Showing 147001 words to 150000 words out of 159724 words

Chapter 50 - WATA KISHIYA COMPLETE DOCUMENT Book by Sa'adatu bintu Abdullahi .txt

da gidaje da har mu mutu baza muyi talauci ba insha Allahu,, a haka har Almuqri'ah ta kai 12yrs zuwa lokacin ta gama JJSS, tana shiga SS1 na fara fuskantar barazana a gurin kanina hydar wanda zuwa yanzu ya kara shahara ya zama babban dan daban da kaf kasarmu ke kara tsoronsa ko hukuma bata ja dashi. Ya dingamin barazana kan in ban kawo masa kaf dukiyar da mahaifin Almuqri'ah ya bari ba ze kashemu nida Almuqri'ah duka,,senaji tsoro na kwashi rabi na kai masa, muka samu ya shafa mana lafiya, Almuqri'ah taci gaba da karatunta cikin gata a jirgin sama ma ake kaita scul saboda tsanar dukiya da ubanta keda shi...tin tana 12yrs ta iya komi na girki, saboda na koya mata, ta iya komi kwarai, ga ilmi ga komari, tana SS2 ta zana Jarabawar fita zuwa makarantar gaba,, kwatsam muna zaune a gidanmu sega hydar da mukarrabansu, ya nunamin wuka ze kasheni, ya dinga zagina wai na masa karya na bashi dukiya kadan, dan haka yanzu ze kwace komi da Khalid ya bari a doron duniya...aiko hkm yayi ya kwace komi yasa aka jefomu a jirgi aka kawomu nigeria garin Abuja, to bamusan kowa ba a abuja, dan haka muka fara bara,,daman tin tini inada blood cancer amma abin beyi kamari ba seda mukazo nigeria saboda bani da yadda zanyi insha maganin ciwon, yazamana abinci ma da kyar muke samu muci, Se munyi bara, kayan jikinmu ma se munyi bara muke samu,, muna barar na fara matsanancin ciwo, gashi bamu dako daki a titi muke kwana a bakin hanya,, tin ina iya tashi har nazo ban iya tashi, kaf jigilata Almuqri'ah keyi wadda maza keta kawo mata hari da iskanci amma inata kafa-kafa itama tanata kafa-kafa da mutuncinta. tin ina sanin inda kaina yake har yazamana ban gane mutane sosai sbda ciwo daya fara cin karfina,, ana haka wani bawan Allah yazo bamu bara yaga halinnda muke ciki, ya daukemu a motarsa ya kawomin asibitinka aka dubani akaga abinda ke damuna, yace ze biya kudin komi amma se Almuqri'ah ta yadda ya tare da ita, ni kuma nace inta amince wani yayi amfani da ita ba mijin Aurentaba Allah ya isa ban yafe mata ba... Fir taki yadda da mutumin ganin hakan yasashi kin temakonmu sbda besamu abinda yakeso ya samu ba a jikin Almuqri'ah...kunji yadda labarina ya kasance, munyi rayuwar kankaci a kasar nigeria bayan da gatanmu, duk Hydar ne ya jefamu a wannan kaddarar, da kuma komi rubutacce ne...nida ubangiji sede ince Alhamdulillahi kawai, amma munsha wahala kuma munga rayuwa, kuma na hadu da jarabawar ciwo iri iri, but Alhamdulillahi..." Ammah ta karashe maganarta idanuwanta duk sunyi jage jage da kwallah, tana jinjinawa kaddararsu, dukda tasan Akwai kaddarar datafi tasu, amma kowani tsuntsu kukan gidansa yasani. Dr mus'ab da jarida duk seda suka zubda kwallah da labarin da Ammah ya basu sun tausaya Ainun. "Mutum nugun icce Ammah, ace kaninka uwa daya uba daya ya jefaka a matsifa..." Dr ya fadi yana meci gaba da kwallah, amma ma kwallar takeyi ta kasa cewa komi a haka ma bata fayya ce musu komiba sbda rike sirrinta, amma kanin nata seda yaso mata fyade har tsawon 5tyms da kyar ta shallekewa kaidinsa, haka yaso yama Almuqri'ah fyade kusan 4tyms itama Amma Allah dukya tsaresu. "Ranka ya dade ai yanzu dana kusa dakai ake cutarka, duk duniya babu me kin ci gabanka kmr makusancinka, duniyaR ce kawai tazo karshe, zamaninnan zaka haifa d'a ya kasheka, uwa 9months kana ciki, amma daka fito duniya zaka rasa mezaka sakawa uwa seka kasheta,,ko kaga d'an uwa ya kashe dan uwansa , ko ya kusanceta, yaran yanzu ma wasu har iyayen nasu shaawah suke basu ta hanyar saduwa, wasuma sesu nemi su haikewa iyayen dasuka haifesu sbda rayuwar dabbobi..." Dr mus'ab dake kuka yace "Me muke nema a duniya? Duniyar data riga ta kare me muke nema a cikinta? Mutuwa fa dole ce, haka hisabi ma dole ne, kodan haka ya kamata mu guji wannan rud'in duniyar, mu sassauta rayuwarmu lamarin duniya..." Dr ya karashe hadi da fashewa da kuka me tsanani, zuciyoyin kowannensu ya kara cikewa da tsoron Allah se kwallah kawai sukeyi.






