Showing 12001 words to 15000 words out of 20457 words

Chapter 5 - MAITAR IDO COMPELET DOCUMENT BOOK By Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

5689

Allah komai? ”


Na ja numfashi na ce “Granny wai mi ya gama Ammy da Daddy faɗa har suke gaba haka? ”
Ta shafi kaina ta ce,“Daddyn ka ya yi butulci,saboda amarya ya mari Ammyn ka da ta so nuna masa kuskuren yin haka ya lakaɗa mata na jaki a ƙarshe kuma ya danƙara mata saki.A ranar da za ta fita ta bugi ƙirji ta ce masa yadda ta fita daga gidansa,haka duk matar da zai auro za ta fita.Wai ka na da ma labarin yau wata amaryar zai kawo?” Granny ta buge da tambayata.


Ni kuwa tun da na ji wulaƙanci da tozarcin da ya yi wa Ammyna na soma jin tsohon fushina na sake bijirowa.Na yunƙura zan tashi,Granny ta yi saurin mayar da ni ta na cewa “ina kuma za ka je? Faɗa min abin da za a yi ma na saka ƴan aiki yanzu nan”
“Duk abin da kika zaɓa Granny ya yi” na faɗa tare da miƙe wa na haura sama.Ina shiga ɗakina na fahimci tabbas wani ya shigo ciki,to amma mi aka shigo yi? Kafin na kai ga lalubo amsa idona ya sauka kan bed sam babu akwatin da na ajiye.
Waya na ɗauko na soma kiran Daddy amma bai ɗauka ba,na fito da sauri ina tambayar Granny “ba ki ga wanda ya shiga ɗakina ba?”
“Lafiya mi ya faru?”
“Akwatina aka ɗauke” na bata amsa kai tsaye.
“Baturen nan ne dai ya ɗauko shi a gabana ya fita da shi”
“Joy?” na tambaye ta ta ce “eh shi fa” na dafe kaina,Joy shi ne soja na hannun damar Daddyna.Da wannan takaicin na zauna zaman jiran shi,a nan falo na sha ruwa tare da taimakon Granny har na je na bayar da salloli na dawo babu ko motsin Joy.Mu na nan zaune ni da Granny,aka kawo amaryar Daddy wata ƴar ficiciya da ita ko kunyar aurenta bai ji ba.
A gaban Granny aka kawo ta ,tun daga danginta har ita amaryar ƴan iya yi ne Granny ta yi musu Allah sa albarka kafin ta nuna musu sashen Daddy suka wuce da ita.




Na dubi Granny cike da jin haushi na ce “yanzu wannan ce ya auro?”
“Babu ruwan ka,dama ya ce na ja ma kunne akan haka.Duk gani yake saboda tsamin ranka matansa ke fita daga gidansa,sam ya ƙi yarda aikin Maimuna ne”
Na ce “Granny ya za ki ce aikin Ammy ne?”
“ A bar zancen to.Mi ka shirya wa goben?”
Ban bata amsa ba sai kwanciya da na yi na ɗora kaina kan cinyarta,ta ce “sai son jiki kamar mage,ga ka dai ƙaroto amma da taɓi'a yara in ka karye ƙafar tawa ai shikenan”
Na yi ɗan murmushi na ce “granny don Allah yi min addu'a na yi bacci ko zan huta da baƙin cikin nan da nake ji”haka kuwa aka yi ta soma yi min karatu,duk da ta na tsohuwa haka take fitar da harufa yadda ya kamata.Sosai nake jin daɗin karatun sai dai baccin ya ƙi samuwa,a ƙarshe ma ita ce ta soma yin gyangyaɗi a doli na miƙe na yi mata rakiya ɗakinta sannan na wuce nawa.A wannan daren ban rumtsa ba sam, system na ɗauka na soma yin binciken da y shafi aikina har aka kira sallar asubah bayan na dawo daga sallah na ɗora daga inda na tsaya.Wuraren ƙarfe tara na tashi na yi wanka na shirya cikin ƙanana kaya wando jean da rigarsa ,ko agogo ban saka ba na fita.
