Showing 33001 words to 33825 words out of 33825 words
Chapter 12 - INDO A BIRNI BOOK COMPLETE 2020 by Rasheedat Usman.txt
ba, suka shigo tare da Innah, da sauri Innah ta ƙaraso gaban Mama ganinta tana kuka tace.
" Mairo lfy meya faru, kike wannan ajiyar Zuciya haka.
" Innah jummalo ta rasu, ta tafi ta barni Innah.
Daɓas Innah ta zauna a ƙasa tare da sakin kukan itama, sai aka rasa waye zai bawa wani hakuri tsakanin su.
Allah sarki Indo, wato duk inda dan uwa yake yana son ɗan Uwansa, kasa kuka Indo tayi, ta zauna itama kusa da jummalo, sai kuma ta tashi ta fice da gudu, ashe Baba ta kira, tare suka dawo Baba yaxo ya same su sai sharbar kuka suke.
" Haƙuri Baba ya basu tare da musu nuni da cewa, jummalo yanxu bata buƙatar kuka a garesu, addu'a take bukata, Allah sarki rai baƙon duniya, jummalo kwanan keso tayi, Indo da Innah kuwa kwana sukayi basuyi bacci ba, washe gari da misalin karfe goma aka kai jummalo makwancin ta, Indo tasha kuka Ranar har idanun ta suka kasa buɗuwa, Innah ce ta kira Baba tace yaje ya nemi waya ya sanar da Haruna rasuwar jummalo.
Haka kuwa akayi Baba ya kira Abokinsa Haruna ya sanar masa.
*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*
Hira suke ciki falon dukan su, suna zaune, har Habeeb, mustapha ne kawai baya cikin su, duban Momy Habeeb yayi yace.
" Momy akwai maganar fah da nake son na sanar dake, shi Daddy na sanar masa.
" Okey ina sauraron ka Habeeb.
" Momy daman ina son jibi idan Allah ya kaimu zan koma London, saboda ina son zan sanar dasu cewa nabar aiki dasu zan dawo gida na cigaba da aiki, so idan na koma zan tattaro duk wani abu da yake nawa na dawo, bazanfi sati biyu ba zan dawo insha Allah.
Murmurshi Momy tayi cikin murna tace.
"Alhamdulillah, daman Abunda nake so kenan Habeeb, nafi son aikin ka, anan gida Nigeria, naji daɗin wannan Albishir da kaxo min dashi, Allah kuma ya kaimu jibin lfy.
Murmurshi Habeeb yayi ya amsawa Momy da ameen sannan ya dubi, RAUDA yace.
" Ke Malama, wai yau bazamu ci abinci a cikin gidan nan bane, naga kamar baku da niyar yi.
Dariya RAUDA tayi tace.
" Kai dai kace yunwa kake ji kawai idan banda haka yaushe ma akayi breakfast, ta inda ya mustapha yafika kenan, shi babu ruwan sa, da yawan ci.
Dariya shima Habeeb yayi yace.
Wai damma shi mustapha baya gari, da yau mun gwada mun gani nida shi waya fi wani ci.
Kallon mamaki RAUDA tayiwa Habeeb, cikin Zuciyarta tace, haba shiyasa tun daya fita jiya shigota gidan nan banga ya dawo ba, ashe tafiya yayi, na shiga Uku anya wannan maganin namu akwai Sa'a cikin sa, kuwa.
Sharifa ce, tace.
" Momy da gaske ya mustapha tafiya yayi Babu Sallama yau.
Murmurshi Momy tayi tace Sharifa.
" Ehh shima baisan da tafiyar ba, sai da ya fita office ake sanar dashi, yaje inugu zasu gana da wani Criminal amma ina ga ya dawo gobe insha Allah.
" Allah ya kaimu Momy ya dawo dashi lfy.
Da ameen Dukansu suka amsa sannan Habeeb yace shi zai shiga ya kwanta.
Tashi RAUDA tayi cikin ɓacin rai tayi kitchen ita da sharifa suka bar Momy zaune a wajen.
Da dare bayan daddy ya dawo sunci abincin dare yake sanar da Momy mutuwar jummalo, sosai Momy ta taji mutuwar a jikinta, shi kanshi Habeeb yaji mutuwar domin yasan jummalo zuwan sa da yayi, yarinya ce mai nutsu da tarbiyya, gata da tausayin iyayen ta, daddy ne yacewa Momy.
" A'ishah inaga Ranar Laraba, zaku shirya gaba ɗaya zamu tafi dasina ta'aziya, da jibi nayi niyan mu tafi, to sai kuma gashi Habeeb zai koma jibin shiyasa nace, gara mu bari idan ya tafi mu kuma washe gari sai mu tafi shi mustapha munyi waya dash daga inugu zai wuce Dasina zamu haɗu acan.
" Shikenan Alhaji Allah ya kaimu jibin idan yaso saimu wuce dukan mu, har RAUDA.
Nisawa RAUDA tayi tace.
" MOMY ai ina da school babu Halin naje, zan dai koma gida idan kun dawo saina dawo nima.
" Okey Allah ya kaimu cewar Momy.
Haka kuwa akayi Ranar talata Habeeb ya wuce London tare da bawa Sharifa sakon idan taje, dasina Innah ta nuna mata Indo tace yana gaishe ta, Kuma yana mata ta'aziya, idan kuma ta samu network ta kirasa a waya ta haɗasa da Indo.
Ranar Laraba da safe su Momy suka ɗauki hanyar DASINA, daddy ne yayi waya da mustapha yake tambayar sa yaushe zai iso Dasina, sanar dashi yayi cewa sai gobe idan Allah ya kaimu, sannan daddy ya kashe wayar sa, RAUDA suka fara sauƙewa a ƙofar gidan su, kafin suka ɗauki hanya, tare da direban Daddy....................
Dan Allah kuyi hkr da wannan wlh yau ina da makaranta, shiyasa ban samu nayi muku typing mai yawa ba.
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*