Showing 18001 words to 20506 words out of 20506 words

Chapter 7 - Darajar Yayana Book 4 end complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt

antilomana wasu yansanda wai masu
tsaron lafiyarmu.
Tinda Yasamu wannan matsayin saikuma
ganinshi yayi wuya,baya zuwa gida ya kwana
kamar da, sai da daddare jefi-jefi yazo yagaida
iya yatafi. Hidima kuwa baifasaba, saima karawa
da yayi. 'Ya'yansa yana aikowa a daukesu ranar
da babu makaranta su yini can, ko zama yakeyi
dasu, komenene bantaba tanbayarsuba.
Daidai wannan lokacin na yaye Sadiq, kuma
muka tsaida lokacin aurenmu. A lissafi yau saura
kwana ashirin da takwas,inna ta shiryeshiryen
gyara jikina da duk wani abu nasha wanda zan
rike mijina,dan kuwa Aunty Abida zugani kawai
takeyi indage innada kishiyoyi,cikin dan lokacin
ni dakaina nasan nayi zam-zam.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Direban dake zuwa daukan yara yakaisu gun
Babansu nagani tsaye nadawo daga makaranta
yace, "Madam ance in kaiki Gida."
Nace, "Inji wa?"
Yace, "inji mai gida,"
Tsaki naja nace, "bazanjeba."
Kasancewar layin shiru sai tsoro yakamani, yace,
"Kishiga kawai da arziki Madam, sabida kalli
can." Yanunamin Karshen titin, motar
'yansandace. Yacigaba dacewa.
"Zasu daukeki da tsiya."
Nace, "ai da kukuke kaini gidan?"
Yace, "Umarni akabamu daga yau, shiga muje
kawai."
Nace, "Innakifa?"
"Hakuri zakiyi ranki ya dade,sabida kare
lafiyarkine." Nace, "Allah ke Kare lafiya ta."
Yace, "To kitemakeni kar inrasa aikina." Cikin
muryar tausayi yayi maganar.
Nace, "zanshigane don aikin naka,amma badan
isar wanda yaturokaba. Yace, " Nagode ranki ya
dade."
Tinda muka hau titi 'yansandannan suka
dafemana baya, haushi duk ya isheni. Munyi
tafiya me tsayi kafin na fahimci cewa ba a
hanyar gidanmu muke tafiyaba, Nace, "ina zaka
kaini?"
"Gida mana."
Daidai lokacin naga munsha wani round about,
kafin nasake magana muka shiga wani layi muka
hari wani babban gate, Nace, "Mallam ina zaka
kainine?" Yansanda dake kofar gidan suka bude
muka shiga.
Gidan yanada dogayen bishiyoyi, dankuwa
girman gidan bazan iya musaltashiba,inna cikin
motar naki fitowa, wayata tasoma ringing,
Bansan lambarba, na daga, muryar Yaya naji
yanacewa.
"Karki zubar da kimata kishigo magana zamuyi
kitafi abinki."
Ban musaba nabi bayan direban kamar yanda
ya bukata. Cikin wani kayataccen falo nasameshi
Zaune kan kujera daya daga kujerun falon na
Alfarma, Laptop ce a kan wani tebur a gabanshi
yana latse latse.jikinshi sanye da wata shadda
ruwan kasa wadda haske da kyanta suka tona
asirin tsadarta,kamshinsa na yau da kullum
yacika gurin.
Batare da yadubeniba yanunamin kujera da
hannunsa Yace min cikin harshen turanci,
"Zauna." Ba musu na zauna, saidai raina a bace
Yake, Jira nake yayi magana insoma zubar da
bala'i.
Yanata danne dannenshi, na dubi agogon dake
falon nace, " Gaskiya innada abinyi, innason
intafi."
Ya dago ya dubeni kibani minti uku kacal in
kammala muhimmin aikina."
Naja tsaki tare da kauda kai. Wayata tayi
ringing, nadauka A'isha ce,nace, "ya akayi?"
Tace, "ga Humra ankawo me kyau," nace, "cikon
nawa zanbada?" Tace, "dubu ukune, namabada,
dama gudun mowar dazanbakine."
Nace, "a'a A'isha zanbaki kudinki, nasanfa
yanayin garin."
Tace, "Kin raina kenan?"
Nayi 'yar dariya, "wallahi ni banrainaba Nagode
Allah yabar zumunci, zanfadawa Alhaji
kokarinki." Mukasa dariya.
Tace, "kina inane?"
"Oho! Ni banmasan inda nakeba, kibari
innakoma gidazamuyi zancen."
