Showing 3001 words to 6000 words out of 13265 words
Chapter 2 - Barauniya Amarya by sadnaf and Mrs fawwaz-1-1.txt
na zubo mata Dan tasan yau asirinta zai tonu a bainar jamma'a agaban danginta Dana mijinta,ita kuwa Hajiya Zulaihat ganin ta rik'e net taki cikawa ne yasa tayi murmushi ta kalli hajiya rufaida dake gefenta,tace"lailai amaryar Khaleed bak'aramin kunya ne da ita ba,d'aukar turaren tayi ta feffesa mata aka saki gud'a ta dauki kwab'ebb'en lalle nan ta lakuta mata a k'afafu ta d'auko rafar dubu ashirin din ta d'ora mata a cinya,aka k'aure da gud'a sunkuyawa tayi tacewa jameela "kicewa kawartaki ta bud'e fuskarta muyi hoto,matsawa jameela tayi kusa da Kausar ta rad'a mata,Kausar ta kara kankame net din tana girgiza kai,murmushi hajiya Zulaihat tayi tace gobe ai dinner zata ga fuskar amarya ta juya suka tafi anan hankalin Kausar yadan kwanta kad'an jameela ta lekata tace " Kausar anya kinada gaskia kuwa ko dai kintab'awa yiwa matar nan halin naki ne, dubi yanda kike gumi jikinki yake rawa, aikuwa in haka ne kin tapka babban asara,Dan yar uwarsu Khaleed ce",Kausar bata Ce komai ba illa ma kara kallon direction din dasu hajiya Zulaihat suke tayi takara rufe fuskarta da net,a takaice ahaka Kausar ta rufe fuskarta taki bud'ewa sai data ga su hajiya Zulaihat sun tafi sanan ta bud'e fuskarta, anan jameela takara gasgata zarginta,ta girgiza kai tana mai nemawa Kausar shirya Dan tasan Kausar tayi nisa.
ASALIN LABARIN
Kausar 'ya ce ga margayi mallam garba su biyar ne agidansu uku maza biyu mata Adamu shine nafari sai bello da kamal,matan kuma Kausar sai auta jidda, usulinsu Fulani ne gaba da baya, mahaifinsu ya rasu ne a lokacin autar Jidda Nada shekara biyu a duniya,dukiyar daya bari gona biyu da shannu,a lokacin suna yola,sanadiyar rasuwar Mallam Garba ne yasa suka dawo kano da zama,tun lokacin da mahaifinsu ya rasu,Hajjo take iya bakin k'ok'arinta Dan taga yaranta basu rasa komai ba, Adamu dinki ya koya tun yana da shekara goma sha biyu har ya girma yakuma iya dinkin sosai dahaka yake tallafawa kanensa,haka ma su bello suna buga buga duk mazan babu Wanda ya zauna haka asanadin hakan ne yasa su Kausar basu wani nemi Abu sun rasa ba koma dai yaya ne suna samun biyan bukatunsu,hajjo ma tana daga gida tana yan sana'ointa. Kausar kyakyawa CE ta ajin karshe Dan komai na mahaifiyarta ta d'auko hajjo,tun Kausar Na yarinya ta koyi d'auke d'auke Dan hajjo zata ajiye yan chanjin ta Kausar sai ta d'auke sai dai hajjo tagaji da nema ta hakura,ahaka har Kausar ta isa sawa a makaranta,yayanta Adamu ya sama mata wani makarantar gwamnati take zuwa,daga fara makarantar ta takara dagewa wajen Dan yan ajinsu insukayi break, suka fita dawowa take ta chaje jakarsu intaga biyar ta d'auka goma ashirin,ba iya k'udi ba har abin ci d'auka take,inta Tara k'
Kud'in data sata ko ta siyi kayan k'wadayi ko tasiyi tasiyi kayan wasan yara,kuskuren da Hajjo tayi inta ga k'udi ko abun wasa a hanun Kausar bata damuwa ta tambayeta a ina tasamu,ranar da asirin Kausar ya tonu a lokacin yan ajinsu sun gaji da kana na kanan satar da ake musu,ranar wasu a ajin bayan a fita break suka lab'e ta window aikuwa minti goma da fita break sai ga Kausar ta dawo aji tafara bincike jakar yan ajinsu,wayanda suka lab'en tuni suka fito suna ga B'??R??UNIY?? mun kamata tuni Kausar ta w'ular da jakar tana Neman hanyar