Showing 15001 words to 18000 words out of 20506 words
Chapter 6 - Darajar Yayana Book 4 end complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
tace, "InshaAllahu, yanzu kaima yakamata
insanka."
Yace, "Sunana Alhaji Badamasi Yunusa,ni dan
asalin jihar katsinane karamar hukumara
Bakori,inna nan gwamna road da iyalina,matana
biyu,yarana goma,ni ma'aikacine a matatar man
fetir dake nan Kaduna."
Iya tace, "to shikenan,Allah ya tabbatarmana da
alherin dake ciki."
Yace, "Ameen."
Kan ya wuce saida ya ajiyewa iya daurin yan
dari biyar guda daya. Nafito daga uwar daki dan
innajinsu,iya tace, "da alama yanada
mutunci,nace, "nalura tin farkon haduwarmu."
nakoma gurinsa inda yacigaba da yimin zancen
aure,shi bayason adauki lokaci,sannan yanason
muma muyi bincike a kansa,bayan nan zai turo
tinda yanzun mu ba yara bane da zamuyi ta
doguwar hira,nace , to! Yabani lokaci nayi nazari
da tinanin kafin ya turo din,Yace to yabani,nima
haka yacikani da kudi,nayi nayi yabarshi yace
Sam; dole nakarba. Yataka zai shiga Mota kenan
Aliyu yayimana sallama,shine ya amsa nikam
gabana sai faduwa yake. Yace, "Alhaji nazone
inyimaka gargadi."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Alhaji Badamasi yace, "name fa?"tare da
dawowa da kafarsa.
Aliyu yace," wannan matatace, dan Allah
karkasake zuwa."
Alhaji Badamasi yadubi gurin danake Yace,
"Wannan ne?"
Koda bansan meyake nufiba Sai nace, "Eh! Shine
Alhajina,shiga motarka kayi tafiyarka sai munyi
waya."
Tamkar me jiran umarnina sai kurum yashiga
mota tare da cewa, "sai kunjini ginbiya."
A hankali motar ta silala ta dauki hanyar barin
layin. Cikin zafin rai yasha gabana, "wato harma
labarina kike bayarwa ko? gani dan iska!"
Nace, "Eh!" Nacigaba da tafiyata."
Yace kinsan Allah zakijamasa bala'i,zan tono
laifukansa inmasa tarko yafada hannunmu,ai
nasan shi."
Tsaki naja nacigaba da tafiya inna cewa dadinta
baka isa kayimasa abinda Allah baiyimasaba.
Innashiga zaure shima yashigo, "Sadiya dan
Allah tsaya kiji." ya tsare hanyar shiga gidan ya
tausasa murya, "Sadiya dan Allah ki rabu da
mutuminnan, yawancinsu suna ta'ammali da
matan banza."
Nasaki dariya cikin izgili Nace, "wannanfa shine
shege! Yi da me zina," nanunashi da yatsa,
"ashe har kai zaka dinga zargin wani cewa yana
bin mata? Kamanta da naka laifin ko? har
sakamako ka ajiye." Nayi murmushi, "bani hanya
in wuce."
Yace, "Naji dai,duk abin da zaki cemin
Kice,amma zan nunamiki cewa nidai nine
mijinki."
Na ratsa ta gefensa na wuce,bansan yabiyoniba
sai da namikawa iya kudin inna cewa "nayi-nayi
yabarsu yaki."
Ta ciro nata tace, "kingansu dami guda, Allah
yashi albarka,tinda yafadi inda yake zansa
yayanku babban a bincikomana,in bashi da wani
aibu shikenana."
Kurum sai Yaya yafado dakin, "Dama sabida
kudi kike sonshi ko Sadiya? Sannan kuma kisani
bazakiyi aureba har sai kin yayemin yarona."
Nace, "ina ruwanka dani? Yaro kuma dashi zanyi
aure a can zan yayeshi."
Yasake daga murya, " kinyi kadan."
Da hannu iya tayimin alama wai inyi banza
dashi, don haka na shareshi Yakara masifarsa
ya nufi waje.
Ranar Aliyu yaga tashin hankali,yanzun yanda
zai shawo kan Sadiya da Iya yake nema.nikam
dan So banson Alhaji,amma zan iya auransa da
in auri Aliyu ko Yaya Usman, in anyi bincike zan
amince muyi aure kawai in huta.
