Showing 12001 words to 15000 words out of 20506 words
Chapter 5 - Darajar Yayana Book 4 end complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
wadannna ? Sai ga Habu
yashigo da sauri yace Aunty Ku kunna TV,Sai
yasamemu cikin kuka,yace iya kutaso muje gidan
me unguwa,na dauki lanbar wayar dayabayar,
gidan sa kuma hayine layin yandinki,dakyar
namike wayata tana ta ringi amma nakasa
dagata,nasan kawyenane dasukaga yaran,tin
kafin mutafi mkota dai shigowa suke suna mana
jaje gami da barka da arziki.
Munshiga gidan,sashin matar me unguwar, Mama
tana wasa,khausar da Al'amin suna ta zantuka
kasakasa,mukayi sallama yaran suka dubemu, da
karfi kausar tace Momy! Se rige rigen tahowa
gurina,na hadasu su ukun na rungumesu
jikina,inna kuka suma suna kka, duk mtanen
gurin suma kuka suke.nadauki Mama inna
kallonta,nadubi Iya cikin kunci
Nace, "dubi yarana yanda suka llce,"
Iya tace, "su da Allah sun cuci Kansu,menene
riba don ka cuci karamin yaro?" Nandai akayi abin
dayakamata muka dauki yara muka nufi gida.
Gidan cike da makota Sai barka da arziki
akeyimana,Allah yasa sunfada hannu nagari.har
lanbar direban na karba dan yimasa godiya ta
musamman sabida taimakon dayayimana.
Tini Habu yafesawa Yaya cewa abga su Khausar
anan Kaduna.Habu yabashi labarin komai,shi
kansa yasan tinda yarannna sukazo gurin iya dole
ya hakura dasu,amma yaji dadin ganinsu.yanufi
office dinsu yasa asaki Mujidat,ta fito tayi wujiga
wijiga, yace to bafa gidanshiba sai ta nemi gurin
zuwa,tace ina Abdul? Yace ai ba yaronkibane
yaronane na amshi dana.
Tace, "kana zaton dan ka boyemin Yaro zanki inje
infadawa iyayenka? ai dole su Sani."
Yace, "kekisani,saidai kisani zakikoma Kadunane
bayan kinkoma gidan Ubanki Lagos."
Aikuwa yasa aka kaita har garin da 'yan
kayanta,ko gani Abdul din ya hana tayi,yakaishi
gidan wani abokinsa a Asokoro.Mujidat ta
jinjinawa wulakancin da Aliyu Yayi mata,Amma
tace indai itace yaci Bashi,sannna tinda be
saketaba da sauki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya nufo kaduna cikin fargaba. Nikam na tsefe kan
yarana na wanne,akaje akayi musu kitso nayi
musu lalle. Munsha labarin irin wuyar da suka
sha a baki Khausar ni da iya, aikuwa munsha
kuka sabida tausayinsu.
Karfe uku ina zaune da 'Ya'yana cikin farinciki
inna yanke musu farce,Mama nakeyiwa magama
yiwa sauran.Khausar na dauke da Sadiq
tanayimasa wasa tace "Momy Sadiq dinki wallahi
dariya Yake yimin damun hada ido ya sannine?"
Nace, "kullum sainabashi labarinku, yasanku
dukkanku...."Sallamar yayace ya katsemu,sainaga
Khausar ta mike da gudu ta nufi daki Al'amin ma
yabita,Mamace kawai naga ta nufi Yaya tanamai
Oyoyo oyoyo,na hade raina tamkar zan saki
kuka,sanna na kauda kai nadauki wayata inna
latsawa. Yanufi cikin daki gurin iya, su Khausar
duk sun makale a bayanta tana Cewa, "lafiya
kuke boyewa?" Sai kuwa Yaya Yayi sallama,tsaki
Iya taja takasa amsa sallamar, yazauna tare da
sunkuyar dakai yace, "ina yini"
Ta kauda kai tace, "lafiya,"
Yace, "nazone inbada hakuri kan laifin danasan
za'a gani nawa,duk dacewa bansan fitarsuna
tinda ni bama na gida,laifin Mujidat ne kuma
nayi mata hukunci."
