miƙe a daddafe domin ya ƙari sa wurin Matarsa. Daidai lokacin kuma ɗaya daga cikin masu kama da samu dawan nan da Mr Aabdar Dawlah ya yi ma alama da ido a lokacin da Yazan ya juya, mutumin ya saita bindigar sa ya ɗana tare da sakin ta saitin goshin Yazan...




Tass...!
Kakeji gaba ɗaya Ɗakin lokaci guda ya amsa da ƙarar harbin. Yayin da Yazan ya zube ƙasa ko shurawa bai yi ba, idanunsa a buɗe suna zubar da kwalla kuma suna duban Ramla. Da jikinta ya ƙame ƙam fuskarta sharkar da jinin Yazan da ya fallasa a saman fuskar nata, idanunta a zazzare cikin maƙurar tashin hankali da kiɗima tun lokacin da jinin nasa ya fallatsa a fuskarta bayan an harbesa ta saki ihu tare da ƙamewa a wurin alamar ta suma a tsayen....😭😭




Gaba ɗaya suka sheƙe da dariya yayin da Mr Aabdar Dawlah yake bin Ramla da wani shegen lalataccen kallo. Bottle water da ɗaya daga cikin yaran nasu ya miƙa masa ya buɗe tare da watsa ma ta saman fuskarta sai dai ko gezau, ganin hakan ya sa ya watsa ma ta gaba ɗaya ruwan gorar mai sanyin gaske, ai kuwa ta ja dogon numfashi tare da zubewa a ƙasa badan ta kuma suma ba.


Girgiza kai kawai take yi tana duban yadda mutumin wato Mr Aabdar Dawlah yake tunkaro ta yana kuma yunƙurin cire kayan dake jikinsa amma duk da girgiza masa kan da take yi bai dena abin da yake yi ba, ganin haka ya sa ta daddage iya kar ƙarfin ta ta tashi tsaye da kyar sai dai tun kafin ta gama tsayuwar wani irin azababben zafi ya ziyarci kanta sakamakon kan bindiga da ɗaya daga cikin mazan ya buga mata. Faɗi ƙasa ta yi idanunta suna juyawa yayin da take fita a hayyacinta saboda tsananin azaba. Ta suma yafi a ƙirga tana tashi dan kanta kuma duk da hakan bai sa waɗan nan azzaluman mutane sun fasa daga abin da suka yi niyyar yi a gareta ba, tanaji tana gani bata da kataɓus ko wani dabara da zata kwaci kanta daga hannun waɗan nan azzalumai tun tana gane Duniyar da take har jinta da ganinta gaba ɗaya ya ɗauke. . . Sai farkawa ta yi ta tsinci