Aliyu fa yadage kullum yana kan hanyar gida
daga Abuja,yana gida yana bawa iya baki,ya
turo wannna ya turo wancan,rokon gafara har
dasu mahaifina. Andau tsawon wata biyu a
haka,lokacin zancen aurenmu da Alhaji yasoma
nisa,dan batun har yakai Zaria. Yaya Aliyu kam
yadan rame duk da juriyarsa. Saifa yadauki wani
sabon salon kamun kafa da yaransa,kawai sai
mukaga yara sun canja ba kamar Khausar, in
Alhaji yazo ta dinga kunci kenan harda
Kuka,dana tanbayeta dalili wai inkoma gidan
Babanta,ranar har marinta nayi, iya tayimin
fada wai indena dukanta,ammafa baza'a
komaba. Ko Yaushe zaizo yakwashesu zuwa
yawo yanatayimusu hidima. In Iya kuma tayi
maganarsa sun dinga kunci kenan,har Mama.
Wata ranar Juma'a muna zaune iya taje
Masallacin Juma'a Yaya yayomin waya inshirya
yabiyamin kujerar maka ni da Iya zamuje,duk
da farincikin daya girgizani amma sainace nikam
nagode bazaniba zamuje da Alhajina,
( Lallai Sadiya kin burgeni,ANaM Dorayi
hhhhhhh)
Bantabaji Aliyu yayi babban zagiba sai yau,ya
kudundumawa Alhaji zagi, da sauri na kashe
waya
Yaya Sulaiman yazo da daddare cikin murna
yana gayawa Iya wai Aliyu yabiyamusu Hajji shi
da Iya da Mahaifina,ga mamakina sainaga tahau
murna harma tasoma kiran 'yan uwa a waya,
saidai banji ana kiran sunana a 'yan tafiyaba
Alhalin ya cemin yabiya ni da iya.washegari
makota sukai ta shigowa taya murna iya tana
yaye baki, amma da yamma da yazo sainaga
tayi kicin kicin,musamman nazo nazauna inji ko
zaiyi batun tawa kujerar, sai naga iya ta tubure,
"Naji sakon, nagode, amfa kasani karkazata zan
hakura da laifin dakayi,hajji kiran Allah ne koba
ta hannunkaba indai an kirani Sai naje."
Yace, "hakane Iya,innadai neman afuwa,kuma
dama kujeru hudune yanzu saura daya shine
nace kowakikaga yadace abaiwa? Har na bawa
wani sai yace bayaso."
Iya tace, "kai wannan wane mara rabone? To kai
kajene?"
Yace, "a'a zanje wata shekarar,sabida Siyasa
datake bullowa a daidai lokacin aikin
hajjin,kasarnan tana bukatar Irina."
Iya tace, "Allah yataimaka "
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nashiga daki cikin takaici, bakina ya
cuceni,da'ace nasan Iya zatayi saurin yadda da
batun da bance banasoba,gashi tace yabawa
kawunmu kaninta na Hadeja.
Aliyu yasamu sassauci gurin iya da yan'uwanshi
sanadin wadannan kujeru da yabiyamusu yanzu
burinsa kawai ya shawo kan Sadiya, amma ta
yaya bayan tabawa wani dama har ankawo
sadakinta.
Daya Isa Abuja kai tsaye Office yawuce sai wajen
shabiyu yaje gida, abinda yabashi shi mamaki
yanda yaga ankulle kofar falon ta ciki maimakon
ta waje, yasaka Key yaki shiga sabida akwai
wani ta ciki,don haka sai ya kwankwasa don
yaga ikon Allah,jim kadan aka bude. Mujidat
yagani, tayi kyau iya kyau,kamar farkon
haduwarsu, ta rungumeshi; Oyoyo Mijina,ya
yakiceta ya tureta yadaga murya, "Wayace
kidawo gidana?"
Tace, " to inna can zaune bakazoba"
Ta nufi ciki ya shiga, ta nunamasa tebur da
hannu; " ga Abinci."
Yace, "bana ci."
Ya nufi dakinshi ta bishi, bandaki ya fada ya
watsa ruwa, yafito yayi shirin kwanciya yana
hawa gado itama ta fada,Yace, "kifita,kuma
nabaki zuwa da safe kibar gida na."
Tace, "Gidanmu dai, dan Allah Honey kayi
hakuri bazan sakeba."
