Showing 1 words to 3000 words out of 20506 words

Chapter 1 - Darajar Yayana Book 4 end complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt

Darajar Yayana4-01
Posted by ANaM Dorayi on 05:26 AM, 08-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Na kalle shi cikin tsananin tsoro, na dafa kirjina.
Ni Yaya? In jiwa??? Saukar mari naii dau! Sannan
yace, Ba zan iya zama dakeba kina cin
amanata.Nadafe gurin tare da gigicewa, jina ya
gushe na wasu 'yan dakiku, jin abin nake tamkar
a mafarki,ahe kuka samun dama ne. Nasa ke
dago kai na kalle shi. Yaya mece ce hujjar ka da
zakayimin wannan zargin? Ya fita, na zauna a
bakin gado ina maida numfashi, cikina yanayi min
wani irin juyi. Ya sake shigowa, a fili nake furta
'Allahumma ajirni fimusibati..... Ya hada laptop
din shi ya dube ni cikin tsawa. Zo ki ga hujjar
tawa, na san kin san komai nema ki ke ki raina
min wayo. Kai tsaye ya shiga inbox din shi, Ki
karanta, duk da na san alaye kikeyi. Duk da dishi
dishin da nake gani na zaku in karanata,da farko
an rubuta.Sunana Sulaiman kuma bana bukatar
sai na fada maka in da nake, amma zan nuna
maka abinda matarka ke ciki da wani malami a
makarantar da take koyarwa. Kila kace ya akayi
nasani? To shi ne yake ba ni labari tare da yi min
forward din duk abin da suka tattauna, kuma
shine ya bani labarin cewa kana aiki ne a Abuja
dansanda ne kai.
Ga amsar da Yaya ya ba shi. "Me yasa ka ke son
fada min?"
Sulaiman. "Sabida tausayinka,sannan ina fatan
yanda na taimake ka nima Allah ya kawo mai
taimakona wata rana ko ba a kan irin wannan
matsalar ba."
Aliyu: "Ina jin ka."
Sulaiman: "To bari in maka forward."Sai ga
sunana ya fito:
Sadiya Abubakar. "Ina jin ka malam, ba nisa na yi
ba,na dan tashi ne savida banason a fahimci ina
tare da kai"
Malam: O.k, to me labari? Ina fata dai za ki shigo
gobe don na matsu inga fuskar ki tana burge ni.
Sadiya ina son ki fiye da matata dan kin fi ta
komai,wai ba za ki iya hada mana wata dabara
ba da za mu je wani guri mu kwana ba?
Sadiya Abubakar. Ba zai yiwu ba malam saboda
ciki,amma ka jira in haihu,ni kaina da a ce tuni
na same ka ba zan aure wannan mijin
nawaba,wanda da shi gara babu,kullum ba ya
gida,ga shi ya kara aure.
Malam. Hahhaha! Ki yi min irin wannan kunshin
da ki ke yi, kwanan nan zan sa a kara miki
matsayi a makarantar nan.
Sadiya Abubakar, turo min hoton sharabarki don
tana burge ni.
Ya kara yin sama kadan sai ga hoton sharaba an
turo. Gashi masoyina. Sulaiman. Kai! Ina jin dadin
kallonta,ina son yadda ki ke min shagwaba,in
muna tare,ina son hannuwanki masu laushi.
Sadiya Abubakar. Da gaske masoyina? Nagode,
zamu hadu anjima ina fata yau za ka yi min hira
cikin dare,zan sauka yanzun don yarana sun
dawo daga makaranta.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Jikina ya jike sharkaf da gumi,haka
fuskata,hawaye da majina sun gauraya, na dago
na kalle shi. 'Yaya ka yarda,wallahi ban san
komai kan wannan abin ba, hasali ma ni nawa
account din ba da sunana na bude shi ba.Ya
daka min tsawa, 'Ke rufe min baki! Wannan ba
sunan ki ba ne? Na ce, sunana ne. Ya ce, To,
inbox din ki ne fa,ko kina zaton wani yana shiga
inbox din wani? Na ce ni ban sani ba abin da na
sani kawai ba ni da wata masaniya kan wannan.
