Showing 3001 words to 6000 words out of 20506 words
Chapter 2 - Darajar Yayana Book 4 end complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
san ba kowa zai fahimce ni
ba, wasu za su ce na cika kawa zucin 'ya'ya,
amma duk wadda ta taba shiga irin wannan halin
ina nufin ta rabu da 'ya'yanta, ba wai ta yi
tafiyane tabarsu taje ta dawoba, ba wai sunje
hutubane, sakinta akayi,sannan aka kwashe mata
yaranta dole zata dandana irin abin da naji, ko
nake ciki yanzun.
Ina ta zaman jiran kiransu. Sha biyu da 'yan
mintuna Usman ya kira wayar Alliyu,a ringing na
biyu ya daga suka yi sallama a tare, Usman ya
amsa,sannan yace, Aboki ina zan same ka,ina
Abuja yanzun haka. Aliyu ya ce, Ina office ko
zaka karaso? Aliyu ya ce, Shi kenan.Sun sameshi
bakin hanya sannan suka karasa gidan.Abida sai
kallinshi take duk ya rame suka gaisa, sannan
suka isa gidan.kamar kullum yaran suna takure a
gurinda suka maida tamkar gurin zamansu,wato
gefen kujeru,Mama da Al'amin duk sun jingina
jikin Kausar wadda suke ganinta tamkar uwa a
garesu,domin itace take yi musu duk abinda
uwarsu take musu,in har kaga Mujidat tayi musu
wani abu to tabbas mahaifinsu yana gidan.
Ko da sukaji sallamar mahaifinsu basuyi wani
yunkuri tashi ba don taryarsa.sam Abida har ta
zauna bataga yaran ba,Aliyu ya kalli gurin.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Khausar ku taso mana,yaushe zaku daina zaman
gurin nan?
Abida ta zaro ido tare da mikewa"Khausar!yaran
suka mike da sauri dukkansu suka rugo da gudu
tare da rungume Abida sannan sukayi gurin
Usman,Aliyu ya cika da mamaki,ya manta rabon
dayaga yaran haka suna murna ya nufi ciki kiran
matar, Abida duk da cijewar da takeyi sai da
hawaye suka soma yimata sintiri,Usman ya kalle
ta ya girgiza kai alamun tadaina, amma ta kasa
saboda yanda yaran sukayi baki suka rame,gashi
ba wata cikakkiyar tsafta,kitson kan su Khausar
duk ya tsufa,ba'a ko ganin layin kitson.ta tuna
yanda yaran suke kansancewa tsaf cikin tsafta da
tsantseni kowa sha'awarsu yake,ta dauki mama
ta rungume.Khausar tace,aunty maman mu fa?
cikin rawar murya tace,lafiyarta kalau,tace a
gaidaku,Al'amin yace yaushe zatazo? Khausar
tace,kai sunzo tafia damu ne.ta kalli Usman
Uncle ai dai zaku kaimu gurin Momy ne ko?kafin
Usman yayi magana,Aliyu suka fito da Mujidat
tana sanye da riga da siket na shadda mai ruwan
kwai,shikuma yana sa6e da Abdul,wanda aka
tsafta ce shi ckin jeans blue da riga ja,sai wani
dacin rai takeyi.ta zauna tana gaida su cikin
yatsina, Usman ne ya amsa Abida kam ta kasa
magana don bakin ciki.
Usman yayi mata sako cewa don Allah ta
nutsu,sabida yaran sun soma kuka suma.Aliyu ya
kalli Mujidat,a kawo musu abinci da abin sha
mana,ta tashi can ta kwalawa Khausar kira da
sauri ta tapi,sai ga ta da pure water leda biyu da
dan kwalin juice,sai kofi 2,ita kuma ta fito da kula
yar madaidaiciya. Abida ko ruwa batayi burin
shaba,bare abinci,Usman dai ya dan kurbi Juice
din da Aliyu ya tsiyaya ta mika masa,daidai
lokacin ni kuwa na kasa hakuri nakira layin
Abida,ta dauka yanda naji muryarta sanyi
kalau,sai na soma kuka,nace Aunty ta mutu ko?
