Showing 18001 words to 21000 words out of 33825 words
Chapter 7 - INDO A BIRNI BOOK COMPLETE 2020 by Rasheedat Usman.txt
dai ba mai raba ku*
Aiko kamar zuga Indo suke yi, ta dage sai jibgar juna suke.
Habeeb da shigowar sa kenan, cikin ƙauyen ya hango yara cike sai zabgar kokuwa ake, parking yayi, tare da fitowa daga cikin motar ya nufo wajen nasu.
" Kai baku da Hankali ne, kuke kokuwa.
Juyowa Indo tayi cikin masifa da rashin Kunya, wa zata gani idan ba Mustaphan ta ba, fit tayi shuru tare da sake yaron tana dariya, tace
" *Tafi abunka kaci albarkacin masoyina mustapha jeka na tafe maka ya Mustapha yaushe ka zoka sannu da zuwa kaga yanxun nan Innah ta shiga cikin gidan mu bari na kira maka ita*.
Zaro ido Habeeb yayi jin ta kirasa da mustapha, kuma masoyina, daga bayan sa yaji yara na cewa lallai yau tasi'u Allah ya ƙwace sa a hanun Indo.
" *INDO Habeeb ya furta sai kuma ya kwashe da dariya tuno labarin Indo da mustapha yake basa, Ashe Itace ALJANAR MUSTAPHA LALLAI BARRISTER MAI ƳAN MATA KALA KALA*.
__________________________
Bana typing Ranar asabar yauma ganin da nayi kwana biyu banyi typing ba, yasa na daure nayi muku🙏🏻
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah)*
[1/13, 3:29 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take a gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••1️⃣7️⃣ ➡️ 1️⃣8️⃣
Cikin dariya Habeeb yace wa Indo.
" To jeki kira Hajiyan, idan kin kirata sai ki wanke jikin ki koh, dan kin Zama dodo.
Sake baki Indo tayi tana kallon Habeeb cikin mamaki wai yau mustapha ne yake mata magana cikin sakewar fuska, mutumin da baya dariya, kullum cikin faɗa yake, ƙara leƙa fuskar tasa ta Indo tayi.
" Lafiya kike leƙen fuska ta, cewar Habeeb.
Wangale yellown hakwaren ta Indo tayi, tace wa Habeeb, gani nake kamar ba kai bane ya Mustapha, shifa ya Mustapha yana da faɗa kuma kullum cikin haɗewar rai yake, kai kuma naga kana dariya kuma baka faɗa.
Dariya Habeeb yayi Yace.
" Nine mana na sanja miki ne, Hajiya Indo.
" *Aradun Allah ya mustapha ka sauya kodai ka fara sona ne, yanda kake min murmurshin nan dafe ƙirjin ta Indo tayi tace har ji nake wasu kifiyoyin sonka na harbi na, a ƙirji na, Wayyo Allah Wlh ya Mustapha sonka yamin ɗaurin huhun goro ina sonka ya Mustapha na dan Allah kaima kace kana sona ko zanji daɗi*
Dariya sosai Indo ta bawa Habeeb dariya yake sosai, domin shi Wlh yarinyar ma, comedy ɗinta burgesa yake.
Cikin dariyar yace.
" Jeki ki kira Hajiyan ni na wuce, gidan nata idan mun sake haɗuwa zan gaya miki, motarsa ya koma yaja shi zuwa ƙofar gidan Innah.
Da gudu Indo ta shigo cikin gidan har tana tuntuɓe.
" Hajiya Innah !! Hajiya Innah.
Innah da suke zaune da Mama suna firar duniya, tace.
" Lafiya Indo kike min wannan kira kamar wacce kike bina bashi.
Mamace tace.
" Hajiya ai kinsan Halin Indo babu hankali sam a tare da ita, kullum cikin shashanci take, bata da nutsuwa sam.
Tura baki Indo tayi tare da ɗaukar bokiti, tayi wajen randa tana cewa.
" Ya mustapha ne, yaxo, shine yace na mishi kiran sa, idan kinga zaki iya zuwa kije idan kuma bazaki iya ba, Sai ki zauna ni dai wanka na zanyi naje *musha fira da masoyina*.