Na kalli agogo, minti ukun tacika, yature na'ura
me kwakwalwar dake gabansa yamike a hankali
yazago gefen danake, kafafunsa babu takalmi.
Yazauna a kujerar dake daf dani ya karkato.
"Sadiya!" Yakira sunana cikin lallausar muryarsa,
nasake tsuke fuska, yacigaba.
"Sadiya meyasa kika zabi ki auri wanina? Bayan
nasan cewa ni kikeso"
Da sauri nace , "a daba, lokacin da bansan inda
kemin ciwoba,amma yanzu gaskiya bana wani
sonka."
Yayi dariyar yake, "nasan kinfadane amma in
gaskene ki kalli cikin Idona kice bakyasona."
Cike da rashin kunya na kalli idonshi, "Aliyu
bana sonka, bana kaunar......"
Yadagamin hannu tare da rintse ido , " naji
nayarda bakyasona,amma kiduba wasu
abubuwa. Nafarko, 'ya'yan dake tsakaninmu,
kinfiso kije ki kula da nawasu kibar naki? Bansan
wace mata zan auroba, ke nifa tinda Mujudat ta
wahakar da yarana na janye batun aure indai
bakebace."
Nace, "wannna ra'aynka kenan, ni nawa ra'ayin
na auri wanda yasan kimata da darajata, wanda
zaimin adalci akan komai."
Yace, "Sadiya dan Allah kitaimakamini, wallahi
inna sonki, haka zaki tafi gurin wani kibarni?
Kinsandai yanayina kullum cikin Azumi nake,
sabida tsoron fadawa barna."
Nace, Aliyu kayi hakuri, kanemi wata, gaskiya
bana sonka,tini kagama fita daga raina."
Namike.
Sai kawai naga yazube gwiwoyinshi a kasa,
"Sadiya kitaimakeni bandamu cewa kowa
yaganni a gaban ki a hakaba, indai zaki amince.
Sadiya inkincire soyayyar Allah da manzonsa, sai
mahaifiyata kece kike bayanta, don Allah
kitaimakeni kisake bani dama, zanrikeki da kyau,
namiki alkawarin zanzama tamkar bawanki."
Nace, " kai bame cika alkawaribane, akwai
alkawurra dakayimin tun a baya wadanda baka
cikaba, nifa gaskiya banajin zan kara rayuwa irin
ta aure da kai, muyi zumunci kawai na 'yan
uwantaka."
Sainaga kwalla tasoma sakkowa daga idanunshi,
ya mike tare da juyamin baya, "
Matsayina,mukamina da Shekaruna duk na
karyardasu na durkusa miki, amma kin kunyatar
dasu."
Nace, "Kaine kaja."
Ya isa kan tebur yaciro tissue ya goge
hawayenshi, yadaga waya yakira direban, ya
dubeshi, "kaita gida." Na mike na fuce, sam
banji tausayinsaba ko kadan a cikin raina.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shi kuwa sintiri ya dinga yi cikin falon cikin
tsananin damuwa, duk yanda yazaci zaisha kan
Sadiya abin yaci tira, saidai bayajin zai iya
hakura da ita. Zumbur ya mike yayi hanyar fita
yakira direbansa, yasa takalmi da Hula ya debi
kudi ya zuba s cikin aljihu yafita.
Zari'a yanufa, yaci sa'ar samun Baba a gida.
Suka gaisa, Baba yayi ta murna da zuwan Aliyu,
'yan uwansa sukazo suna kara yimasa godiya
game da aikin hajjin da sukayo, Aliyu yace
bakomai. Yakalli Baba yace "Baba dama nazone
in nemi wata alfarma a gurinka."
Yace, "Kamar mefa?"
Yace, "Innson in maida Sadiya mu rike yaranmu,
nabi ta iya, yarinyar kuwa har durkusawa nayi a
gabanta amma taki."
Ya karonto masa irin azabar da yaran sukasha a
hannun Mujidat, da matsalolin da suka shiga
sakamakon rashin kasancewarsu tsakanin uwa
da Uba, har yanda Mujidat ta shiga harkar
banza da irin kamun da yayi mata, yakara da
cewa, " nayi mata saki biyu, don na tanbayi
malamai sunce yin uku babu kyau."
Baba yace, "dama kanason maidata kayi shiru
aka karbi batun wani? Amma kabari InshaAllahu
dakai za'ayi domin dama ni mutuminnan bai
kwantamin a raiba, saboda bai taba zuwa
yagaisheniba, tinda yaturo wakilabsa, bawai inna
neman wani abun hannunsa bane, amma mai
son auren yarka yakamata yakawo kansa
gurinka ku gaisa, kodon haduwa a hanya.
