tsara plan nasu yadda komai zai tafi musu a daidai tsawon awanni sannan daga bisani suka sama matsaya kuma suka ware rana da lokacin da zasu aiwatar da misson ɗin nasu.
“Kamar kullum dai ina ƙara tuna muku cewar Badan komai muke wannan gwagwarmayar ba sai dai dan samun ADALCI not for revenge na abin da azzaluman suka mana. It just for Justice haka ne?.!”
Gaba ɗaya suka jinjina ma ta kai cike da gamsuwa. “Oakay ohya let go a yi abin da a ka saba.”
Ta faɗa tana buɗe musu hannayen ta daga tsayen da take gaba ɗaya suka ƙari sa tare da rungumota suna ɗan Murmushi dama sun saba tun bayan haɗuwar su da zamanto War su family guda kuma team ɗaya da suka kafa domin samarwa kansu dama al'umma musamman marasa galihu da a ke zalunta adalci duk lokacin da zasu shirya wani plan ƙa'ida ne idan suka kammala sai sun rungumeta tare da fatan Nasara ita kuma a koda yaushe cikin tuna musu cewar ba don ɗaukar fansa suke abin da suke ba, sai dan samun adalci da ya yi ƙaranci a ƙasar take yi kuma sun ji sun aminta sannan sun gamsu da hakan.
Harɗe hannayensa gaba ɗaya ya yi a ƙirji tare da zuba musu ido yana Murmushi. Murmushi ita ma Neina ta yi tana kallon sa ɗan uwanta mai ƙaunar ta da fahimtar ta a ko wani hali Bubba nata.
*WANNAN KE NAN*
*UMNIA POV.*
Zaune take a office ɗin ta kamar ko yaushe sanye cikin uniform nata na aiki hannunta riƙe da files tana dubawa tare da Nazarin su.
A hankali ta ɗan ɗa go kanta kaɗan tana duban Amelia da ta shigo office ɗin ba tare da neman izni ba kamar dai yadda ta saba. Ɗan Murmushi ta yi domin tasan abin da ya kawo ta. Bata ɗauke idanunta a kan Amelia ɗin ba ta ce.
“Amelia! Ke ce a wannan lokacin ya kike kwana biyu?.”
Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta ƙari sa gaban madaidaicin fridge dake gefe, ta buɗe tare da ɗauko Bottle na ruwa sannan ta dawo ta miƙa ma Amelia da ta zauna tana amsa ma ta da faɗin.
“Ni ce Officer ke har kya tambaya ya ya nake bayan sanin yanayin aikin nawa ko hutu bana samu balle lokacin kaina koda yake ya muka iya gaba ɗaya duk a cikin aikin al'umma ne kuma munji mun gani.”
Ta ƙari she maganar tana dariya tare da karɓar bottle na ruwan da Umnia take miƙa ma ta tana faɗin. “Thanks Dear.”
“Never Mind.”
Umnia ta faɗa tare da komawa ta zauna tana mayar da hankalinta ga Amelia ɗin da ta a je bottle na ruwan a saman desk dake gabanta bayan tasha kaɗan, tana faɗin.
“Kwana biyu bamu haɗu da shi ba, ina fata dai yana lafiya ya ya Bito fa?.”
Umnia ta ɗan rage girman idanunta tana dubanta cike da sheƙiyanci ta ce.
“Wa ke nan kike nufi?.”
Ta tambaya tana dariya. Amelia ta galla ma ta harara.
“Bana son Rashin M fa Umnia ai kin fi kowa sanin wa nake nufi Hamraz nawa mana.”
Umnia ta ɗan taɓe baki tana gimtse dariya ta ce.
“Af sorry fa na ɗan manta ne.”
“Ke kika sa ni dai, ni dai bani amsa ta yana lafiya?.”
Baya ta yi tare da jingina bayanta jikin kujerar tana faɗin. “Nima dai ban sa ni ba kam amma zaki iya zuwa ki duba, kuma ba Bito a ke cewa ba Bittu ne. Amelia har yanzu Hausar ki da sauran ta bata gama nuna ba.”
