Showing 18001 words to 21000 words out of 29175 words
Chapter 7 - Rainon Soja Book 2 Complete Hausa Novel By Maman Teddy .txt
a ranta da zuciyar ta . Ma'eesha ƙanwa ce a gare ka .
“Ohhh Mami ” ki daina faɗin haka , Ma'eesha ba ƙanwata Bace mami nine fa Aliyu , Ai Ma'eesha ƴa ce a gare Ni . Wanda na ɗauke ta da hannu na kuma na Raine ta . Mashaallh Uban san girma , na baka Ma'eesha a yanzu ma .... Ma'eesha na! Ta kira sunan ma'eesha da ta zuba mata lumsassun idanun ta kamin tace “ Na'ma Mami”.
Kin shirya Uncle Haidar ya ƙara Miki RAINON SOJA a karo na biyu?. Zai kula dake sosai ina da yarda dashi da amincewa da zai kula mun dake 💯 . Cike da Yarinta ta saki Murmushi tana gyaɗa kan ta tace da cewa “ Eh mami nasan Uncle zai kula dani sosai . Muje fara shirin tafiya 💃🏻 nidai kam sai da ɗan hawaye ya tsillo daga ido na😢 don na tausaya ma Ma'eesha a hannun Ali haidar a wannan karon ”.
Tana Rungume a jikin mami suka nufi bedroom din ta suna barin falon . Jidder taso hana wannan tafiyar amma kuma bata da yanda zatayi saboda Tafi son taga ta raba Mami da Ma'eesha kamin ta dawo ta ɓanɓareta ta da Haidar,amma ita har a yau so take taga Ta bude ido Ma'eesha ta bar cikin gidan .
**
7:00pm.
Zaune suke duka a falon Daddy kowa da Abin da yake yi. Ma'eesha na gani daga ƙasa inda Ƙafar Daddy yake tana rungume da yar teddy din ta Pink mai kyau tana murmushi alamun Daddy wani maganan yake faɗa mata . Ɗagowa tayi tana kallon Khalil da shima ita yake kallo . Sosai yake tsintar kansa cikin yanayin jin daɗi a duk lokacin da yaga murmushi a tare da Ma'eesha ”. Ya Khalil i will miss you ”. Ta furta tana kallon sa . Murmushi yayi yana danne abun dake taso mata kamin yace “ i will miss you too Ma'eesha na”...Da Sauri Ma'eesha ta miƙe tana nufar inda Khalil yake tare da rungume shi.... Rungume ta yayi yana murmushi tare da cewa "nan kusa zaki dawo ai . Wani irin zafi Aliyu................!
*Ban yarda ki karanta mun baki biyani ba . Wanda ya karanta shi da Allah . Masu ɓukatar regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank*
[1/6, 4:25 PM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
23
Barkan mu da dawowa wannan tafiya da muka ɗan jinkirta wurin kawo maku shi ,hakan ya faru ne Sakamakon ɗan rashin lafiya da nayi ,amma yanzu jiki alhmdlh komai normal💃🏻 ina sauraren sharhin ku tare da fatan Alheri ina kuma godiya sosai . Taku Ayshatu Mrs Usm...(Maman-teddy).
*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya kudin littafin ba . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 yan Niger katin Artel zaku tura na 500f*
Wani irin zafi Zuciyar Aliyu keyi ganin yanda Khalil yasa hannayen sa biyu yana rungume Ma'eesha cike da kulawa . A hankali Zuciyar sa ta fara tambayar sa da “ Me yasa kake jin zafi a duk lokacin da kaga Ma'eesha da Wani ɗa namiji bayan kai koda kuwa jinin ka ne? . Ɗan lumshe dulu-dulun idanun sa yayi yana ba kansa amsa da cewa “ Saboda ina son kare mutuncinta ne ,don babu wanda yasan darajarta da ya wuce Ni . Su duka sauran ganin ta suke kamar kowacce ƴa , Ni kuma a jinin jiki na ke jin ta . Wannan shine banbancina da su . Shi kuma yasa nake jin zafi a duk lokacin da na ganta tare da Wasu maza . Saboda maza basu da tabbas.
