Showing 15001 words to 18000 words out of 20457 words
Chapter 6 - MAITAR IDO COMPELET DOCUMENT BOOK By Mrs Sadauki .txt
ni ban taɓa rarrashi ba,don banda ƙanwa sannan cikin aikin soja na girma ta yadda zuciyata ba ta san soyayya ba in ka fidda ta iyayena da kuma abokina.Rasa yadda za a yi na rarrashe ta na,kamar wani mai jin tsoro haka na jawo ta jikina tare da ƙoƙarin haɗe dafin da nake ji a cikin maƙogorona don na samu na yi mata magana.....
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM*
```soldier man```
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️
*FCWA ☀️*
#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓
*YA Ubangiji rahama don ƙarfin ikonka ka wanzar da Zaman lafiya a ƙasata Nijar da Nigeria da ma duk sauran ƙasashen da ke fuskantar ƙalubalen rayuwar nan alfamar Manzon Rahama*👏🏻
5-6
“Yi shiru mana,ban son kukan nan Mary . Addu'armu ya fi buƙata a wannan lokacin,ki godewa Allah ɗan uwanki yayi mutuwar mazaje wacce ba kowa ne ke samun irin ta ba.Mutuwa a filin daga,domin kare ƙasarsa” na faɗa tare da ƙara janta jikina ina goge mata hawayen da suke ta faman yi mata zarya.
Cikin muryar kuka ta ce “ abokin Yaya ina cikin damuwa na rashin ɗan uwana,amma Ammy ta ce da kai da shi duk ɗaya ne duk kulawar da yake min kai ma za ka iya kuma zan fi jin daɗin zama da kai fiye da in zauna wurin ta”ta yi maganar ta na faman cusa kanta a ƙirjina.
Na ce “ eh gaskiya Ammy ta faɗa ,kin manta Abakar ƙanena ? Kin ga ke ma ƙanwata ce.Daga yau ban son ƙara ganinki ki na kuka,duk abin da kike so kuma ki sanar da ni”
Ta gyaɗa kai tare da cewa “ Ammy ta ce za ka kai ni ƙaton kanti ka saya min kaya”
Na ce “ eh sai in kin huta za mu je”
“ Yaushe kenan?”
“ Ko zuwa jibi haka”
“ Ba gobe ba?”
“ Za mu je goben to” na faɗa ina mai janye ta daga jikina tare da ƙoƙarin sauka daga bed ɗin,ta ce “ kenan kai ne mijina?”
Dariya tambayar ta bani,na ce “ Mary shekarun ki nawa?”
“Sha tara” ta bani amsa,na juyo ina kallon ta ban san mi yasa ba sai nake ji a raina ina son jan ta wasa na ce “ mai ƙarya dai ɗan wuta ne”
Ta buɗe baki ta na murmushi,na kafe ta da ido ganin fara'ar nan yasa na ji daɗi .
“ Na waɗa ma gaskiya ?”ta yi tambayar cikin Hausar ƙauyensu na Sokoto.
Na yi murmushi na ce “ eh faɗa min”
“Kai dai shekaruna Sha shida na”
“Sha shida ne za ki ce”
Ta turo baki ta ce “ ni wa ba zan iya yin Hausar ku ba,yawwa na ce ku nan kowa na da abun hawa na? Gari duk ko ina motoci na birjit awar an taso daga sallar idi ”
Ban bata amsa ba na soma shafa mai da turare,ta madubi nake hango yadda take kallona.Na yi gyaran murya na ce “ ki je ki ci abinci”
“ Ban jin yunwa”
“To koma falo zan shirya” da “toh” ta amsa ta fice.
Drower na buɗe na fiddo kayan da zan saka,ina tsaka da saka kayan kamar an ce in juya na hange ta ta na leƙe na.Muna haɗa ido ta tuntsire da dariya kafin ta gusa,na girgiza a zuci ina cewa ‘ yau na ga ikon Allah ’ bayan na gama na fita falon na tarar da ita a zaune ta ƙura wa ƙofar fitowa ido.
Na ɗan haɗe rai na ce “ mi yasa kike leƙe na?”