Amelia bata dena hararar Umnia ba ta lura yau tsiya takeji, ta daure ta amsa ma ta da faɗin.
“Na lura yau magana kike nema, ni kuma ba biye miki zan yi ba domin kina daf ne da zama surukata saboda haka ki ci gaba da min rashin m yadda kika ga dama zaki sa ni ne very soon.”
Ta faɗa tana Miƙewa tsaye domin ta lura ja ma ta rai kawai Umnia zata yi ba zata bata amsar da take nema ba na jin lafiyar Abin ƙaunarta, gwara kawai gobe idan zatazo aiki sai ta biya ai ba nisa ne a tsakani ba.
“Oh sorry masoyiya indai Hamraz ne kun fi kusa saboda haka yana lafiya Qlau Qlau ma, ki zauna mu ci gaba fira dama babu abin da nake yi a yanzun.”
Murmushi Kawai Amelia ta yi halin Umnia sai ita, bata tunanin banda ita da kuma Safiyya (wato twin's sister ɗin Umnia ɗin) sai Hamraz banda su da wuya a sama mai iya jure zama da Umnia domin murɗaɗɗen halin ta. Ita ma ɗin har yanzu bata gama sabawa da wasu halin na Umnia ba, duk da cewa tsawon shekaru suna tare a jami'a suka haɗu har ta kai su ga yanzu da suke aiki da Dss ita Amelia fannin na'ura ta karanta, kuma sanadin haɗuwarta da Umnia ta san Hamraz sannan har ta fara son sa tun kafin Matarsa ta rasu gashi har yanzu da ta rasu ko kyakyawan kallo bata samu daga gare sa ita kuma taƙi ta haƙura da shi, duk da cewa ba wasu shekaru ne mai yawa tsakanin ta da shi ba, she's just thirty something domin Umnia ta girme ta.
“No thanks bar shi gobe zan biya da kaina na dubasa, ki ci gaba da aikin ki da kika ga zaki iya kam, na zaƙulo makashin commissioner domin na lura D.G a zafafe yake a kan lamarin, nima komawa zan yi wurin nawa aikin ɓangaren da na fi kwarewa.”
Amelia ta faɗa tana ya mutsa Black Beauty fuskarta.
Shafa goshinta Umnia ta yi tare da mirza hannunta da hakan ya zama ma ta ɗabi'a, ta dubi Amelia da idanunta da suka yi ja tsaban rashin samun wadataccen bacci da zafafa ga aiki, ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin.
“Tohm shikenan a gai computer uwar na'ura.”
Murmushi Amelia ta yi tana girgiza kai tare da fita daga office ɗin.
Yayin da Umnia ta yi shiru tana kallon gefe guda ba tare da ta ci gaba da abin da take yi ba ƙwaƙwalwarta da bata gajiya a kan komai ta fara tariyo ma ta wasu shekaru baya wani abu da ya taɓa faruwa, lumshe ido ta yi tare da tattare gaba ɗaya nutsuwarta tana tariyo abin da ya faru.
*Flash Back...*
Tana zaune ne saman tabarma ita da Hamraz da ya kasance ɗan ƙanwar mahaifinsu da ta rasu tun a wurin haihuwarsa, da ga nan matar baban nasu Uwani ita ta ci gaba da kula da shi tare da ‘yar ta da take goyo a wancan lokacin.
Duk da cewa fira suke amma hakan bai hanata jiyo ƙarar takun Uwani ba mai kama da na samu dawan farko, tsaban ƙibanta da girman jiki. Wani irin zillon bugu tamkar zata fito waje haka Zuciyarta ke ma ta, ta miƙe da sauri tana ƙoƙarin amsar ledojin dake hannun Uwanin. Ai kuwa ta daka ma ta wani uban tsawa da gardiyan Muryarta a ɗa ge take dubanta tana faɗin. “Umnia!! Yau ni ce zan shigo tsaban gulma kike neman kwatarmin ledar hannuna saboda maita irin na uwarku da ta manne wa ubanku har ya ma ta cikin da ta haifeku ba tare da Aure ba, kuma ta tafi ta bar ku da halinta na kwaɗayi da son abin Duniya. To aradun Allah ba zata saɓu ba. Aure zan Miki na huta kuma ban ga uban da zai hanani ba domin ni ke ciyar daku ba wancan mashayin uban naku ba. Sama'ila Tantus shi zan aura Miki Gobe Goben nan zaki bar min gida ki koma can gidansa domin a Goben za'a ɗaura.”
