Showing 3001 words to 6000 words out of 33825 words
Chapter 2 - INDO A BIRNI BOOK COMPLETE 2020 by Rasheedat Usman.txt
Baffah mahaifin Hansai ya hanata kula Indo acewar sa zata Lalata masa tarbiyar yarinya.
Juyawa INDO tayi tare da zagawa, ta katangar Ban d'akin su Hansai da nufin ta dirk'a ta ban d'akin yanda zata samu shigewa d'akin Innar su Hansai ba tare da Baffah ya ganta ba.
Kama katangar INDO tayi, kasancewar katangar guntuwa ce, ta dira cikin ban d'akin.
Lami kishiyar mahaifiyar Hansai dake tsugunne Kan shadda tana bayan gari, taji dirowar mutum cikin ban d'akin, cikin tsoro ta fara bin k'afar INDO da kallo, ba tare da ta d'aga kai ta kalli fiskar taba, ihu Lami tasa cikin tsoro, tana cewa.
" Na shiga Uku ni Lami, dan Allah kuyi hkr wlh mantawa nayi, na shigo ba tare da nayi addu'a ba, kuyi hkr dan Allah *ku kuke ganin mu, ba muke ganin kuba ba* wayyo Allah ku kawo min agaji yau Kuma Nayi gamo.
Yayin da fitsari ke bin k'afofin Lami.
Dariya INDO ta shek'e dashi har hawaye na fita cikin idanun ta, ganin yanda Lami ta gigice ta fice hayyacin ta har tana fitsari a jikin ta, yayin da Idon ta, ke rufe gam tak'i bude su.
D'alewa saman katangar INDO tayi ta zauna tana cin dariyar ta, tare da nuna Lami da yatsa.
Nan zan dakata sai naji yanda kuka karb'i book d'in kafin naci gaba da typing.
*Yawan sharhi yawan typing.*
*Share*
*And*
*Comment*
*Alk'alamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah)*
[1/2, 8:05 PM] MAKAMAR KAINUWA🏻: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽* *A͓̽* *B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*N̸͟͞A̸͟͞*
*R̸͟͞A̸͟͞S̸͟͞H̸͟͞E̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞* *U̸͟͞S̸͟͞M̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞*
*(U̸͟͞m̸͟͞m̸͟͞u̸͟͞ N̸͟͞a̸͟͞s̸͟͞m̸͟͞a̸͟͞h̸͟͞)*
*( ოႩlႩႪႩR kႩiႶႮwႩ)*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*(Baya hana gamji)*
*Toho*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza yar Amana*
Uwa mabada mama k'aunar ki dabanne gare Ni, domin ke d'in shugaba ce dake Adalci ga duk na k'asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P* 3️⃣ ➡️ 4️⃣
Ilu d'an Lami ne da Baffah sai Innar Hansai sukayo ban d'akin da gudu jin ihun Lami, turus suka tsaya sakamakon ganin *INDO* zaune saman katanga sai washe yellown Hak'waren ta take, tana cin dariya, Salallami Innar Hansai ta d'auka cikin Al'ajabin meya kawo INDO ban d'akin su.
" Ke INDO meya kawo ki nan, yau kuma tsiyar taki cikin gida na kika kawo sa, cewar Baffah.
Jin an Kira INDO ne yasa Lami saurin bud'e idon ta, fes kuwa ta sauk'e su kan INDO dake ta famar dariya ta maida su mahaukata, Cikin Haushin INDO Lami tace.
" Amma dai Allah ya isa tsakanina da ke INDO, tsabar rashin mutunci duk k'ofar gidan nan bai isheki sai kin diro ta ban d'aki, baki sani ba koda mutum koko Babu, ki shigo ki sami mutum a Halin da bai dace ki samesa ba.
Dariya INDO ta sake shek'ewa dashi, cikin dariyar take cewa.
" Kamar dai yanda naxo na same ki kina *Kashi* kai Amma Lami Anyi matsoraciya, duba fah kiga yanda kika jik'e zanin ki da fitsari, sai kuwa ta k'ara shek'ewa da dariyar, *Aradun Allah Lami kashin ki wari gare sa, ni kin gama ma cika min ciki da warin kashin ki*.