Karkadamu kakoma zanzo gidan gobe."
Aliyu yacikasu da kudi yatafi zuciya fal murna.
Nikam inna ta shirina, iyace kurum me tayani,
amma Khausar ko zancen bataso.
Washegari Lahadice, inna kwance daki yara suna
hadda, najiyo muryar Baba cikin Falo, sama
sama yake magana, nafito da sauri nashigo
falon, daidai lokacin dayake cewa.
"Don ni indai ni na haifi Sadiya to takoma gidan
mijinta shine albarkata, ta rike yaranta, ai
banzaci yana ta bintaba da yaushe zan amshi
batun wani, wanda ma ban isa yazo
yagaidaniba, matsayin mahaifinta."
Cikin sauri na zube gabanshi, "Baba wallahi
dama gobe zamuje yagaidaka."
Iya tace, "nima zanfiso suna tare da 'yan
yaransu, amma Aliyu yasaki damarsa tin farko,
don haka ni duk abinda Sadiya takeso nima
innasonshi,"
Na mike nakara kusanto Baba, "don Allah Baba
ka taimaka."
Yace, "inni na haifeki to kikoma kirike yaranki."
Ya mike.
"Ranar da akasa ta auranki babu fashi, amma
da Aliyu za'a daura."
Na kalli Iya, "kinfayi rantsuwa akan bazan
komaba."
Iya tace, "Mahaifinki ya nuna ikonshi natsaya
inyi ta jayayya? In takasance yanda yakeso zanyi
azumin kaffara guda uku."
Fuuu! Nayi daki,wato iya madai danta takeso
baniba. Nakira Aunty Abida a waya inna kuka na
fadamata, nace yanzu anyimin adalci kenan?
Tace, "Eh!, wannan shine adalcin, ki zauna ki
rike yaranki shine daidai, kiyi hakuri da rayuwa
duk inda kikaje shine jagoran zama ballanatana
tsakanin kishiyoyi ." itama na kashe waya kafin
takarasa abindatake cewa. Bankira Ayshaba dan
nasan ita yar partyn Aliyu ce.
Na kira Alhaji inna fadamasa cewa Aliyu yaje ya
zuga Babana bansan me yafada masaba. Sai
kawai mukaga yazo wai inkoma gidana.yayi shiru
yanaji har nagama,bayan kusan minti biyu
sannan yace, "Shikenan Allah yasa haka shine
mafi alkahairi." Nasaka sabon kuka , "Haka
zakace kaima? Dama ba sona kakeba?"
Yace, "Inna sonki mana, ammafa ni ba yaro
bane da zan tsaya inna jayayya, sannana tini
jikina ke bani gidanki zaki koma, Allah yasa haka
shine mafi alkhairi."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ranar yini nayi kuka har yara suka dawo,
Khausar da Al'amin suka tsareni da tanbaya ,
haushinshi yasani jin haushinsu suma, nace, "Ku
fita ko inyu muku dukan tsiya," suka fita sukaje
suna tanbayar Iya.
Iya tace, "wai dan kakanku na Zariya yazo yace
takoma gidan Babanku." Sai iya taga yara sun
soma murna, Khausar me wayon tsiya sai ta
saci wayar iya ta nufi dakinsu ta kira layin
Babansu, Cikin murna tace, "Abba innayimaka
murna, ashe Momy zata dawo gidan ka?"
Yace, "Eh, Babyna. Ina Maman naku yanzu?"
Tace, "gatacan daki tana kuka,dan Allah kada ka
karayimata abinda zaisa kuyi rigima."
Yace, " To Khausar zan kiyaye, kije ki lallasheta,"
Tace, "To." Tana aje wayar yayi murmushi,
yarinya yar shekara tara da rabi wayonta kamar
na manya.
Yashigo, "Momy inji Abba wai yana gaisheki,yace
kiyi hakuri kidena kuka."Tsawa na dakamata ta
tashi, ga mamakina sai naga tana dariya.
Cikin dare naga sakonsa, wai: Saura sati uku ko?
Nakosa inrike lallausan hannunki, My choice ya
kike ganin darenmu na farko zai kasance? Inna
jiran amsa.
Tsaki naja na goge sakon.
Shida na safe naki tashi infita,sabida inna fishi
da kowa na gidan, wayata tasoma ruru na duba,
koda banyi saving number shiba nasan yayane,
don haka naki dagawa. Kiranshi goma inna
lissafawa, sannana sako yashigo.