Ya ce, 'O.k, za ki ci gaba da raina min wayo
kenan? Ga shi nan kun yi labari a kaina kun
tattauna sirrin gidana, Allah Ya Isa Sadiya, ina so
ki sani zaman mu ya kare da ke. Na ce, 'Haba
Aliyu ka yi bincike mana? Jikina ya soma bari.
Yace, Abin daba zahiri ake yiwa bincike. Ya nufo
durowa ya yage takarda ya dauko biro daga
aljihun gaban rigarsa. Da karfi na furta. Yaya
Aliyu kada ka sake ni ba'a son sakin mace mai
ciki!!! Ban san cewa na rike hannunsa ba,sai da
na ji ya fincike ya miko min takardar,ban karba
ba sai dai idanuna sun haskomin in da ya ce
'SAKI DAYA. Na daga idanuna na kalle shi,sai na
ga yana dusashe min,ina kallon bakinshi yana
motsi,amma bana jin ,me yake fada,sai kuma na
ga ya soma juya min da shi da dakin a hankali
duhu ya mamaye idanuna sunfara dushi-
dishi,haka nan dana farka da dishi dishin na
farka,ban fahimci komaiba ban tuna komai ba
har tsawan dakiki.sannan naga Iya tsaye bakinta
na motsi,amma banajin me take fada.A sannu na
fahmci ina asibiti ne,sabida shigowar likita da
kuma ma'aikaciyar jinya(nurse)mai fararen
kaya,likitan ya dafa iya yana min magana da karfi
kinsan wannan?na kalli Iya,sannan na daga kaina
nace eh yace wacece? Dakyar na daga lebunana
nace mamana,ta kallon bkina ya gane abinda na
fada,naji yce Alhmdullh ta farfado yanda ya
kamata zata warware a hankali,kwatsam na tuna
cewar inada ciki nan take na soma tuna
komai,gaske ne yaya ya sakeni?na kai hannuna
na shafa cikina sainaji wayam,na yunkura zan
tashi sai naji Iya takamani ta maida ni nace iya
nayi 6ari ne?tace a'a kin haihu ne sai dai dan bai
cika taraba.
Nace y mutu? Tace a'a,yana can garinsu sun sa
shi a kwalba.
Na lumshe ido a fili na furta cewa,shikenan nayi
IDDA.
Wasu zafafan hawaye suka soma zubomin.
Iya tace Sadiya me kikace?
Na bude idanuna nima ina kallonta,take kuma
naji dan karfi na ciji le6e nace,iya ai in mace mai
ciki ta haihu tayi IDDA ko?Ta sake tattaro
hankalinta gareni,in an sake ta ba?me ya kawo
wannan tunani cikin kwakwalwarki?ta yunkura.
Bari in kira likinta nan ina zaton har yanxu b ki
dawo cikin hayyacinki ba Gam!nariketa iya! Ina
cikin hayyacina,na soma kuka,yanxu ni ba matar
shi b ce salati naji Iyar ta saka,sannan ta sake
tambayata,saki kuma sadiya?na kama
hannunta,kiyimin addu'a in cinye wannan
jarabawar.shiru tayi ta kasa magana sallamar shi
ce tasani lumshe ido,sam bana son ganinsa kojin
muryarsa.Iya ta subule hannunta daga nawa ta
fita,kuma cikin fushi,sanan taki ansa sannu da
yayan keyi mata.yabita da kallo har ta fita,y iso
kaina,na bude ido na kalleshi,kallon tsana,fuskar
shi babu alamar nadama yace.
Daga ganin yanda Iya ta fita rai a bace,nasan kin
fada matane,banso kikayi saurin fada ba,sabida
in rufa miki asiri,kamar yanda kikayimin.
Duk da halin da nake ciki ban san lokacin dana
tashi zaune ba,cikin kuka nace Aliyu bana bukatar
rufin asirinka,domin in kaji mutm yana neman
rufin asiri bashida gaskia,sai dai bansan mekazoyi
nan ba,tunda yanzu ba matarka bace,nayi
iddarka ka tafi banason sake ganinka,yace nasan
haka zuwa nayi in duba jikin ki matsayina na
yayanki kadai kuma uwar yarana,Nace,to
nagide,tafi yace yanxu kuwa,sai dai zan miki irin
halaccin da kikayimin,har abada iya bazata ta6a
jin dalilin sakin ba.nagirgiza kai,dole tasani,don ni
zan fada mata,ka tafi bana son ganinka,ka tafi,na
jefeshi da filo,Iya ta shigo,Gadanga fita daga nan!
ya juya ya fita.tazo ta kamani ina kuka ta
rungumeni a jikinta tana lallashina tana bni baki
har na hakura nayi shuru.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwana na 2 na dan murmure mutane suna ta
zuwa dubani,sunayimin barka,amma kishiyata da
yarana shuru bare yaya.tsakanin da da mahaifi
sai Allah,zuciyita tana can gurin yan yarana dana
tuno su sai inji hawaye yana bin kumatuna,Iya
tayi ta lallashjna.