guduwa,yan ajinsu suka rufar mata suna mata ihun B'??UR??UNIY??, aranar headmaster dinsu ya zaneta agaban Assembly, ya tura aka kira yayanta adamu aka fad'a mishi abunda Kausar keyi,duka kam aranar Kausar tasha a gurin y'ay'enta Dan takaicinsu ba abinda Kausar ta nema ta rasa,atakaice ahaka Kausar taringa yan d'auke d'auke har taje secondary school anan tahad'u da Jameela suka zama k'awaye,fara secondary dinta ne yasa idonta yakara bud'ewa da kud'i, duk satar da akeyiwa yan ajin basu tab'a kawowa Kausar bace,amma suna dai Adduar Allah ya tonawa b'arawo asiri,akwai wata bilkisu dake kawo alewar madara su aya kantu da sauransu,kullum inta kawo tagama siyarwa inzata K'irga kud'in baya cika abun na mutukar damunta, nan kuwa Kausar CE ke d'aukar mata,wani Sain ma ba kud'i kawai take d'auka ba alewar madara take diba tasa ajakarta injake gida tayi ta sha,Jameela CE tafara kama Kausar ranar bataje break ba ta batada lafiya ta kwanta kamar mai bacci amma ba bacci take ba,Kausar data shigo zata yi Dan halin,sai data leka fuskar Jameela taga alamar bacci Take sanan tafara chaje jakar yan ajinsu,batasamu komai ba Dan yan ajin ganin irin satar da ake musu akai akai ne yasa suka daina ajiye k'udi ajaka, ganin batasmu komai ba yasa ta dibi alewar madara da kantu da bilkisu ta ajiye Jakarta ta d'auko Dan ta zuba,taji ance ajiye,dagowa tayi cikin fad'uwar gaba ta kalli Jameela data zauna tana kallonta,Jameela fusge jakar hanunta tayi ta wular tace mata ta "mayar mata da kayanta, anan Jameela kecewa Ashe itace B??R??UNIY??R ajinsu Kausar rok'on ta tayi data rufa mata asiri ta daina sharrin shaidan ne, atakaice ahaka Kausar taringa yan D'auke d'auke jameela tana rufa mata asiri sai ranar da dubunta ya cika.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Wanan page d'in sadaukarwa ne ga duk fans *B'ARAUNIYAR AMARYA* Muna jin sak'onni Ku kuma mun gode d'umbin k'aunar ku.
We love u??
Page 25-30
Tun lokacin da su Kausar sukaje SS 1 aka kapa doka a makarantar akan duk ajin da akayi sata,sai yan ajin sun hada kud'i anbawa Wanda akayiwa Satan koda nawa ne, sabida yawan complain d'in da principal ke samu na Satan da akeyi a ajinsu Kausar,bayan sun had'a kud'i akwai punishment d'in da za a yiwa yan ajin gaba d'aya ko kaine kayi Satan ko ba kai bane,idan kasha wuya zakayi k'ok'ari kaga kanemo b'arawon,tunda yan ajinsu Kausar sukaji irin matakin da hukumar makaranta ta kapa,hankalinsu ya tashi,suna komawa aji, monitor ajinsu tace su had'a kai su samo Wanda yake musu sata,kuma kowa ya kiyayi ajiye kud'insa a ajaka,kuma sunyi alk'awari duk lokacin da asirin B'??R??UNIY?? ya tonu sai sun mata zigidir,tunda Kausar taji haka tashiga hankalinta dan sai da Jameela tak'ara bata shawara akan ta daina idan ba haka ba tana tausaya mata ranar da dubunta ta cika,aikuwa Kausar ta d'au shawarar Jameela Dan taga alamar inbatayi wasa ba asirinta tsaf zai tonu,dan ta lura yan ajin burinsu kawai su gane B'??R??UNIY??R Ajinsu, tunda aka kapa dokar yan ajinsu Kausar suka samu sauk'in satan da ake musu,Wanda hakan yasa Kausar cikin tashin hankali dan yanzu bata samun kud'i,a gida hamsin ake bata, ko break baya isarta takuma saba da kud'i, hakan data gani ne yasa tafara tunanin hanyar da zata bi tasamu kud'i dan akwai ankon da takeso tayi na wata kawarta dazatayi aure,wani dabara ne yafad'o mata tahau murna,gidansu