Ilu ne zuciyar sa taxo kusa, cikin haushi da hasala yayi kan INDO da gudu, da niyar ya mata dukan da sai anxo an kwashe ta.
Ganin ilu yana nufa ta yasa INDO dirawa daga katangar, ta kwasa a guji, shima ilu rufawa INDO baya yayi, da Gudu,
Babu inda Indo ta nufa sai gidan, *Hajiya Innah* tasan a nan kawai zata tsira daga Hanun Ilu.
Hajiya Innah dake Zaune gindin murhu tana ixa wuta ne taga shigowar INDO da gudu a birkice *Hajiya Innah* itama ta tashi tabi bayan indo da gudu.
Gudu suke sanda suka shiga cikin d'akin Innah, sannan suka tsaya suna haki, Hajiya Innah ce tace
" Ke indo gudun me kike haka, meya faru macijin nan ne, yauma ya k'ara biyo ki.
Dariya indo ta shek'e dashi tana nuna Innah da Hanu, tace.
" Amma dai Inna ke ba k'aramar matsoraciya bace wlh, daga gani na Ina gudu sai ki biyo baya na.
K'ara shek'ewa tayi da dariyar tana nuna Innah yanda taga Innah tayi tsamo a gefe, kamar wanda za'a ce fit ta D'iba da Gudu.
Yanxu ke Innah Idan macijin ne, sai na tsaya harki iso ban rufe ƙofa ba, ai wlh kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai Kuma kisan tayi.
" Amma ke dai INDO akwai ja'irar yarinya, yanxu dan baki da mutunci, sai ki rufe ƙofar ki barni a waje, idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba Koh.
" *To me zai dameni Innah, dan kin mutu ai ba Abun damuwa bane, tunda kin mori duniyar, wlh Innah na rufe ƙofar nan baki iso ba shi yafi sauki a wajena.*
Haɗa fiska Hajiya Innah tayi kasancewar ta tsani taji ana kira mata mutuwa muraran, tace.
" *Bari muga idan na mutu a ina zaki dinga samun taliyar turawa mai harɗe ki dinga ci, tunda gani na ne baƙya ƙaunar ganin ina numfashi*.
" Ehhh fah haka ne, kuma Innah, wlh Idan kin mutu Babu inda zan samu taliyar turawan Nan, *to Gaskiya Allah ya Raya min ke Hajiya Innah kodan karna Rasa taliyar turawa,.*
Washe Baki Innah tayi tace.
" Ameen ƴar Albarka shiyasa nake sonki, faɗan mu baya nisa, saboda kin iya farar Addu'a, yanxu........
Shigowar Ilu yana Banbami ne ya hana Hajiya Innah ƙarasa maganar ta.
" *Lafiya mlm ƙaton gardi da kai zaka shigo min cikin gida, ko sallama Babu, kamar wanda ka shigo gidan Ubanka.*
Nuna INDO Ilu Yayi, yace.
" Ga Wacce na biyo, ki fito INDO wlh idan kika yadda na shigo ɗakin Nan, sai na karya ki.
" *To Uban ta, Bismillah shiga ɗakin tunda ɗakin Ubanka ne, cewar Hajiya Innah, har wani cewa kake zaka ƙarya ta, to idan ka fasa ƙarya ta ka raina Uwar da ta haife ka.*
Kallon Hajiya Innah ilu yake cikin mamakin ta, yace.
" Hajiya kinsan Abunda ta mana kuwa, kike ƙoƙarin shigar mata faɗa.
" *Ban sani ba kuma bana son Sani, dake ku mutanen garin nan, manyan ku da yaran ku kun tsani INDO, ko wani laifi ku ɗauko, ku ɗaura Mata, to wlh ta Allah ba taku ba, aniyar ku ta biku, har gadan Baccin ku wlh INDO tafi ƙarfin ku*
Hayaniyar da mustapha yaji ne yasa shi fitowa daga ɗakin nasa, yayo wajen Innah, turus ya tsaya yana kallon Innah yanda ta zage, sai zagin Bawan Allah take, ƙarasawa mustapha yayi tare da dafa kafaɗar Ilu yace.