*Kaduna*
Seda hajiya saude tayi sati daya cir a kwance a asibiti kana ta fara gane wanda yake kanta, ta farfad'o kmr gaske, se kuma ta kara suma saboda zallar bala'in tashin hankalin da idanuwanta suka gani brain dinta ma rikicewa tayi, asibitin sukaga abu yafi karfinsu dan haka sukayi mata transfer zuwa 44, a can aka samu ta samu kanta bayan tayi 10days kwance kmr matacciya batasanma wake kanta ba. 7:am ta dawo hayyacinta tana bude idanuwanta taga larai ce kusa da ita, ta lumshe idanuwanta yayinda larai ta bita da sannu, ai bata da hankalin dazata amsa sannu da jikin da larai ke mata gaba daya zuciyarta azabar tukiki take mata. Tinda Abdoljalal ya bar asibitin be kara dawowa ba bema kara saninna wani hali sauden take ciki ba, yana can yana fama da tashi matsifar dayafi karfin ta saude zuwa yanzu ya fara zama kamar mahaukacn gaske daya ga ahamad seyace "An ganta ne? Ta haifarmin cikinane?an kawomin baby na ne?'' Ahamad na cikin na cikin dmwa shima babba, ya kira Dr mus'ab kmr zeyi hauka amma shiru, jalalu ma da kanshi ya kira dr mus'ab amma kaf numbers dinsa basa shiga, tashin hnklinsa da jalalu yake ciki a kullum doubles suke zama. A bangaren Jimmali ma tana cikin dmwa har yau bata bar kukan rashin Almuqri'ah a gidan ba ko ruwa setayi yaki da zuciyarta take iya shama cikinta.


Lumshe idanuwanta ta karayi da tsananin karfi yayinda abinda idanuwanta suka gani suka dawo mata sabo fil zuciyarta tayi nauyi, idanuwanta suka kawo kwallar bakin ciki, kunnuwanta sukayi dum-dum abinda sukaji basu tabajin irin su ba har abadan,ji takeyi kamar a mafarki take, ta bude idanuwanta ta kalli saman slin din dakin asibitin, batasanma a asibiti take ba se yanzu. zumbur ta tashi zaune jikinta duk ya mutu , tamkar ba ita ba, "Dama mutuwa nayi da ganin wannan matsifar..." Ta fadi a bayyane duk tabi ta fada a lokaci kankani se zare ido takeyi, larai ta kureta da ido, matsifa da zallar bala'i kawai ta hango a cikin idanuwanta. "Ina Abdoljalal?'' Itace tambayar data fito daga bakin hajiya saude wadda tayi tmbyr kmr tayi hauka sbda tashin hankalin datake ciki ya kara dawowa sabo fil idanuwanta suka kara kawo kwallah. Larai ta tabbatar da tashin hnklin da saude take ciki babba ne sbda bata taba ganin tashim hnkli a tattare da ita ba kmr na yau, dadin da d'awa ga kwallah, bata taba ganin kwallah a idanuwanta ba se yau . "Yana asibiti a farko amma zuwa yanzu yana gida..." Cewar larai da tayi mgnr kmr tana tsoro kasa-kasa. Hajiya saude ta watsa ma larai wani irin mugun kallo ba tare datace komi ba, gabaki daya haushin kowa takeji a duniya musammanma su larai, tanada tabbacin sun san komi dake faruwa amma basu ankarar da ita ba seda Hajiya lubah tazo ta ankarar da ita, se yanzu take nadamar cin mutumcin datayi ma hajiya lubar, ta kulla aniyar kaf ma'aikatan gidan seta musu axaba mara misaltuwa. "Hakkina ne ya tabashi yasashi ciwo....Abdoljalal yaci amanata, wlhi se Amanar Allah tacishi, ..." Cewar hajiya saude,datayi mgnr yayinda zuciyarta ke kuna, hawayen idanuwanta suka kara tsinkewa. Larai ta bita da ido kawai a zuciya tace "Kede haka zaki mutu cikin rashin wayau...hakkinki din me ya dauka daze sashi ciwo kece de hakki ke dawainiya dake ,haka zaki kare harki mutu, duk abinda ka shuka shi zaka girba..." Hajiya saude ta sauke nannauyar ajiyar zuciya , ji takeyi daman ranar