Ma'eesha ya kamata kiyi barci yau da Wuri kar gobe kiyi mun barcin mota . Don NDA zamu fara zuwa daga can mu wuce Aviation .
Muryar Aliyu ya katse su , yana mai zuba idanun sa zuwa inda Ma'eesha take zaune a jikin Khalil suna magana ƙasa ƙasa wanda babu mai jiyo su . Wato yarinyar nan har Tasan ta rinƙa irin wannan maganan amma bata iya girki ba? Zata sani ne? Duk wani kalan girki sai kin iya shi haka Aikin cikin gida , don ko Bedroom baki iya gyaran shi ba . Wannan ɗabi'un naki duka basu yi mun ba dole na sauyaki zuwa yanda nake SO .
Duka maganan yake a zuciyar sa , yana yi yana ɗaura yatsunsa bisa pillows din dake Daga saman Cushine ɗin da yake zaune ,yana matsasu ji yake tamkar bakin Ma'eesha yake matsawa da ƙarfi haka don ya ɗau Aniyar ganin ya saita ta yanda yake So, don a ganin sa Sangarta ta Mami tayi ba tarbiyya ta bata ba . Muryar Mami ne ya katse su inda take cewa “ my baby A tashi haka nan , nasan ki da son barci kinji tun yanzu sharuɗan da ya fara yi Miki . Nifa Ali indai wannan tafiyar taka da Ma'eesha da takura wahalar mun da ƴarinya zaka yi Tom a haƙura , Nima ba SO nake nayi nisa da ita ba ” . Mami ta ƙare maganan tare da Watsa ma Haidar kallon uku saura ƙwata .
Cike da Ƙwantar da kai da murya Ya furta “ Mami please ki daina tunanin komai fa , Ma'eesha tawace! ....gigif Khalil yayi yana miƙewa daga kishingiɗen da yake bisa ga jin Furucin Ali Haidar ...Muryar Aliyu ne ya cigaba da cewa “ Ba zan Wahalar Miki da ita ba , cool your mind please ” . Hummmm ... Mami ta sauke wani gauron numfashi kana tace “ Alright ga Amanata nann” . Uhmm Mami kenan . Nifa mamaki kike bani wallahi ...Haidar ne zaki ba Ma'eesha wai kuma kike tunanin ba zai wahalar da ita ba? Ai kima bar wannan tunanin Allah dai ya bata ikon cinye jarabawa ”.
Dariyar Mugunta ne ya kusa kama Jidder don ita a rayuwar ta bata da Burin da ya wuce Taga Ma'eesha cikin mawuyacin hali . Amma sai ta dake tana cigaba da latsa Wayar ta tare da karƙaɗa ƙafa ɗaya .
Buɗe baki Mami tayi tana shirin magana Muryar General Saleh Yelwa ya katsesu da cewa “ Ya kamata yanzu fa kusan kun girma haka nan. Khalil Haidar , wai yaushe saɓani ya fara shiga tsakanin ku? Ƙwata² babu jituwa kaman ba kaine Ali haidar mai tausayin Yayan ka ba . Mai kuma haƙuri da masa biyayya....Kai kuma Khalil kamar ba kaine babban Yaya ba , Wanda koda ya ɓata maka kake dannewa Bama kason mu sani . Please ku cigaba da yanda kuke a da baya . Abun naku yana neman zama sakarci kuma na rasa gane menene ya kawo maku wannan rikicin haka!
Tsit...!!
Falourn yayi har Daddy yayi maganan sa ya gama , sai Muryar Mami da ta furta “ Suma dai yi , Ni nawa ido , zasu daina ,abin da basuyi farkon shi ba ai baxasu yi ƙarshen sa ba. Ma'eesha na taho muje kiyi barci .
“Da sauri Ma'eesha ta miƙe tana kallon Mami kana ta saki Murmushin nan nata tana cewa “ No mami zan ƙwanta ba sai kinzo ba . Wankan kuma fa? .