Salati Mama ta ɗauka tana cewa.
" Lallai Indo rashin kunyar taki ta shahara yanxu gaban mu kike kiran masoyi, Allah ya shirya ki, to waima ke a hakan za'a soki baki da hankali da nutsuwa, ga rashin mutunci, da fitsara, babu wanda baki iya ba, ciki, Babu mai sonki a haka.
Dariya Hajiya Innah tayi tana cewa.
" A'a maryama aiko INDO sai tafi ƴan matan garin nan farin jinin Samari kinga indodo na maza jeki kiyi wankan ki, rabu da maryama.
" Ai nima Innah yau banda lokacin ta, bare naji haushin zancen ta tunda ya Mustapha yamin dariya Kuma yace naxo zaice min yana sona.
Zaro ido Innah tayi tace mustaphan, ne yace miki haka, wannan ɗan bakin Halin tsiyar, ikon Allah, naga wata sabuwar yaudara gurin Muhammadu, anya ma kuwa mustapha ne, yaxo garin nan, gani nayi kwatakwata satin sa ɗaya da zuwa, amma ban sani ba ko ubansa Haruna ne ya aiko sa, maryama bari naje gidan na gani.
" To Innah na gode a huta gajiya.
Cewar Mama.
INDO kuwa wankan ta, ta shige tabar Mama zaune tsakar gida.
Da sallama Innah ta shiga cikin gidan Habeeb ta hango Zaune bakin ƙofar ɗakin ta, daga nesa itama INNAH tayi zaton mustapha ne, sanda ta ƙaraso daf dashi, taji Habeeb ya sureta yana hajijiya da ita, domin tasan shi kaɗai ne, mai mata wannan yahudancin, rufe idonta Innah tayi gam, tana zagin Habeeb.
" Ka sauƙe ni dan ubanka Haruna, kaji ɗan iskan Yaro zai ƙarasa ni.
Cikin dariya Habeeb ya sauƙe Innah tare da cewa.
" Missing ɗinki nayi fah Amarya ta, an juma ba'a haɗuba, yanxu na ganki kuma ai dole na juyaki.
Dariya Innah tayi tace.
" Ja'iri Habibu aini nasan babu mai min wannan iya shegen sai kai, yaushe ka dawo ƙasar, kullum saina tambayi Muhammadu, kai sai yace min ai baka da Ranar zuwa ɗan albarka Ashe kaine kake tafe, ni fah nayi mamaki da naji Indo tace min Muhammadu ne yaxo.
Dariya Habeeb yayi yace.
" Nine nan Innah nayi nayi mustapha mu taho tare wlh wannan bawan Allah yaƙi, wai ba yanxu ba, ko dai kina basa ciwon kaine Innah.
" Toni ina ruwa na, dashi idan yana soma karya ƙara zuwa waje na, daga nan har abada, dan ubansa.
Dariya Habeeb yayi Yace.
" Ni Babu ruwana a tsakanin ku, kunfi kusa, nine bare tsakanin ku, bari naje nayi wanka, akwai kaya cikin but ɗin mota, bari nayi wanka saina nemo yara su kwashe, yace akwai wanda za'a kai gidan Mlm Musa.
To saika fito cewar Innah, ɗakin da mustapha yake sauƙa inda yaxo garin shima Habeeb nan ya sauƙa.
Wanka Habeeb yayi tare da kwantawa baccin gajiya.
Wanka Indo tasha fes da ita, ta taho gidan Innah, Innah tana zaune tsakar ɗakinta Indo ta shigo tana leke leƙen ta ina zata ga mustapha, ɗakin Innah taxo ta zauna tare da cewa Innah, ina yaya Mustapha yake.
Dariya Innah tayi, tace.
" To shasha wannan ba Muhammadun bane, Habibu ne, ɗan uwan haihuwar sa, kamace kawai suke, sai banbancin hali da suke dashi.