wata makociyarsu taje Rahama sa'anin juna ne kuma k'awaye akwai wani agogo mai k'yau da yayan Rahaman ya kawo mata tsaraba da yaje aikin Hajji, shi Kausar taje ta ara agurin Rahaman tace mata zata nunawa yayanta ne Dan yasiyo mata irinshi,Rahama data bata agogon makala shi tayi ahanunta ta tafi dashi makaranta,da isarta kuwa ajinsu ta cire agogon taringa nunawa yan ajin tana cewa yayanta ya kawo mata tsaraba,babu Wanda bata nunawa agogon ba,aka ta ta yata murna wasu harda karb'a su d'ana, ana dab da fita break Kausar ta tafi gaban aji Dan tanaso kowa yaganta, cire agogon tayi tasa ajakarta, ta ajiye jakar a Inda ake ajiyewa,takoma ta zauna,bayan anfita break,dawowa tayi ta d'auke agogon ta cusa a gashinta dayake tanada gashi ta d'aure kanta sosai yanda agogon bazai fad'o ba,bayan andawo daga break,Kausar Jakarta ta d'auko tafara dube dube,can ta juye littattafanta akasa ta saki sallati,yan ajin gabad'aya hankalinsu ne ya tashi Dan sun San dak'yar in b'arawo baiyi halinsa ba,Kausar kuka ta fashe dashi tace an sace mata agogo tashiga uku ta lalace,yan ajinsu gurinta suka nufa suna tak'ara dubawa,monitor Jakarta ta k'arba taK'ara dubawa taga babu,yan ajin tuni suka ringa zaro jakankunansu suna dubawa ,monitor kuwa ganin ba aga agogon ba ta tafi wajen displine master ta gaya masa anyiwa Kausar Satan agogo,sai dayasa takira labour prefect da wasu prefect d'in suka nufi ajinsu,kowane da bulala hannu,tuni yan ajin wasu suka fara kuka Dan sun San yau sai sunci duka dan displine Master bashida mutunci,cewa yayi wacce akayiwa satar tafito yaganta,fitowa Kausar tayi gaban aji tana kuka,tambayarta yayi ya agogon ta yake,ce mishi tayi sabo ne yayanta ya siyo Mata shine yau tazo dashi makaranta dan ta nunawa k'awayenta shine aka sace,tambayarta yayi ko tasan nawa ake siyo mata agogo,cewa tayi dubu uku da d'ari biyar yayanta yace yasiyo mata,g'yada kai displine master yayi yace dole "su biyaki agogonki,amma kafinan zan zaneki sabida kinzo dashi makaranta,kallon yan ajin yayi yace ba kun iya sata ba yau zan koya muku hankali,kowace acikinku takawo sabain sabain gobe idan bahaka ba kunsan sauran,b'arayin banza b'arayin hofi ba kun iya sata ba yau zan koya muku hankali,kowace sai na mata bulala goma,sanan kunje kunyi wanki b'andaki gobe inkuka ga abun mutum bazakuyi marmarin d'auka ba,inku zuciya yau kuhad'a kai fito da wacce take sata a ajinan, tuni yan ajin suka hau kuka suna rantse rantse,Kausar kuwa said yanzu tayi da ta sanin abinda tayi Dan ta d'auka cewa zaayi kawai ahad'a mata kud'in gashi yanzu harda ita za'a Zane,jin datayi displine master nacewa labour prefect sufara chaje kowace a cikinsu tunda mata ne su chaje ko INA har ita kanta Kausar d'in a chaje ta,duk wacce taki tsayawa a chajeta su mishi reporting,zai fita waje ina an gama zai dawo,ficewa yayi waje prefects d'in suka kulo k'ofar ajin,sukasa sukayi layi aka zagayesu,suka fara zuwa d'aya bayan d'aya ana chajesu dai-dai da d'ankwalin sai kin cire,Kausar tuni ta jik'e da gumi dataga haka yan ajin kuwa dayake sun san sunada gaskiya cire komai suka ringayi ana chajesu,in aka gama chajeka sai kayi waje kayi kneel down,Kausar kuwa kuka taringayi a b'oye dan tasan yau asirinta ya tonu, saura layi biyu azo kanta tacewa wata prefect tanaso taje tayi fitsari harta barta tafi,labour prefect ta dawo da ita tace ta cire