My choice kiyimin addu'a zantafi wani daji
dakaina zan jagoranci yarana don cafke wasu
barayin dana gano suna tare da tsohon
kwamishinan da aka canza daga Kaduna.
Nafadamikine ba dan wani abuba sai dan kila
bazan dawo ba, nafitane a bakin raina.
Shiru nayi, dan kalaman sun tsirka zuciyata
kadan, amma duk da haka sai na tabe baki na
ture wayar.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tamkar almara karfe goman dare na jiyo muryar
Usman a dakin iya, can sai naji tana salati na
fito ina tambayarta lafiya? Tace, "Aliyu ne wai
yan fashi sukai masa harbi uku, amma dai anyi
nasarar kama wasu, sannan aka harbe wasu."
Take zan tukan da ya turo min dazu da safe
suka fado min, na zauna kan kujera nace, "Iya
yanzu yana ina?" Usman yace, "an tafi dashi
Abuja babban asibiti."
Kai gaskiya hankalina yayi mutukar tashi, cikin
daren nayi ta kuka amma bazance ga dalilin
kukanaba.
Washe gari su Usman da sauran yayyanmu su
yaya Sulaiman suka kwana acan sannan suka
dawo, sunce an cire masa harsashin amma ba'a
bari ma anganshiba saboda tsaro. bance
zanjeba amma zuciyata tana can. Satin shi daya
iya ta matsa zataje ta dubo shi, ya samu sauki
sosai sannan hankalin iya ya kwanta.
Data dawo nace, "ya jikin?"
Tace "da sauki,ana dai bashi kulawa ne."
Nace, "masha Allah."
Ban ko kirashi ta waya ince ya jiki ba harya
dawo gida, satinshi biyu da kwana biyu wanda
ya rage saura kwana biyar aurenmu, nan gidan
aka kawo shi can shashinshi. Su Baba Hauwa
sunzo duba shi shine yake bata labarin ban taba
ce masa ya jiki ba, tazo tana yi min fada. Su
Abinda da Aisha kuwa gaba suka dauka dani. Iya
dai bata taba ce min inje ba niko zuciyata ta
kekashene ina saran zaice ya fasa tunda na
nuna masa kiyayya karara.
Washe garine ya tako zuwa ban garen mu ina
zaune a falo ina kallon T.V ya shigo, yadan rame
kuma yayi haske, yace, "ina kwana?" Na kalle
shi cikin jin kunya nace, "lafiya, ya jiki?" Yace,
"au ashe kinji, koda yake nasan kinso ace na
mutu ko?"
Nace, "duk wanda lokacinsa ya yi babu kari,
harni din." Bai sake magana ba ya shige wajen
iya, ina jiyo muryar ta tana cewa na zaci za'a
daga bikinne,shi kuma ya ce a'a jiya su Yaya
Sulaiman sunje Zaria sunyi magana da Baba,
sunkai sadaki ya ce yau zaizo gurinki
Tace, "to Allah yasa albarka," wani abin haushi
wai ashe ya ba Usman sun hado min setin
akwatuna cike da kaya masu tsada harda yara
duka, nidai ina ta kallon ikon Allah za'a yimin
auren dole.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ranar daurin aure kuwa kwanciya nayi abina,
gida cike da dangi, su A'isha suna tamin tsiya
wai inaso ina kaiwa kasuwa, jin haka naki
wanka, sai dare nayi wanka dan naji iska. Ina
sallar isha'i sai gasu Baba Hauwa tace, wai na
fito a kaini gidan mijina, sai da nai kuka mai
isata sannan na fita, wai inje gurin iya taimin
fada, "nace ba zuwan da zanyi, ni yanzu meye
ban sani ba sai kace wata yarinya? bayan itama
Iyan ta daina sona." Ashe Iya tana jina sai
kurum tace, "ni dai da kike fishi dani Allah ya
bada sa'a, fadan ku da Aliyu ba'a shiga kwanan
nan za'a jiku shuru." Haushi ya sake kama ni na
saka sabon kuka, dan wulakancin sai aka samin
dariya.
Gidan shi aka kaini, dakina yayi kyau mutuka,
sai dai ba kayan gadon dana zaba bane
wadannan sunfi su kyau da tsada. Sha biyu ya
shigo dakin, cikin fushi nace, "indai kana wa
girman Allah ka fita in kuma nizan fita to in
fita." Sai yace, "Asuba ta gari."
Tin daga ranar bai sake shigowa daki naba,
kullum shine yake min magana amma bana
kulashi. Ya siyo wannan ya siyo wan can inya fita
zai kirani yafi sau biyar naki dagawa.