Ta sunne kai ƙila ta tsora ta da yanayin nawa,ta ce “ Ammy ta ce kar na ji kunyar ka kai mijina ne duk abin da za ka yi ni zan taya ka har saka kaya da wanka”
Na waro ido ina mamakin ya kuma Ammy za ta faɗi haka,na ce “ shi ne sai ki leƙe ni ?” ta ɗago kai ta ce “ to mine ne in na yi hakan kai ai mijina ne” sai ta soma wasa da awarwaron hannunta na duwatsu.
“ Na ji tashi mu sauka ƙasa” ta maƙe kafaɗa ta ce “ Allah tsoro naka ji”
“Nake ji ake cewa” na gyara mata da sauri kafin na miƙar da ita tsaye ta na turjewa muka fito.
“Kwarankwatse ba zan sauka ba” ta faɗa ta na shirin zubewa ƙasa ta riƙe ni gam.
Na ce “ to waye ya hauda ke saman?”
“Ammy ce da wata tsohuwa”
“To na ji ki nutsu babu wuya fa ki kalli yadda zan yi”
Ta ce “ Na wa san bene, kai hawar shi ta a ban yi saboda ina ganin jiri ”
Cak na ɗauke ta na soma sauka da ita ƙasa,ido ta rumtse gam har muka sauka na aje ta ina mai cewa “ baƙauya” Ammy da Granny suka saka dariya ni kuma na fita zuwa masjid.Ina can aka kira sallah,bayan an gama na shigo ciki muka je muka ci abinci gaba ɗaya Granny ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Kusa da Ammy na dawo na zauna ji nake kamar kar lokacin ya shuɗe,“ Ammy yanzu tafiya za ki yi?”
“Tambayata ce kake?” ta faɗa tare da kallona,na gyaɗa kai. Ta ce “ zuwa gobe in sha Allah zan koma”
“Don Allah ki tsaya ko sati ɗaya ne ki yi” na faɗa .
Ta ce “ a'a ba zan jure ba Heemu,ɗazu ai ka ga rainin hankali da matar Ubanka ta yi yadda take wani kiran ka da gadara so ta yi na tanka mata don kawai a yi faɗa ”
Na ja numfashi na ce “ Ammy mi yasa ba za ki dawo nan da zama ba? Ban son ganin ku a rabe ke da Daddy ”
Sai da ta kalli Maryam kafin ta ce “ jeki sama Maryam ”
Ta ce “Ammy na dai je ɗakin waccan”
“Okay tashi ki tafi” ta miƙe da saurinta ta na gyara hijabinta wanda tun da ta yi sallah ba ta cire ba.
Bayan tafiyar ta ne Ammy ta dube ni da kyau ta ce “ faɗa mini matsalar ka”
“Babu Ammy ni burina kawai ki dawo nan ɗin” ta girgiza kai ta ce “ na bar Daddynka har abada,tun ka na goye na bar gidansa bai taɓa tunanin dawo da ni ba sai ni ce zan sarkawa? Ya je yayi ta aure-aurensa wata rana sai ya auro aljana”
“Ammy na sani Daddy yayi laifi amma hukuncin da kika ɗauka ne yayi tsauri sosai ” na faɗa cikin jimami ina tuno abin da Granny ta ce min game da mafarin rabuwar.
Ammy ta yi wani murmushin wanda ka ganinsa ka san na takaici ne kafin ta ce “ tun bayan da na koma gida bai taɓa tako ƙafarsa ba sai da ka shekara goma a ranar da ya zo ya tafi da kai ya saka ka makarantar sojoji,ya nuna min iko ya maido ka gidansa da ace ya na ra'ayina ai a tare zai maido mu” idonta ne na ga sun cika da hawaye,da sauri na miƙe ina cewa “ kuka kuma Ammy? Don Allah a'a” sai na shiga goge mata su.
Jiniya ce ta cika gidan alamun Daddy ya dawo,muna nan tare da Ammy amaryasa ta fito cikin murna.Daddy na shigo wa ta yi tsalle ta rungume shi ba tare da ko kunyar escort ɗinsa ba da suka yo masa rakiya.
Raina ne na ji ya sosu musamman da na ji Daddy na cewa “ za ku iya tafiya yanzu lokacin iyalina ne” Ammy ta je ta miƙe na mayar da ita.
