Showing 6001 words to 9000 words out of 29175 words

Chapter 3 - Rainon Soja Book 2 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt

13 Jan 2025

4293

mene wannan tijaran nasa yake nufi kawai saboda nayi hugging ɗin ta. Ya manta Meye ban sani ba na jikin Ma'eesha. Hattara tsarki Ni nake yi mata amma a yanzu yake faɗa mun munanan maganganu....ko yana tunanin ina jin wani abu dan gane da ita...Aikin banza sai na shayar dashi mamaki tare da shi za'a yi mana baiko dole na fidda ɗaya a cikin biyu , Maryam ko Mimi. Hummmm....sauke numfashi yayi mai huci kana ya cigaba da maganar zuci da cewa “ Duka ba zaɓi na bane....Mami ke liƙa min su , a wannan karon i must accept it. Dole na zabi ɗaya don na ƙaryata tunanin Khalil akaina da Ma'eesha.............✍🏻






Tom kunsan night update Babu yawa🥱 mu tara ana safe lafiya....muje yanda al'amarin zai kasance . Shin waye Mimi??? Sannan kuma Wacece Maryam? Wacce a cikin su Ali gadanga zai zaɓa😄 ya kuke kallon wanga tafiyar......ku Cigaba da biyo alƙalamin mamanteddy✍🏻 . Yau inshallah zamu bude Comment GRP don jin sharhin ku bisa ga wannan labari na rainon soja.......!
[12/20/2023, 7:52 PM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*






Page 15
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*


#Always Alhamdulillah🙏🏻 ________________________


Da wannan tunanin ya nufi falon Mami inda Ya tadda su duka a Dinning table suna breakfast. Takawa yayi yana isa gare su tare da jan kujera yana zama , Bin sa da kallo Mami tayi a ranta tana cewa “ Da'alama Khalil ne ya hana shi wahalar da Ma'eesha da wannan masifaffen morning exercise ɗin nasa”. Dariya ta Gimtse ganin yanda yake cika yana batsewa ita dai Ma'eesha tun da ya zauna tayi ƙasa da kan ta tana sabgogin ta don bata son su haɗa ido bare ya ce tayi wani laifin. Gaishe da General Saleh yayi kana y juya yana ma Mami Barka da Safiya...daga nan kuma ya ɗaure fuska yana mami na fara serving din shi ....Kallon Mami yayi yana cewa “ Mami kina gida gobe? ”.


Ɗago fuska mami tayi tana kallon sa kana ta ɗan Girgiza kai tare da furta “ A'a gobe ina so na leƙa gidan Hajiya na gaida ta ....da wani Abu ne Haidar?. Girgiza kai yayi alamu a'a , yana Cigaba da Karin kumallon sa....Sam Ma'eesha ta' rasa' samun natsuwar ta , haka ta kasa sakin jikin ta .


Kallon Haidar tayi tare da kallon Daddy cike da zazzaƙar Muryar ta wanda tana fara magana Haidar ke furta yi mun shiru ki rage mun murya. “Daddy Uncle Haidar gobe zai koma ko yaushe? ...Dariya ne ya kama General Saleh Wanda sai da yayi mai isar shi kana yace“ Ma'eesha bagaki ga Uncle ɗin naki ba? Ki tambaye shi mana....ya kare maganan yana kallon inda Ali Haidar yake ,yana jin duk abun da suke cewa amma tamkar baiji ba ko baya a gurin. Muryar Daddy ne ya katse su yana Cewa “ Ali kayi shiru Ma'eesha fa tambaya take yaushe zaka koma? . Dariya mami ta sheƙe dashi tana buɗe baki zatayi magana Muryar Jidder ya katse su wanda cike da masifa ta furta “ Tun da gidan na uban ki ne dole ki ƙosa ya koma ”.


Shiru Ma'eesha tayi ta tsaya turusss gwiwar ta yayi sanyi qlau.