Iya tace, "can da matsalarku, sai dai abinda
zanfadamaka yarannan sunzo kenan,kuma abin
da kukayi musu Ku da Allahnku,"
Aliyu yace, "Dama ni bawai zan Koma dasubane."
Iya tace, "ai nazaci takardara sammaci kazo
kawomana." Ya mike yasake fadin aymin afuwa.
Ya dubi Khausar, "bazaku gaisheniba?"
Tace, "ina wuni Abba,"
Almin kuwa cewa Yayi, "mudai bazamu bikaba,"
Yace dama badaku zan tafiba.
Ya iso gurin su Khausar ya dauki Sadiq yafita.
Bai zaci zai samu sauki a guri Iyaba,yasandai
damuwar dama kar yakuma daukan yaran, kuma
dama ya yanke hukuncin barinsu fishintama na
yaune.
Yakira Usaman a waya suka gaisa samasama yace
,"Aboki kana gidane in iso ? Yunwa nake ji,gidan
su Iya kuma babu fuska."
Usaman yayi 'yar Dariya sannnan yace, "ka isa
gidan zan sameka a can."
Aliyu yace, "kayi nisane?"
"Inna Office din 'yansanda na nan unguwar."
Aliyu yace, "lafiya me kake a gurin?"
Usam yace, "wani dan case ne."
Aliyu yace, "shine bazaka sanar daniba, bari
inzo."
Ciki yakoma yamaida Sadiq, a cinyata ya ajiyeshi
ya fita,yana Isa office yansanda suka soma
kamewa suna sara masa, Oga yana ciki.
Agaban DPO yasmu yaron tare da Usama, DPO
ya mike ya kame sannan suka gaisa. Aliyu ya kalli
Usman, "Yaya, me yafaru aboki,"
Usaman yace, "irin yarannanne masu bude
account da Sunan mutane su kullamusu sharri."
Aliyu yace, "to shi wa yayi?"
Usma yace, "shine yayiwa Sadiya,"
Aliyu yace cikin sauri, "wace Sadiya,"
Usman yace,"wadda nake neman aurenta."
Kan Aliyu ya kulle yace, "dama zakayi aure?"
Yace, "Eh,bamuyi zancen dakaiba ko?"
Ya kalli yaron, "kasan Wannan?"Yanuna masa
Aliyu, yaron yace, "a'a,"
Daga nan Usman ya kalli DPO; "yanzu ni zan tafi "
Aliyu ya zauna, "bangane zaka tafiba, wai yaya
case din yafaru?"Nan aka umarci Jamilu yayi
bayani kamar yanda Yayi dazu.
Jamilu yace, "nidai wani yarone kanin Aunty
Ramatu ya kirani inzo zanyiwa wata Auntynsu
wani aiki,dama yana zuwa Cafe dinmu yana
Browsing, danazo sai tace inbudemata wasu
account guda biyu,zata yiwa kishiyarta sharri,
kawai Sai na yarda sabida ta yarda zata bani
Dubu5,nikuma dama inna neman dubu 5 din
sabida zanse JAMB Form dan shiga Jami'a.shine
nayi mata har yau kuma bata cikamin dubu
biyunba,sunma tashi daga garin."
Aliyu ya dinga kallon Jamilu tamkar yanason Yayi
tajin labarin kokuma labarin ya burgeshi. Usman
yace Jamilu sakamakon wanna hada Chat din
danayi nafada maka kasan aure yarabu? karaba
uwa da 'Ya'yanta? yanuna Aliyu Kaga mijinsu
nan,wadda kayiwa sharrin da wadda tasaka kayi
aikin."