Yace, "kina takama da aurene ko? To ni zan
ball....." Ta katseshi ta hanyar manna bakinta a
a cikin nasa,hmm Mujidat yar duniya, sai datasa
ya manta komai,yashiga shawagi cikin duniyar
Ma'aurata. Haka ya hakura ya barta sannan ya
dakko mata danta daga inda yakaishi Ajiya
bayan taimasa alkawarin bazatasake
sabamasaba,kuma zata mutunta kowa nashi.
An ajiye lokacin bikinmu nan da wata
biyar,lokacin na yaye Sadiq,Alhaji Badamasi
nason yin dawainiya damu danma iya tana
hanashi,su Khausar sun tsaneshi,har shidakansa
ya fahimci hakan,har yataba cemin, meyasa
yarananan ko yakirasu basason Zuwa? Nace
haka suke basu da sabo.
Cikin yan kwanakin da suka biyo baya Yaya
banda kyautatawa dangi baya komai,ya
kammala gidanshi dankarere yace Iya takoma
donshi ba shiga zaiyi ba,namu nada kuma Yaya
Sani yakoma.
Nadauka Iya zatace a'a,sainaji tace zatayi
shawara, Nace, "to iya komawa zamuyi?"
Tace, "Eh,ai abinda baifaruba shi ake gudu
Sadiya, wanda ya faru saidai a kiyayi gaba.Aliyu
yariga yanemi afuwa ta yaya zanyi? Sai addu'a
inna nunamasa fushi nane don ya kori gaba
yakuma gane yayi ba daidaiba."
Nace, "yanzu dai za'akoma gidan kenan?"
Tace, "to waye bayason cigaba yarnan?"
Natabe baki cikin takaici nace, " to saidai
kukoma kubarni a nan, ko kujira in nayi aure ku
kuntare." Iya dai banza dani tayi. A raina nace
wato da da Mahaifi sai Allah,yanzu iya har
tamanta da fishin datakeyidashi.
Wata ranar asabar yazo har da Abdul su
Khausar suna ta murna ganin dan'uwansu nidai
beganeniba yaron,lokacin iya na makota.
Yaya Yace, "gabar harda danki?" Nidai ban
tankashiba, Allah-Allah neke iya tashigo naga
irin warwarar dazataimasa amma tana shigowa
sai naga ta hau washe baki.
"Ai harda Abdul din kazo."
Al-amin yakamomasa hannu, "gashi Iya."
Ta daukeshi tanacewa Khausar ta debomasa
ruwa a firij,Yaya ya kalleni harda yin wani
murmushi,wato inganidai bashi da wata
matsala, nima dan inkular dashi nadauki wayata
nakira Alhaji Badamasi mukagaisa,nace, "Alhaji
zanje unguwa kozaka aiko akaini."
Cikin murna Yace, "dole inbar komai inzo inkaiki
"
Nakalli fuskarshi kamar zai fashe da
kuka,murmushi nayi na tashi na hau yin
kwalliya, minti shabiyar saiga kiranshi,
"Na'iso ranki ya Dade "
Nace, "dama kana kusa kenan,to ganinan
fitowa."
Nadinga yiwa jikina aman tirare har saida ya
time,yace,"wai ke ina kike shirin zuwa haka?"
Nace, "Sai kaji? Ba matsalarkabace."
Ya kalli iya, "haka take yawo kamar mara
mafadi?"
Iya tace, "shi zata aurafa."..
Nazo fita ina wucewa ina cewa, Iya zanje gidan
Aisha,tace, "ki dibarmata kwai."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya kara kulewa,sai yatare bakin kofar, "To Koma
ki dauki Sadeeq bazakibarshi ya tashi yadinga
kukaba."
Dariya ke nema ta kufcemin,Nace, "Kasan Allah
yayi kukan jini inyatashi nikam bazani dashiba."
Yayo kaina, nayi bayan Iya inna fadin, "Dukana
to zakayi?"
Yace, "bakin rashin kunyar zan buge."
Nace, "Aiko daka amsa tanbayoyin Alhaji,domin
matsayin matarshi nake." cike da rashin kunya
nayi maganar.
"Inma matsayin uwarsa kike be
dameniba,amma daukarmin yaro aje duk inda
za'a dashi."
Na kalli iya wadda tinda tayi magana dazu bata
kuma yin maganaba, sai nagama dariya take
kunshewa dan abin dariya itama yabata.