Sati na 1 aka sallameni,Usman ne ke tsaye gurin
kula dani da biyan kudin Asibitina,sam baiyi
mana zanchenba,muma ba muyi masa ba,Anty
Abida kecemin wai yayi bakin cikin abunda Aliyu
yayine yasa shi jin kunyata.nace rayuwace kice
masa ba komai,shida yayi bai ji kunya ba sai shi?
Kai tsaye gidan Iya muka wuce,sun bani dana sun
mana gargadi banda jagwalgwalonshi.
Daran ranar Usman yazo kan batun sunan
yaro.Iya ta bamu wuri na mika masa
yaron,sannan na zauna muka gaisa,Ya dubeni
Sadiya,wallahi nauyi da kunya sun hanani in miki
jajen abinda ya faru,lokacin da Aliyu yazomin da
batun nan wallahi karkiga tashn hankalin dana
shiga,na tabbata an hado sharri ne don kawai a
tarwatsaku,hawaye suka soma kwaranya daga
idanuwana,na soma magana cikin kuka,
Yaya Usman wallahi bansan komai akan abinda
Abban Kausar yazo min dashi ba,sannan yaki
tsayawa ya fahmci hakan.A tunanina yafi kowa
sanin wacece ni,kuskurena 1 daya ce in rufe
account dina sai ban rufe ba,wannan kuma
mantawa nayi don ina ta kaina bana hawa.
Yace,kiyi hakuri ki dauki abin amatsayin
jarabta,Allah ya baki lafia,sannan ya raya miki
yaronki.wane suna za'ayimasa huduba dashi?
nace,ni bani da za6i a sa masa duk wanda
yakansance rabonsa.
Usman yayiwa yaro huduba da Abubakar,nace
sunan babana?yace rabon shine,Iya ta fito daga
uwar daki dama tanajinmu tace Allah yaraya
Abubakar Saddiku mukace amen. Ta
zauna,sannan tace,Usman abinda Gadanga yayi
sam bai kyauta ba,ba'a ta6a 6atamin rai b kamar
wannan tunda nazo dunia,Sadiyar ce bai sani ba?
in ya gaji da zama da ita sai yayi mata sharri?
abin da batayi da kuriciyartaba shine zatayi
yanxu wai tana bin wani Malami? Murya iya ta
soma rawa.Allah zai saka mata insha
Allahu.Usmn yace kiyi hakuri Iya,rashn bincike ne
kar kiyi masa baki.da sannun gaskia zatayi
halinta,nikaina baram baram muka rabu
dashi.ina kalln kiranshi dazu ban daukaba,
saboda ina son ya san cewa yayi laifi.nafada
masa in an bincika za'a gano duk wanda ya
shirya wannan sharrin sannu a hankali,mudake
aiki da internent muka san computer mun san
ana yin irin wannan sharri sai wani can ya bude
account din mutm ya kwace yayita aikata sharri
ko batsa ko kuma hotunan banza yayita turawa
da sunan mai wannan account mutane kuma su
zata shne.Inatasan inyimasa bayani lokacin
amma yaki'saida y iso gida ya aikata abinda da
yasha masa kai,amma insha Allahu komai zai
wuce a koma tamkar da.nayi yar daryar takaici
tare da cewa ta6di! Insha Allahu hakana bar
auren yaya.Iya tace insha Allahu kuwa,nidai
dama na guji hakan,amma ganin sun zauna lafiya
harda yan yaransu sai na saki jikina,ashe yace
tsiyar tana gaba,Usmn yace insha Allahu komai
ya wuce,yaba Iya yaron yamike tare da cewa
yana zuwa.jim kadan y dawo da manyan ledoji
dauke da kayan shayi zuwa su pampers.nace
yaya Usman dan Allah kabar dawainiyarnan dani
haka,yace haba dai ina abinyake?mukayi gidiya
tare da cewa ya gaida Anty Abida da yara,yace
zasuji.