Mamaki Yakama DOP yace, "Dama abin yafaru ne
a gidan Oga?"
Aliyu dai hannu a cikin aljihunsa yarasa me zaice,
Jamilu kuwa zubewa Yayi gban Aliyu yana
rokonshi cewa a yafemasa, shi dama wannanne
karo na farko da yasoma kuma bazai karba.Aliyu
yamike yakalli Jamilu, "Ayimaka hukunci daidai da
lefinka sabida masu hali irin naka." Har waje DPO
ya rako Aliyu, sam Yakasa magana sai zufa
yakeyi, zuciyarshi nata fadin kayi wauta.
Suna tafe shi da Usman shiru babu mai magana
saidai shi Usman ranshi Fes yaji dadi komai
yafaru a agaban Aliyu.
Koda sukaje gidan Usman din Aliyu Yakasa yin
tinanin komai,yamaji cewa yakoshi,duk da irin
yunwar dayakeji, idanunshi sunyi jazir.
Usman yace,"Aboki bisimillah"
Aliyu yace,"haba aboki, yakake tinanin zan iya cin
wani Abu a halin danake ciki? Don Allah kaima ka
ajiye muyi magana."
Usman Yayi murmushi, sannan yasake cika
cokalinshi ya tura baki yace, "wace magana
zamuyi."
"Ta Sadiya mana , gaskiya nayi wauta danaki
natsaya nayi bincike,kuma saida tace inbincika."
Abida dake jiyosu batasan sanda dariya ta
subucemataba, saidai taji Aliyu yana cewa "au!
dariyama nabaki Madam?"
Abida tace, "yanda kake maganar ne yabani
dariya."
Usman yace, "ai abin dariyarne,ni yanzu bazan
saka bakinaba cikin wannan lamarin, Sadiya
Alkawari nayimata zanyi bincike ingano masu
hannu cikin wannan lamarin kuma Allah ya
taimaka nasara tasamu,daga nanma sai can gidan
sabida insanar da ita,saikuma mudora daga inda
muka tsaya kan maganar auranmu."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yakalli Usman cikin tsananin bacin rai
yace,"kai nalurafa ba kasan kawaiciba ko?"
Usman yace, "kamar yaya?"
Aliyu yace, "wallahi dan kaine kunnuwana suka
jure jin kanacewa zaka auri Sadiya."
Yamike tsaye,"Wato damacan kanason matata tin
muna aure ko?"
Usman yace, "sam karkayi wannan tinanin,
hasalima ka manta kaine kabani shawara in
aureta lokacin danake lallabaka kamaida ita? Kace
ai bai haramtaba inna aureta, katuna? Shine
kawai mukayi shawara da Abinda,kuma
Alhamdulillah zance yasoma bisa...."
Aliyu ya harari Usman, sannan yaja tsaki yanufi
waje yanacewa, "Kadakatar da Neman aurenka."
Usman yace, "Sabida me?"
Aliyu wanda yakai bakin kofa, "najanye shawarar
dakace nabaka,inkuma kaki ji kada ka zargeni
akan abin dazaibiyo baya."
Usman yace ," aboki kazo muyi magana a zaune"
Tsaki Aliyu yayi tare da bugamusu kofa yayi
waje,ranshifa yayi zafi.,dama Habu yagayamishi
Usman ke zuwa gurinta duk kwana uku,saidai
sam bai tsammaci yanazuwa don sontabane.
Yashigo gidanmu inna shirin fita zuwa Isalamiyyar
'ya'yana tada domin inmaidasu, yanda naganshi
yashigo a sukwane nadan tsorata.yace, "ina iya?"
Nayi masa banza,yashiga daki tare da cewa, "zo
Sadiya!" Yayi maganarne cikin taushin murya.
Nashiga.
Yace, "Sadiya don Allah kinyafemin nayi
kuskure,ashe Mujidat ce duk ta kullamiki Wannan
Sharrin?"
