Showing 18001 words to 20457 words out of 20457 words
Chapter 7 - MAITAR IDO COMPELET DOCUMENT BOOK By Mrs Sadauki .txt
ne ya tashe ni daga dadaɗan baccin da nake.Ina ware ido na yi tozali da fuskar Maryam kwance kan ƙirjina sai baccinta take,moments ɗinmu na jiya ya dawo min na ɗan yi murmushi ina mamakin kaina .Janye ta na yi na nufi toilet na yi wanka,da na fito na shirya caf cikin jallabiya ruwan ƙasa .Sai da na yi nafiloli sannan na wuce masjid ,bayan mun gamo sallah na dawo gida har yanzu ba ta farka ba.
Blanket ɗin na yaye ina mai kiran sunanta “ Mary ? Mary tashi ki yi sallah” ta ware idonta kaɗan kafin ta sake lumshe su har da gyara kwanciya ta ci gaba da baccinta.Na dafe goshi na ce “ Ammy kin kawo min aiki” ƙara tashe ta na yi,ta na gunguni ta tashi zaune ni kuma na fita na ɗauki key na je na buɗe mota na ɗauko takardun Daddy ya bani.Ina komawa bedroom na ga ta sake komawa bacci,raina ne na ji ya ɓace cikin ɗaga murya na ce “ keee! Tashi na ce har yanzu ba ki yi sallar ba ne ko me”
A firgice ta tashi ta na kuka tare da zuba min manyan idonta,“ ba za ki wuce ba kenan?” na faɗa ina nufo ta da sauri ta ruga ta shige toilet ina jin ƙarar shower na tabbata wanka take.Falo na koma na soma yin aikina,wani iri nake ji na rasa gane mike damuna ma a yanzu.
MARYAM
Wani irin mugun tsoron Ibraheemu ne ya shige ta,duk yadda take da tsiwa sosai take shakkar idonsa.Ta na shiga wanka ta soma yi kamar yadda Ammy ta sanar da ita kullum kafin sallar asubah ta fara yin wanka ta yi kuma brush.Maclean ɗin da ta gani ta matsa ta wanke bakinta,soso ma da nasa ta yi amfani sannan ta fito ta saka rigar sallah ta gabatar.Bayan ta gama ta soma karatun Alkur'ani inda ta iya kafin ta zo wanda Granny ta yi mata,ganin ta na ta yin gargada yasa ta yi shiru kar ta yi saɓo.
Miƙewa ta yi ta gyara shimfiɗar gadon ,ta fesa turare wanda tun jiya Ammy ta nuna mata ma'ajiyarsa.Toilet ma sai da ta je ta wanke ta sannan ta fito ta haye bed sai bacci.
IBRAHEEM
Ina nan zaune ina aiki kiran Ammy ya shigo wayata, Allah na gani abin da yasa ban je na gaishe su tun da asubah ba don kar ta yi min zancen tafiyarta ne.
Kiran na ɗauka ko kafin na ce wani abu ta ce “ ka sauko ƙasa” sai kuma ta kashe.
Na ja ajiyar zuciya ina jin wani yanayi kafin na miƙe,sai da na duba bedroom na ga Maryam ta koma bacci sannan na sauka.
Ƴan aiki ke ta faman gyaran falo ana ƙara ƙawata shi ,haka na wuce sai gaishe ni suke.Sashen Granny na wuce da sallama a bakina,bayan na gaishe su ne na maida hankalina ga Ammy.Ta sakar min murmushi ta ce “ zan tafi Heemu sai in na dawo wajen suna”
Da sauri na sauke idona ƙasa ina cewa “Ammy don Allah ki zauna”
“ Mu je ka sauke ni na hau mota”
Na ɗago a karo na biyu na kalle ta,sam babu alamun wasa kan fuskarta hakan yasa na dubi Granny na ce “ don Allah Granny ki sa baki mana”
Ta ce “Baba tun da ta ce tafiya za ta yi na san babu wanda zai canza mata ra'ayi,haka halin Maimuna yake yadda ka san mutanen farko sai shegiyar kafiya ”
Ba don na so ba haka na ɗauki ƙaramin trollynta muka fito,har mota Granny ta yi mata rakiya ta na mai cewa “ wancan tsohon ya ƙi fitowa haka za ki tafi ba ku yi ban kwana ba”
Ammy ta ce “ bai komai Mama ai na yi abin da ya kawo ni” addu'a sosai Granny ta yi kafin mu wuce.Gidan Bus na kai ta don Ammy sam ba ta son doguwar tafiya cikin ƙananun motoci,har muka kai ta na yi min nasiha game da zaman aure da kuma jaddada min girman amana .Har ciki na yi mata rakiya,na kunna mata AC seat ɗinta kafin na fito.Ban baro wurin ba har sai da na ga motarsu ta tashi,ina isa gida lokacin ƙarfe takwas na safe ya buga.Sashen Daddy na duba alamun har yanzu su na ciki ba su fito ba,wani takaici ya rufe ni a haka na haye sama.