Abida tace a'a lafiyarsu lau,bari kijisu.
Ta kamo Kausar zoki gaida Mamanki,cikin doki ta
amsa tace Momy,nace na'am...'kukan yaki tsaya
min,cikin rishn nace kausar.ita ma yarinyar ta
saka kuka tana cewa Momy don Allah kizo ki tafi
damu,hankalina yakara tashi nace,Khausar kuyi
hakuri kinji?ki lura da yan uwanki kinji? Cikin
kuka mai tsanani tace,wayyo Momyna! don Allah
zamu zo Momy.
Abida cikin hawaye sharkaf ta amshi wayar ta
rungume Khausar,Sadia yaya zakiyi haka?kinsan
zaki kara tadamin hankali ne,kika kirani,nace yi
hakuri Aunty,Aunty kibani Al'amin da Mama.tace
a'a bazan baki suba dan ganin Khausar tana kuka
suma gasu nan sunayi.Khausar ta sake janyo
hannun Aunty Abida tana cewa,Momy don Allah
kinji Momy!!! Tilas na kashe wayar na dasa sabon
kuka,iya dake kallona itama hawayen take
sharewa tana cewa "Sadiya kidangana da 'ya'yan
nan. Na kalleta Iya kitayani addu'a Allah yaba ni
hakurin jure rashin su kinji Iya? Tace to Sadiya ta
taso ta kamani ta rungume tana lallashi tamkar
yarinya karama. Su kuma a can Aliyu ya kalli
Khausar meye abin kuka? Mujidat dake gefe ta
tabe baki tare dace " a to" Ta gatsina hanci gami
da hararar Abida tana magana kasa kasa Abida
tace Kuka ya zamar musu dole wadannan yaran
kanana a ce an rabasu da uwarsu? Aliyu na
rokeka arziki kayi hakuri ka bamu yaran nan
mutafi dasu Uwarsu tana cikin damuwa Yatabe
baki Kadan tagani ma kin san Allah bazan bada
yarannanba ko zasu mutu daga ita har su,Usman
yadagawa Abida hannu alamun tayi shiru sannan
yakalli Aliyu Aboki zamu tafi daman munzo ganin
yarane,ya dauko ledar gefenshi Khausar yi shiru
ga tsarabarku tana sheshshekar kuka ta amsa
tana ji da dan nauyi har ya mike ya cewa Abida
tashi muje sai kuma ya tuna da binciken shi
yadawo yazauna yace Aboki ina son wani taimako
daya Aliyu ya kalle shi inajin ka. Yace zaka bani
sunan wannan account din zanyi searching zan
gudanar da wani bincike Aliyu yaruntse ido
wallahi bana son a tunamin komai game da ita
ban san tuna account din nan. Usman yace bazan
samu ba kenan? Aliyu yakalli Mujidat dauko min
laptop dina sun kunna inda suka fito da komai.
Aliyu yadauke kai inda Usaman yashiga bincike
cikin sa'a akwai lambar kuma ta MTN sannan
shima Malam din ya dauki lambarsa haka nan
yadauki ta wanda yakawo gulmar wanda yace
sunan shi Sulaiman yakulle komai sannan yamike.
Mujidat tazaro ido tana kallon Usman cikin
zuciyarta tana tsine masa, suka mike suka tafi
Abida tana kuka su Khausar na kuka haka aka
rabu yaran suka ruga daki suka dora sabon kuka.
Mujidat da gudu tashige daki lokacin da Aliyu
yatafi rakasu Usman takira layin Jamilu daya
dauka yace lafiya? Ina ta kiran layinki kin ki
dauka don kada ki bani cikon dubu 2 na koh?
Tace zan baka mun tashi daga kaduna ba shirine
zan aikowa Anty Ramata zata baka amma kana
ganin asiri bazai tonuba? Yayi Tsaki Sungama su
hkr Mujidat ta sauke ajiyar xuciya sannan takashe
wayar.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yakalli Usaman Aboki na godefa tunda
abinnan yafaru banga wani nawaba sai yau ga
tunanin Iya a xuciyata bansan ya zan tunkaretaba
dan nasan Sadiya ta fadamata abinda nabinne.