Nace, "kifada masa yadena zargin mijina." Sai
naji jifa a kafadata da wayar shi, nashiga uwar
daki inna sosa gurin domin naji zafi,bakina bai
mutuba innacewa, "Ba inda zanje dashi kome
zakayimin."
Iya tace, " ina ruwanka da sune? Yaza'ace
saitafita da yaro dole?"
"Iya amma inyatashifa yanason nono?"
Nace, "nawa kake biyana kudin shayarwa?"
Yace, "kifadi kudin nonon gabadaya a biyaki."
Iya tadaure ta hade rai tace, " to tinda ban
isaba kacigaba."
Yazauna tare da fadin, "shiyasa tagama
rainani,domin kankomai sai a nunamata tafini."
"Au, hakama zakace?"
Sai kuma cikin sauri Yace,"iya kiyi hakuri." Nidai
nafi to na debi kwai kawai nayi gaba.
Tin bayan fitata kai yadafe, baisan ta ina zai
bullowa lamarinaba,abinda dai yayiwa kansa
alkawari shine , bazai taba bari Sadiya ta auri
waninsaba,yadogara ga Allah ta hanyar
tsayuwar dare tsananta addu'a,Allah baya bacci.
Nikam a gidan Aisha inna fadamata yanda
mukayi munata kwasar dariya,Aisha tace Sadiya
nidai bazangaji da fadamiki da Aliyu kadai kika
daceba,shima dake yadace, nace tabdi, ni yanzu
nacire batun wani so ko dacewa a cikin raina,
nafiso inyi aure inda za'a ga mutuncina,insamu
tsabtataccen miji mara aibu,tace ai bari
infadamiki Sadiya a wannna zamani da wuya
kisamu mara aibu,sai dai wani yafi wani,ni
innagudun kar kiyi gudun gara ki afkawa zago,
amma shi din kinbincika halinsa?
Nace, "iya ta bincika ba matsala"
Tace, "shikenan Allah yazaba mafi alkhairi."
Aliyu yacewa iya yagama zubamusu kaya a
wancan gidan sati me zuwa zasu tare.
Iya tace, "Ai nazata sai mundawo aikin hajji anyi
bikin Sadiya don batason tarewa a gidan."
Yace , "a'a, tafiyarku saura wata Daya da
kuntare kawai,"
Tace, "ko a barshi mutafi daga nan inmundawo
lafiya sai musauka a can."
Ranar tafiyarsu iya har kuka nayi, nace yanzu ni
kadai zan zauna a gidannan sai yara, gashi
zandinga tafiya makaranta, iya tace, "bana
fadamiki matar kawu Hauwa tana nan tahowaba
daga Hadeja tare zaku zauna,in Allah yadawo
damu lafiya sai sutafi tare da kawun naku ko?"
Nace, "shikenan,"
Amota Daya Yaya yadaukesu wata kuma aka
debi 'yan rakiya, nidai dama nafadawa Alhaji
kuma yaturo direbansa yakaini, Aliyu ya hana
yaransa shiga motar, nace ohodai.
Bayan tafiyarsu Iya da sati daya sai ga yaya
sunshigo da Habu, na daure fuska muka gaisa
da Habu,dama alokacin zantafi gurin aiki, sai
kawai nafita.
Aliyu yasa Habu yayi ta jidar kayan yana kaiwa
gidansu, irinsu kujeru,TV harma da fringi,Baba
Hauwa tace lafiya? Aliyu yace dama zaku
tashine,kayan nabaiwa uwar yaron nanne
mokatanmu."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tace, "harda firingin? Amma danasani na
tanbayi firing din innasonshi,Aliyu yace, "inzaki
tafi sai insemiki wani"
Tasoma godiya yace ai ba komai,nidai addu'ar
dazakiyimin Allah yasa Sadiya ta yarda tadawo
gurina.
Baba Hauwa tace, "Ai dama kanasonta baka
yunkuraba?"
Aliyu yace, " Ai babu irin yunkurin da banyiba
amma yarinyar nan taki yarda dani,yanda
kikasan inyi hauka."
Baba Hauwa tace, "shikenan zan tayaka
addu'a,sannan zan dinga dan cusamata ra'ayi."
Yace, "nagode, nikuma zanmiki alkhairin da
bazaki mantaba indai kika shawomin kanta."
