Showing 9001 words to 12000 words out of 13265 words
Chapter 4 - Barauniya Amarya by sadnaf and Mrs fawwaz-1-1.txt
sai yace "dan haka kike damuwa" hanunta ya ruk'o yace "beauty wlh yanzu haka banida kud'i, kud'ina duk sun kare awajen bikin nan,kinga kud'in Dana shigo dashi jiya wlh ba Nawa bane nawani abokina ne Banbangida kuma gobe yacemin zai k'arba Dana ranta nabaki amma ina zuwa bari natabo Aunty zulaihat naji ko zan samu agurinta,sai da gaban Kausar yafad'i dataji ya ambaci Hajiya Zulaihat ,wayarsa ya d'aukar yakirata yasa a handsfree sai da yakusa katsewa ta d'aga bayan sun gaigaisa ta tsokaneshi yake cemata yana bukatar kud'ine Dan Allah zai samu a gurinta,murmurshi tayi tace kar yadamu zai samu Dama tayi wanka shiryawa take tana so tazo taga amarya su gaisa Dan jibi zata bar kasar watak'ila ita da dawowa sai amarya ta haihu dan haka gata nan zuwa intazo ta kawo mishi kud'in murmushi Khalid yayi cikin Murna yace sai tak'araso,Kausar kuwa dataji mai tace tuni cikinta ya murda hanjin cikinta ya Kad'a gumi sai keto mata yake, Khalid cikin farinciki yakalleta yace sai ki kwantar da hankalinki yanzu Aunty Zulaihat zata taho mana dashi,ganin yanda ta Kausar ta canja gabad'aya hankalinta a tashe ne yasa ya ruk'ota yana " lafiya kuwa my Angel yanaga kin d'aga hankalinki bakiji abinda Aunty Zulaihat tace bane zata taho mana da kud'in ki k'wantar da hankalinki" "d'aurewa tayi tace Honey pls ka kirata kace tabarshi basai tazo ba pls anjima zankira Hajjo ta kai mata kud'in" kallon mamaki yabita dashi yace" saboda me zance kartazo ai ko badan kud'in ba tanada niyyar zuwa bakiji mai tace bane ki kwantar da hankalinki ita ta raineni babu wani Abu dan tazo" Kausar wani yawu ta hadiya kut tace "to shikenan sai tazo" mik'ewa tayi dagudu tayi band'aki dan gudawan daya matsota ,Khalid bin bayanta yayi da kallo yana mamakin yanda tabi ta firgice lokaci guda,Kausar kuwa tana band'aki rufe bakinta tayi tana kuka dan tasan yau babu makawa asirinta ya tonu dama Jameela tafad'a mata,jitayi gabad'aya ta tsani kanta wanan abun kunya ina zata kai tayiwa Kanwar sirikinta sata,indai yau hajiya Zulaihat taganta yau babu abinda zai hana ta ganeta, wani kukan takara fashewa dashi yau kwana d'aya da tarewarta Khalid zai San halinta na sata sai yau take mut'ukar nadamar abinda ta aikata watak'ila yau ne ma karshen zamanta agidan Khalid dan lura datayi da yanda yace ya tsani B'??R??UNIY?? arayuwarsa take wani zazzabi yarufeta tsaftace jikinta tayi tafito ta nufi d'akinta tana rawar d'ari Khalid jin shiru shiru bata dawo bane yasa yabi bayanta hangota dayayi akan gado tana ta rawar d'ari ne yasa yak'arasa kan gadon dasauri yana "subhanallah princess mai yasameki" kasa magana tayi hakoranta sai kar kar suke, cewa tayi ya lullub'eta da bargo sanyi takeji har fuskarta rufeta yayi,yana mata sannu ya mik'e dan ya d'auko mata magani horn ya jiyo abakin gate,yace " ga Aunty Zulaihat dinma ta k'araso inazuwa bari nashigo da ita"waje yayi dasauri,Kausar kuwa a lokacin kiris yarage tasaki fitsari sai adduoi takeyi tana karatu sadak'arwa tayi kawai yau asirinta ya tonu,zumbur ta mik'e ta zauna tana Neman hanyar guduwa dan ta gwammace ta gudu da hajiya Zulaihat ta tozarta ta agaban Khalid,jin sun