Usman yayi murmushi, ay Sadiya mutumce
wallahi har yazu Iya batasan wancen zancenba
kayi mamaki koh? Aliyu yayi ta kallon Usman
tunanin cewa zata fada shiyasa ya tattara ya bar
kaduna ya maimata bata fadaba? Usman yace ko
daya Aliyu yace Uhm duk na zata ta fada. Usman
yace shiyasa nace kayi bincike kan wannan laifin
dakake zarginta. Aliyu yace tafa aikata laifinnan
bazanyi mamakiba sabida shaidan ba rago bane,
nima nazaci zan tsinci kaina acikin haka?Usman
yace inma gaske ne bazakayimata adalci ba? Aliyu
yace adalcin kenan nayi mata na saketa kalau ba
tare danayi mata dukan hauka ba sannan banda
ta fada na so in ramawa kura aniyarta wato in
bar zancen tsakaninmu inkuma dauki nauyin
zunubin zagin da za'ayi min na sakinta batare da
tayi min laifi b kawai sai ta tona. Usman yace
Aliyu kenan bari muwuce Allah yabayyana gaskiya
inga yanda zakayi Aliyu yace wahala kawai zaka
sha amma gaskiyar ce tabayyana in kalura da
hirar data gudana atsakanin ta da malamin.
Koda suka tafi ya jima bai shiga gidanba yana
mamakin yanda Sadiya taci gaba da rufa asirin
shi yayi ta ganin kiran kiran yayunsa. Yaya
Sulaiman, Yaya Sani, Yaya Zakari, kai har kawu ya
kirashi amma ya ki dagawa nashi ganin asirin
shine yatonu zasu kira suyi Allah wadai dashi to
shi in ya dauka dabatun sakinnan ze kare kanshi
Aliyu Kenan.
Koda Anty Abida ta dawo sam bata nunamin
cewa yarana suna cikin matsalaba, illa fadan da
tayimin na kukan danayi tace shine yasa su kuka.
Jin hakan sai na kwantar da hankalina kadan, don
har Usman ma yace min kada in damu suna
samun kulawa. Haka na dangana sai dai duk na
rame yarona kawai ke tafka kibarshi har mukayi
kwana 70 nace baxan koma aykiba,Iya tazare min
ido dole nakoma yanzun mota nake hawa zuwa
gurin aiki dan ban waiwayi motarshiba.
Ranar asabar ina zaune a tsakar guda yarona
yana cinyata na kifa shi ina karanta dan karamin
alkur'ani mai girma suratul Bakara kamshin
turaren yaya naji kafin sallamar shi tabiyo baya
badon na san mahimmancin amsa sallama ba da
baxan amsaba, sannan banko dago kainaba bare
nadube shi yayi sallama dakin Iya tana ciki can
kan gado don haka bata jishiba shima din be
tankaba yashiga dakin. Natashi nagoya dana naja
Hijabina a igiya na dauki pose dita da yan canjina
napita sai gidan Aysha, taganni hankali tashe tace
lafiya har yanzu baki kwantar da hankalinkiba?
Haba Sadiya. Naxauna hawaye suka soma zuba
daga idona nace ni na hakura Aysha yayane yazo
gidan yanxun, wallahi shine yafama min bakin
cikin daya cusamin,ta dapani yi hakuri meyace?
Nace bamu ko kalli junaba fitowa nayi dan ko
ganinshin shi banasan yi. Aysha tayi ta lallashina
tana bani hakuri tace kin fadawa Iya shima
abinda yayi? Nace har abada baza aji daga
bakinaba wannan ya wuce saidai taji gurin wani.