Nadawo naga gidan wayam, yarana da
murmushinsu suka tareni da batun wai Abbansu
yace yau zamu tashi,tsaki naja tare da cewa dan
Allah kukauce kubani guri,raina yabaci daganin
hukuncin da Yaya ya yanke, na dinga zaga dakin
inna kallon jakunkunan kayanmu a kasa anfito
da komai sai gashi yashigo, "kufito Habu yayi
gaba damu nikuma zantaho da jakunkunan, ko
bata dawoba?"
Baba Hauwa tace, "tadawo tana ciki."
Yashigo cikin dakin, "Sadiya" nakalleshi cikin
bacin rai,har saida yayi in'ina kafinyacemin,
"kizo Habu yakaiku" Nace ina? Yace sabon
gidanku, na girgiza kai gami da tabe baki,
gidanka dai bazaniba.yashigo tare da tausasa
murya yace , Sadiya wai bazaki yafeminbane?
najuyamasa baya, "wai me zanmikine kiga
haskena Sadiya?" na waiwayo na dubeshi,
"rabuwa dani kawai za'ayi kadena shiga harkata
sai inyafemaka." Ga mamakina sainaga yazube
gabana gwaiwa biyu biyu yanacewa, "Sadiya dan
Allah na rokeki ki yafemin kidawo aurena wallahi
ke kadai nakeso,kanki nasoma sanin wacece
mace, dake kadai nake samun nutsuwa, Sadiya
ki amince kiyimin takaba."
"Takaba kuma?"
"Inna nufin kikoma gidan har inmutu kiyimin
takaba."
Na tabe baki,"ga Mujidat can zatayimaka takaba
ni bazan iya zama dakaiba," nasake juya baya,
sainaji muryar Khausar, "Dan Allah Mama dan
girman Allah mamanmu," nace nifa bazan koma
wani sabon gidankaba bare aurenka inkamanta
abindakayimin to ni banmantaba, yamike, "ke
wace irin zuciya gareki bayan na kaskantar da
kaina na rusuna a gareki akan kiyafe kidawo
kince a'a to bari kiji dole nema ki Koma gidan,"
nace, "bazan komaba" Yace, "to ai nanma gidan
ubanane,meye banbancinsa da nawa?" Na
kalleshi cikin bacin rai, "dadin abin nima ubana
yanda gidan, kuma zankoma yanzunnan."
Nasoma hada kayana, da sauri yafito yana
fadawa baba Hauwa wainace zantafi gidan
banana, sai gata tashigo, "haba Sadiya, me yayi
zafi haka,"
"Gorin gida yayimin, dan haka zan tafi gidan
ubana,"
"inkinyi haka kuwa iya bazataji dadiba," nasoma
kuka to Baba Hauwa duk yatakuramin, ina
ruwansa dani? gara intafi abuna." Tace, "ba inda
zakije, kuma yanzunnan zamu tare a sabon
gidan idan na isa dake, inkuma taurin kan zaki
nunamin ina yabinki to bisimilla."
Shiru nayi dan babu abinda natsana a duniya
irin babban yaga na raina shi, banson ayimin
shaidar rashin kunya, inna kuka riris Muka shiga
Mota zuwa gidan da yaya ya ginamana.
Sam barka,gaskiya gidan ya tsaru. Abin mamaki
can Muka samu makotanmu sunje kallon gidan,
inna zaton Yayane yasa Habu yasanar musu
zamu tashi. Anzuba komai sabo, tafkeken falo
da dakuna hudu, nawa dana Iya dana yara,sai
na baki. Can gefe ga wani gini, dana tanbayi
Habu sai yacemin na megidanne in yazo hutu,
"muje kigani." Nace bazaniba. yara kuwa sai
murna suke suna tsalle ga kayan wasansu nan
kala-kala. Bayan kowa ya watse na daga waya
nakiraki Aunty Abida inna gayamata yanda
mukayi, tace zatazo, A'isha ma haka.
Inna kitchen dinmu mai dauke da kayan girkin
zamani, inna yiwa yara abincin tafiya
makaranta, dayake da safene, zani na daura
akan rigar baccina,Sai hula akaina, sai naji
maganar Yaya a bayana.
"My choice, me kikeyine.? Nadafe kaina cikin
takaici,na kalli jikina, yaci ace da hijabi a jikina,
sabida kirjina yafito, dayake rigar tana da katon
wuya, nace, " Lafiya?"