" Abokina lafiya me yake faruwa.
Juyowa ilu yayi, ya fara bawai, mustapha labarin abunda INDO tayiwa mahaifiyar sa, yace wlh da gaske nake, har banɗaki ta faɗa mata.
Shi mustapha baima lura da INDO a wajen ba, sai dai yaji akanta ake Case ɗin tukunna, A zuciyar sa yake cewa, " wannan yarinyar itace Iblis ɗin wannan ƙauye, yanxu tsabar shaharan yarinyar nan, a fanni Rashin hankali har ki dirƙawa mutane katangar tollet ɗinsu, cewa Ilu yayi.
" Shiga ka jawo ta kaci Uban ta, wannan ɗan iskan bakin nata wanda kullum yake cikin ƙazanta, ka tabbatar kayi rugurugu dashi.
Daga cikin ɗakin Indo tace,
" Nidai wlh ba Uba na ba ehe.
" Zaro Ido mustapha Yayi, yace.
" Sai Uban waye kenan.?
Babu tsoro fiskar INDO ta mayar masa da amsa.
" Sai Uban Wanda ya tsargu.
Kallon ilu yayi yace.
" Ka shiga ka sanja mata kamanni nace maka.
Tare ƙofar Innah tayi tace,
" Naga shegen da zai wuce cikin ɗakin nan, munafiki, idan banda munafurci, meya fito da kai daga ɗakin ka, sai ya fasa mata bakin mu gani.
Jawo Innah mustapha yayi😄 suka hau kokuwa, yayin da ya riƙe mata Hannayen ta gam yana cewa, Ilu ya shiga.
Ganin da INDO tayi da gaske, Ilu zai damƙe ta, yasa ta daka tsalle sai ƙarƙashin gadon Innah, can ƙarshe.
Neman Indo Ilu yayi sama da ƙasa ya Rasa, ko motsin ta, baiji ba cikin ɗakin, fitowa Yayi cikin Huci yace, ta fah ɓace babu ita cikin ɗakin nan.
" Babu ita kamar Yaya cewar Mustapha, Yanxu na hango yarinya, kace bata nan ta ɓace sai kace Aljana.
" Wlh Babu ita, kaxo ka duba ka gani.
Sake Innah mustapha yayi, yasa kansa Cikin ɗakin, bai ganta, dube dube ya hau yi Amma Babu INDO sama da ƙasa, ko a ransa bai kawo INDO zata shige ƙarƙashin gado ba.
" Haba ai daman *Biri yayi Kama da Mutum* yanda yarinyar nan, take dole tana Aiki da Aljanu ne, Idan ba Aljani ba waye zai ɓace ɓat lokaci ɗaya.
Kallon sa ya mayar kan Ilu yace kaje kayi hkr, kawai ka barta da Allah dan yarinyar nan tafi ƙarfin mutum sai dai Aljani.
Shigewa Ilu yayi yana cewa wlh ido na Idon INDO, sai na mata shegen Duka.
" Kama kashe ta idan kaga dama, cewar Hajiya Innah kuma zanje har wajen Ubanka naji idan shiya turo ka gidan nan kamin rashin mutunci.
Ficewa waje shima mustapha yayi ba tare daya kalli Hajiya Innah ba.
Ɗakin ta shiga, tace.
" To fito ja'ira marar Kunya nasan ai kina cikin ɗakin, ashe daman Bala'i kika nemo shiyasa kika shigo a guje, har nima kika Sani gudu, yau da sun kamaki sai dai wani bake ba wlh, daman haushin ki, suke ji.
Fitowa INDO tayi tana dariya, tace
" To ya suka iya dani Innah, ni ɗin tsayuwa zanyi su jibge ni, ni dai yanxu Innah ki bani taliyar turawan Nan, naje gida na tafasa, dan baxan tsaya gidan nan ba, ya mustapha yaxo ya ritsani.
" Ai kuwa kinga ɗauki wannan, kwalin ki kaiwa Uwar taki ta tafasa muku keda ƙannen ki.