Iya dake cikin daka tace, " Usman yakira waya
yayimana bayani yanzunnan,binciken da kakasayi
shi yayi kuma Allah yatoni asirinsu."
Aliyu yace,"Usman ai ba don Allah yayiba,yayine
don manufar kanshi,kuma wallahi Usman inbai
kiyayeniba za'ayi danyen aiki"."
Iya tace, "kai Gadanga da girmanaka kakeyin
wannan zancen,duk taimakon dayayi baka
ganiba?"
Aliyu yace, " Bansaniba". Yanunani.
"Kekuma zanfadamiki wallahi bake bashi."
Namike, "baruwanka da rayuwa ta don ni yafimin
kai."
Iya tace, "sau dubuma,kuma wallahi innaji wani
abu tsakaninka dashi Sai ranka yabaci,tsakaninka
dashi sai godiya."
Yace , "Iya matata fa yakeso,banda cin amana
yazaice yanason Sadiya?"
Nace, "Ok! Sabida bakasona shikenan kar kowa
yasoni ko?inkaga ban auri Usaman ba saidai
inbansoba kokuma shi yafasa....."
Ban ankaraba sainaga yatasomin zai
dokeni,nagudu nayi bayan iya innacewa, "Wayyo
Iya zai dokeni"
Yatsaya yana huci, "ni kike gayawa zaki auri
Usman?"
Iya tace , " tafada , hauka kake kadoketa?"
Yace, " inna tacigaba da yimin irin wanna zancen
bashakka zan jimata ciwo,kuma Usman zaisha
mamakin abin da zanyi masa."
Nace, "karkaga wani kana dansanda,inkatabashi
baza'a barka ba."
Yace, "kimin shiru,karkibari inzonan wallahi zan
ballaki." Yajuya fuuu! Yafice rai a bace.
Nasauke ajiyar zuciya,nace, "wallahi natsorata
ban manta da irin fishinnan ba,irinshi yayi lokacin
da akayimin wannan sharrin,jikinshi har rawa
yakeyi, Allah yatemakeni badan keba da yau naci
duka."
Iya tace, "tinanina yanzu Usman,ko kiranshi zakiyi
yanzu kicemasa inna nemansa?"
Nace , "to , bari inkirashi."
Tace "kishin banza ne ke cinsa a rai.
Nace , " Dama yabar Usman,danni ba auranshi
zanyi ba, na fadamasa hakane don kawai yaji
haushi.shima Usman din ina zaton dan yaturawa
Yaya Haushine yace yana sona."
Iya tace, "banda matar shi dake tsakanin ai
Usman mijine."
Daidai lokacin kiran yashiga, yadaga ,nace,"Yaya
Usman wai kazo inji Iya"
"Lafiya?" Cikin daga murya.
Nace "lafiya,kodai ba kalau ba."
"Ko Abokinane?"
Nace, "eh, ai yacene wai kace kana sona,a ina
yaji?"
Nina fadamasa,Kice iya karta damu, ni dashi
babu a binda zaifaru,nasan dama dole yayi
haka,ni dama hakan nakeso."
Nace, "to shikenan,sai anjima" nakalli iya bayan
nakashe wayar nace, "yace babu abinda za'a
faru." Nandai mukayi ta tattauna zancen.
Shikam yaya police yakoma yasake bincika Jamilu
ya tabbatar da gaskiyar lamari,sannana yawuce
Zuwa Abuja cikin damuwa. A daki ya kulle kan shi
yana tinanin tsantsar rashin kyautawar da yayiwa
Sadiya,baimasan ya zaiyiba.ya daga waya yakira
layin Usman har takatse yana kallo bai dagaba,a
karo na biyu ma saida takusa katsewa sannna ya
daga.
Aliyu yace, "Usama nakirakane ince kafita harkar
matata,zan dawo da Ita dakinta."