Wannan wacce irin ɗabi'a ce kike dashi Jidder? Wani irin mugun hali ne ke gareki? Ina yawan faɗa Miki ki kiyaye mawa Ma'eesha billahil Azeem ranar da na shige Miki ba zakiji da daɗi ba ......! Mami ta furta tana ƙanƙance idanun ta cike da faɗa don ranta ya ɓaci. Muryar General Saleh ne ya katse su yana furta“ Maza Ma'eesha kiyi karin kumallon ki ,idan kin gama kizo Falo na yau zancika Miki alƙawarin ki ....Buɗe baki Ma'eesha tayi tana wangalewa tare da washe shi tana furta “ da Gaske Daddy?”.


Ƙwarai kuwa....” Gimtse fuska Jidder tayi Khalil na kallon ta yana zabga mata harara.
**
Da hantsi wuraren ƙarfe 12 na rana bayan Mami ta tafi gidan Hajiya tsohuwa mahaifiyar General Saleh Yelwa...tun daga falon farko har zuwa na tsakiya zuwa Ɗakunan barcin su kowanne shiru kake ji tamkar babu ɗan adam a cikin gidan . A dai-dai wannan lokacin ne Ma'eesha ta zauna tsakiyar gadon ta tana Fiddo da littafan ta tana karatu . Ɓarayi guda al'ƙur'ani ne da ta gama karantawa kamin ta fara na karatun boko . Gyfen ta ruwa ne wanda ta dauko daga ƴar ƙaramar fridge ɗin ta . Littaffin ta na Chemistry take karantawa duk da kasantuwar Hutu suke yi a wannan lokaci amma hakan bai hanata kullum kasancewa cikin karatu ba . Atom and molecule take karantawa tanajin daɗin karatun don sai da ya fito masu a exam nasu na wannan zango . Hummmm.....numfashi ta ja tana saukewa tare da Lumshe Idanun ta , fuskar Ali haidar ta gani wannan yasa gaban ta yankewa yana faɗi da ƙarfi dafe kan ta tayi tana saurin ware idanun ta. Zuciyarta kawai taji ya tsinke tsoron jarabar sa take yi a ko yaushe.


Motsin Handle door ɗin ta yasa ta saurin kallon direction ɗin tana kara zare ido tamkar wanda tayi ƙarya , a halin yanzu tasan Ya Khalil baya cikin gidan nan don wuraren 11 yazo ya same ta yana faɗa mata zai tafi wurin zaitoon budurwar sa da'akayi masu baiko , har yana tambayar ta abun da zai zo mata dashi na tsaraba anan tace masa cup cake take so....Don mai masu kayan snack jidder Wancen satin tayi mata bakar tijara , Tom kasantuwar itama tana da Dan ilimin ta kawai dai tana son sana'ar snacks ne yasata yin mawa mami wannan hidimar ana biyar ta duk wata . To a wannan karon Jidder da tayi mata zagin tijara takasa Haƙuri don dole ta bar aiki a cikin gidan . Tabbas a yanzu tasan daga ita sai jidder sai kuma dodon nata Aliyu Haidar wannan yasa tana jin motsin Handle duka ta maida hankalin ta idanun ta duka ga ƙofan....“Daaaam”. ƙirjin ma'eesha ya buga ganin Haidar ya shigo yana zuba wani irin Sanyayyar ƙamshi gaba ɗaya wurin ya mamaye da ƙamshin sa . Sam bata san wani duniya take ba har ya iso inda take kana taji Arrogant voice ɗin sa ya katse ta yana cewa “ Keeee dallah rufe baki , kin wani saki baki kaman sakarya.