Ɗauka Indo tayi tana cewa, shiyasa nake sonki Innah, kodan wannan taliyar, ficewa tayi tana waige waige kar Ilu ko mustapha su riƙota, cikin sa'a kuwa har ta shiga cikin gidan bata haɗu da suba.
Zaune mlm sa'idu mahaifin Hansai yake gaban mai gari, yayin daya kawo ƙarar INDO kan Abunda ta shiga cikin gidan sa ta masa.
Nisawa mai gari yayi tare da cewa.
" Ita Indon ce tayi wannan ɗanyen Aiki, umurtan Dogari yayi akan cewa yaje yaxo masa da Mlm Musa mahaifin INDO.
Da sauri dogari ya tafi aiken da mai gari ya masa.
Sallama Dogari ke kwalawa a ƙofar gidan su indo, Yayan Indo Tanimu shine ya fito, jin sallama da ake yi, Dogari ya gani tsaye.
" Lafiya kuwa Dogari, cewar Tanimu.
" Lafiya lau mlm Musa Nake nema, mai gari ke kiran sa, yanzu a fada.
" Me gari kuma, Allah dai yasa lfy.
" Koma menene idan yaxo yaji, ka shiga kamin Sallama dashi.
" Baya nan Amma bari naje kasuwar na kira sa, zaizo yanzu insha Allah.
" Shikenan bari na koma, ka tabbatar yaxo yanzu.
" Insha Allah zaizo.
Tanimu bai koma cikin gida ba, ya shige, kasuwa wajen, mlm Musa, yana zaune bakin shagon nasa na tireda, yana jin rediyo, yaga Tanimu ya masa Sallama.
Amsa Sallamar yayi yace.
" Tanimu kaine cikin shagon nawa, yaushe ka dawo daga wajen Raken naka.
" Yanzu na dawo Baba bamma daɗe da dawowa ba, naji sallamar dogari, shine yace min mai gari na son ganin ka yanzu.
Mlm Musa baiyi mamakin jin kiran mai gari ba, yasan *Tatsuniyar Gizo bata wuce ta Ƙoƙi* wannan kiran da mai gari ya masa bazai wuce wata maganar Indo ta jawo masa a gari ba, tashi yayi ya kulle shagon nasa ya cewa, Tanimu muje.
An taro fadar mai gari, ana jiran isowar mlm Musa, sai Kuma ga shi ya iso, zama yayi tare da gaishe da mai gari, sannan mai gari ya dubi, mlm Sa'idu yace
" Maimaita masa Abinda ke tafe dakai.
Duban mlm Musa, mlm Sa'idu yayi tare da fara jero masa tijarar da, Indo ta masa cikin gida.
Ya ƙarasa zancen da cewa, na gaji kawai mai gari ya min tsakani da Indo da Kuma ƴata, babu mu Babu ita, ko a hanya taga Hansai, karta ƙara koda kallon ta.
"Allah ya huci Zuciyar ka, mlm Sa'idu, duk Abinda kace Indo tayi banda musu ko ja akan haka, fiye da haka ma zata aikata, Kuma insha Allah daga yau na maka Alƙawarin cewa, Indo ko ƙofar gidan ka, bazata ƙara kallo ba, duban sa ya mayar kan mai gari, yace yallaɓoi dan Allah Ayi hkr insha Allah hakan bata ƙara kasancewa ba.
Nisawa mai gari yayi yace,
" To mlm Sa'idu kaji bayanin mlm Musa, nima ina ƙara baka hkr, tabbas kam yarinya bata kyauta ba, kayi hkr, gaba idan ta sake zamu ɗauki ƙwaƙwaran mataki a kanta.
" Shikenan mai gari, Nayi hkr, Allah ya yafe mana duka.
Godiya mlm Musa yayiwa mlm Sa'idu da mai gari, sannan yacewa Tanimu ya tashi su tafi.
Tanimu Allah Allah yake, ya isa gida ya samu Indo, wlh yau kam mai ƙwacen Indo a hanun sa Sai Allah.