Usman yace, " innaki fa?kawai Mallam ka shiga
layi zawarawa nima inna ciki mai rabo
Yasamu,kuma banda abunka wannan baikamata
yashafi zumuncinmuba."
Aliyu yazo iya wuya,ranshi yakai matuka gurin
baci,yace, "ok! Haka kace? To shikenan kajira a
abin dazai faru." Yakashe wayar yanata kai kawo
a dakin,zuciyarshi tagama sakamasa abinda
zaiyi,kawai zuwa zaiyi yasa akama Usman, baza'a
fito dashiba har Sai anmaida auranshi da
Sadiya,inyaso saiyaga da wanda zaija.
Mujidat tasauka a garin kaduna kai tsaye
unguwar Mu'azu ta dosa,muna tsaka da cin
abinci kwanonmu daya da Yayana,tire ne dan
babba nazubamana,Danwake mukayi munaci
muna hira,Iya kuma tana gefe tanacin sauran
Tuwon Masara da Miyar Kuka.
Kwatsam sai mukaji sallama,zunbur namike ganin
Mujidat nace, "me kikazo yi gidanmu?"
Tace, "Ba gurinki nazoba,gurin sirikata nazo."
Iya tamike itama,"karki shigomin gida,juya."
Su Khausar kuwa tini sun ruga daki sun rufo
kofa,nace ," azzaluma kinje kin cutarmin da yara
duk da irin taimakon Dana yimiki."
Mujidat ta sheke da dariya sannan tace, "kikadai
taimaki mijinki,yanzu kuwa nazo na kwance kullin
da kukayi ke da mijinki."
Nace, "Ina ruwana,yanzu mijinkine ba
nawaba,inkinso ki tona,inkinso ki rufa."
Iya kawai ta tsaya tana kallonmu tare da sonjin
asirin da ake cewa za'a tona."
Mujidat ta kalli Iya tace, " Tsohuwar ba zama
nazo ba, nazone in fadamiki gaskiya tsakanina da
danki."
Gabana yashiga faduwa,tamkar in tashi in toshe
bakinta kar ta sanar da Iya taji bacin rai,banason
'ya'yana suji abin da ubansu yayi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mujidat tace, "Danki Aliyu ciki yayimin tin a
Ilori,yace inna yarda dashi zai aureni.Yayi min ciki
ya taho, nikuma na biyoshi,shine sukace inyi
shiru kar ince haka zasuce mijinane ya mutu
yabanni da ciki,kisani Abdul jikankine."
Na kalli Iya wadda takasa magana, na iso gurin ta
na kamata nace, "Iya zauna karki damu."
Iya ta fincike hannuwanta tace,"Sakar min
hannu."
Ta nuna mujidat "fita tinda kinfadi sakonki."
Mujidat tace,"Yanzu kuwa zan tafi burina yacika
tinda kinsani."
Nace , "To me yadame mu? Saiki fita ai ko?"
Ta saka dariya, kidena min korar kare,domin ko
bana auren yayanki uban 'Ya'yanki inna da yaro
daku."
Nace, "naji jeki."
Kafin insake magana Iya ta isa bango ta dafa,na
isa gurin ta,sannan nadauki wayarta na kira Yaya
Usman , nacemasa, "dan Allah kazo in kana
kusa,Mujidat tazo ta dagawa iya hankali."
A zaton ta Yaya Aliyu nakira,don haka saitafice da
sauri.Allah yasa Yaya Usman yana kusa ya iso
mukayi ta bata baki. Tace, " Ashe dake za'a hada
baki a rufeni?"
Nace, " Iya kiyi hakuri, alokacin ko anfadamiki
babu abinda hakan zai kareki dashi sai bacin rai."
Usman yace, " Iya lokacin abin da zaifaru yariga
yafaru."
