Showing 9001 words to 12000 words out of 20457 words
Chapter 4 - MAITAR IDO COMPELET DOCUMENT BOOK By Mrs Sadauki .txt
waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai.
Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama.
Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki.
#GIDAN ANTY HINDA
Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke.
Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi”
Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ”
“Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi”
Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa.
Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar .
Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba”
“Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu.
Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa”
Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa.
“ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya”
Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki”
“ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa.
Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi”
“Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?”
“Allah Mama na cire”
“Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu”
“To wannan ɗin ya za mu yi da shi?”
“Ko almajirai sai na rabawa ”
Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda .
“ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe.
“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.
Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne”
“Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara.
# GIDAN BILAL
Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ”
Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo.
Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita”
“Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu”
“ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar”
“ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana.
“ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna”
Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin.
Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya.
Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?”
Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ”
“Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo”
A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idonsa ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi .........
Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f.
NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne.
29 jully 2024
MRS SADAUKI ce 🌚
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM*
```soldier man```
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️
*FCWA ☀️*
#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓
*Ƙirƙiraren labari ne,bai faru ba a gaske .Ban yarda a juya shi ko a mayar da shi audio doli sai da izinina*
1-2
A nutse nake sauraren mahaifiyata ido a lumshe,tun da ta fara nasihar nake daɗa jin nutsuwa na sake samun gurbi a zuciyata har sai da ta zo da furucinta na ƙarshe wanda yayi tsananin razana ni har ban san lokacin da na furta “mi kika ce Ammy?” na yi tambayar da tunanin ko kunnena ne bai jiye min daidai ba.
“A yau an ɗaura aurenka da Maryama ina so ka riƙe amana zuwa gobe in sha Allah zan kawo ta da kaina” ta sake maimaita wa,shiru na yi ina jin wani yanayi marar misaltawa.
“Ibraheemu haƙuri za ka yi, wannan ne kawai gatan da za mu yi wa Maryama don nuna soyayyarmu gare ta da kuma jadadda girman alƙawarin da na ɗaukar wa mahaifiyarta kafin ta bar duniya” yanzu ma dai shiru na yi ba don ban ji ba sai don abubuwa da dama da suka dinga gwaro a kwanyata.
“Heemu ka na ji na kuwa?”
“Na'am Ammy ina ji” na faɗa ina jan ajiyar zuciya,ita ma ajiyar zuciyar ta sauke kafin ta ce “ ina Daddyn ka?”
“Ya fita tun jiya bai dawo ba”
“Okay sai an jima ”
“Ammyyy!” na faɗa da sauri,sai ta tsaya da ƙoƙarin kashewar ta ce “ ya aka yi yarona ina jin ka?”
Kamar mai koyon magana na ce “ki bar ta nan wurin ki har zuwa wani lokaci ”
“Saboda me?”
“Kawai Ammy ”
“Sai mun zo” ta faɗa tare da kashe kiran na furzar da huci ina jin duniyar na juya min.Screen ɗin wayar na ƙurawa ido ina kallon hotonmu wanda shine hoton ƙarshe da muka ɗauka tare da ɗan uwa kuma abokina.
«Zo mu ɗauki hoto ina jin a jikina kamar ba zan fito daga wannan yaƙin ba»cewar Abakar ya na dariya,wacce ba ta kai ga gushe wa ba na yi amfani da wayata na ɗauke mu selfie.Hoton na shafa yayin da kuma muryarsa ke yi min amo a dodon kunne,da sauri na miƙe na nufi ɗakin motsa jiki na soma training.Na shafe kusan awa biyu kafin na fito na wuce bedroom wanka na yi na shirya cikin t-shirt ta soja da wandon kaki.Key ɗin mota na ɗauka kafin na sauko ƙasa inda ƴan aiki ke ta shawagi,su na gani na suka soma gaishe ni kamar kullum da kai kawai na amsa masu na fita zuwa harabar gidan.