mutuwarta tagani da wannan ranar data gani , bata tabajin ta gaji da duniya ba kmr yau. "Ke dan bura uban ubanda ya haifo ubanki, tsinannu, yan iska butulu, dukse na hada na kwashewa kaciyar bura ubaku albarka, tsinannu, yan iska, yayan Allah bani ko yaya ne,,,,ai dani kuke zancen.... Dan bura ubaki tashi jeki kirawo nurse ta ciremin wannan ruwan banga amfaninsa a jikina ba...."hajiya saude tayi mgnr cikin azabar ruwan wutar bala'i da matsifa hadi da tashin hnklin dake cike da zuciyarta. Jin irin uban zagin data antayowa larai yasata mikewa jiki na rawa ta fice a dakin, a zuciyarta tace "Ai kadan muka gani,,,nasan duk se kinci ubanmu ko baki fadi ba, tinda baki mutu ba ai tashin hankali be kare ba a gun uban kowa,yanzu ma aka fara ..." Zuciyar larai ta shiga dukan uku uku, ta nufa inda nurse's suke cikin hanzari.






"Ni saude matar saraki, yau nice mijina kecin wata mace, har yake sambatu, har ya mata ciki, wai kuma ina raye...never! Wallahi senayi kisan kai, wlhi sena zama rikakkiyar yar daba, sena dauki rayuka da dama koshi jalalun wallahi bazan barshi ba!! ..." Saude ta fadi kmr mahaukaciya bayan fitar larai a dakin. Se kuma ta tashi tsaye zumbur kamar mahaukaciya ta fasa wani irin mahaukacin gigitaccen ihu, seda kaf asibitin ya amsa gata abu ba kadan ba.




Paid book ne.0810162648440
Dai-dai ta fasa ihun dai-dai Nurse da Larai suna kofar dakin nata, jin ihun datayi yasasu dannawa cikin dakin a gigice suka ganta tsaye se zare ido takeyi kmr zararriya, idanuwanta duk sun kumbure, hawayenta ta kasa yi. "Ke dan ubanki karaso ki ciremin wannan tsinanninan drip din..."cewar Saude da tayi maganar da nurse. Abinka da asibitin kudi, kudinma ba yan kadan ba, nan da nan nurse din ta Kara so ta cirewa saude drip din jikinta, se uban matsifa takeyi tana zage-zage, ta fice a asibitin kmr mahaukaciya,larai na biye da ita a baya, suka fito harabar asibitin ba mota,. Larai ta kira dreva ba jimawa yazo. hajiya saude ta hau sirfafa masa zagin dabesan dalilinsana,. Ya dinga bata hkri kawai domin yasan abinda ke cinta a zuciya, dmn sun shiryawa bala'inta tini. Ya bude mata gidan bata ta shiga jikinta sam ba karfi, sun tada mota zasu bar asibitin kenan a guje doctor din dake kula da Hajiya saude, yazo ya dktr dasu daga fita, yace si basu sallametaba. Nan fa saude ta zakalkalo mata ta zagesa tass, dr yaga abu yafi karfinsa ya bata hkri kawai suka fice a asibitin. Se girgiza kawai takeyi a cikin motar har suka isa tana kukan zuci,,ta rasa ma ta ina xata fara, amma ta Ayyanawa ranta yau seta kashe Almuqri'ah, idanta idanta to tabbas ota ce ajalinsa koda hakan dazatayi shi ze zama na karshe a duniyarta daga nan se a kasheta ta yarda da hakan. Suna isa gidan ko packing dreva be gamayiba saude ta fito tabi masu gadi da ido, taga duk an chanzasu, tanaso ta tambayi larai ina wadancan masu aikin amma bala'i be barta ta tayi tambayarba. Ta nufa dakin Almuqri'ah ko kallan gabanta batayi sbda bala'in dake cinta. Tana isa dakin ta banko kofar dakin cikin bala'i da matsifa,idanuwanta cak suka tsaya a kan Abdoljalal wanda ke zaune kasan dakin duk yabi ya rame ya lalace, jikinsa duk kasusuwa sun bayyana a wuyansa tmkr wanda yayi ciwon shekara da shekaru, yanzu nan dakin yake rayuwarsa gaba daya, sallah kadai ke fita dashi daga dakin, gaba daya baya hayyacinsa, ko ruwa besha, tunanintane