" *Haba haba daman dai akwai walakin goro a miya, nidai nasan mustapha bai taɓa min dariya ba, wannan kuwa yana dariya, harma da kula mutum, kallon jikin ta, tayi yanda tasha wanka harda ɗige ɗige da tasha a fuskar ta, sai kuma tasa kuka 😩 tace yanxu kenan nayi wankan banxa, wlh danasani banyi wannan wankan ba*.
Dariya sosai Innah tayi tace.
" Yanxu ke INDO baza kiyi wanka danjin daɗin jikin kiba, sai dan wani, amma dai kinji kunya Wlh.
Ƙara sautin kukan ta Indo tayi, tsakanin ta da Allah take kuka tana yiwa Innah masifa, cikin ɗaga murya.
" *Ni ki ƙyaleni nayi kuka na, Wlh banyi niyan ƙara wanka ba, sai wani sati Ranar juma'a shine ya cuceni yasani nayi, har yasa naji kifiyar Son ya Mustapha ta sokeni ashe ba shi bane, Kuma wlh wankan Allah ya isa nayi, tunda banyi niya ba, kuma Innah kiga fah yanda na zage nayiwa fuska ta kwalliya, duk dan ya Mustapha yace nayi kyau*.
Habeeb da tun sanda yaji hayaniyar Indo ta hanasa bacci ya fito, ya tsaya gefe yana kallon shirmen Indo, shi Wlh burgesa take idan tana wasu abubuwan.
" To kukan ya isa haka.
Taji Muryar Habeeb daga bayan su.
Tsale Indo tayi ta diro gaban Habeeb tana ƙara sautin kukan ta, tana cewa.
" *Baxan yi shuru ba Wlh yau wuni zanyi ina kuka, kuma Na wuni ina zan Allah ya isa, dan ancuce ni Wlh.*
" 😆 Ikon Allah yau ni Habeeb ina ganin ikon Allah, to naji, idan kin wuni kina kuka ai kanki ma wuni zaiyi yana miki ciwo, to wai Allah ya isan wa kika jawa shi?.
" *Kai kai na jawa Wlh, tunda kaine kayi kama da ya Mustapha na, shine harda cemin kaine ya Mustapha, ashe ƙarya kake min, KUMA NA JAMAKA YASIN DOGUWA, MAI JAN WANDO KUMA BULLUƘUTU BAƘAR MUTUWA TSAKANINA DAKAI ARADUN ALLAH BAN YAFE BA*.
kaɗa kansa Habeeb yayi cikin jinjina yarintar Indo, Yace.
" Badai akan mustapha kike jamin Allah ya isa ba, to zo na miki hoto saina kai masa gida yaga wankan naki, ba shikenan ba.
Shuru Indo tayi tace.
" A shagon waye zamuyi photon shagon salisu zamuje.
" A'a a wayata zan ɗauke ki, wayar ya ciro daga cikin aljihun wandon sa, tare da cewa kin gani, fito waje na miki.
Tana washe bakin ta, Indo, Indo ta fito, Innah kuwa haɓa ta riƙe tana kallon rashin mutunci da Indo ke tsulawa, Habeeb ya yiwa indo pictures wajen kala Uku kafin ya mata da Innah, sai kuma sukayi sulfie shida INDO, suka zo sukayi su Uku harda Innah.
Cikin son zolayar mustapha Habeeb ya cewa Indo zo mamana, na miki video, ki faɗi saƙon ki, wajen masoyin naki, yana gani motsin bakin ki.
Zaro ido Indo tayi tace.
" Nice mamanka ƴar mitsitsiya dani, kai kuma ƙatoto dakai, nidai ka kira ni da indo na.
Dariya Habeeb yayi Yace.
" Nikam baxan kira sunan kiba, Saboda sunan mamana ke gare ki, idan kuma kince baxan kira ki da mamana ba, to na fasa miki video.
" Shikenan to na yadda, ka shirya na fara.
Dariya Habeeb yayi tare da saita Indo da wayarsa yana cewa ehh na shirya.
Gyaran murya Indo tayi sannan ta fara jero kalamai.