Washegari da safe wayar Iya na kar6a na kira
Anty Abida nace mata kayan sawa na dana Baby
za'a kwaso min a gidan Yay Aly.iya tace ai ba
kayan sawa ba anjima zan nemi mota komai naki
za'a kwasomin tas.
Haka kuwa ranar a ka kwaso gadona da kujeru
dake falo tare da kayan kicin dina,iya da kanta
taje gidan.Mujidat sunata shewa da wadannan
yaren nasu,ta shigo da yaran makota da Anty
Abida suka kwashe.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nace iya kingasu kausar tace a'a suna
makaranta.
Nasoma kuka,gaskia Iya zan kar6o yarana,wallahi
Mujidat bazata iya rikeminsu ba,Iya tce Sadiya!
nasan cewa da ciwo inaso ki danne ki kau da
kai,musawa Gadanga ido nace shikenan.
Cikin 'yan kwanaki duk na rame na kade ba na
iya cin abinci sai Iya ta matsa min da fada,sabida
tunanin yarana ina son in gansu. Wata rana Aisha
ta zo min yini, na ce don Allah ta je ta dubo min
yarana,amma tana zuwa gidan an datse shi da
kwado,cikin kuka na kira Yaya Usman ina
tambayar shi ina yaya ya kai min yara? Ya ce
Sadiya ki yi hakuri ya kwashe iyalan shi sun koma
Abuja. Na lura baniba hatta Iya ranta ya baci,
tace wato ban isa ma yace min zai bar garin
ba,shi kenan yayi in dai duniya ce ga shi ga ta
nan.
Nafi sati ina kukan yarana,sai da Iya ta saka aka
yomin rubutu wai na dangana,ni dai duk da haka
ban dangana ba.
Aliyu zaune a kan kujerar shi ta office,duk da
ayyukan da ke gabansa da kuma matukar son
aikin shi, ya kasa yin aikin. Baya ya tura kujerar
shi ya jingina da bango yana tuna tun daga
shigar sa dakin Sadiya zuwa yanda ta zube a
sume ya kwashe ta zuwa asibiti,ko da uban shi
ya mutu bai yi kukan da yayi saboda cin amanar
da Sadiya ta yi masa ba.A fili yake fadin,Sadiya
dame na rageki?meye bana miki,me yasa zakibi
wanina ina mijinki?Ya kalli saman silin,inasonki
Sadiya,saidai bazan iya zama dake ba,ya mike
tamkar an tsikare shi y nufi kofar fita,kai tsaye
gida ya nufa,kmar yanda ya zata yaran suna
zaune guri 1,Mama ta kwantar da kai a cinyar
Kausar shima Al'amin ta kafadarta yasa kanshi,ya
tsugunna gabansu.Kausar yaku ka zauna anan?
ina kayan wasanku?
Ta dubeshi da wayayyun idonta,Abba ka taimake
mu ka kaimu gurin Momy,kaga Mama kuka ta
gama yi yanzu,karya nayimata nace kaje
kawotane.
Ya rungumesu,nace kuyi hakuri zan kaiku ina
Auntynku?
Khausar ta ta6e baki,tana ciki.ya dafo fuskar
Al'amen ga mamakin shi sai yaga idon yaron biyu
yace kunci abinci?
Khausar tace a'a bama jin yunwa.yasa hannu ya
dauki Mama jikin yarinyar zafi rau ga dukkan
alamu bata da lafia. hankalinshi ya sake tashi,ya
kira Mujidat wadde ke can kwance kan gado da
yaranta tana faman yin sana'ar tata chatting da
abokanta,ta tura wayarta a kasan fiilo,sannan ta
tashi,yace yaya za'a bar yarannan?tace to ya
zanyi musu,suci abinci sunqi,na kunna musu TV
sunki,tome zanyi musu?