★A ɓangaren su Daddy kuwa ya na shiga Zeey ta cika bahon wanka ya shiga kamar wani ƙaramin yaro haka ta yi masa wanka.Daddy irin mazan nan ne masu budurwar zuciya sam bai ganin ya girma shi dai burinsa kawai ya ji shi jikin mace ,a kullum bai gajiya haka kuma bai kwanan banza.Yawan buƙatarsa na ɗaya daga cikin abin da yasa ya yi wa Ammy kishiya don an yi rashin sa'a ita ba kalarsa ba ce,auren kuma bai je ko ina ba ya mutu haka yake ta aure-aure har Allah ya kawo shi ga Zee wacce ta kasance bazawara ba ta taɓa haihuwa ba fitinarta yasa mijinta ya sake ta.Yanzu kuma da ta auri Daddy sai ta ga kamar tasu ta zo daidai duk da ta fi zaton ta fi shi juriya, wannan kuma har da don ita da sauran ƙarfinta ba ta yi shekarunsa ba.
A wannan daren tamkar sallah haka su Daddy aka ta more aure,sai kace wasu karnai.Sallar asubah ma yau a ɗaki yayi ta,sai wuraren ƙarfe tara suka tashi suka yi wanka Zee ta taimaka masa ya shirya cikin kakinsa na sojoji ta ɗora masa hulla sannan suka fito falo.
Jin ta yake kamar ƙwai ya na jin wata muguwar ƙaunarta,ba don komai ba sai don ta iya jure nauyin buƙatarsa.
Kan dianing suka zauna,da sauri mai kula da lafiyarsa ya matso ya auna abincin da wata na'ura aka tabbatar normal yake ba komai sannan Zee ta zuba musu suka fara ci ta na masa hirar soyayya.
“ In ka tafi zan yi kewar ka sosai Baby ”.
“ Zan dawo ai kar ki damu,duk inda zan je ki na maƙale a birnin zuciyata ” Daddy ya faɗa ya na wani murmushi.Zee ta rausayar da kai ta ce “ banda kallon mata Baby don in ka ce za ka yi min kishiya zan kashe kaina”
Da sauri ya ce “ haba don Allah bari yi min zancen mutuwa,na yi miki kishiya akan me? Sai in canzawa kika yi kika dinga min rowar kan ki”
Ta yi wani fari da ido ta ce “ haba Baby in na yi wa rowa ribar mi zan ci? Ai ni taka ce” cike da murna Daddy ya kamo hannunta ya ce “ Baby kin ci kyautar mota ” Zeey ta yi wani irin ihu tare da rungume shi,daidai nan Granny ta fito a gaban idonta.Ta girgiza kai cike da masifa ta ce “ Allah wadaran naka ya lalace! Yanzu kai Isah mi na faɗa ma?” da sauri Zeey ta janye daga jikinsa ta duƙa har ƙasa ta ce “ ina kwana Mama?”
Ba ta amsa ba sai ci gaba ta yi da cewa “ daga yau ku dinga zama can falon ku kuna cin abinci na soke fitowa nan,in kuma wallahi ka ci gaba zan bar ma gidan ka”
Hankalin Daddy ya tashi don ya tsani fushin Granny,haƙuri ya soma bata kafin ya je ya kama hannunta ya zo ya zaunar da ita kan kujera.Da kansa ya zuba mata abincin cike da kulawa,ita kuwa Granny hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba.