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM*
```soldier man```


© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*


#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓






3-4




Tun daga nesa nake ƙare musu kallo,sai kace wani ƙaramin yaro sai ririta amayar yake ya na bata abinci a baki ko kunya bai ji har da wani ɗora ta kan cinyarsa ita kuma uwar iya yi da rashin kunya ta na gyara masa hullar kansa.
Na ɗauke kaina,har na ida sauko wa daga kan benen ban kalle su ba ina shirin zama kan kujera na ji Daddy na wata irin dariya mai cike da tsantsar farin ciki ya na cewa “Baby ba fa haka ake ɗora hullar ba,na faɗa miki kan zakin can gefe yake kallo”
“Uhum!Umhum! Ni dai haka ta fi min kyau Baby” ta faɗa cikin wata shagwɓar da tasa na yi saurin ɗaga kai na kalle su ,aka kuwa ci sa'a shi ma Daddyn ya ɗago ya na kallon saitin da nake.Da ido na tsure shi da su rai ɓace,da sauri na ga ya sauke ta daga kan cinyarsa ya ɗora ta kan kujera.Ta taɓe baki ta na kallona,ashe kallon tsoro na yi mata a jiya tsohuwar yarinya ce ƙaramin jiki ne kawai da ita ta ci uban bleachin ta yi fayau.




“Ibraheem ka fito?” Daddy ya tambaye ni,ban amsa ba na fasa zaman na wuce part ɗin Granny ina jin zuciyata na tururi.A zaune na tarar da ita ta na shafa maganin ciwon ƙafa,na zauna kusa da ita ina mai gaishe ta ciki-ciki.
Ta amsa da “lafiya lau ka ci abinci ne?” na girgiza kai ta ci gaba da cewa “da kaina fa na zaɓi abin da za a dafa ganin jiya ba ka ci wani abin kirki ba” ban ce komai ba sai ƙafarta da na soma matsawa.




“Babana ban son shirun nan,faɗa min mi aka yi?”


“Daddy ne” na faɗa cike da takaici.
“Mi yayi kuma?”
“Shi da matarsa ne...” na cije leɓen ƙasa kafin na ci gaba da cewa “kamar wani ƙaramin yaro shine zai zo tsakiyar falo da girmansa da darajarsa ya na ba ƙaramar yarinya abinci a baki har da ɗora ta a cinya? Granny in ni ɗansa ne na kawar da kai su kuma ma'aikatan gidan nan fa?”




“Don Allah fita batun su,bani makullin ɗakin ka zan sa a ƙara gyara shi kafin Ammyn ka su ƙaraso” Granny ta faɗa .
Na ce “wato ke ma kin basa goyon baya ya ci gaba da yin haka?”
Granny ta ce “to mi kake so na ce Babana? Duk tsiyarsa dai ai ba zai koma saurayi ba,ban makulli ka ji”
“Wai yanzu gaske kawo ta Ammy za ta yi? Allah ni ban shirya wani zama da mata ba” na faɗa ina mai kwanciya kan lalausan capet ɗin.


Granny ta ce “yau na ga abin da ya fi ƙarfina wai tsohuwar da ƙirgen dangi! Yanzu Babana kai ne ba ka shirya zama da mata ba? To halan so kake sai ka zama tuzuru sannan?”
Na turo baki tare da lalubo key ɗin na miƙa mata na ce “ni dai wallahi inda ma wurin ki ta zauna”
Ta na dariya ta miƙe tsaye ta ce “tun da ni aka aura ma ita ba.Tashi mu je ka ci abincin”
“A kawo min nan ba zan sake fita na ga kayan takaici ba”
“Ka ji wani zancen mutum da matarsa,kai ma ai ka kusa hutawa da zamana gwabranci can a yi wa kaji zabbi hira suke” ban sake cewa komai ba har ta fita,can sai ga ɗaya daga cikin ƴar aiki ta shigo da sallama ta kawo min abincin.
Da kaina na zuba na ci sama-sama kafin na sha ruwa na haye katifar Granny,wani bacci ma na soma ji amma ina tunawa da Abakar ya bar duniya sai na ji ya fita idona.Da sauri na fito don tambayar Daddy inda yasa aka kai min akwatina sai kuma na tarar da shi a tsaye ya na kallon tv da ke manne a jikin bango.