Ta ƙari sa maganar tare da kifa ma ta lafiyayyun maruka dama da hagu tare da jifa da ita gefe tamkar kayan wanki.
Wani irin wahalallen kuka Umnia ke yi kukan da yake fitowa tun da ƙasan zuciyarta wannan wacca kalar Rayuwa ce Aure kuma nawa take kwata kwatan ta da za'a ce aure za'a ma ta kuma bada kowa ba sai Sama'ila Tantus Mutumin da kowa ya shedesa da shan giya da neman mata.
Da kyar ta samu ta tashi daga jifan da Uwani ta yi da ita, da gudu tana ɗingisawa ta ƙari sa wurin Uwani dake ƙoƙarin shiga ƙazamammen ɗakin da yake daf da rushewa. Da dukkan hannayenta ta kamo ƙafafun Uwani cikin zubar hawaye take bata haƙuri a kan ta janye maganar Auren da ta yi.
A fusace kuma cike da zalunci da mugunta Uwani ta watsar da ita gefe tare da kai ƙafa zata hamɓareta sai dai gam, taji an riƙe ƙafar da mugun ƙarfi, da sauri ta ɗa go tana duban wacca ta yi hakan.
“Safiyya!.”
Ta faɗa tana duban matashiyar budurwar dake gabanta tana fitar da huci.
A fusace Safiyya tayi wurgi da ƙafar Uwanin da har sai da ta kusa faɗi domin ƙibanta rinjayrta yake yi.
Wurgi da bokitin fenti dake hannunta ta kuma yi ba tare da damu da ragowan kunun dake ciki da ya zube a ƙasa ba sakamakon fashewar da robar ta yi. Dawowarta ke nan daga tallen kunun da take ma Uwanin a kullum takai bakin tasha.
Da gudu ta ƙari sa wurin ‘yar uwan nata tare da ɗa ga ta tsaye, tana duban Uwani da ta miƙe tana muzurai domin kuwa duk iya shegenta da muguntar ta baya aiki a kan Aunty wato Safiyya saboda zafin kai da Yarinyar take da babu mai iya tankwarata ta tankwaru har ita kanta Uwanin balle kuma mahaifin su da babu abin da yake taɓuka wa a gidan domin Uwani ita ke ciyar da gidan gaba ɗaya shi dai abin da ya sa ni shi ne kawai yadda zai sama kuɗin da zai sha giya ya yi tatul ya yi ta bacci shi ne kawai a gabansa.
Duk da cewa sai taga dama take basu abincin idan kuma bata ga dama ba sai dai su kwana da yunwa ba zata basu komai ba har da Hamraz da yake ƙaramin su domin shekaru huɗu ne tsananin sa da su Umnia ɗin.
“Wannan lalataccen kallon da kikemin da waɗan nan idanun naki kamar na kyanwa, ba shi ne zai hanani abin da nayi niyyar yi ba domin gobe Goben zan ɗaura Aure tsakanin Umnia da Sama'ila Tantus babu wanda ya isa ya hana Aikin banza kawai mtsww.!”