“Muuuah! Muuuah!” kawai kake ji amaryasa na masa kiss wanda ina da tabbacin da gayya take yinsa ,shi kuwa Daddyn kamar wani soko yayi tsaye na yi imanin bai lura da mu ba da tabbas ba zai tsaya ba.
“Mi kika girka min Bab...” sauran maganar ce ta laƙe a maƙoshinsa da muka haɗa ido da shi.Da sauri ya janye ta daga jikinsa “ jeki ɗaki ina zuwa” ya faɗa ita kuma ta harare ni kafin ta wuce.
Daddy ya wani haɗe rai ya na mai ƙaraso wa inda muke,na taɓe baki tare da barin wurin na fita zuwa masjid.
Daddy yayi gyaran murya ya ce “fatan kin sauka lafiya?”
Ammy ta ce “ lafiya lau alhamdullah har ina shirin komawa ma”
Ya shafi gefen wuyansa ya ce “ to madallah ” Ammy ta ƙure shi da ido ta na kallonsa kafin ta ce “Isah sai yaushe za ka sanin ciwon kan ka? Aure-auren naka har ya kai ka auro karuwa wacce ba ta san mutumcin kanta ba? A gaban ɗan cikin ka kake sumbatar mace? Ayir ɗinka wallahi ka bani mamaki ....” Daddy yayi saurin katse ta da “ don Allah Maimuna ban son tsiyar gumi.Ina ruwan ki da matata ? Wato kishi kike don kin gan kin koma tsohuwar akwala babu mashunshuni haushi ya kama ki kin ga na auri ƴar shilla?”
Sam ba su ga zuwan Granny ba sai saukar marin da ta kifa wa Daddy,ya dafe kumci ya na kallonta “ Mama...” da sauri ta katse shi “ rufe mini baki! Wato kai ba ka ƙaunar zaman lafiya daga ta na faɗa maka gaskiya shikenan sai cibi ya zama ƙari?”
“Wace gaskiya Mama ? Kawai banda ikon sakewa da matata?”
“A gaban ɗanka? In shiriritar kuke so mi zai hana ku yi ta can sashen ku? Kai yanzu ba zubewar girman ka ba ce da matsayinka da ikonka a gan ka kana abin yara? Dubi gemunka farin gashi ne ya fara tsiro wa amma a haka kake rungumar ƙanƙanuwar yarinya a gaban ɗan cikin ka.Maimuna mu je,ke ma da naki laifin ban ma san mi ya tsayar da ke nan ba” Granny ta faɗa tare da jan hannun Ammy suka koma can ɗakinta.
Maryam na zaune ta na karatun Alkur'ani,yanayin da ta ga Ammy ne yasa ta yi saurin rufewa ta nutsu sosai.
“ Tashi ki koma sashen ku Maryam ki tabbatar kin yi wanka kin yi sallar isha'i kafin ki kwanta” cewar Ammy, Granny ta ce “a'a ki barta a nan har a jima”
Ammy ta ce “ to ni zan ɗan kwanta ” dama fashin sallah take hakan yasa Granny ba ta ce komai ba.Karatun suka ci gaba da yi ita da Maryam inda ta yi kuskure sai ta gyara mata,Maryam ta ce “ ya aka yi kika iya karatu Kaka?”
“To in ba abin ki ba ta ya ba zan iya ba tun da ba makarantar Boko na yi ba mai zurfi”
“ Tun ki na yarinya kenan kika iya?”
Ammy ta ce “ Maryam ba a tsare babba da tambayoyi”
Granny ta ce “ a'a bar ta mana ita ma in ta tsufa haka jikokinta za su tsare ta da tambayoyi”
Maryam ta ce “ ni dai gaskiya ban so na tsufa” Granny ta dinga dariya ta ce “ ai baƙin gashin nan a sannu zai koma fari sol” Maryam ta hau kukan sangarta.
Ammy dai na jin su ba sake kula su ba,furicin Daddy sosai yayi mata tsaye a zuciya wai ta ƙi yin aure saboda babu mai sonta.Wasu hawayen takaici suka zubo mata a zuci ta ce ‘ in sha Allahu zan baka mamaki zan cire ka a rai na je na auri wani’ da wannan tunanin dai ta yi bacci.