Muryar mami ya katse ta , wanda jin haka yasa ta saurin juyawa tana kallon inda Ali Haidar yake , gabanta na bugun uku² , a Zuciyar ta tana cewa “ Na shiga uku kar Fa Uncle yace Har Wankan ma ban iya ba naja ma kaina ”. Shagwaɓe fuska Ma'eesha tayi tana cuno ɗan mitsulun bakin ta tare da cewa “ Mami nifa ba kya mun wanka tuntuni Ni nake yin abu na ”. Dariya Daddy da mami suka saka harda Khalil .....Wannan yasa Ma'eesha juyawa tana barin falourn , Don sun fahimci Ma'eesha ba son zancen wanka take yi ba a gaban su Khalil da Haidar .
Kaman mintuna biyu Khalil ji yake tamkar ana tsingulunsa , Abubuwa da yawa na cunkushe a cikin Zuciyar sa . A hankali yakai hannun sa yana dafe ɓarayi guda na Zuciyar sa kana ya rintse idanun sa .... lokaci guda Idanun sa sun sauya kala sunyi jah....miƙewa yayi yana kallon Su mami kana yace “ Ammmm Bara na duba Ma'eesha ta ƙwanta kuwa! . Uhmmmm aifa duba mun ita , don kwana biyu bata barci sai Game a laptop ɗinta tun da suka samu Hutu itama take Hutawa abinta. Mami tayi maganan tana bin bayan Khalil da kallo don tuni ya nufi hanyar da zai kaishi zuwa Bedroom ɗin Ma'eesha ”.
Ɓangaren Aliyu kuwa tun da Khalil ya miƙe yaji jikin sa bai basa ba , wannan yasa shi Oga ne 😎 bai tsaya yi ma kowa magana ba yayi gaba yana nufar Bedroom ɗin kansa tsaye.
Hannun sa yasa a Handle Door din yana ƙoƙarin murɗawa yaji furucin Khalil daga ciki wanda sai da Ƙirjin sa ya buga da ƙarfi . Wannan yasa shi dakatawa yana Sauraren kalaman Ma'eesha ”.
Ya Khalil Menene? Meke faruwa ya Khalil? Tana maganan Muryar ta na rawa alamun kuka ....Muryar ta ne ya cigaba da Amon cewa “ Ya Khalil ƙwallah ne fa nagani ko nace hawaye a ƙwance a idanunka . Hummmmmmmm Jan Ajiyar zuciya yayi yana saukewa kana yace “ Yessss Ma'eesha hawaye ne wannan sannan kar kiyi mamakin ganin su” .
Ya Khalil menene ya saka ka kuka? Mene ya faru? Kukan......Shiiiii ɗaura yatsarsa yayi bisa laɓɓanta yana katse zancen nata kana yace “ Sorry dear Kece kike saka zuciyata wannan kukan tuntuni wanda a yanzu ta kasa daurewa da jurewa har idanuna sun fara zubda Ƙwallah ” .
Jikin ma'eesha ne ya hau Rawa , ƙwallah na ciko idanun ta . Cikin kuka ta fara furta “ Ya Khalil me nayi maka Ni? Ka faɗa mun na baka haƙuri ”.
Numfasawa yayi kana cikin wani irin sarƙaƙƙiyar murya ya furta “ I love You Ma'eesha.... Nasani ya Khalil nasan kana so na , nima ina Sonka. No! Ba Wannan soyayyar ba. Son ki nake Don Allah Ki Aure Ni mu rayu tare A matsayin miji da mata😱 yayi maganan yana zubewa Gwiwowin sa ƙasa a gaban ta😢 . Wani irin bugawa ƙirjin ma'eesha keyi ....cikin Muryar kuka ta furta.........................!
*Ban yarda ki karanta mun wannan labarin ba tare da kin biyani ba . Don Allah kar a soma ayi hakan . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 ƴan niger katin Artel 500f zaku turo🙏🏻.*
[1/7, 3:59 PM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to MAMAN TEDDY channel @youtube.
24.