Zuciyata har wani tsalle take tsabar yadda allurar soja ta motsa,bresking New ne ake ƴan ta'adda sun kai hari a wani ƙaramin ƙauye da ke cikin Zamfara sun kwashe shanu da kuma wasu samarin garin.


Daddy na kalla na ce “sai yaushe ne ƙasarmu za ta bar fuskantar ƙalubalen nan? Gagarar mutane ne suka yi ko rashin iya aikin jami'an tsaro ne?” kallona yayi ba tare da ya ce komai ba ya fita,da sauri na nufi matakalar da za ta sada ni da sashena.Bibiyu nake taka ta har na isa,ina shiga ɗakin na tarar da Granny da ƴan aiki su na ta gyaran falon direct bedroom na wuce nan ɗin ma akwai masu gyara shi.Falo na ce su koma na canza kayan jikina zuwa kakin soja,na saka takalmi da belt na ɗora hulla sannan na ɗauki baƙin gilashi na manna.Ƴar madaidaiciyar bindiga ta na ɗauko na soke a ƙugu kafin na fito,Granny ta tare ni ta na cewa “ina kuma za ka je?”
“Wani ɗan aiki za mu yi ki sa min albarka ”
“Allah tsare ya dawo da kai lafiya”
Na amsa da “amen kafin na fito”




Ina saukowa ƙasa na ji matar Daddy na waya “iyeee ke tsohon ɗan duniya ne inda kin ga yadda ya susuce jiya a kaina,na san tun da yake aure-aurensa bai taɓa samu mace haɗaɗiya kamar ni ba”
Godiya na yi ga Allah da falon babu kowa masu tsaron gidan duk su na waje,da wannan takaicin na fito na ɗauki motata na bata huta.
Sai da na hau kan titi sosai sannan na daidaita gudun motar na kira Ammy,har ta tsinke ba ta ɗauka ba sai a kira na biyu.
“Ina kwana Ammy kin tashi lafiya?” na faɗa cike da kwantar da murya.
“Lafiya lau alhamdullah! Ga mu a mota muna hanya ina ta bacci sai da Maryam ta tashe ni” cewar Ammy,na ɗan jan numfashi na ce “Ammy ni da na so na ce ku ɗan jira kar ku zo yau”
“Saboda me?”
“Ammy jiya fa Daddy ya kawo wata” na faɗa ina cije leɓena na ƙasa.
Ta ce “ina ruwana da matarsa? Ai ni bai gabana ballantana wata can banza”


“Zan sake kiran ki in na sauka Allah tsare hanya” na faɗa ,bayan ta yi min addu'o'in da ta saba na kashe.Ina isa can babban Barack na tarar da sojawa birjit duk sun yi uban layi,na san bai wuce umarnin Daddy ne ya na son tura su can inda abin ya faru.
Mota na parker sannan na nufi hanyar da za ta sada ni da ofishinsa,duk da ya na mahaifina sannan kuma na kasance soja hakan bai hana masu tsaron ƙofar hana ni shiga ba.
“Shi ne ya bada umarnin kar wanda ya shiga”
“ Ku bar ni na ce akwai maganar da za mu yi” na faɗa a karo na biyu,amma suka ƙi nan fa muka hau rigimar da ina tunanin ita ta jawo hankalin mutanen ciki har aka buɗe ƙofar.


Sergent Yakubu ne ya na ɗaya daga cikin waɗanda Daddy ke hulɗa da su ba a harakar aiki ba kaɗai,“ku bar shi ya shigo” ya faɗa ya na bani hanya don na wuce.Na yi musu kallon banza sannan na shige,a zaune na tarar da Daddy ya zube wasu duwatsu akan teburi alamu dabarun yaƙi yake shirya wa.




“Daddy?” na furta ,shiru bai amsa ba na sake cewa “Daddy ina son zuwa don Allah ka sa a tafi da ni ” nan ma ɗin shiru yayi har sai da Sergent Yakubu ya ce “ shugaba za ka ce”
“Ka dai barsa ya ɗauka nan a gida muke”




Shiru na yi ina kallonsa,ya ɗago ya shi ma ya na kallon nawa kafin ya ce “ a gabana za ka tsaya da baƙin gilashi?”