Inda motata ke parker na nufa direct, ɗaya daga cikin escort ɗin ne ya rugo ya na tambaya ta inda zan je.“ Ni kaɗai zan tafi babu buƙatar rakiya ko ba ga cikin kayan da nake ba?”
“Sorry mai gida yalɓai ne ya bada umarnin duk inda za ka je mu yi ma rakiya” ya faɗa cike da girmamawa.
“Yi tafiyar ka” na faɗa tare da shige wa ciki na yi wa motar key,wurin fita ma sai da sojawan da ke tsaron ƙofa suka ɓata min lokaci kafin su bar ni na fita.
A hankali nake gudu ina duba yanayin garin da yadda al'amurra ke tafiya,a haka har na isa barikin soja.Daidai ɗakinmu na yi parking,na jima sosai kafin na fito ,key nasa na buɗe ƙofar na shiga a nan take duk wani tsohon tarihi ya dinga dawo min.Dakyar nake cira ƙafa ina takawa izuwa ciki,daidai akwatinsa na je na tsaya tare da buɗa shi na ciro kakinsa mai ɗauke da sunansa Abakar.Na rungume rigar ina jin ƙamshin jikinsa na ratsa hancina,karon farko da na ji idona sun cika da hawaye tun bayan dawowar mu daga yaƙin da ya zame mana shamaki ni da abokina.
Sosai nake hawaye ina jin dutsen da ya jima da yin gini a zuciyata na motsawa haɗi da zubar da tururi .
“Ibraheem!” ya kira sunana a dake,duk da na san ko wane ne bai sa na juyo ba har lokacin da nake jin takunsa na matso ni.
“ Mi yasa ka fito alhalin na ce ka zauna gida? Shi ne kuma ka hana escort su take ma baya,mi yasa ba ka jin magana ta? In fa wani abu ya same ka?”
Sai a lokacin na juyo muna facing juna,ban ce masa komai ba sai idona masu cike da baƙin ciki da zafin ɗaukar fansa na ƙura masa.
“ Wannan zuciyar da kake ji da ita kar ka manta ni ka gado amma shine don tsageranci za ka ƙure ni da ido ka na kallo kamar sa'an ka.Abakar ya mutu ba shine sojan farko da ya taɓa rasa rayuwa ba a wurin yaƙi amma duk ka bi ka adabi mutane da hauka,shi Abakar ɗin wa ya fi ne da ba za a kashe shi b...”
“Daddy???” na faɗa a zuciye kafin kuma na juya na mayar da rigar C
cikin akwati na rufe na sungumi akwatin na fito,don yanzu shi ne kawai abin da ya rage min nasa.
Bayan mota na saka shi,sam ban damu da tarin sojawan da suke tsaye ba waɗanda na san tare suke da mahaifina.Ko ɗakin ban koma na rufe ba na yi wa motar key,ina tafe ina tunanin ƙiyayyar da Daddy ya ɗorawa Abakar dare ɗaya wacce a can farko ba haka suke ba.
Na ja wani huci ina mai danganta abin da don ya fito gari guda ne da mahaifiyata,a haka na isa gida can sama na haura da akwatin na ajiye shi bisa bed ɗina.
Gaban mirror na je na yi tsaye na ƙurawa fuskata ido wacce ta ƙara yin ja don ɓacin rai,baƙar sumar kaina mai tarin yawa na hargitsa ina kai wa ƙaton ƙirjina duka ina mai yin wata hargowa kamar kumurcin zaki har manyan damatsana su na masu motsawa.
Wayata ce ta ɗau ruri sai da ta yi na uku kafin na ciro ta na ɗauka haɗi da karawa a kunne.
“Ka sauko ƙasa ina son yin magana da kai” shi ne abin da ya faɗa kafin ya kashe, toilet na shiga na wanke fuska ta kafin na sauka ɗin.A zaune na tarar da shi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,shi ma sanye yake cikin na soja mai ɗauke da adon galolin yabo birjit.Kujera mai facing tasa na zauna ina mai sunne kai saboda sai yanzu ne na ji ban kyauta ba game da abin da na yi masa.