Ya Khalil nifa ƙaramar yarinyace kai ne fa naji kana yi ma Anti Jidder faɗa kan karta fara soyayya! “Yesss”Na sani Ma'eesha, amma tawa soyayyar ba shiririta bane irin nasu . I really......A'a Ya Khalil Anty Maryam fa? Kwanan fa Za'a yi baikon ku . Muryar Ma'eesha ya kuma katse ta wanda har kyarma jikin ta ke yi . Ma'eesha!!! Ya kira sunan ta cikin wani irin Murya wanda bata taɓa jin sa da irin ta ba . Hummmm .... Furzar da Huci yayi kana yace “ Ma'eesha Ni SOJA ne , duk Abinda zai saka Soja ya gurfanar da kan sa da Gwiwowin sa ƙasa ba ƙaramin abu bane ba , babba ne , wanda girmanta ya kai Akira wannan abun da rayuwar sa . Ma'eesha idan na rasaki numfashi na zai dakata da Aiki . Ina nufin zan zaɓi mutuwa da Rayuwa ta😭”. Dam-dam-dammmm ƙirjin Ta ya buga da ƙarfi ....cikin Muryar matsanancin kuka ta furta “ Sorry Ya Khalil ina Sonka”. Wani irin baya Aliyu yayi da yake jikin ƙofan yana zame hannun sa a hankali duhu duhu na gilma ma idanun sa . Ji yayi jikin sa yayi Wani irin mugun sanyi sam babu ƙarfi a tare dashi bisa ga jin Furucin Ma'eesha na “ Ina Sonka!”. Zazzaƙar Muryar ta ne ya kuma katse shi tana faɗin “ Kar kayi tunanin bana sonka Ya Khalil kome kace nayi maka a shirye nake zan maka shi ”.
“ Cikin Sauri cike da jin Daɗi mara iyaka Khalil ya miƙe daga gurfanen da yake , Hannun sa biyu yasa yana tallabo kuncinta ta tare da saita idanun sa yana Ɗaurawa bisa nata. “Thankyou Ma'eesha , na gode!
Ya Khalil to Anty Maryam fa? Da.....shii ki manta da Wannan maganan zan Auri Maryam a wannan shekarar ke kuma zan cigaba da dakon soyayyar ki har ki girma ki kai lokacin da Daddy zai Aurar dake , A wannan lokacin zamuyi Aure mu gina Rayuwar mu cikin jin daɗi . Kece nake so ki haifa mun ƴaƴa masu kama dake ....ya ƙare maganan yana Ɗaga mata gira tare da Sakin mata murmushi kana ya cigaba da cewa “ Zan Auri Maryam ,amma ba zata haihu ba . Kece zan jira ki zo ki haifa mun masu Albarka ”.
Cike da Yarinta Ma'eesha ta gyaɗa masa kai tare da cewa “ Shikenan Ya Khalil zan yi barci yanzu ”. Alright sweat dream...ya furta yana kama ta tare da nufar Bed ɗin ta sai da ta kwanta sannan ya rufa mata bargo yana takawa tare da rage hasken fitilun Bedroom din yana nufar Ƙofar fita .
Jin takon sa yasa Ali Haidar Saurin barin wurin yana nufa falo .
A wannan dare a taƙaice sam Aliyu ya gaxa rintsawa , zuciyar sa na masa saƙa da Warwara . Inda ya kasa gasgata wani ɓangare ɗaya na Zuciyar sa . Sai dai kafewa da yayi akan cewa “ Khalil na son lalata Ma'eesha ne . Har ya fara tunanin ɗaukar mataki da fushin Zuciyar sa ,sai kuma yace “ A'a ba haka zan yi ba , Ni yanzu da zan tafi tare da ita , ganin ta sai yayi masu duka wuya .bare har ya kawo wani zancen shashanci mtsww .
**
7:35am.