Cikin Sa'a kuwa Tanimu suna shiga shiga cikin gidan itama Indo tana shigowa, da kwalin Indomie ɗinta a kayi, karɓar kwalin Tanimu yayi ya ajiye a gefe sannan yaja Indo har ɗakin da Mama ke kiwon tumaki, rufe ƙyauran Tanimu yayi, Mlm Musa na ganin haka, yayi murmurshi tare da shigewa cikin ɗakin sa, dan yasan yau Indo ta shiga Uku hanun Tanimu.
Kallon Tanimu Indo tayi tace.
" Me zamuyi Anan ɗin yaya, naga ka rufe ƙyaure, kayi sauri ni zanje na dafa taliya tace.
Tanimu bai tanka Indo ba, sai ma sunkuyawa da yayi ya ɗauki bulala, ya hau zabgawa Indo, ihu Indo take tana ƙoƙarin riƙe bulalar Amma Tanimu bai bari ta riƙe bulalar ba, sosai Tanimu yake dukan, Indo, ita kuwa sai cewa take.
" Allah ya isa zai kasheni mungu, azzalumi, wayyo Mama, yaya zaiyi kisan kai cikin gidan nan, ka sakeni shege mugun banxa.
A jiye bulalar Tanimu yayi ya daki bakin Indo da ƙarfi sanda ya kawo jini, take kuwa bakin ya kunbura suntum, sannan ya buɗe ƙyauren ya fice, yabar Indo tana birgima tare da ihu, Mama da Mlm Musa ya sanar da ita abunda ya faru, ko kollon inda Indo take Mama bata kalla ba saima, ɗage kwalin Indomie da tayi ta mayar gefe, tasan baxai wuce Hajiya innah bace ta bata taliyar.
Har dare Indo tana zaune ɗakin tumakin nan taƙi fitowa, zagi kuwa Babu irin wanda Tanimu baisha ba, Jauɗo kuwa ƙaninta daya leƙa da duwatsu ta jefe sa.
Babu wanda yace mata fito, kowa harkar gabansa yake, koda Mama ta gama abincin dare ma Indo ƙinci tayi, mama dai mayar da abincin ta tayi cikin madafi, cikin dare kuwa da yunwa ta Addabi Indo Babu wanda ya sani ta zaga ta ɗauki Abincin taci.
Washe gari da safe Mustapha ya fito cikin shirin shi na komawa cikin dutse dake Garin Jigawa, Hajiya Innah ya samu tana cin ɗumamen tuwon ta, zama yayi gefen ta, tare da Gaishe ta, Amsawa tare, dace.
" Muhammadu har ka fito baxaka bari kayi karin kumallo ba.
" A'a innah idan na koma gida na karya, kuɗi ya ciro dubu ashirin ya ajiyewa innah, tare da mata sallama.
" Allah ya kiyaye hanya ta masa ka gaishe da iyayen naka, habibu kam wannan karon baka haɗamu munyi magana ba, tare da basa su daddawa kuka harda kuɓewa bushashiya tace gashi ka kaiwa uwar taka sayi Amfani dashi.
Karɓa yayi yace innah kwana biyu wayar Habeeb idan na kira bata tafiya, ina ga babu network ne cikin garin naku.
" Shikenan to sai Allah ya ƙara dawo dakai ka haɗamu.
Har zauren gidan ta rakosa sannan ta koma.
Mustapha ya buɗe motar sa da niyar shiga kenan yaji Muryar Indo na cewa.
" Masoyina komawa zakayi kuma, ni dai wlh ban gaji da ganin kaba ka bari sai gobe ka koma, kafin nan zan maka kafi tsire sai ka kai tsaraba gidan ku.
Juyowa Mustapha yayi a fusace da niyar make Indo, sai kuma yayi tozali da bakin Indo dake kumbure sun tum harya sanja mata kammani, dariya ce ta kwacewa Mustapha yana nuna Indo, yace yau kuma waye ya iya jada Aljana.
Gaskiya ku ƙara yawan sharhi ko na ajiye Alƙalamina, domin bakwai sharhi mai tsawo.
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻
*(Ummu Nasmah)*
[1/3, 8:05 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty Fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gare