Kallon sa tayi cike da danne fushin ta don maganan sa ya ɓata mata rai ta kalle sa tana sakin Murmushi Gyefe da gyefen kuncinta na loɓawa . Uncle Barka da rana. Hummmm Me kike yi anan ? Yayi maganan tamkar bai ga littafai a gaban ta ba , Cigaba yayi da cewa“ Dama naji labarin Daddy ya saya Miki waya har da sabon laptop saboda gata . Baki iya komai ba sai sangarci....Humm yayi ƙwafa yana kallon ta tare da zuba mata Lulun idanun sa . Cike da nuna irin ke ya dama yace “ Kar ki manta ke yarinya ce karama SS1 yanzu ne ya kamata kiyi amfani da damarki, sannan charting kar ki so ranar da zan duba wayar ki naga kina ko wani irin media bana son ganin Film ko wani iri a laptop ɗin ki ko a wayar ki duka . Fatan kin fahimce ni?. Y furta yana mai Gimtse fuskar sa babu wasa . Cikin sauri jikin ta na kyarma kar-kar-kar ta gyada masa kai tana cewa “ Ehhh Ehhh..eh Ya khal....Ya Haƙuri Uncle ba zan yi ba Wallahi . Gani tayi ya kafe ta da ido kaman a wannan ranar ya fara ganin ta a rayuwa . Sosai ya tafi tunani na yan sakonni kana ya furta “Kin iya girki? Kamin ta basa amsa ne ya furta“ Ko da yake shekarar ki nawa a yanxu ace baki iya girki ba . Maza miƙe yau wanda tunanin zan iya aure zasu zo . Mimi da Maryam. A cikin su i must choose one ko mimin ko Maryam amma dole sai nayi masu jarabawa wacce taci ita nake tunanin..........Shiru yayi yana kallon Ma'eesha da ta zuba masa ido yana sauraren sa . Tashi ki bani wuri ki ɗaura masu Abinci kala ɗaya ya isa . Sai lemu da ruwa . Ki haɗa masu da farfesun naman rago.


Idan kin ɗaura girkin ki tafi bedroom dina ki gyara mun ba falo ba.


Gyaɗa masa kai tayi tana sauka daga gadon tare da ƙoƙarin ficewa daga Bedroom ɗin .


Ma'eesha kin iya jaloaf rice ne?.


Ɗan ƙasa tayi da kanta a zuciyar ta tana Cewa “ Oho dama kasan ban iyaba ka sani ..ai na bari ne nayi maka sai kaci kai da ƴammatan naka ,dagani basa da kamun kai tun da har zaka haɗa su wai kayi masu jarabawa. Shi me yake taƙama dashi ne wai? . Keeee ba magana nake Miki ba ?.


Ɗagowa tayi tana motsa masa ɗan motslun bakin ta tare da cewa“ A'a ban iya ba”. What? Baki iya girki ba? Shekaran ki nawa suke? Kalle ki ? A girki baki iya komai ba kike so Kice mun?. Ɗan jimmm tayi tana tunanin furucin Hauwa mai girki da takance mata idan zaki fara girki indomie zan fara koya Miki yafi duka sauƙin iyawa. Cikin sauri Ma'eesha tace da Aliyu “ Dadd.... Sorry Uncle na iya indomie. Tsayawa yayi yana kallon ta yana nazari kana yace tafi ki yomun jalaop na indomie ki kawo mun .




Tom guda biyu ko uku .
“Biyu ya furta yana kallon ta ”. Juyawa tayi tana saurin ficewa shima yana takowa tare da biyo bayan ta yana zama a tsakiyar falo na biyu .


Kaman mintuna biyu yaga Ma'eesha ta fito daga kitchen din tana nufar ɓangaren sa . Da yake shi ba mai yawan surutu bane ba , shiru yayi mata yana rakata da ido har ta shige Zuciyar sa na mamakin yanda ta tafi ta bar gass wanda a minti biyu ruwan indomie ya juya ta zuba . Cigaba yayi da latsa wayar hannun sa yana duba Yanayin weather din garin . Har mintuna kusan goma Ma'eesha bata fito ba. Wannan yasa Aliyu miƙewa yana bin bayan ta .