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace ki dauko hijabinki mukai yarinyar nan
asibiti,bada son ranta ba suka tafi,,anbata
magunguna har da allura,sannan suka
dawo.ranar dakinshi yayiwa yaran
masauki,Mujidat anyo kwallia anzo dakin miji sai
ta tarar da yaran kwance kan gadonsa,ya tasa su
ya zabga tagumi,turus ta tsaya,Anan zasu kwana?
ba tare da yadubetaba yace eh.tsaki taja sannan
ta juya zuwa dakinta,Wannan ta zamar mata
baka,kuma tsanar yaran ta ninku a ranta,tana
murna ta kashe maciji ashe bata sare kanba,dole
ne tayi wani abu akan yaran nan,shikuma sam
bai runtsaba yatasa yaran yana kallonsu hawaye
na bin kumatunsa,bai san ko na mene neba
hawayen,na tausayin yaran ne ko na bakin cikin
da uwarsu ta kunsa masa?ckin haka Mama ta
farka,Momy kawai take kira,hankalin shi ya sake
tashi,zafin jikinta na nan,ya bata magani yasata a
kafada,Kausar ma tatashi ta zauna tsakiyar gado
tana kallonsu,itama kukan take amma na
zuci,dakyar Mama tayi barci,sannan yaje kusa da
Kausar ya dafata,'Yata kiyi hakuri kar karkiga
laifina,mamanku ce ta jawo hakan,Khausar tace
metayimaka Abba?intayi maka laifi ne Abba ka
yafe mata,kaji?yaushe zaka kaimu,Anty bata
sonmu Abba,yarungumeta,kiyi shuru zan kai ku
kinji,amma sai kunyi hakuri kun dan kara kwana
2 kinji?Haka yayita lallashinta har tayi bacci.
Hudu daidai aka bukaceshi wurin aikinshi,
sakamakon yan fashi da suka shiga wani
gida,dole y fice zuciyar shi cike da tunanin
yaran.Mujidat kuwa yana fita ta koma gurin dan
ta tare da cewa babu wanda zai hanani
bacci,tanajin lokacin da Mama ta tashi,tana ta
kuka amma matar nan taki fitowa,Khausar ta
farka taje ta dora kan Mama a kan cinyarta dan
bazata iya daukar taba tana ta jijjiga ta tana cewa
yi shiru Mama zan kira miki Momy,in kira miki
ita?tayi shuru.
Al'amin ma ya tashi ya zauna,kashi da fitsari
mama tayi,Khausar ta rasa yanda zata yi gashi
jikin Mama y saki,ba zata iya daukarta ba,haka
suka tasata suna kuka,har gari ya waye.Khausar
ta je dakin Mujidat ta same ta tayiwa danta
wanka tana bashi madara,ta ce, 'Anty Mama ta yi
kashi. Mujidat ta dalla mata harara, sannan ta
ce, 'To ina ruwana? Kije ki wanke mata. Khausar
ta dawo da kuka, suka ci gaba da zurawa Mama
ido.
Fitar Aliyu zuwwa takwas na safe ya kira Mujidat
sama da sau biyar yana tambayar yaran, tana
fada masa cewa suna bacci har yanzun basu
tashi ba. Badon ya kira ta cewa gashinan ba to
da zai samu yaran a yanda ya bar su, ko kuma
yanda suke. Jin cewa ga shi nan sai ta nufi dakin
da gudu ta dauki Maman zuwa bandaki inda ta
shiga wanke mata tana yi tana zagi,da ta fito sai
da ta rankwashi kan Khausar wai me yasa da ta
ji kashin ba ta kai ta bandaki ba?
Kausar din da Sadiya ke yi wa wanka yau ita ce
da yin wanka da kanta,sannan ta yi wa kannanta.
Maama tana ta rawar sanyi, Mujidat dama tun
da ta nade zanin gadon ta aje tare da cewa. In
ubanku yazo dole ya wanke ko inyardashi.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tana hada musu tea ya shigo,duk suna zaune
rakube lungun kujera, Mama tana manne jikin
Khausar, ya isa gurin ya dauke ta.Mama ya jikin?