Ta ƙari sa maganar cike da ƙarfin hali domin ta tsargu da irin kallon da Aunty ke ma ta, ta ja tsaki tare da shigewa ɗaki tana muzurai cikin ranta kuwa tana tunanin yadda zata haɗa Aunty da sabon Bokan ta da ta yi, domin ayi ma ta kurciya ta bar gidan gaba ɗaya idan hakan ma ba zai yiwu ba a saka ma ga sha'awar maza ta tambaɗe kamar uban ta domin ta gaji da ganin su a Gidan babu abin da yake tashin hankalin ta sai tsaban kyau da suke da shi kamar Balaraba wa wannan shi ne abin da yake da ɗa hura wutar tsanarsu a Zuciyarta domin ita ‘yar ta da take ɗaya tilo gare ta, ba ta da wannan kyau da suke da shi kuma suka yi gado wurin mahaifiyar su domin taji Labarin cewar shuwa Arab ce duk da cewa bata taɓa haɗuwa da ita ba sai sau ɗaya Ranar da ta kawo wa mijinta Adamu yara mata da ba za su wuce shekaru biyar ba a duniya a matsayin yaran da ta haifa bayan ya yi ma ta ciki ba tare da Aure ba, kuma ta yi tafiyarta abin ta tun daga Ranar basu sake ganinta ba har yau dake motsi haka yaran suka taso a gidan uban nasu Adamu wanda da shi gwara babu domin babu abin da ya sa ni ko kuma ya iya sai shan giya ya yi ta bacci kamar matacce. Gidan gaba ɗaya a hannun Uwani yake ita take ciyar da su shi ya sa take Rashin mutuncin da ta ga dama babu mai taka ma ta birki. Ba ƙaramar azabar wahala yaran suka kwasa a hannunta ba tun tasowar su babu nau'in wahala da basu san da zamanta ba daga hannun Uwani kuma babu mai iya kwaɓar ta a kan abin da take yi a kan su domin har da Asiri ta haɗa wurin mallake gidan da mutanen ciki.
*Present Day....*
Ƙarar da wayar Umnia ta yi shi ne abin da ya dawo da ita hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya bayan ta yi picking call ɗin tana sauraren Muryar ‘yar uwanta nata kuma Rayuwarta da takeji kamar tana cikin damuwa. Saboda jin muryarta da yi tana sheshsheƙar kuka.
“Aunty! Mene ne yake faruwa wai? Please ki faɗa min naji Muryar ki da alama kuka kikayi ko kike yi?.”
Umnia ta faɗa tana Miƙewa tsaye hankali a ɗan tashe.
Da kyar ta samu ta saita Muryarta tare da rage sautin kukan nata sannan ta ce.
“Betterhalf Yarana! Ina nufin ina buƙatar Yarana a tare dani ba zan iya ci gaba da jurewa ba Betterhalf har yau na kasa yarda cewa Yarana sun mutu sanadin rushewar da gidan marayun da na kaisu ya yi. Betterhalf bazan taɓa yafewa kaina ba a kan Hakan...!”
Maganar take yi cikin matsanancin dauriya da kuma sheshsheƙar kukan da yake cin ranta.
Hankali tashe Umnia take faɗin.
“Calm Down other half just calm down your Mind gani nan zuwa gidan yanzu.”
Ta faɗa hakan tare da kashe wayar hankalinta a mugun tashe ba tare da ta tsaya jin abin da Auntyn zata faɗa ba, cikin sauri ta haɗe tarkacen ta tare da fitowa daga office ɗin sauri sauri ta shiga mahaya ta sauko ƙasa sannan ta ƙari sa motarta ta buɗe tare da shiga ciki ta bar Headquarter ɗin da gaggawa.
___
_Masu ƙorafi a kan cewa ba'a ci gaba*daga inda a ka tsaya a Page na gaba, sai da a taɓo wani wurin daban, abin da nakeso ku fahimta shi ne, labarin yanayin salon sa ne yazo a hakan saboda zaku ga ana yawan Flash Back kuma har yanzu ba'a tsaya a wuri guda ba a taɓo nan ne a kuma taɓo can, kuyi haƙuri da yadda yanayin Labarin yake zuwa haka salon yake ba dole ne sai an tashi a wurin da a ka gama a fejin baya ba_*
____
_(0708 521 2808.) 👈 Wannan lambar da nake bayarwa ga masu Buƙatar a yi musu Graphic Design ta sama matsala what'sapp sun rufe saboda hakan zaku iya samun mu ta wannan lambar a halin yanzu. (08081129487.)_
_____
*Kar a manta da danna sharing koda zuwa ga Group Biyar ne da kike ciki, sai kuma sharhi a kan abin da ya shige muku duhu, na gode Nkd's ce taku a har kullum. 😊🥳👑*