" *Assalamu alaikum yaya Mustapha ina kwana ya birni, da kuma mutanen cikin ta, yaya Mustapha yaushe zaka zo, Wlh nayi kewar ka, kuma gashi kullum kibiyar sonka harbi na, yake, ina sonka da yawa da yawa yaya Mustapha na, kaga wannan kwalliyar ma, kaine nayiwa, tana maganar tana fari da ido tare da washe haƙwara*
Dariya sosai Habeeb yasa sanda yake kallon videon, kafin ya bude data ya turawa mustapha su.
A wunin Ranar sabone sosai ya shiga tsakanin Indo da Habeeb.
Kusan tare suka wuni Habeeb na cin dariyar indo, tana basa labarin soyayyar da takewa mustapha, sam Habeeb bai nunawa INDO ƙyama ba, yanda kika san ƙanwar sa ta jini haka suke mu'amala da indo.
*Dutse local Government*
Da gudu RAUDA ta shigo cikin gidan nasu, shige Mamy tayi a falo tayi ɗakin ta, a saman gadon ta, ta zube tare da sakin wani marayan kuka, mai tsuma Zuciya.
Tana kukan mamy ta shigo cikin ɗakin, cikin tashin hankali, kusa da RAUDA ta zauna tare da ɗago kanta ta ɗaura bisa cinyar ta, tace
" RAUDA menene meya faru, wani Abu aka miki, kika shigo min gida haka.
Cikin matsanancin kuka, harda majina RAUDA tace.
" Ya mustapha ne, Mamy ya Mustapha baya sona, ya tsaneni mamy ƙirjina nauyi yake min, soyayyar ya Mustapha zata kasheni Mamy, ki taimake ni Mamy, Wlh idan ban Auri ya Mustapha ba mutuwa zanyi Mamy.
" Tsuka mai ƙarfi Mamy taja, tare da cewa.
" Haba RAUDA ke baki da wani aiki sai Mustapha Mustapha kullum ke kenan wannan sunan ne a bakin ki, waye ma mustapha me yake dashi da kika liƙe masa yana wulaƙanta ki, ga samarin da suka fi mustapha suna zuwa miki amma kinƙi sauraron su, meya fiki dashi da zai ke wulaƙanta ki, *kyau ya fiki Asali ko gata, ba komai ba laifin ki bane laifin wannan shegiyar Zuciyar taki ce, mai nacin tsiya, zanje na nemo miki soyayyar mustapha koda kuwa komai nawa zai ƙare, dole zanbi shawarar Habiba, zanje Niger wajen malamin nan, mustapha sai yayi dana sanin wulaƙanta ki a cikin rayuwar sa, Mu zuba mu gani, nida kai shege ka fasa, domin kuwa karen bana shike maganin zomon bana*
Kiyi hkr ki share hawayen ki, bari na ɗauki gyale na, naje gidan Hajiya Habiba mu tattauna.
Ɗagawa mamy kai kawai RAUDA tayi, Mamy na ficewa daga ɗakin RAUDA ta tashi taje gaban babban ilajimen ɗin mustapha dake maƙale a bangon ɗakin, ta tsaya tana magana kamar wacce take gaban sa.
" *Why mustapha why baka sona menene Aibuna, meyasa ka tsaneni, shin laifi ne danna soka, ko kuwa haramun ne, idan na soka,? tabbas nasan kasan zafin soyayyah, bai kamata ka Azabtar dani ba, kaji tausayi na, dan Allah ya Mustapha, ta ƙarasa maganar cikin kuka tare durƙushewa a wajen tana kukan hade da ajiyar zuciya*.
Shiko mustapha yana zaune cikin office ɗinsa hankali kwance yake harkokin sa, yama manta da wata RAUDA cikin rayuwar sa, zama yayi tare da kunna ƙira'ar Mlm Ibrahim Abdulrasheed, yana sauraro tare da bin karatun, cikin suratul Muminun.
Kamar wanda akace ya kunna datar sa, yana kunnawa saƙon Habeeb na shigowa.
Buɗe wa yayi, sai kuwa yaga pictures ɗin Indo guda Uku tare da video, da kamar bazai buɗe ba, sai kuma wata Zuciyar ta sashi buɗewa.