doso k'ofar d'akin ne yasa tayi Saudi takoma ta kwanta k'irjinta kamar ya fito dan fargaba,sallama sukayi ,Khalid ya amsa yana Aunty Zulaihat inaga fa asibiti zan kaita jikinta yayi tsanani"hajiya Zulaihat cewa tayi ba dole ka kaita ba ka wahalar da yaya mutane,Sosa kai Khalid yayi yace kai Aunty ba abinda namata fa,zama tayi a gefen gadon tana "Amarya sannu kinji tashi muje asibiti,wani irin zazzafan hawaye ne yazubowa Kausar tana shikenan mun had'u,jitayi tana " Khalid 'd'agata mukaita asibiti"yaye bargon Khalid yayi Kausar ta runtse idonta dak'arfi,wani irin mik'ewa Hajiya Zulaihat tayi taja da baya tana kallon Kausar cewa tayi Khalid wanan B'??R??UNIY??R CE matarka,kallonta Khalid yayi cikin mamaki yace kamarya Aunty Kausar cefa naga kuma kinganta jiya,wani irin shu'umin murmushi tayi tace Alhamdulillah in k'ere na yawo zabo na yawo wataran zasu had'u ke dan ubanki bani zobena kafin naci ubanki tace tana shak'o Kausar.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
***
In dedication to:
Eshat aysm
Aysha ali garkuwa
Momyn sultan
Maryam s bello
Janart
Husnah
Fhareeda
Dija waziri
Kausar luv
Momyn Jana
Sadnas
Mmn ihsan
Page 50-55
Kausar kallo tabi khalid dashi dan taga matakin dazai d'auka akanta.
Khalid dasauri yace "Aunty you must be mistaken wannan kausar ce ba fateema ba, dan Allah ki cikata". Yace yana k'ok'arin rik'o hannunta.
"Dalla matsa kabani waje! wannan itace wacce nake fad'a ma tayi sata a saloon d'in Aunty Oke ana shirin kaita police station na taimaketa amma dayake butulu ce sai tarasa da mai zata saka min sai tamin satar Gold d'in da mijina yabani. Ai ko a mafarki ne sai naganeta, nice har da mata nasiha nad'auko kyautar kud'i na bata, ta musa min dan ubanta tace min ba ita bace wlh da sai munje shagon Aunty Oke munje ka tambayeta kaji".
Wani irin kuka kausar tafashe dashi tace
"Hajiya wlh bani bace sai dai in kama muke da wacce ta miki sata dan ni bansan wata Aunty Oke ba, bana sata. Mai na nema na rasa hajiya akan me zanyi sata, ni bantab'a ganinki ba ma inba ranar kamuna ba".
Kausar ta fad'a tana kara fashewa da kuka
Khalid magana yafarayi cikin 6acin rai dan ya yarda da maganar kausar
"Haba Aunty? ya zaayi kausar tayi sata wlh mai kama da ita ne tamiki sata, amma badai kausar ba wlh".
Hajiya zulaihat sakin baki tayi tana kallon ikon Allah tana kuma mamakin k'arfin halin kausar. Wani tunani tayi tace "eee gaskiya ne khalid sai yanzu naga kamane suke kamar waccan tafi haske kuyi hakuri"
Kausar kallon mamaki tabi hajiya zulaihat dashi, ita kuma ta zuba mata ido. Khalid tsaki yayi yace
"Allah Aunty abinda kika min banji dad'insa ba sai kace wacce tafara tsufa yanzu wacce ta miki satar ma kin kasa ganeta bansan ma mai yasa kika damu da zoben nan haka ba dan nasan kinfi karfinshi, in kikayi niyya zaki siyi dubunshi". Murmushin tak'aici hajiya zulaihat tayi tace
" Hakane Khalid nafi k'arfin zoben da B'??R??UNIY??R ??m??RY?? ta sace min, abinda yamin ciwo shine ace nidana taimaketa ba a tozarta ta ba, ni tadawo tayiwa sata tana 'ya mace tana sata"
Duk maganar datake tanayi tana kallon kausar dan da biyu take magana, kausar kuwa k'irjinta inbanda dukan uku uku babu abinda yake dan tasan rufa mata asiri hajiya zulaihat tayi amma tasan itace.