A Bedroom ya tadda ita tana tsugune bangaren mirror din sa tana tsince kwalban turaren sa da ta rotsa da ƙasa .... Ma'eesha! Ya kira sunan ta yana bin ta da wani irin kallo wanda sai da Hantar cikin ta ya kaɗa.....jikin ta ne ya hau kar kar kar....saurin mikewa daga tsugunnen da take tayi tana yin rau rau da ido kana tace “ Don Allah Uncle kayi haƙuri Wallahi Ni yarinya ce mami tace saurin girma nayi......🤣. Sakin baki yayi yana mata kallon mamakin magana nata . Tayi masa laifi tana cewa ita yarinya ce saurin girma tayi ?. Fita ki bani wuri kije ki kawo mun indomien ina jiran ki anan mintuna biyar na baki yanzu ki kawo mun .


Gyaɗa masa kai tayi da gudu tana nufar ƙofa .cike miskilalliyar Muryar sa ya kuma kiran sunan ta cakkk ta tsaya kana yace “ Minti nawa nace Miki?. Da sauri ta furta “Five minutes ”.




Lumshe idanun sa yayi yana mata alama da okay kana ta fice da sauri tana nufar kitchen din. Da kanta take haɗa masa komai kayan yaji kaɗan maggi kuwa bayan na indomie din sai da ta zuba me star huɗu da onga biyu duka a cikin indomie ƙwaya biyu . Wani irin ruwa ta zabga shi cimbul a tukunyar tana zuba indomien don ta zo taga yana ta tafasa . Zubawa tayi tana cewa “ Na shiga uku anya ba sai na ƙara ruwan ba , na gode m ALLAH da Uncle bai zo ya ga ruwan nata tafasa ba. Rufe ƙaramar tukunyar tayi tana ja baya tare da kallon tsintsiyar hannun ta tana dubawa mintuna uku kenan . Kallon gass din tayi tana miƙa hannun ta tare da bude indomien da ta ganshi ruwa ya taso sama indomien na ƙasa daga gyefe saboda tsaban ruwan da yayi yawa . Alhamdulillah nasan yau Uncle zai sha mamakin girkin nan ,don ko ba'a faɗa ba kai daga jin ƙamshin sa kasan yayi daɗi ƙwarai . Tana maganan ita ɗaya sai farin ciki take yi yau shine da girkin ta na farko kuma Uncle ne zaici😌Hummmm Uncle zaici Dadi yau 🤣 .ko kuma Ma'eesha jibga zata sha Allah masani....mu tara page 16 na safiyar gobe inshallah . Yau nayi matuƙar busy ne shiyasa kuka ji shiru har wannan lokacin. Ina maku fatan alheri.




*Don Allah kar wacce ta karanta mun ba tare da ta biyani ba regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202032...Maman-teddy*
[12/21/2023, 8:08 AM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*






Page 16
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*


Morning update🕊️________________________


Tana Tsaye Indomie ɗin ya fara kama jikin sa alamun ya nuna luguf yayi ga uban ruwa da yayo sama . Sam bata damu da ganin wannan ba ,don a ganin ta Mami irin shi take masu . Plate ta ɗauko tana juye masa duka tare da saka Fork , tana ɗauka zata fito zuwa falo . Cakk ta tsaya tana Faɗin Ai ban saka masa Ƙwai ba . Ɗan juyawa tayi tare da kallon saman kitchen cabinet ɗin tana bin inda ake aje ƙwayayan da kallo . Kai gaskiya ba zan tsaya dafawa ko soyawa ba . Dole sai dai Na zuba masa kifin Gwangwani.


Hannun ta takai tana sauke plate ɗin tare da aje shi bisa cabinet ɗin tana ɗauko kifin Gwangwani tana juye masa duka a ciki kana ta dauki plate ɗin indomien tana nufar direct ixuwa falon sa . Zaune ta tadda shi ya harɗe ƙafarsa tamkar wani basarake. A gaban sa ta aje plate ɗin tana komawa tare da zama kusa dashi tana bin bakin sa da yake motsa laɓɓansa a hankali wayan sa na kare da kunnen sa . Duk maganan da yake yi babu ɗaya da taji.