hijabinta da dankwalinta achajeta ido awarwaje Kausar tafara tari,ganin tana bata musu lokacine yasa ta tsinka mata mari Dan bata wasa ta fuzgo hijabin Kausar tare da cire dankwallin kanta aikuwa sai ga agogo ya fad'o kuka Kausar ta fashe dashi,prefect d'in tabita da kallon mamak'i dagudu d'aya daga prefect d'in takira displine master tafad'a mishi Kausar ce ta saci agogonta,tuni wata a ajinsu Kausar mai zuciyar ta shak'e Kausar, dak'yar aka rabata da wuyan Kausar,prefect sukayi waje da Kausar data rufe fuska tana ta kuka,yan ajinsu dagudu suka bisu suna kaiwa Kausar duka suna janyo rigarta,a tak'aice Kausar sai da a ka koreta daga makaranta,Hajjo sabida bak'inciki sai da suka bar unguwar dan yan makarantarsu Kausar sun hana Kausar sakat,ya'yenta ma Dan takaici fita sukayi daga harkarta Dan basu San me Kausar ta nema ta tarasa ba, Hajjo ce ma tasa ayiwa Kausar addua a fad'arta Kausar aljanu ne da ita na sata,Kausar kuwa tunda yan ajinsu suka tozartata,tayi sanyi tarage sata,indai tak'arasa secondary awani makarantar,kawancen su na nan da Jameela bata gujeta ba ,tana gama secondary tahad'u da Khalid,inda soyayya yayi k'arfi a tsakaninsu har takai ga manya sun Shiga maganar, gabatowar bikinsu ne ya d'aga hankalin Kausar dan ta raina abinda ya'yenta suka mata anan tahau Neman kud'i k'arfi da yaji bashin dataci ba a magana,kud'i take nema Wanda zata biya basukan da ake binta.
CIGABAN LABARIN
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
*UP UP PURE MOMENT OF LIFE WRIT ERS YOU GUYS ARE DOING A GREAT JOB,MAY ALLAH's BLESSING AND LOVE BE WITH US LOVE YOU GUYS SO VERY MUCH THIS PAGE IS FOR EACH AND EVERYONE OF YOU*❤??❤????
Page 30 -35
Tunda aka gama kamu Kausar ta fara tunanin hanyar da zata bi tak'i zuwa dinner da Khaleed ya had'a dan tasan intaje dole Hajiya Zulaihat taganta,dan d'azu taji tana cewa Jameela zata ganta gobe,da wanan tunanin jikin Kausar yayi sanyi zazzab'i k'arfi dayaji ya nemi ya rufeta dan tasan asirinta yagama tonuwa indai Hajiya Zulaihat ta ganta gobe,ga Khaleed yanaji da dinner daya had'a gobe dan komai nasu iri d'aya yamusu,gashi rabin 'yan uwansa da basu Santa ba musamman zasuje dinner gobe dan suganta, kasancewar Khaleed d'an dangi ne gaba da baya. a wanan halin Jameela tazo ta sameta, ba yanda Jameela batayi ta gaya mata abinda ke damunta ba Kausar tak'i. kiran Khaleed ne ya shigo wayarta ta d'aga, yace mata yazo yana waje. doguwar Riga kawai ta zura tafita waje ta sameshi akan mota a zaune,murmushi ya sakar mata dan shi kullum cikin godewa Allah yake dazai mallaka mishi sarauniyar kyau, sunan dayake kiranta dashi kenan,tsokanarta ya hau yi da Amarya kinsha k'amshi,daurewa kawai tayi tana murmushi,hira suka d'an tab'a sama sama inda Rabin hira Khaleed keyi,hirar yanda dinner gobe zata kasance, D'an murmusawa tayi tace mishi tana so ta tambayeshi,yace yana sauraranta "akwai wata Hajiya d'azu da ita ta kamani, ya kuke da ita bansanta ba?"
"Wai Aunty Zulaihat kike nufi,k'anwar Babanmu ce ai ita nake baki labarin bata K'asar zanso ace tana nan za ayi bikin mu dan tana bala'in Son taga matar dazan aura,lucky enough kuwa ta dawo, kuma kinsan wlh sabida bikina ta dawo? ai d'azu take cemin "ko Amaryar tawa mummuna ce shiyasa tak'i bari naga fuskarta?", nace mata "ta kwantar da hankalinta gobe idonta zai gane mata inke mummuna CE ko kyakyawa,".