Ina gisan har dare sannan suka rakoni ita da
Bellonta, itama dai tana tayi min korafin cewa
Bello yanzun sai bakin halaye yake shigo mata
dasu, ya soma doguwar hira sai yakai sha daya
bai dawo gida ba yayi ta 'yan daure daure da
fadace fadace. Nace lallabashi zaki Aysha kiji ko
kin masa wani laifi ne kar ki dauki fushi da
mijinki karamar matsala tazama babba, kar kiyi
sanadin dazaki nesanta kanki da yaranki ni na
isheki misali Aysha 'ya'ya sune rayuwar uwa
kamar yanda uwa take rayuwar 'ya'ya yanxun
duk macen da bata tare da 'ya'yanta ina tausaya
mata dan na dandani ciwon dataji. Cikin bacin rai
nasamu Iya nace, Iya ya ne? Tace Sadiya ina
kikaje? Nace gidan Aysha natafi kiyi hakuri
banfada miki ba wallahi ganin yaya ne naji bazan
iya zaman gidanba shiyasa natafi. Tace baki
batamin raiba Sadiya bacin ran Ali ne yaron nan
na zata yayi nadama ne ashe zuwa yayi yabani
hakuri, nace me kayimin? Ni awa zakazo bani
hakuri? Ali banzaci zan sake sakaka a idona ba.
Yace sabida me zaki ce haka Iya? Na tafine don
ki huce sannan inzo in baki hakuri dan na san
cewa babu wanda zai fahimceni ko yabani
gaskiya akan sakin danai wa Sadiya duk kuwa da
cewa yin hakan ba laifi bane. Iya tace sai na tari
numfashinsa cikin gatse nace to dama Ali waya ce
kayi laifi? Ko guda banga laifin kaba don ka auri
mace kana sonta lokaci guda kuma kaga ka daina
sonta ko ta maka tsufa ka sake ta sai ace kayi
laifi? Laifin da kayimin daya ne bata min ita da
sharri wai tana bin maza wannan kazafi yayi min
ciwo sosai domin yarinyar nan har ta gama
kuriciyarta a cikin gidan nan kaganta kace kana so
ka aura bata taba dauko min maganaba. Iya tace
Sadiya yau har nauyin na aje gefe na tsakanin da
da mahaifi na tambayi gadanga cewa ko ba
budurwa kasame taba? Sai ya sunkuyar da kai
nace in ba budurwa kasameta ba sanar dani.
Yace Iya duk ba wannan zancen bane ai mutum
yakan canza kuma ni fara koyarwar ta dinnan ne
ta hadu da abokan banza. Iya tace na ce dakata
bata tare dakowa nabanza kai dai ka gaji da ita
ka saketa ka kuma hada mada da sharrinka na
'yansanda to kaje Allah ze sakamata ina raye sai
naga sakayya sannan 'ya'yanta in kun lura dasu
kuda Allah inma kun wulakantasu kuda Allah. Ya
kasa magana sannan wai ina jaririn? Nace yana
gurin uwarsa ai danaga baka waiwayeshi ba na
zata zakace ba danka bane? Yace ni bance ba
Iya, yaciro kudi ya aje wai gashi kibata sabida
siyan wasu abubuwan na yaro Iya tace dauki
kudinka babu abinda muka rasa yayi shiru can ya
sake cewa. Ina kara baki hakuri iya nace kai ne
da hakuri amma dauki kudinka in ba so kake
kaga bacin raina ba,ya dauka yafita.Na sauke
ajiyar zuciya nace, Iya na gode dabaki karba ba
na sani sosai Iya cewa bashine yayi min sharriba
wasu ne daban amma takaicina yanda yakiyin
bincike kuma yayarda cewa nice, kobe sakeni ba
aure baya yiwuwa da zargi.Iya tace ay na gaya
masa nace lokacin daka fito da abunka kana
ganin ya maka tsufa sabo kake so, lokacin wani
kuma zai ga cewa na kannan shine sabo agurinsa
Allah yayi miki zabin Alkairi, nace amin.