Ɗan shiru Ma'eesha tayi kana a zuciyar ta tace“ Tab a haka ita wacce yake magana da itan tana ji ? Zama dashi kaɗai wanda yayi wahala yake sha , to inaga wacce tayi gigin fara soyayya dashi kuma?. Muryar Aliyu ne ya katse Ma'eesha yana cewa“ Ɗauko mun ki bani naci ”. T...tom . Ga furta tana saurin yin ƙasa tare da ɗauko masa plate ɗin indomien tana miƙa masa .


Lulun Idanun shi ne suka duddulo waje yana bin plate ɗin da indomien ciki da wani irin ƙazamin kallo . Rintse idanun sa yayi yana ji tamkar yayi mata duka da ita da indomien. Uncle yaune girki na na farko , kuma nasan yayi daɗi sosai ka cinye sai na ƙara girka maka Wani yanzu.........Ma'eesha! Ya kira sunan ta cikin wani murya da ta kasa tantancewa .wannan meye kika yi kenan? Is that how to cook indomie? Haka kika ga mami nayi? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..... Gaskiya Mami ta sangarta ki da yawa babu abun da take koya Miki tsawon wannan lokacin sai sangarci duka kin lalace wannan me kika girka mun faɗa mun naji yanzu ko nayi ƙasa ƙasa dake anan Wurin ....!!!




Ya furta cike da doka Tsawa yana kallon indomien da ransa ya gama hasala baki ɗaya .


Hannun Ma'eesha kyarma ya kama yi tsoro na ɗarsuwa ma Zuciyar ta . Bakin ta na rawa ta furta “ Ba indomie bane ba ”. To menene sunan wannan abun da kika girka?”. Hawaye ne ya fara bin kuncinta narke fuska tayi tana fara kuka ko ina na jikin ta kyarma yake yi kar kar kar na tsoro. Kayi hakuri Uncle kar ka bugeni don Allah.


Sunan Abun da kika girka mun zaki faɗa idan kuma ba haka ba tabbas yau zan zane ki bari na ɗauko.....Saurin saka hannun ta tayi tana riƙe ƙafafun sa tare da ƙara fashewa da wani irin Raunanniyar kuka . Uncle na tuba kayi hakuri zan maka Wani yanzu....Wallahi zan maka wa.......Ma'eesha wasa dake nake yi? Yayi maganan yana haɗe gira , hannun sa yasa yana ɗago hannayen ta daga jikin sa kana ya cigaba da cewa“ Sau na uku kenan ina tambayar ki me kika girka mun , idan nayi na huɗu wallahi mai ƙwatar ki a cikin gidan nan babu......Ƙafafun ta sun kasa tsayuwa da kan su. Ji tayi tana baya tamkar zata zube anan Wurin . Kuka take yi sosai har da shashsheƙa kana tace“ Talia ne ba indomie ba”.


Talian wata ƙasa ne wannan? Ba dai Nigeria ba ko ?.


Ɗaga masa kai tayi tana faɗin eh . Okay maza zauna ki cinye mun shi tasssss ke da kika girka. Cikin sauri tasa hannun ta tana amsan plate ɗin tare da zama gyefen sa inda yake nuna mata da hannun sa . Ɗauke Fork ɗin yayi yana mata alama da ta sa hannun ta , wanda babu musu Ma'eesha ta kai hannun ta tana diban indomien tare da kaiwa bakin ta .


Wani irin ɗauke wuta tayi jin taste ɗin girkin da bata taɓa ji ba a bakin ta . Maggi kuwa har wani circulating brain ɗin ta yake yi . Lahaula wala ƙuwata na shiga uku ....Uncle babu daɗi ba zan iya ci ba . Wani irin kallo yayi mata yana furta “ Tun kina yarinya abun da kike cewa kenan , always you can't....yau sai kin cinye abincin nan Tassss kuma ki gama ki ƙara girka wani idan bai daɗi ba ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login