“Ka yi haƙuri yalaɓai ban iya kallon tsakiyar idonka ne shi yasa,amma ina neman alfarma don Allah ka tsara tafiyar nan da ni”


“Captain IBRAHEEM Isa ba za ka je ba” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye ya mayar da hankalinsa ga Sergent Yakubu ya ce “ daidai nan da nan za mu baza dakarun mu ta yadda za mu zagaye abokan hamayya,ka ga duk yadda aka yi dai mune da nasara in sha Allah saboda kowanne bango mun zagaye su”


“In kuma aka yi rashin sa'a kafin su isa su ƴan ta'addan sun bar wurin?” Sergent Yakubu ya tambaya.
Daddy ya ce “ har yanzu dai su na wajen kuma ba zata ce za mu yi musu ”


“An bi didigi an gano inda suke?” na yi tambayar ni ma ina ƙara matsawa,Daddy ya ɗago a hassale ya ce “ wai mi kake jira ne? Ba na sallame ka ba?”
“Don Allah Daddy ka bar ni na je”
“Ba za ka je ba fitar min daga ofis ko na sa a zo a fitar da kai ta tsiya ” ya faɗa cikin tsawa ya na nuna min ƙofa.
Amma abun ka da soja na dake na ce “ Yalaɓai mine ne amfanina kenan in har wata matsala za ta taso ba tare da na bai wa ƙasata kariya ba?”




“ Sai ka ajiye aikin tun da ba ka ga amfaninsa ba,Sergent Yakubu biyo bayana” Daddy ya faɗa tare da kwashe duwatsun kan teburin ya nufi wani ɗaki da ke cikin ofishin.Haka na bi su da kallo har suka shige ina jin lokacin da aka murɗa key ta ciki,na ja ajiyar zuciya tare da zagayawa na zauna kan kujerar da Daddy ke zama .Kamar an mitsike ni na jawo ɗan ƙaramin aljihun table ɗin,wani ƙonanen agogo na gani na ɗauke shi ina dubawa a kallon farko na gane na Abakar ne don ga farkon sunansa nan da na mahaifinsa a jikin ƙarfen kamar yadda duk wani soja da za a bai wa ita ake masa haka.Mayar da ita na yi na soma bincike har na kai ga liste ɗin sunayen waɗanɗa suka mutu,a nan ne na gano ita gawar Abakar sam ba a ganta ba.Jikina har rawa yake wurin maida komai yadda yake kafin na fito,tuni sojawan har sun shiga motoci riƙe da bindigogi.


Na je kusa da babban Sojan da ke kula da duk wani yaƙi ko tafiya in ta kama na ce “ a wacce mota zan shiga?”
“ Banda sunan ka a jerin sunayen da Shugaba ya bani ikon na tura” ya bani amsa.
“Saboda me?”
“Ƙila don ba ka daɗe da dawowa daga mission ba”
“Amma ya na ga har da waɗanda a tare muka dawo ɗin wasun su na ciki?”
Ya dube ni da kyau ya ce “ mahaifin ka za ka tambaya ba ni ba” ya na gama faɗa yayi gaba ya bar ni nan.Ina ji ina gani motocin suka fita suka bar ni,ina cikin wannan takaicin Daddy ya aiko kira na.Ina shiga Sergent Yakubu ya fita ya bar mu,“zan saka wani aiki ne ka cike min takardun nan,sannan ka binciko min bayanai dangane da ƙauyukan nan” ya faɗa tare da miƙo min tulin takardu.Na karɓa har zan fita ya ce “zo ka zauna a nan ka yi” ban musa ba na ja kujera na soma cike takardun ,in jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa har sai da na ji muryarsa ya na cewa “Ammyn ka ta kira ni ...” sai kuma yayi shiru ya na kallona,na ce “mi ta ce ma?”