Sai ga hawaye yasoma zuba daga idanunta, tace,
"Wato shi Aliyu ko yaushe shi zaidinga sani zubar
da hawaye "
Usman yace , "sai hakuri iya"
"Nagaji da hakuri da laifukan da Yake
aikatamin,ya batawa zuri'a ta suna,ya
gurbatamin zuru'a yabani mamaki."
Kukana ya tsananta,nace, "Iya kiyafemasa."
Tace,"kema ai a gurina me laifice balleshi,kike
cemin inyafemasa."
Usman yaciro wayarsa yakira laying Aliyu, lokacin
yagama shirya yanda zaisa a kama masa Usman
din domin bazai yuwu a kamoshi batare da wani
laifiba,dolene a nemi laifin da za'a
joganamasa,kamar kada yadaga layin, saikuma
yadaga cikin isa yace.
"Malam Lafiya?"
Usam yace, "kana inane yanzun?"
Cikin jin haushi yace, "menene kake son jin inda
nake? Innaso fa ka manta kasan ni."
Yace, "kafin in manta nasanka din kazo ga
matarka nan tazo ta kunce kullun da Kuke ta
boyonsa yanzu haka Asibiti zamu kai Iya."
Tace, "daina kiransa Usman, na yafeshi cikin
Yayana,ya nemi wata uwar shi ba zuri'a ta
bane..." Ta fashe da wani kuka mai ban tausayi.
Aliyu duk yaji wadannan kalaman dama wasu,don
Usman sam ya manta bai kashe wayar ba,sabida
wata irin sheshsheka da Iya tasoma.
Yace, "Sadiya dakko mayafinki da nata muje
Asibiti."
Ta dakko,suka kama iya zuwa Mota.
Sai da Sadiya tace zamu bar yaranne ? Sai yaciro
wayar tare dacewa, "bari inkira Abida tazo ta
kwashesu," a lokacinne yaga bai kasheba don
haka sai yakashe,sannna yasake kiran Abida.
Aliyu yanata kai kawo cikin ofishinsa gumi yajika
rigarsa sharkaf,ya balle duk botiran gaban
rigarsa, ana kallon singiletinsa,Sam bazakace da
Akwai AC a cikiba.
Kiran wayane yasashi isa gurin
wayar,kawimishinane ke nemansa wai zasuyi
wani dan meeting, a isa ofishin yana balle botiran
gaban rigarsa,sai kwamishinan yabukaci daya
zauna.
Bayan ya zauna be suka gaisa da sauran
mutanen daya gani ciki,fuskarsu ba boyayyabace
'yan siyasane na gwamnati me ci a wannna
lokacin,wasu masu neman tazarce wasu kuma
masu son sababbin mukamai.Aliyu fa ya hade rai
sabida ya lura 'yan siyasan nanfa sun raina
jami'an tsaro.
Wanda suka wakilta yayi magana shine ya
gabatar da kudirinsu na Neman goyon baya daga
jami'an tsaro,su zama suna bangarensu.
Kwamishina ya kalli Aliyu tare da bashi izinin
magana.
Aliyu cikin isa yace, "Ranka ya dade mu ba 'yan
siyasa bane,bazaiyuwu mu cusa kanmu cikin
harkar siyasaba,mu jami'an tsarone dole yazama
muna tare da kowa ku da 'yan adawarku,bai
kamata gwamnati maici dan kawai tana ganin
tanada madafan ikon a hannunta tayi anfani da
hakan gurin tursasamuba,mun San aikinmu,kuma
inshaAllahu in zabe yazo zamu tsay kai da fata
ayi zabe a gama lafiya.......zandakata anan
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Darajar Yayana4-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:27 PM, 16-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Wakilin siyasa yace, " amma mu muke daku tinda
muke da gwamnati." Ya kalli kwamishina.
"Ranka ya dade kai yakamata kace wani
abu,sabida wannan mataimakin naka ya nuna
karara baya tare damu."
Yace,"zantukanshi suna kan hanaya,sai dai
zamuga taimakon da zamuyi muku."