Duk tsare gidan mustapha da haɗe ransa sanda video nan ya basa dariya, sanda ya gama dariyar sa, sannan Yace.
" *Wannan kece mahaukaciyar kam cikakkiya ma, Habeeb kuma an haɗu da indo, lallai Innah kema kin shiga Uku da shiririta, HABEEB HABEEB mutum ya girma amma har yanzu baisan ya girma ba, ita kuma shasha, waini tayiwa kwalliya, koda yake ance idan baka da hankali ka aikata komai.*..............
*YAWAN SHARHI YAWAN TYPING*
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah)*[1/14, 3:19 PM] MAKAMAR KAINUWA 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*BANSO YIN MAGANA BA, AMMA DOLE SAI NAYI MAGANA, HABA ƳAN UWANA YA KAMATA KUKE YIWA WRITERS UZURI, IDAN HAR KIN BIYO WRITERS PRIVET KINCE TA TURO MIKI BOOK, BATA KULAKI BA KAMATA YAYI KI MATA UXIRI HAR ZUWA WASHE GARI, KIGA IDAN BATA KULAKI BA, BAREMA IRINA DA YAU DUK SAƘONNI NA A WAITING MESSAGE SUKA ZO MIN KAƊAN NE WANDA SUKA ZOMIN A BUƊE, KU DAINA KIRAN CEWA WANE NADA GIRMAN KAI DAN ALLAH.*
*DUK DA DAI BANI AKA ZAGA BA, AMMA DAI ƳAR UWATA CE WRITERS, KUMA ABUN YAMIN ZAFI, TAYA BAƘYA COMMENTS CIKIN GROUP ƊINTA, DAN TA CIREKI SAI YA ZAMA LAIFI ITA BATAJI GANDAN MIKI TYPING BA SAI KENE ZAKIJI GANDAN MATA COMMENT, TA CIREKI KUMA KIN BIYOTA PRIVET DA ZAGI, HAR KINA KIRAN CEWA, IDAN KINGA DAMA SAIKI MATA MUGUNTA KI ƁATA MATA SUNA.*
*KIJI TSORON ALLAH DOMIN KUWA BABU ABUNDA ZAKI IYA MATA, SAI DAI IDAN UBANGIJIN TANE YA ƘADDARA MATA DOMIN IDAN UBANGIJIN TA BAI YADDA BA BABU ABUNDA KE KIKA ISA KI MATA.*
*DUK WACCE NA ƁATAWA RAI SANADIN WANNAN MAGANA YAYI HKR 🙏🏻 NI DAI NA FAƊA NE DOMIN WACCE TAYI MAGANAR TASAN CEWA BABU MAI ƘADDARAWA MUTUM ABU SAI UBANGIJIN SA YA SO*
*P*••••••1️⃣9️⃣ ➡️ 2️⃣0️⃣
Hanun sa yasa da niyar goge video da pictures ɗin sai kuma yaji kira a wayar tasa.
daga kiran yayi tare da amsa Sallama.
Ya daɗe yana wayan kafin daga ƙarshe naji yana cewa, shikenan Abdul Babu damuwa sai kazo goben, yana gama wayar.
tana mutuwa Babu chage, tsuka yaja tare da tattara, kayan sa, ya kulle office ɗin, ya nufi motar sa, kasancewar lokacin tashin sa daga aikin yayi.
" Kinga sharifa tashi ki ajiye wannan wayar da tun ɗazu kika sata gaba kin kasa min Aikin komai, tunda shi girkin nayi, aikuma dai zaki samu ki min gyaran kitchen ɗin koh.
Ajiye wayar Sharifa tayi tana haɗa rai ta nufi kitchen ɗin, wayar ta Momy ta ɗaga tare da dannawa RAUDA kira, ringine ɗaya RAUDA ta ɗauka tare da cewa, barka da yamma Momy.
" Yawwa RAUDA Barka dai, ya naji Muryar ki, kamar wacce kikayi kuka.
Goge guntun hawayen ta RAUDA tayi tace.
" A'a Momy ba kuka nake ba, ina ga