Ta saki murmushi ta ce “ Allah yi ma albarka ”
“ Amen Mamana ki daɗe ki yi ƙarko,sai kin yi Hajiya Mama uwar shugaban sojoji kike doli a lalaɓa ki a sannu in ba haka ba a tayar da yaƙin duniya na uku” Daddy ke faɗa har da wani sunkuya wa ya na yi wa Granny kirari.Ranta fari ƙal ta kai hannu ta ɗora kan kafaɗar shi ta ce “tashi ya isa haka nan wuce ka tafi aiki kar ka makara”
Sai da Daddy yayi kiran waya ya shaida fitowarsa kafin ya fita,masu take masa baya ne suka yi masa rakiya har motarsa kafin su fice.
Zee kuwa kasa zama ta yi kawai ta miƙe ta bar Granny nan ta na cin abinci.Ɗaki ta wuce,akwatin da ta zuba kayan matanta ta buɗe ta zaɓi waɗanda za ta yi aiki da su na daren yau.Murmushi kan fuskarta ta soma jijiƙa su a gorar ruwa ta na girgiza wa,ita kaɗai ta san irin tanadin da ta yi wa Daddy.A fili ta ce “ ba dai lamarin nan kake so ba,yau zan fito ma da asalin maitata sai na gana ma baƙar wuya ” sai kuma ta kece da dariya.
IBRAHEEMU
Ina shiga ɗaki ko ta kan takardun ban bi ba na wuce bedroom, doguwar jallabiyar na cire na tsaya iya wandon cikin.Hasken ɗakin na kashe na raɓa gefen Maryam,wannan tiririn da zuciyata ke yi na baƙin cikin Daddy na can da wata baƙar amaryasa nake son na kashe.
Abin da na lura shine kiss na yaye damuwa,ban taɓa sanin haka ba sai jiya da na yi wa Maryam shi.Bakina na ɗora kan lips ɗinta ,tun ina yi a hankali har na soma zaƙewa saboda abubuwan da nake ji su na ratsa ni.Zuciyata ce ta ƙara ƙarfin gudu jin Maryam na mayar min da martani,ba sai an faɗa min ba ita ma koyo take kamar dai ni tun da jiya ne muka fara sanin al'amarin.Kiss ɗin ne na ji bai isa na haɗa da romance,rigar jikinta na yi nasarar cire wa na soma sarrafa ta.Kuka ta soma yi min wannan yasa na mirgina baya ina mayar da numfashi,ta tashi zaune ta ɗauki rigarta ina kallonta na ga ta mayar da abar ta kafin ta dire daga bed ɗin.Sam ban yin ƙoƙarin hana ta ba sai ma haushin kaina da na ji,ƴar ƙanƙanuwa yarinya ta kwance min tunani abun takaicin kuma ƙanwar abokina.Na ja wani numfashi tare da ɗauko pilow na rungume.Shiru na yi ina tunanin kaina ‘ yaushe na samu wannan canji? Sanina dai sai lokacin damina kawai sha'awa ke damuna,ko kuma in an yi ƙololuwar sanyi’ sai kuma na ja tsuki a fili wani sashen zuciyata na bani amsar da ‘ ƙila don yanzu an yi maka aure ne an gama ka da mace ɗaki guda’ da sauri na miƙe na shiga toilet jin abin na sake yin gaba-gaba.
Shower na sakar wa kaina,ina tsaka da wanka na soma jin wayata na ruri.Kiran Ammy ne don waƙarta ta musamman ce,a gaggauce na yi wankan na fito.Ina maida kiran amma ba a ɗauka,gabana ne ya shiga faɗuwa ina shirin aika wani saƙon text ɗinta ya shigo ``` Heemu ƴan ta'adda sun tare motarmu a hanya ba zan iya ɗaukar kira ba don tuni sun sauko mu ƙasa an fara lalubar wasu ma```
Ji na yi kamar an buga min wani ƙaton dutse a kai,da sauri na saka kakina na soja da bindigogi.Jikina har rawa yake,ko kallon inda Maryam take ban yi ba na fita da gudu-gudu.Ina cikin mota na kira Daddy na shaida masa amma yake min zancen banza wai kar na je na jira zai tura sojoji amma ina tuni na soma bibiyar layin Ammy na ƙure gudun mota.