Tunda ya fara magana Kausar jikinta ya hau rawa dan tasan babu gudu babu ja da baya asirinta ya tonu,zancen zuci tafarayi
"yanzu Ashe Hajiyar dana yiwa sata K'anwar Baban su Khaleed ce? nashiga uku na lalace ina zan kai wanan abun kunyar?"
K'arya tayiwa Khaleed da kanta ciwo yake zata je ta kwanta,nan kuwa gudawa takeji. Khaleed jin Amarya na ciwon kai ne yasa hankalinsa ya tashi, dagewa yayi sai ya kaita chemist yasiya mata magani amma fur tak'iya, da k'yar dai ta samu ya tafi.
Tana komawa cikin gida band'aki ta wuce tana sukurkuta gudawa,hankalin ta a tashe.
Ita da kanta tayi Allah wadai da wannan hali nata,gashi yanzu tayi inda abin ya sha mata kai,to amma ya ta iya? Buk'atar kud'in ne ya ja mata shiga wannan halin don bashin da ta ci idan ba satar tayi ba babu yanda za ayi ta iya biyan kud'in.
Da dare bacci ya k'aurace a idon Kausar, sai tufka da warwara take yi na yanda zata samu ta kaucewa zuwa dinner d'in gobe,don ta San idan har ta je asirin ta ya gama tonuwa kuma in khalid ya San tana sata Ai kashinta ya bushe,. A haka tana ta tunani ta kasa samun mafita har aka yi sallar asuba.
Da safe haka ta tashi idonta sun kumbura ga kuma headache na rashin bacci da damuwa. Ganin haka ya sa ta k'ara langabewa wai ita a dole bata da lafiya,ko don wannan Ai ta San dole dai Khalid ya k'yale ta da batun zuwa wannan dinner d'in.
Ita kanta ba k'aramin buri ta ciwa dinner d'in ba, amma kuma dole ta hak'ura don ta tsira da mutuncin ta,tunda ma ya ce Anty Zulaihat ba a k'asar take ba don haka zata yi ta b'oye mata har sai ta koma inda ta fito.
Wuraren 5:00pm Khalid ya kira a phone ya sanar mata gashi nan mai makeup zata zo gida ta mata makeup.
"Ai my pretty na San dole ne ki yi kyau ki fito sosai, don na biya makeup artist d'in sosai,so nake kowa ya ganki yasan babu raini"
Mak'ale voice ta k'ara yi cikin shagwab'a tace "hubby ni fa bani da lafiya tun jiya d'in nan".
"Haba my pretty me ya same ki? Ya salam sannu pretty na am on my way sai muje in kai ki asibiti a duba ki",Kausar sad'akarwa kawai tayi da zata je dinner dan tasan duk abinda zatayi Khaleed bazai barta ba sai taje,har yanmata sunfara cika gidansu Kausar kowace inka ganta sai kasan batada matsala dan su burinsu suga ma lokaci yayi suntafi Wanda ita kuma duk motsin da agogon bangon d'akinsu yayi sai k'irjinta ya buga,Jameela ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi," Kausar wai mai yake damunki ne tun jiya awajen Kamu kika susuce yau ma dakikafi ciwa buri sai gashi kin langab'e dan Allah kifadamin damuwarki kinsan nasan sirrinki, kifad'amin damuwarki nikuma insha Allahu zan baki shawara"dagowa Kausar tayi haka kawai taji aranta gwara ta gayawa Jameela halin datake ciki, tunda tariga tasan halinta, watak'ila ma Jameela tasamo mata mafita, gyaran murya tayi ta labartawa Jameela komai har satar datayiwa Aunty Oke, da irin taimakon da Hajiya Zulaihat tayi mata anan takarasa zancenta da "Jameela babu yanda zanyi sai nayi satar zan iya biyan bashin dake kaina kuma insha Allahu inagama biyan bashin nadaina sata dan naga alamar Khaleed nada rufin asiri babu abinda zan nema narasa", tunda tafara magana Jameela tasaki baki tana kallonta cikin tsananin mamak'i dan bata tab'a tunanin satar da Kausar keyi yayi tsamari haka ba, sallati Jameela kawai take tana girgiza kai"Kausar