A can ɓangaren Daddy kuwa cike da jin haushi ya nufi ɗakin amarya Zainabu,a yadda ya tarar ta ci uban shiri cikin kananan kaya sai ya nemi fushin ya rasa.Ita ma cike da iya yi ta zo ta rungume shi suka gama shiriritarsu,kafin ta yi masa rakiya zuwa toilet yayi wanka .Sai da ta cika masa tumbinsa sannan ya je masjid ,ganin IBRAHEEM ne yau zai ja su sallar ya ji haushi sosai don ya matsu ya koma ciki wurin amarya .
Cike da nutsuwa nake gabatar da sallar har muka kammala,kamar sauran lokuta a tare muke komawa gida ni da Daddy.Da sauri na miƙe na isa gare shi,ina son yi masa magana ne akan Ammy sai dai shi ya tari numfashina ya na mai cewa “ don Allah ka bar jan dogon karatu,wasu ba sa iya jurar tsayuwar nan ka yi ta karatu sai ka ce muna ƙiyamul laili?”yayi maganar ya na ɗaga ƙafa da alamu sauri yake.
Na ce “ yaushe soja ya fara tsoron tsayuwa? Duk sojawa ne sun saba dama to ai ni ban ga wata damuwa ba don an ja dogon karatu.Aka yi tsayuwa akan lamarin duniya sai wurin bautar Ubangiji ne za mu samu rauni?”
“To in fa mutum na da uzuri ? Irin hakan dai babu daɗi na faɗa ma”
“ Daddy na ga alamun kamar ka na sauri ga shi kuma ina son yin magana da kai” na faɗa ina jan numfashi daidai nan muka iso ƙofar da za ta sada mu da babban falon gidan.
“Ya ce ba yanzu ba ka bari zuwa gobe”
“Amma Daddy...” shiru na yi sakamakon ganin amaryar ta sake fitowa cikin wata shiga ta riga da wando duk sun matse ta rabin mamarta duk a fili .Da sauri na kawar da kai ganin ta rungume mahaifina duk da kuwa ƙoƙarin hanata da ya so yi,“ Haba Zee ya za ki fito haka wuce gani nan zuwa”
“ Ni dai... Ni dai Baby na ƙi wayon mu je ƙafarka ƙafata na sh....” sauran maganar ban ji abin da ta ce ba,na fi zaton Daddy ya toshe mata baki ne.
“ To na ji na baka minti biyu” ta faɗa kafin kuma na ji ƙarar takalminta alamun ta tafi.
“ Ibraheemu mi ka ce?” Daddy ya tambaye ni a ɗan daburce,sai yanzu na juyo na kalle shi da jajayen idona da suka rine tsabar ɓacin rai .A nan tsaye na barsa na wuce part ɗina, matakalar ma ban ganin ta da kyau.
Ina shiga ɗakina direct bedroom na wuce na kwanta rairan ina kallon sama,zuciyata sai tuƙuƙi take.
‘ Wai mutumen da in za ka gansa sai ka yi fiye da sati guda ka na shan wuya,mutumen da in shugaban ƙasa zai fita sai ya bayar da izinin zai iya fita babu wata matsala,mutumen kowanne soja jininsa a akaifa yake in ya aiko kiran ka ko kuma in ransa ya ɓace shine waccar abar take cewa ta basa minti biyu?’ na yi wa kaina tambayar a zuci ina jin farashin ƙunci,baƙin ciki da takaicina su na ƙara yin sama.
A daidai wannan gaɓar mutum ɗaya ne kacal ke saurin yin nasara kaina wurin sauke fushina,yanzu kuma ba ya tare da ni mutuwa ta yi mana yankan ƙauna.Haka na ci gaba da juyi a bed ina ta ƙoƙarin tunkuɗe lamarin amma abu ya cuttura,sama da awa biyar ina cikin hali guda.Dakyar na miƙe na je na shiga toilet,ko kayan jikina ban cire ba na sakarwa kaina shower.Ina nan daga tsaye na ji kukan Maryam,Ammy kuma na yi mata faɗan doli ta koyi hawa bene sannan ta jaddada mata nan ne ɗakinta kar ta saki ta kwana ɗakin Granny.