Mami na hango gaban dressing mirror tana gyara gashin kan Ma'eesha da yake fidda Sanyayyar ƙamshi , ga tsawo da cika sunan ta kama mata shi ne wuri ɗaya amma Tudunshi har yayi yawa gashi ya sauko har gadon baya . Ka rantse da Allah Jinin mami ce itama wato fulani . Riga da Wando ne ta jikin ta ,irin suit masu kyau na mata . Sai mami ta ɗaura mata Hijab ƴar ƙarama wanda bai ƙare sauka kafaɗa ba ”. Turare take sa mata tana murmushi tare da cewa “ Yau sai na Lagos . Yessss Mami😄 Ma'eesha tayi maganan tana Wangale mata baki cike da fara'a kaman mai jin daɗin tafiyar ,nan kuwa dole ne yasa ta murmushin . Gyara mata fuska tayi cikin simple make Up Babu Hayaniya. I love my daughter .....Ina sonki Nima Mami ”. Hannu Mami tasa tana rungume Ma'eesha tare da cewa “ ki kula sosai kinji Eaasha na?”............!
**
Dinning room
Tun da Aliyu da Khalil suka zauna babu abin da suke yi ma juna face auna ma juna kallon banza . Duk da shi Khalil na kai Zuciyar sa nesa . Sannan duk abin da suke yi babu wanda ya gane daga gare su .
Keeee Da Allah kici a hankali ....kaman Ƴar matsiyata wanda suka fito da ga fari? . Muryar jidder ya katse su inda take doka mawa ma'eesha Tsawa cikin Faɗa da hantara . A hankali Ma'eesha ta janye Fork ɗin da take cin Irish tana Ajewa a gyefe....inda cikin Faɗa Mami ta katse jidder da cewa “ Akan ki take ne? Masifaffiyar banza kawai , Ai sauri take kada Ali ya fara Mata nashi sababin.....ku kiyaye ni duka ”.
Gummm Jidder tayi tana cigaba da Kai Cuscus bakin ta , ranta a ɓace don bata son tayi ma Ma'eesha faɗa Mami ko Daddy su katse ta .
Muryar General Saleh ne ta katse su inda yake furta “ Kici a hankali Ma'eesha ba zaki bishi ba sai kin ƙoshi kinyi nakkkk sannan .
Gyaɗa masa kai tayi kana ya cigaba da cewa “ Kai kuma Ali ina so nan da 1 mount to 2 mount kafin bikin Khalil ka fidda wacce kake so ka Aura yanda muna gama nashi sai naka . Saboda dukan ku kun isa aje iyali kuna da Abunyi da ƙarfin ku haka da Arziƙin ku ka fahimce ni?.
Shiru Haidar yayi na yan sakanni don a yanzu shi babu lissafin aure a rayuwar sa , a cewar sa Abin da ake yi ma Auren yana Samun na bati a banza a waje . Kuɗin sa nayi masa komai don haka baya sha'awar aure a yanzu .
Aliyu da kai nake yi .....Muryar Daddy ya katse shi inda cikin sauri Aliyu ya furta “ Okay Daddy inshallah kamin lokacin ma , Abun da yasa har yanzu kuka ji shiru saboda Ni ina so na Auri SOJA ce . Ma'ana matar da zan Aura ta kasace SOJA kama na ” .
SOJA...!!!!
Duka suka haɗa baki wurin furta kalmar ciki har da Daddy da abun bai masa ba sam . Ita kuwa Mami buɗan bakin ta cewa tayi “ wow that's very good, Hakan yayi sosai Haidar Nima zan so ganin hakan . Ai hadin yayi ko Janar? . Ta ƙare Maganan tana duban inda Daddy yake ya saki baki yana kallon ta .
Kamin Daddy yayi magana ne Khalil ya amshe da cewa “ No Mami Sam baiyi ba . Ni fa babu Abin da na tsana irin naga mace wai SOJA abun ba burgewa sam .
Hahahaha!
Wani irin dariya Aliyu yasa wanda duka sai da suka tsaya suna binsa da kallo . Kana ya tsagaita yana kallon Khalil tare da cewa “ I found the solution, Ma'eesha taho mu wuce ”.
Cikin Sauri Ma'eesha ta miƙe tana ma su Mami waving tare da furta