“Za ta zo nan gida”
Na ci gaba da abin da nake kafin na amsa masa da “eh na sani”
“Zuwan nata ne ba na tunanin zai haifar ɗa mai ido,ka san halin ta ba ta ƙaunar zaman lafiya”


“Shugaba wannan fa tsakanin ku ne bai kamata ka shigo da ni ciki ba” na faɗa ina mai kwashe takardun,na fita.
Motata na shiga ban zarce ko ina ba sai ɗayar Compagnie ɗinmu inda a can wurin kwana yake.Ɗakin na buɗe,duk yadda na so kar na yi tunanin Abakar abu ya cuttura.Rabi da rabi na yi aikin,sallah kawai ke tsayar da ni sai dab da magrib na fito na nufi gida.Bayan na yi parking sai da na ɗan zauna na wani lokaci kafin na fito,da sallama na shiga falon idona ya sauka kan Ammy.Da sauri na je gabanta na gaishe ina mai gaishe ta,cike da fara'a ta amsa ta na tambaya ta ya aikin na amsa “Alhamdullah”


Granny ta ce “baƙauyar amaryar ka ta zo,sai kuka take da rantse-rantse ita ba za ta haura saman bene ba”
Shiru na yi ban ce komai ba,na miƙe na ce “Ammy zan je na yi wanka lokacin magrib ya gabato”
“A fito lafiya” ta faɗa ,ni kuma na wuce na fara taka matakala kenan na ji muryar matar Daddy na cewa “Baby ga IBRAHEEM ɗin nan sai yanzu ya shigo,kaiii?” ta wani kira ni kamar ƙaramin yaro ko waigawa ban yi ba na idasa hayewa.
Ina tura ƙofar falon wani ƙamshi ya ziyarce ni,na lumshe ido ina shaƙar ƙamshin kafin na wuce bedroom.Allah na gani sam ban lura da ita ba sai da na ji uban ihunta,“na shiga uku na lalace mugun abu soja na a gabana?” ido kawai na zuba mata duk uban ihun nan na zata tsoro ta ji wai ashe murna ce take ta ga soja .Rikitatun idona na zuba cikin nata,da sauri na ga ta je bayan labule ta ɓuya kafin ta fara leƙe ban ce mata komai ba na je gaban mirror na yi tsaye idona na ga sun yi ja sosai.
“Je ki waje” na faɗa dakyar don so nake na canza kayan jikina .


Da gudu ta fita ta na bangaje ƙofa, cire uniform ɗin na yi kafin na shiga toilet wanka na yi haɗi da alwala sannan na ɗauro towel daidai ƙuguna.Kan bed na tarar da ita ta zuba uban tagumi,muna haɗa ido ta ja blanket ta rufa ta na karkawa har gadon sai da ya dinga rawa ta ce “yi haƙuri....”cikin raunataciyar murya ta na mai fashewa da matsanancin kuka mai cin rai.
Na rumtse ido,a duniya in akwai abin da na fi tsana to kuka ne shi yasa ma ban cika son yara ba .Ina shirin fara shafa mai na ji sai ƙara ƙaimi take wurin kukan,zuciya cunkushe na nufi bed na zauna tare da yaye blanket ɗin.Da sauri ta yi baya ta na curewa wuri guda,kamar mai koyon magana na ce “ mine ne?” shiru ta yi bata bani amsa ba,“ ban son kukan nan ki yi shiru”




Cike da ƙurciya ta ce “ tsoro nake ji”
“Tsoron me?”
“Matakalar bene kuma ...kuma ni ban son nan wurin Ammy nake so kar ta tafi ta bar ni ban san kowa ba” ta bani amsa ta na shasheka kamar ranta zai fita.


“Ni wane ne?” na jefo mata tambayar ba tare da ni kaina na shirya ba.Ta buɗe fuskarta ta tsure ni da manyan idonta,kafin ta ce “abokin Ya Abakar wanda azzalumai suka kasheee” shaaa kuma sai wasu hawayen tare da ɗaukar wani sanfarin kukan.Ji na yi tamkar ta taƙalo min wata masifa daga can ƙasan zuciyata,raɗaɗin rashin Abakar ɗin ya dawo min sabo dal kamar yanzu ne aka shaida min mutuwarsa.A duniya tun da nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login