Tsawon lokaci ina sharara gudu kafin kira ya shigo da lambar Ammy,na ɗauka da mamakina sai na ji muryarta ce.“Sun yi tafiyarsu sun gudu! Sun bar mu lokaci guda bayan sun yi mana mugun duka Heemu ” na rumtse ido haɗi da jan wani dogon burki ina sauraren yadda Ammy ke rera kuka,dakyar na ce “ gani nan zuwa Ammy don Allah ki bar kuka ki na ɗaga mini hankali”
“ Kar ka zo Heemu yanzu ai za mu tashi daga nan...” daidai nan kiran ya katse,a ta na'urar da na jona nake bibiyar Ammy na ga sun fara gusawa daga wurin alamun motar ta tafi.Amma duk da haka bai sa na koma ba,haka na ci gaba da gudun kusan a tare muka shiga gidan Bus ɗin ni da motarsu.
Ko jira ban yi ba na nufi motar,ana buɗewa na shiga ciki na riƙo Ammy.Fuskarta ta yi ja sosai ga sawun yatsu nan kwance raɗau,haka na fiddo ta na kai ta motata ina jin haushin kaina.Asibiti na wuce da ita duk ƙoƙarin hana ni da ta yi a cewar ta lafiyarta lau kawai kanta ke ciwo,sai ga shi da muka je asibitin an ce jininta ya hau.Ƙarin ruwa suka saka mata,ina daga gefenta zaune ina saƙar zuci so nake yi na yi mat tambayoyi amma ina jiran har ta dawo hayyacinta.
Kamar ta san abin da nake saƙawa a rai sai cewa ta yi “sun tafi da wasu daga cikinmu Heemu”
Na dube ta da sauri,idonta na lumshewa take ci gaba da cewa “da dukkanmu za su tafi da mu sai ogansu ya samu kira bayan ya dawo daga wayar ne yake cewa a tafi da iya maza kawai a bar matan”
“Da yayi wayar ba ki ji abin da ya ce ba?”na yi tambayar zuciyata na mugun bugawa,Ammy ta ce “ban ji ba,sai dai lokacin da ɗaya daga cikinsu yake tambayar ogan mi yasa ba za a tafi da mu duka ba sai ya ce umarnin Dagaci ne”
Dagaci babban ɗan ta'adda ne shine shugaban duk wasu manyan-manyan ƴan daba don ƙungiyarsu guda ce. Shiru na yi ina wani tunani haɗi da zargin da ban son ya zama gaskiya ,sai dai duk yadda nake son tunkuɗe zargin abin ya cuttura sai ma wasu abubuwa da suka faru masu kamanceceniya da suka shiga dawo min.
Ganin Ammy ta samu ta yi bacci na miƙe na fita waje na kira lambar Daddy,bugu biyu ya ɗauka kafin ya ce “ina jin ka” sam yanzu babu alamar tashin hankali ba kamar ɗazu da na sanar da shi an kama Ammy kuma gani a hanya zan je ƙwato ta.
“Ya ake ciki ka aika sojojin ne?” na jefo masa tambayar ,shiru yayi bai ce komai ba har sai da na sake maimaita tambayar sannan ya ce “ka ga Abraheemu aiki nake ” ƙittt ya katse kiran.Na bi screen ɗin wayar da kallo ina juya maganar Daddyn.Karon farko da na tuna ina da wasu abokai na biyu bayan Abakar ,zama na yi na dinga gwada wayarsu babu wacce ta shiga sai ta mutum ɗaya ya na ɗaga wa ya ce “ya ne Soldier Man ya ƙarin haƙurinmu?”
“Alhamdullah! Shamssudeen don Allah ina son ganin ka akwai aikin da nake son ka yi min”
Ya ce “yanzu dai ina kan hanya mun je Katsina wani aiki sai gobe za mu koma Kano”
Na ɗan nisa na ce “fatan kun yi nasara?”
Ya ce “eh mun kama biyu daga cikin yaran Dagaci”
Da sauri na ce “yaran Dagaci ka ce?”
Ya ce “eh zuwa jibi za a wuce da su Abuja”
Wani irin daɗi na ji ta faɗi gasasa kenan.Na ce “to kawai zan bari har ku ƙaraso Abujar ido da ido ma za mu fi fahimtar juna” nan muka yi sallama sai a lokacin kawai na je na yi sallolina,Ammy na farkawa na bata jus ta sha magani kafin mu wuce gidanta.....