Yace, "lafiyalau, nazo ingaishekine "
Nace, "nagode, jeka."
Ya iso daf dani, "kintashi lafiya?"
"Don girman zati kafita, mufa musulmine, bai
dace kazo inda nake cikin kowane yanayiba."
Yace, "Ok! Hakane, sai anjima,amma
ataimakamin da abin kari." Sabida yafita nace, "
toh."
Banyimasa abin karinba,ina sallamar yara
nakoma na kwanta. Baba Hauwa tashigo gurin
sha daya ta tasheni.
"Kin karyane Halimatussa'adiyya?"
Nace, "a'a"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Alhajima yana ta shigowa, wai kin hadamai abin
kari. Nace, "bazan hadaba Baba Hauwa, ni
matarsace?"
Tace, "amma Kanwarsace ko?"
"Eh, amma banason wata alaka ta hadamu."
"Aiko da alaka ta hada, 'Yaya hudufa, don haka
kibar batunnan,abin karidai nayimasa, shine ma
ya kunna kayan girkin."
Nace, "ni bamanajin yunwa, sai anjima zanci na
rana gaba daya."
Tace, "to shikenan, Allah yakaimu."
Can saiga Aunty Abida wajen karfe daya muna
kitchen muna girki. Gaskiya tayi santin gidan,
muna cikin hira sai mukaji sallamar A'isha, nan
muka yini muna hira, dan ko dakko yara a
makaranta Baba Hauwa ce ta dakkosu.
Aisha tace, "Kyan gidannan kunmaida aurenku."
Na daka mata duka a baya, "aniyarki tabiki."
Abida tace nidai ba ankimuba, mene aibun
mijina? Kin gwammace mai mata biyu da yara."
Nace, "Haka nake sonshi."
A'isha tace, "kikoma gidan mijinki Hajiyar Allah
Ku rungumi yaranku."
Nace, "Zanje in haifi wasu a can." Tace,
"shikenan."
Sun yini har dare sannan suka tafi,nakira Alhaji
a waya nace mai muntashi har yakemin korafin
Cewa bandaukeshi da muhimmancibane sai
bayan muntashi sannan nafadamai? Nace masa,
"tashinne yazomana cikin bazata, Yayane ya
uzzura."
Yadanyi dif, sannan yace, "nifa duk lokacin da
kikace Yaya dinnan sai gabana ya fadi gani
nakeyi kamar har yanzu kinasonsa ."
Nace, "dan Allah adaina maida hannun agogo
baya, ni bazan Koma gidansaba."
Yace, "to zaibari inshigomasa gida?"
Nace, "tinda yakawoni dole inshigo dakai."
Yace, "a'a, bazan shiga gidansaba, in nazo kya
fito. Ina kikacema gidan Yake?"
"Nan unguwar mu'azune,Amma sabon gurine."
Yace, "to zamuyi waya, anjima zanzo."
Nace, "Allah yakawoka."
Washegari yashirya zaitafi Abuja inna kwance
kan gadona na saki A.C inna Karanta wani littafi
maisuna Yayana safara na Asma'u Lamido
sainaji sallama,kafin na amsa har yashigo, naja
hijabi na rufe jikina, fuskata a hade na dubeshi.
Dan murmushi naga yanayi, sannan yace,
"menene Bako ake rufe-rufe?" Cikin zolaya yayi
maganar.
Nace, "aidai haramunne ka kalleni cikin wannan
yanayin."
Yace, "to nidai zantafi." Nacigaba da
karatuna,kudi ya ajiye a gefena, bankalleshiba
ballantana kudin, har yakai bakin kofa sai yajuyo
yace.
Karkijawa wani kato duka dan nacewa 'yansanda
dake gadi su daki duk wanda yashigo gidan.
Tsaki naja tare da cewa, "Dadin abin nasa gidan
yafi Wannan." Bai tankaba yafita yabani ina ta
fada.
Kamar ance ya wai waya, Aliyu yaga Mujidat
cikin mota tare da wani Mutum,kasancewar bata
ganshiba, sai kurum yabi bayansu,dayake mota
ukuce tsakaninsu, amma yaga Hotel din da suka
shiga, shima yabisu, ga alama ba lokacin zasu
kama dakinba,sun kama tuni, don baigansu nan
gurin karbar bakina.(Reception)
Yashiga kai tsaye yanuna katin shaidarsa ta
zama Dansanda, sannan yayi tanbaya game da
dakin da suka kama, yayimusu kwatance da
motar da yagansu, har dakin aka kaishi, ya
kwankwasa shiru, sai ya murda kofar, baizaci
zata budeba,amma sai ta bude.Irin kamun
dayayimusu ya kazanta,domin haihuwar uwarsu
suke, sannan maimakon saduwa irin ta mace da
namiji, sai yakamasu yana saduwa da ita ta
dubura,wato luwadi.