Sai suka mike tsaye suna zantuka,wani harda
Cewa, " kujerarku tana rawa,domin kunsan akwai
nasama daku,kuma su namune inkunce Ku ba
namu bane."
Aliyu ya lumshe Ido,baiyi wani mamakiba domin
yasan su basu da wani buri sai son kansu,amma
indai yana nan da yardar Allah sai ya hana
ruwansu gudu,zai dawo da martabar 'yan sanda.
Bayan tafiyarsu kwamishina ya kalli Aliyu yace,
"kamin dai-dai,shiyasa nakiraka."
Gida Aliyu yanufa,sintiri yakeyi tare da kai kawo
daga falo zuwa dakinshi,yarasa ta ina zaibi kuma
wa zaikira yabashi shawara? Yazauna yaciro
wayarshi yanabin lanbobin daya bayan daya
yanason yaga wa yakamata ya canja abokin
shawara madadin Usman. Yaduba har karshe
baisamuba,wata zuciyar tace dole dai Usman ne
zaibaka shawarar data dace.
Tsaki yaja,sannan yabi shawarar zuciyarsa
yasoma kiran layin Usman,duk dacewa shi yafi
tsana a halin yanzu.Ringing biyu Usamna ya
dauka,yace,"Aboki ya akayi?"
Cikin tsana yace,"bawani zancen
Aboki,nakirakane inji ya jikin mahaifiyata?"
Yace,"da sauki,amma zaifi kyau kazo kadubata."
Yaja tsaki ,"bayan kaje ka shishshige a gurinta
don tabaka matata."
Usaman yasa dariya,"Aboki ka aje kishi a gefe
guda,muyi magana me muhimmanci, Sadiya
allurace cikin ruwa,kaga kenan me rabo
kadauka."
Aliyu ya runtse ido,jiyake maganganun Usman na
sukarsa cikin rai,amma dayake shawara yake
bukata sai ya danne yace, "InshaAllahu matatace
ni Daya." Yacigaba da Cewa.
"Kana ganin inzo gurin ta ko Yaya?"
Yace,"zaufi kyau kazo din don kabata hakuri."
Yace, "kana ganin inzo yau ko gobe?"
"Kabari sai jibima,domin lokacin ta dan huce," inji
Usaman.
Aliyu yace, "to shikenan zamudinga yin waya."
Iya ta tara sauran 'ya'yanata tafadamusu abinda
Aliyu yayi,kuma tace musu ba'ita babu
shi,tacireshi daga sahun 'ya'yanta,nima da kyar
na wanke kaina daga zargin datakemin wai na
rufeta.
Yaya Sulaiman yakira Aliyu yamasa Nasiha kan
abin da yayi,Aliyu yabashi labarin yanda
abubuwan suka faru,yakuma yimasa rantsuwar
cewa yanzuma yadena.Yaya Sulaiman Yayi masa
fadan girma sannan yace yaje yanemi iya
gafara,don tadau zafi dayawa.Kwananmu Daya a
asibita aka sallamemu,Yaya Usman da sauran
'ya'yanta sunbata kulawar data kamata.
Na idar da Sallar La'asar na nufi kitchen domin
dafawa Iya wake da Alayyahu sai naji sallamar
Yaya, na amsa amma ba lallai yajiba,bankuma
kalleshiba nacigaba da harkar gabana.Bakin
kitchen din yazo ya tsaya,kamshin turarensa
yacika kitchen din,nakalleshi cikin tsana.
"Lafiya?"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace, "in ina cikin damuwa da nakalleki sai inji ta
yaye."
Naja tsaki, "dan Allah kabani guri kaje kaji da
kalubalen da yake gabanka."
Yace, "Don Allah kitayani bawa iya hakuri nasan
zaki iya shawo kanta."
Nace, "eh, dama bakasan daniba sai matsala ta
sameka wadda kake ganin nice zan iya yima
maganinta." Najuya baya.