abincinta tunanintane abinshansa , kukansa kuma shine samuwar sassaucinsa a kan tunaninta, zuwa yanzu ya kwammaci mutuwa a kan rayuwar tashin hankalin da yake ciki, bayasan kowa a duniya for now se ita, daze bada uban kowa bnda iyayensa a bashi ita wallahi zeyi hakan, zuwa yanzu ba cikin jkinta Yake bukata ba har itama yana tsananin bukatarta. Abdoljalal ya dago shima ya zubowa hajiya sauden ido, sam ma ya mance da ita in ba yanzu ba daya ganta. Saude ta kara kuresa da ido zaune yake ya wani rakube kmr maraya sanye yake da jallabiya milk color, wani irin haushinsa ne ya turnike hajiya saude, kishi da zallar bala'i da matsifa suka turniketa. "Maci amana wato yanzuma kana nan dakin nata kenan...wallahi wallahi bazan barku ba, har kai bazan bari ba, ... Ina ita yarinyar take dan wallahi yau nice ajalalinta..." Cewar saude dake mgnr kmr zata cinye kanta dan zallar bala'i da matsifa, hnklinta ya kara tashi sosai, saboda mijinta data kara gani yau kuma a dakin yarinyar. "Abdoljalal ka cuceni!'' Ta fadi wasu zafafan kwallah na zubowa daga idanuwanta, yayinda takeji a zuciyarta koda ta kashe yarinyar da Abdoljalal din duka bazata huce takaicinndake zuciyarta ba. Tinda ta fara magana kawai kallanta Abdoljalal yakeyi, se yanzu ya kara fahimtar tsoron saude ne yasa Almuqri'ah barin gidansa, haushin saude ya rufe Abdoljalal, be tabajin ya tsani saude ba kmr yau. Saude tana kuka ta shiga dube dube a dakin tana fadinn"Ina take tsinanniyar..." Ta duba toilet taga bata ganta ba, ta dawo kan Abdoljalal tana haki kmr zuciyarta ta tarwatse. "Ina tsinanniyar take..." Ta fadi da karfi kmr zata tsage dakin. Dago red eyes dinsa yayi ya zubo mata su , zuciyarta ta fara turiri yayinda kiyayyarta ke yawaita a zuciyarsa. "Batanan ta gudu saboda ke..." Abdoljalal ya fadi kmr ze fashe da kuka. Kallan rashin fahimta saude tabishi dashi. "Ta gudu kmr ya..." Cewar saude,. Abdoljalal ya tashi tsaye yayinda jiri ke neman kwasarshi kmr zautacce yace. "Ta gudu ta barni sbda ke, ta gudun min da ciki sbda ke,...kema yanzu ki fita ki barmin gidana banasan ganinki na tsaneki..." Abdoljalal ya fadi da babbar murya, yayinda kmr ya rufeta da duka. Nan take Saude tayi mutuwar tsaye, yayinda jikinta ya dauki rawa hnklinta ya tashi, tashiga tunanin anya kuwa wannan jalaluntane?'' mamaki da tsananin tashin hankali suka rufe hajiya saude. "Abdoljalal, dan Allah kaine kuwa? Ni kake cewa in bar maka gida yau?'' Ta fadi jikinta na kara macewa yayinda tashin hankalinta ke kara ninkuwa, wai yau itace jalalu ke kora a gidansa,tabbas tasan tata ta kare, tayi babban sakaci, ta fara tunanin asiri yarinyar nan tayima mijinta wanda yafi nata sihirin karfi. "A, dake nake...ki bacemin da gani bnasan ganinki ki barmin gidana...!!!''' Abdoljalal ya fadi cikin tsananin tsawa kmr ya daketa hk yakeji. Ganin hakan yasa jikin hajiya saude macewa sosai, mamakinta ya ninku, ganin Abdoljalal na niyar dukanta, yasata ficewa a dakin kmr mahaukaciya ta fito tana fadin "shikenan ta kasheni, ta kwacemin miji, ta bashi asirin dayafi nawa yasha... Nashiga ukuna ni saude..."saude ke sambatun tana tafiya, ta daura hannu a kai, ta nufo dakinta kmr zararriya ta daukko wayarta ko gyara jikinta bata tsaya tayi ba, ta dawo compound kmr zararriya tana tafe tana sambatu, ta karaso packing space ta kwalowa dreva kira, yazo ta kalleshi ta watso