Daren ranar su Yaya Sulaiman suka zo da shi su
hudu wai iya tayi hakuri tayafe masa sannan
suka matsa masa cewa ya maido da matarsa
kuma ya yarda amma da sharadin zata daina
koyarwa. Ina kwance kan gado a uwar daka ina
jin su tamkar in taso in fito in ce bazan koma ba
amma sai na tsaya inji me iya zatace? Ay kuwa
sai naji Iya tace da farko dai kamar yanda na
shaida masa dazun ni bai min laifi ba bare ya
bani hakuri in da ace ni wata ce lokacin da
rigimar tafaru yaneme ni mana sai kurum yatafi
ya aikata son ransa yanzun yazo yana ban
hakuri,ni a wa? Batun kome kuwa ga matarsa
nan adaki tazo in zata koma bazan sata ba kuma
bazan hanata ba, Tadaga murya Sadiya na'amsa
tace zo nafito da dana akafada na zauna
gefe.tace nasan kinji komai dan haka in zaki
koma sai ki fada musu, shidai sun bashi baki ya
yarda,Budar bakin da nayi sai kuka nace yaya
kuyi Hakuri da abinda zance in Yaya Aliyu ne ya
rage namiji a doron duniya wallahi tallahi bazan
aure shiba bana kosan ganin shi ya fita a raina
sam.Iya tace tashi ki koma ciki sannan tace kunji
koh? To kuma na roke ku da kar ku sake
zuwamin da wannan zance ko gaba an rufe
wannan babi in dansa ya isa yaye yazo ya
dauka,bansan lokacin da nace Iya harda wannan
ma za'a rabani tace Allah ya baki wani mijin na
gari ki haifi wasu yayan Sadiya,sai lokacin Aliyu ya
dago ya dubi Iya sabida yaji zafin kalmarta
sannan ya sake sunkuyar da kai Aliyu yaba yaya
Sulaiman kudin yadan matsa yace iya ayita hakuri
shin ina Sadiyarne? Na fito ya miko mini nace a, a
yaya muna da komai na koma ciki yace ke Sadiya
zoki karba hakkinkine da danki Iya tace tunda
tace bata so saiku barta ko ku tashi kuje zamu
kwanta...zamudakata anan,fatan zamuyi sallar
juma'a lafiya
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Darajar Yayana4-02
Posted by ANaM Dorayi on 12:11 AM, 12-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan
shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona
wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da
kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan
rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai
Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar
dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai
hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na
sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda
dama na dora ne a saman dogon wando na
goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi
cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk
abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace
nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima
danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace
karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin
kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan
kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace
don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona
in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa
yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi
nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin
ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma
yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja
sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan
ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na
harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da
gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo
da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego,
kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na
karasa sa masa pampers din na mika mata shi.
Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi
a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna
shima yaharareni sannan yazauna yana kallon
yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce
Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban
tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam
a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina
karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan
haka yadauki kayan yana sa masa yagama
yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da
gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya
zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri
Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma
kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki
yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona
asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli
Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa
gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko
minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera
nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin
asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro
birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar
dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba
wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani
abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in
ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga
shirginku.Ni dai sim sim nayi daki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar
shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba
na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga
hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a
tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar
daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje
tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya
nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar
shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin
tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda
nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa.
Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna
akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin
dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun
same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan
kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi
tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa
nan ina son Iya kitaya ni da addu'a Allah
yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa'a. Yace
amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son
duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana
siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da
ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da
shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi
nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin
yaciro kudi gashi Iya. Tace a'a ai na fada maka
bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya
Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki
amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki,
Ya'ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce
komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin
kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin
gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi
fuska daure cikin harara nace bani da gida bare
mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja
sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba.
Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har
kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi
kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin
shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi
yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin
nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi
tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi.
Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin
kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai
magana zaice yana addu'a an san dai ita ce
dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka
mataba wato ma tausayin shi takeji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn
limamin unguwar da sunan cewa shi bakone
matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2
yace a nema masa daki na haya yana son yadan
kama sana'a yafada musu cewa rani yake Zuwa
garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi
masa tambaya game da wasu unguwanni a can
Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne
ya kuma fada masa cewa ya