Satina biyu ya debo yara, niko yaranma Sadiq
kurum nake kulawa kuma yaki zama shi sai
gurin Iya, nace a sauka lafiya, itama Iyan ta
sami dan tayin hira tunda ita daya ce, danma
da masu aik.
Ranar wata Alhamis ina xaune bayan isha kusan
tara saura Khausar ta shigo, "momy kizo inji
Abbammu yana dakinsa," nadanyi shuru nasan
ya hada da Khausar ne dan yasha kirana kullum
dare ta waya inki zuwa, ta zauna bakin gado,
"Momy yace kije fa," ta katse min tunani, nace,
"ke karki dame ni, kije zanje," data fita taga
shuru ban fito ba sai ta shigo da takardunta
tahau tsakiyar gado na wai zatayi home work,
nace in gani in tai maka miki tace, "a'a kije Abba
na kiranki ko kinje?" Dole tasa na mike, acikin
dakunan bansan wannene dakinsa ba sai da
Abdul ya fito nace inane dakin Abba? ya nuna
min nace meya fito dakai yace ina neman yaya
Khausar ne bata yimin Home Work ba, nace ka
shiga dakina. Na murda kofar dakin ta bude na
shiga yana sanye da jallabiya mai gajeran hannu
kamshi da sanyin A.C suka buge ni na ji sanyi
yana ratsani sabida yanayin sanyinne ake ciki
nace "lafiya?" Yace, "Shigo mana ciki," Na shiga
tare da maida kofa na rufe, ya tako ya kama
hannuna ya zaunar dani a bakin gado shima ya
zauna ya lalubo hannuna ya matse cikin nasa ya
sauke wata irin ajiyar zuciya, na kalli fuskarshi
idon shi a lumshe, Yaya mutum ne da yayi dai
dai da kowanne zamani yana da kyau abin son
kowacce mace amma ni sam bana jin sonsa a
zuciyata, ya bude ya kalli cikin ida nuna, "nasan
kin tsaneni koh?" Nima na cigaba da kallon cikin
idanunshi, wata siririyar kwalla ce naga ta taru a
cikin idanunsa yace, "duk da haka ina neman
alfarma ki bani hakkina,wallahi ina cikin wani
hali sai dai bazan matsa mikiba, babu matsala
in kinga cewar da takura kije abinki karki damu
kiyi baccinki," nayi shiru ban motsaba, ya cire
hijabin jikina, rigar baccina ta bayyana, Sky blue
ce mai santsi, ya soma shafa min gashin kaina
hawaye suka soma zubo min, bansan ko na
menene ba,sai na tsinci labbansa saman nawa,
jikinsa kuwa bari yake sai kace tsohon daya
dauki budurwa, ni kaina ban san ina muradi ba
saida abubuwa sukai nisa. ranar dai mun kwana
muna aikin lada cikin wata duniya da masu
auren sunna ne kurum suka santa.
Wannan karon yaya bai dauki al'amarina da
wasaba, ji yake dani kamar yar yaye Ko laifi
nayi baya yi min fada, inna ce ina son abu baya
ja ko aiki da nake nace zan daina yace a'a in
kina son dai nawa na daina jayayya dake, nace
to zan daina dan dan nasan bakaso, yace
nagode.
Haka nan tun ina dari dari da shi na saki jikina
da shi nima ina nuna masa kulawa, zamammu
yafi na farkon aurenmu, 'ya'yanmu sun
warware, damuwarsu ta yaye, sun ganmu a tare
cikin aminci sun zama cikin farin ciki da walwala
karkashin kulawarmu.
Wurin shi na sami labarin Mujidat ba lafiya tana
asibiti wai bata rike kashi da fitsari, yace, "kinga
illar zina da Luwadi ko?" Nace, "Allah ya bata
lafiya," yace, "yanda nake samin labari gwara
mutuwarta da rayuwarta, Allah yasa mufi karfin
zuciyarmu." Nace, "ameen ya rabbi........"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tammat bi hamdullahi taku Halima Abdullahi k/
mashi kecewa kusaurari littafinta na gaba,
SAUYIN RAYUWA........
Alhamdulillah yaudai cikin ikon Allah gamu
mumkawo karshen wannan labarin da muka dau
tsahon lokaci muna yi, fatan zamu anfani da
dukkanin anfanin da yake ciki sannna mu kiyayi
kusakuran cikinsa. Inna neman afuwarku idan
na sabawa daidaikunku kokuma jamhuri.
Nagode sai kunji daga gareni.


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login