Wa'iyazubillah! Allah yayimana tsari da mugunji
da mugun gani, Ameen.
Salati Aliyu yasaka,Mujidat tayi wuki-wuki,Alhajin
yasoma yiwa Aliyu fadan meyasa yashigo?
Mujidat tace mijinane, juyawa yayi batare
dayace kalaba.
Ni naga yasake dawowa washegari da Abdul da
kaya niki-niki,ko kallonshi banyiba,Baba Hauwa
itace ta tare shi,itacema ta bawa Abdul
abinci,nabar falon nakoma dakina, sai gashi
cikin raunanniyar murya yace,"Sadiya inna
maikara nemana afuwarki, jiya naga abin
dayaban tsoro bayan komawata daganan, wai
ashe har yanzu Mujidat tana bin maza, dumu-
dumu na kamata da aurena akanta wani kato
yana luwadi da ita."
Na kalleshi cikin zaro ido,ban tankaba yacigaba.
"Don Allah ga Abdul nan na rikeki kisakashi cikin
'ya'yanki, kodadai yazone ba tahanyar data
daceba jinine, nasani bashi da gadona amma
baidace inbarshi ya wulakantaba,donshi ba
ruwanshi." Ya aje kudi a gefena.
"Kisashi makarntar Isalamiyya da Boko wadda
'yan uwanshi keyi, nasan zaki iya."
Duk bantakamasaba, har sai dayace "zakuyi
kwanaki baku ganniba akwai aikine a hannu na
kila ya daukeni lokaci, kiyimin addu'a."
Na tabe baki, "Allah ya tare ."
Yace, "nagode."
Haka kuwa cikin kwnaki uku Abdul yasoma bin
'yan uwanshi makaranta.
Aliyu wani course yaje na wata biyu
India,Yasamu Wannan damarne daga gwamnati
me ci a yanzu,yasan sunyi hakane Don ayi zabe
baya nan,tinda yanuna baya goyon bayansu suyi
yanda suke so, shikuwa ya karbi wannan dama
da zuciya daya, dankuwa ba kowane
dansandane ke samun wannan damar ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Su Iya sun dawo, muna ta murna,kullum
gidanmu sai yacika da Iyalai da abokan arziki,
anata rabon tsaraba, abakinta nakejin inda Yaya
Yake.
Baba Hauwa daki daya muke kullum sai tayimin
zancen Yaya tayi ta kwarzantashi tana bani
shawara har abin ya isheni nagudu dakin yara,
suma suka isheni da tanbayar ina Abbansu,
nace bansaniba kuma kada wanda yasake
tanbayata. Iyace kurum ke goyon bayan aurena
da Alhaji, ni dama tsarabar zannuwan gado
yayomin sai Jallabiyya.
Kwanci tashi saiga Yayay kamar daga sama,duk
dacewa natsaneshi bankasa ganin kyawun
dayakaraba, har da dan haske, a raina nace
anje course ko anje Hutu?......zandakata anan,
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Darajar Yayana4-05
Posted by ANaM Dorayi on 02:28 PM, 20-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
__________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Assalamu'alaikum, kuyimin afuwar shiru da
kukajini, hakan yafarune sakamakon tsaiko dana
samu sabida wasu dalilai,saidai yanzu nayi
yunkurin kawomuku Babi na karshe fatan kuna
tare dani, inna kuma fatan kuna sane da inda
muka kwana...
Tsarabar daya kawo dan gulma harda ni,banki
karbaba, Pakistan yakawomin kala shida masu
kyau sosai, zanyi gayuna a gidan Alhajina, ga
turaruka masu tsada. Yara kam ba'a magana
harda yaran Usman.
Ba'ayi wataba sai karin girma zuwa matakin
kwamishina 'yansanda na jihar Kaduna, anyi biki
tare da duk wani abu dayakamata,. Tuni yatare
a gidan kwamishinan yansanda dake kaduna. Sai
naga