_MARUBUCIYAR...!_
1. SARAUNIYAR KYAU
2. ANEESERH (Innocent Girl.)
3. TSANTSAR SO
4. KIN CUCENI
5. RANAR BIYAN BUKATA. E.T.C. 😄
*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_
*-100, Herbert Macaulay Way, Garki, Abuja, Nigeria*
*IRSHAD POV.*
Tafiya yake yi cikin nutsuwa hannunsa na dama cikin aljihun Navy Denim Trouser ɗin sa, yayin da yake sanye da riga neutral armless, daidai lokacin da ya ƙari sa bakin entrance na palon ya ciro hannun tare da buɗe ƙofar ya shiga ciki da sallama ɗauke a bakinsa yana cire longwing Shoes dake ƙafafunsa. Sai dai babu kowa a palon hatta Triples ɗin Aunty domin sun tafi School shima don yau ya makara ne shi ya sa har yanzu yake a gida bai fita ba yanzu haka Breakfast ɗin nasa ya zo ci kamar yadda ya saba.
Shiru ya yi yana nazarin ya tafi ko kuwa domin ya ga alamar babu kowa a palon. Har ya juya ke nan da nufin fita ya jiyo sheshsheƙar kuka da magana ƙasa ƙasa kuma da alama Aunty ce ke yi domin muryarta ya ji, da sauri ya juya tare da nufar ɗakin da yake jiyo sheshsheƙar, daidai lokacin da ya shiga yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin ita kuma tari ya sarƙe ta wayar dake Hannunta ta faɗi yayin da jini guda guda ya fara fitowa daga bakinta da hancinta idanunta suka fara ƙafewa tarin kuma bai barta ba.
A hanzarce ya ƙari sa wurin tare da tallafota yana kiran sunanta sai dai da alama bata jinsa domin ta riga ta suma a lokacin. Abin da zai iya tabbatar wa yaji a cikin maganar da take yi shi ne kawai Yaranta da yaji ta faɗa. Sai dai halin da take ciki bai bashi damar tunanin ko wasu yaran take nufi ba.
A hanzarce hankali tashe ya saɓe ta a ƙafa ya fito da ita compound na gidan yana kwalawa Driver kira. Da sauri ya saka ta a mota bayan Driver ya buɗe, a hanzarce shima Drivern ya shiga tare da jan motar Irshad yana saba umarnin su tafi hospital dake kusa domin tana jin jiki sai a hanya Irshad ya samu ya kira Daddynsu Alhaji Khalil I Khalil sannan ya faɗa masa abin da ke faruwa ai kuwa hankali tashe shima Alhaji Khalil I.K ya baro abin da yake yi ya nufa asibitin.
*UMNIA POV.*
Tuƙin take yi amma tsaban yadda hankalinta yake a tashe sai taji kamar ma motar bata sauri duk da gudun da take yi a titi. Cikin nufar Ubangiji ta ƙari sa Gidan lafiya.
Ajiyar zuciya kawai take saukewa lokacin da ta fito daga motar ta da ta paka a tsakiyar compound na gidan, zata shiga ciki amma sai wasu daga cikin securities na gidan da suka san ta suka tsayar da ita, ɗaya daga cikinsu ne ya ce.
“Madam bata nan ba'a daɗe ba ƙaramin Oga (Irshad ke nan) ya tafi da ita zuwa asibiti bata cikin hayyacinta ina ga ma suma ta yi.”
Dafe goshi Umnia ta yi hankalinta yana da ɗa ɗugunzuma wurin tashi da kyar ta samu ta saita nutsuwarta tare da tambayar sa address na hospital ɗin.
Ya ce bai sa ni ba sai dai ya kira ƙaramin Oga ya tambaye sa.
“No need bar shi kawai zan kira sa da kaina buɗemin gate na tafi.”
Ta faɗa tana ciro Wayarta tare da nufar motarta ta shiga ciki bayan ta dannawa Irshad kira, wurin kira uku ta yi bai ɗa ga ba, sai a na huɗun ta samo ya ɗa ga nan yake faɗa ma ta asibitin da suke. Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan ta tayar da motar ta ta bar gidan direct zuwa address na asibitin da ya bata.