Ina jin lokacin da ita Maryam ɗin ke cewa “ Ammy shikenan ba zan sake komawa bacci ba tun da kin tashe ni”
Ammy ta ce “ ni ma ai don baccin ya sace ni ne amma ai sam da ba zan bari ki kwanta can ba,ki tabbatar kin yi wanka kin yi brush kafin ki kwanta” tsit kuma ban sake jin sautin muryoyinsu ba.
Na ja ajiyar zuciya kafin na tuɓe na yi wankan soso da sabulu na fito ɗaure da towel a ƙugu ,ɗan ƙarami kuma ina tsane gashina.
Zaune na tarar da ita ta buɗe trolly duk ta zubar da kayan da ke ciki sai wani turo baki gaba take,gaban dressing mirror na tsaya na yi shafe-shafe sannan na zaɓo kayan bacci masu riga mai sauka har ƙasa.Ina ganin lokacin da ta shiga toilet matse da kayan da za ta canza,da wannan ni ma na saka nawa kafin ta fito na je na haye bed bayan na kashe ƙwan lantarki sai na kunna fitilar bacci.
Tunani na soma yi kan shuɗaɗiyar rayuwarmu ni da Abakar,«aboki don ba ka da ƙanwa ne da ka ji irin yadda nake ji,Maryam komai ce nawa.Farin cikinta ya fi min komai daɗi a duniya,aikin nan ma domin ita da Umma nake yinsa.Na ci burin yi wa Maryam kayan ɗaki na kece raini a matsayina na waliyinta maɗaurin aurenta» wannan na ɗaya daga cikin zantukan da yayi min game da Maryam.
Yadda ta fado jikina ta bi ta kaina yasa ta katse min tunanin,“ ni wallahi sanyi naka ji ba don na yi wa Ammy alƙawarin ba,in na yi wankan nan shegiya nakai ” ta faɗa cikin mita tare da gyara kwanciyarta ta ja bargon da nake ciki ta rufa.Duk da ta rufa ɗin bai hana ta rawa sanyi ba,kamar wanda aka yi wa doli na ɗan matsa kaɗan sai gani kusa da ita sosai.A hankali na ɗan kwanta ta samanta na yi mata rumfa da ƙirjina,hannunta na ji gefen cikina ta sarkayo shi haɗi da riƙe wa gam ta ce “ ina jin sanyi sosai”
Bargon na ida ja ya rufe mu har wajen kai,a hankali kuma na matsa fuskata kusan tata ta yadda muna jin numfashin juna.Ƙamshin turarenta ne ya sakar min wata kasala da na kusanci wuyanta,ban san lokacin da na saki wani gauron numfashi ba ina mai sake saka ta ƙirjina.Tuni Maryam ta fara mitsirniya,gefen wuyanta na soma aika ma sumba kafin na yi sa'ar lalubo bakinta na fara kissing.Sam ba ta yi ƙoƙarin hana ni ba da alamu ma ta na jin daɗin haka don sai ƙara riƙe ni take, wannan yanayin da na tsinci kaina sam ba zan iya faɗar yadda yake ba.Bugun zuciyata ne kawai ke ta tsananta ya na bada sauti na musamman,sama da minti talatin kafin na janye daga jikinta na koma gefe ina mayar da numfashi.Blanket ɗin na janye na maido shi iya ƙirji,idona a lumshe ina jin raina yayi ɗan sanyi ba kamar ɗazu ba.Na kai hannu na jawo ta na ɗora kanta kan ƙirjina yayin da kuma hannuna ke kan bayanta.Murya can ƙasan maƙoshi na ce “ kin bar jin sanyin ?” kamar wata munafuka ta ce min “ eh!” “ ok yi bacci” “ uhumm !” shiru duk muka yi ina ta mamakin kaina ,ɗaya ɓangaren kuma na sakawa Ammy da alkhairi da ta haɗa auren nan...
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM*
```soldier man```
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️
*FCWA ☀️*
#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓
7-8
Kiran sallar farin