"Malam kaje da matsalarka,Yanzu ni babu wata
alaka tsakaninmu dazan iya yimaka wannana
arzikin.jeka da kanka,innace mahaifiyarkace?"
Ya tausasa murya, "Don Allah kizo muje innason
muyi zancen gabadayane harda batun auranmu."
Naji tamkar ya watsamin wuta,Nace,"Allah ya
kyautamin,." Naja tsaki tankashima bata
lokacine,don haka yagaji da surutunsa da
banbakinsa ya kyaleni.
Inna jiyoshi yanatayiwa iya magana tayi banza
dashi,nasaka kujera bakin kofa na zauna,yayi ta
bata hakuri,amma kala bataceba,sai datagaji
sannan tace, "Don Allah kafitar min daga gida,
Innaso insanar dakai tini nacireka daga sahun
'ya'yana, bana koson ganknka."
Yace, Don Allah iya kiyi haku...."
Ta katseshi, " inkanaso inyimaka baki to kacigaba
da zama a cikin dakinnan "
Tsam yamike yafito yanufi waje cikin damuwa,
baifi minti 5 da fitaba yayomin text wai in yara
sun dawo daga Islamiyya inshiryasu zasuje shan
Ice cream,tsaki naja na aje wayar gefe.
Shida da mintina,suna shigowa yana shigowa,
saikace dama yana wajen yana jiransu,jin
muryarshi duk yaran sukaje suka makalkaleshi
harda Sadeq dake koyon rarrafe,sai daga hannu
yake wai dole yagane babansa.Ina Mamakin
yaron.
Yace, "kuje kucire kayan makaranta kuxo muje
shan Ice cream." Yarannan sai suka hau murna
da tsalle.
Khausar ta nufi iya tana murna tana cewa, "Iya
zamu fita da babanmu."
Wata tsawa da iya tayiwa Khausar ni kaina saida
na tsorata,tace,"Ku tashi sama mana da Baban
naku me yadameni?"
Karshe dai da kayan makaranta ya tattarasu suka
tafi harda Sadeeq.
SaKu ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347i Tara saura suka
dawo,lokacin sadiq yayi bacci,ni da iya wai har
tsaraba yayimana don neman gindin zama.
Yanda iya bata kalli ledarba, haka nima nayi
saida Iya tafita sannan nace dasu Khausar Su
dauka su hada datasu.
A daren ne Alhajin nan yasake zuwa karo na
uku,biyun ban fitaba,nace ace bana nan,Amma
yau sainafita sabida nasan Yaya yana
nan,tayiwu yazo zanso ya ganmu. Kwalliya nayi
sosai, sannan nafita.
Cikin wata dankareriyar Mota yazo sai kamshi
Yake,na kwankwasa motar sai gashi yafito daga
gidan baya yace, "ranki ya dade yau dai naci
sa'ar samunki,amma naji Dadi."
Nayi murmushi sannna na rage tsawo nace, 'ina
yini?"
Yace, "Lafiya kalau," Bayan mungaisa yace,
"Mama tana ciki?"
Nace, "Eh"
"Inna son mugaisa."
Tofa!,bani da zabi,dole saidai inkaishi din.
Na shiga nagayawa Iya za'a shigo gaidata,tace,
"toh"
A gaban iya yazube ya gaisheta,itako Iya harda
fadamasa cewa; ni marainiyace,dan Allah in
aure ya hadamu yarikemata ni amana, saboda
na wahala a gurin mijina na farko,shi kam sai
yace ,yaji komai game dani, tinda ya ganni
yasan innada tarbiyya sabida naki yarda inhau
motarshi, mata yanzu da zakaga suna tare mota
da kansu wai dan a ragemusu hanya! Yacigaba
da cewa, "Sai danasa akaimin bincike akanta,
kuma naji sakamako me kyau don haka nashigo
da karfina zan aureta."
Iya