“Ibraheem ka ɗago ka kalle ni” yayi furta cike da kulawa,ƙin ɗagowar na yi saboda kallon tsakiyar idon Daddy sai mutum ya shirya,na sha jin sojawa na faɗar su na shakkar kallon nasa wanda ni ma shaida ne ba a ko wane irin yanayi ba ne nake iya kallonsa.
“Mine ne damuwar ka? Abakar?”
Sai a lokacin na ɗago na dube shi,murya cike da rauni na ce “ Daddy shi ɗin abokina ne tun na ƙurciya ina mugun sonsa,tamkar yadda Wa ke son ƙanensa...” shiru na yi ina jan ajiyar zuciya.
Daddy ya ce “ saboda mutuwarsa ce nake ganin rauni a idon ka? Ka gaji ne da aikin sojan na tsige ka?”
Wani irin halbawa zuciyata ta yi,da sauri na ce “ haba Daddy ya za ka ce haka? In na bar aikin soja mi zan yi ?”
Ya miƙe tsaye ya na cewa “to in ka na son ci gaba da zama a ciki,ka fidda Abakar a ranka ko sunansa kar na sake jin ka ambata” har ya kai bakin ƙofa kuma sai ya juyo muna kallon juna kafin ya ci gaba da cewa “zuwa an jima sabuwar mahaifiyar ka za ta tare ban son jin wata matsala ta fito daga gare ka” ya na gama faɗa ya fice.
Tsakanin baƙin cikin sharaɗin da ya gindiya mini da kuma kishin Ammyna da nake yi jin zai kawo wata mace matsayin mata sai na rasa da wanne zan ji.Ɗaki na koma na kunna karatun Alkur'ani ina saurare,a haka bacci ya ɗauke sai wuraren sallar zuhur na farka.Na yi wanka haɗi da alwala na saka jallabiya na wuce masjid da ke nan cikin gidanmu,ni na ja su sallah bayan mu gama na zauna nan na ci gaba da lazumi ban fito ba sai bayan sallar Asar.
“Babana yau mi za a girka ma na buɗa baki?” Granny ta tambaye ni,mahaifiyar Daddy ce a nan gidanmu take zaune tun kafin ma a naɗa shi komanda sojoji.Muna gane wa juna ni da ita don ni ɗaya ne kaɗai jikanta,kaf ƴaƴanta kuma tun su na jarirai suke mutuwa Daddy kawai ya tsaya.
“Tsohuwa mai ran ƙarfe ina kika shige duk yau ban gan ki ba” na faɗa tare da nufar ta ina ta ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi.
“Ina ɗakina,ai ba ka neme ni ba tun jiya ƙafar nan ta matsa min da ciwo” ta faɗa ta na nuna min ƙafar wacce ta ɗan kumbura.
Kan capet na zauna na soma matsa mata ƙafar,cikin sigar zolaya na ce “ko sai an yanke ƙafar nan dai?” ta dungure min kai ta na mai cewa “ka ji min shashanci in an cire gobe da mi zan tarben amaryar ka?”
Fuska na kwaɓe ina mai kallonta,ta sakar min murmushi ta ce “Ammyn ka ta kira ni ai ,t sanar da ni yadda kuka yi da ita.Ka na ji Babana ita wani sa'in rayuwa ita ke tsara mana yadda za mu yi,ba kowanne lokaci ba ne abin da mu muka tsara zai zamana daidai” sai kuma ta canza yanayin fuskarta kafin ta ci gaba da cewa “ka ɗauki misalin Daddynka mana,tun ya na yawo da ragga Maimuna ke sonsa kawai daga samun canjin rayuwa ya wulaƙanta ta ita kuma ta ɗauki abin da zafi mine ne na ɗaukar mataki maimakon ki bar wa