masa wani ashar se kuka takeyi ta kasa controlling tashin hankalinta, dreva din ya kalleta yace "Kiyi hakuri hajjaju..." Saude da jikinta ya gamayin sanyi ga tashin hankali ga dmwa, a hasale tace "Kutmar bura uban ubanda ya haifo ubanka duniya kaida hakurin dan durin uwarka,,,,shegu si duk kune munafukan yan bura uba shegu munafukai, bari in gama da wannan bala'in na gabana, in dawo kanku duk se naci kundun bura ubaku wlhi nice ajalinku kaf ma'aikatan gidannan, bade daku aka cuceniba..." Saude ta fadi tana kuka, tashiga byn motarta, drevan data gama zagi ya kalleta kawai yaji zafin zagin amma ya shanye , ya fuskanci hakkina ke dawainiya sa ita Adduarh ya shiga mata Allah ya karo mata abinda yafi hakan, murmushi yayi a zuciyarsa yashiga motar yaja suka fice a gidan se kallan saude yakeyi tana kuka sosai harda majina ta glsss. "Sakwato zamuje..." Saude ta fadi cikin kuka kmr ranta ze fita, har tsatstsede sumar kanta takeyi da hannayenta, ji takeyi kmr zuciyarta zata fashe, duk tabi ta rame, wandan dake jikintama rawa yakeyi a kugunta. Jin tace suje sakwato Dreva ya kalli agogon motar yaga 11:pm ake nema yanzu,amma ba halin yayi magana, dole ya hau titin zuwa sakwato.








Manage.41
Suna tafe saude na kukan bakin ciki, har mamakin kanta takeyi anya itace kuwa saude? Se yanzu t take nadamar daukar yarinyar aiki a gidanta sauba adadi. Lalubo wayar hajiya Abulle tayi, ta kirata bugu biyu ta daga, saude ta fasheda wani irin kuka kmr ranta ze fita. "Hajiya jalalu ya cuceni..." Saude ta fadi yynda kmr ranta ze fita. Abulle taji wani farin ciki ya rufeta ruf, dukda batasan meya faru ba a bayya ne abulle tace "Meke faruwa hajjaju?'' Cikin muryar dmwa a zahiri. Nan saude ta kwashe labarin komi ta shaidawa Hajiya Abulle,. Nan farin ciki ya lullube abulle a zuciya tace "Komi ka shuka aishi zaka girba...Allah ya ninka miki bala'i..." abulle ta fadi a ranta, amma a zahiri tashiga jimami mara misaltuwa."kai wannan Abu ya tsananin dagamin hankali hajjaju,,,innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Shin yanzu yaza muyi? Ina boka yake har hakan ya faru...kai wlhi har zazzabi ya rufeni hajiya wannan bala'i dame yayi kama..." Cewar Abulle, da iya harshe tayi maganar. Saude ta kara rushewa da kuka tace "Wlhi bansan mani ta ina zan bullowa wannan matsifar ba Abulle, ji nakeyi daman mutuwata nagani da wannan tashin hankalin, yanzu haka gani a hanyar zuwa gun boka ..." "Okay karki damu kawata ki kwantarda hankalinki, tinda ma zakije gun boka ai magana ta kare...yanzu wai ina ita yarinyar?''cewar Abulle. Saude ta kara jin wani bakin ciki kmr ze kasheta , ta tsani yarinyar nan , bata taba tsanar wata halitta ba kamar yadda ta tsani yarinyar nan ba. "Kamar ta gudu a gidan yarinyar ,,, haka Abdoljalal ya nunamin,,, wlhi Abulle wannan lamarin yamin shigar bazata ko a mafarki ban taba tsammanin hakan ba, ji nakeyi kmr na kashe Abdoljalal dinma kowa ya huta....." Abulle tace "aah karki kasheshi ai shine ke din, yanzu de ki karasa gun boka muji yadda zata kaya..gobe zan dawo nima, wannan tashin hnkli ai dole in dawo..." Saude tace toh, daga hk sukayi sallahma ta ajiye wayar, yayinda kunci be bar ranta ba, data tuna Almuqri'ah se taji gabaki daya ta tsani kanta,. Se tsakar dare suka isa garin sakwato. Dreva ya ajiyeta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login