Khausar ta soma kuka, 'Abba don Allah ka kaimu
gurin Momy, kaga Mama bata da lafiya, tayi kashi
na fadawa Anty sai ta koreni, kuma har ta
dokeni. Ya kalli Mujidat rai a bace, da sauri ta ce,
'Ta shigone ba sallama, da yake ta san tun a
gaban uwarsu in sun shigo ba sallama yana
korarsu yace suyi. Khausar tace Allah Abba nayi
sallama. Nan yashiga ruwan bala'i, ya ce itamafa
zai iya rabuwa da ita kan yaranshi, ta soma kuka
duk abin da take yi baya gani, ta aje hada Tea
din ta nufi dakinta,nan ya hada musu kawai suka
sha da kyar, sannan ya shiga gurinta. Ya ce shi
dai ya roketa ta duba masa yaranshi amma in
har son datace tanaymaasa na gaskene, tsakanin
mata da miji nan da nan ya lallabata suka shirya,
kuma tayimasa alkawarin lura da yaran.Tun daga
ranar sai ta dauki salon da mata da yawa
sukeyi,in yana nan ta nuna kulawa in baya nan
sai zagi, hantara gami da kyara. Hakan ya sa shi
sakin jikin cewa zata rikesu, har ma ya daina
yarda da korafin Khausar na cewa ta musu kaza,
ta yi musu kaza.
Cikin wannan halin ya nemi makarantar boko
yasasu, sannan ya samo musu malamin
Islamiyya,sai dai sam yaran tamkar kurame ko
sun je makarantar basa magana bare karatu,in
an tashi break sukan hada kansu guri guda, kallo
daya zaka yimusu kasan suna da matsala.
Ni kam zuwa yanzun an samu wata biyu rabona
da yarana har na dangana da kukan fili sai na
zuciya. Haka nan kullum cikin tunanin su da
ambaton su tare da yi musu addu'a Allah ya kare
minsu. Wani dare nayi mafarki wai Mama ta rasu,
tun Asubahi nake kuka, Iya ta yi ta lallashina wai
taci ta koshine, duk da haka shida daidai na kira
Anty Abida nace tataimakeni tabani Yaya Usman,
tabani shi nace, 'Yaya ka taimake ni ka je ka
dubo min yarana, ina zaton akwai wadda ta rasu
a cikinsu,dan na yi mafarki. Ya ce, Sadiya nutsu ki
kwantar da hankalinki. Nace, Yaya don Allah
zakaje? To shi kenan zanje jibi ranar Lahadi. Na
ce, To yaya na gode.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina ajiye wayar ya kalli Abida 'Wallahi ina
tausayin yainyar nan kinsan Allah banda ita,
wallahi bazani inda aboki yake ba,domin ranar da
zai bar garin nan sai da naje na sameshi, ba
yanda ban yi ba a kan cewa ya bar yaran gurin
uwarsu,sai ya ce shifa sam bazai bar mata yaran
shiba,tunda ita iskanci ta zaba,nace masa baka
da tabbas, kana yin abu sai ka ce bakaje
makaranta ba, wai kuma kana jami'in tsaro, ka
gaggauta maido da auranku ta hanyar sake daura
wani,domin idan ba matata ba ce nasan cewa ba
za ta iyaba. Kin san me ya ce? Abida ta ce, 'A'a.
Usman ya ce, Budar bakinsa sai cewa yayi ba zan
maida taba,kaima kana da dama bai haramtaba
inka shiga layin zawarawa,sai ka aure ta kasata
gidanka. Abida ta zaro ido tare da rike haba
'Lallai Aliyu ya dauki abin da zafi. Usman ya ce,
Shi duk ya manta abin da ya yi na zaci yarinyar
nan za ta tona masa asiri,saboda abin da yayi
mata, amma da yake 'yar halak ce. Abida ta ce,
In nice Allah saina tona. Usman ya ce mata, Da
yawama bazasu shanyeba, ita wannan yarinyar
daban ce, amma bazai ganeba sai nan gaba
(Nasan dayawanku kuma bazaku iya abin da
Sadiya tayiba ko idan kuma da wacce zata iya ta
fada muji! Duk da banayiwa kowace mace daga
cikin fatan makamacin wannan rayuwar...ANaM)
Abida ta ce, Inzaka je muje tare ina son ganin
yaran. Yace bari mugani. Har gida Yaya Usman
yazo yayi ta lallashina tare da daukar min
alkawarin zaije ranar Asabar ko Lahadi, sannan
ya ce ya yi alkawarin binciken duk wanda yayi
wannan kulli. Cikin kuka nake masa godiya. Haka
kuwa ranar Lahadi Anty Abida ta kirani ta sanar
da ni cewa gasu a hanyar Abuja,cikin raunanniyar
murya nace. 'Anty ki taimakeni in kunje ki kirani
mugaisa. Ta ce to. Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login