Khalid zama yayi a gefen gadon yace "Kiyi hakuri kausar, aunty satar da aka mata ne yamata ciwo shiyasa take neman shegiyar B'ARAUNIYAR data mata sata ido rufe banji d'adi ba da aunty tace kamarku d'aya da ita yanzu sai dai muyi a hankali wajen shiga cikin mutane dan Allah kad'ai ne yasan adadin mutanen datayiwa sata kar aganki a d'auka itace kiyi hakuri kinji"
Gyad'a kai kausar tayi tana satar kallon hajiya zulaihat data k'afeta da ido.
Zama Hajiya zulaihat tayi itama tace "Khalid yafita yabasu guri zasuyi magana da Kausar"
Hankalin kausar ba k'aramin tashi yayi ba data ji abinda tace ba. Khalid kuwa dayaga fuskar Hajiya zulaihat babu wasa mik'ewa yayi yabar d'akin yana fita kausar ta sauko daga kan gadon ta durkusa agabanta, ta fara yi mata magiya.
"Hajiya dan Allah dan Annabi kiyi min rai. Wlh sharrin shaidan ne, dan Allah ki rufa min asiri kar khalid yasan nice na d'auke miki zobe dan Allah hajiya ki taimaka ki rufamin asiri"
Tunda kausar tafara yiwa hajiya zulaihat magiya, taringa mata wani wulak'antaccen kallo.
"Ke yanzu dan Allah baki ji kunya ba? Tunda nake bantab'a ganin mace mai k'arfin halin sata irinki ba, har ni dana taimaka miki. Ni zakiyiwa sata. Kash! Banji dad'in kasancewarki matar khalid ba mai zaayi da kyakyawa mara hali wlh daraja d'aya kikaci ban tozartaki ba narufa miki asiri sabida khalid bazai ji d'adi ace B'??R??UNIY?? ya aura ba naga alamar kuma yana sonki badan haka ba wlh daga kaina bazaki k'ara marmarin sata ba akarshe ina mai k'ara baki shawara wlh ki guji sata wataran dubunki zai cika a bainar jamaa karshen abun kunya dai ace kinyi sata dangin mijinki sun sani kinga kuwa kunyar dazaki ji nan gaba idan baki gyara halinki ba sai yafi yawa duk da nasan mai hali baya fasa halinsa duk ranar da kika bari khalid yasan Ke B'??R??UNIY?? CE babu abinda zai hana yasakeki kuma sai kowa yasan abunda kika aikata
Allah ubangiji ya shiryeki shirin addinin musulunci ya rabaki da san zuciya"
Mik'ewa tayi kausar tayi sauri ta rik'e mata k'afa tahau yimata godiya ko saurarenta batayi ba tayi waje.
A Palo ta tarar da khalid a zaune yana kallo, tace mishi zata tafi. Allah ya sauwake "Ameen" yace yana ta hakura da neman wacce ta mata sata tace bakomai ta hakura Allah yashiryeta hannu tasa ajaka ta d'auko dubu hamsin tabashi ta kuma d'aukar wani dubu ashirin d'in tabashi ya bawa kausar godia yaringa mata tace "Bakomai"
Har bakin motar ya rakata yadawo da murna yanufi d'akin.
A kwance yasamu kausar ta lumshe ido, ajiye kud'in yayi a gefenta yaruk'o hannunta yace
"Princess kiyi hakuri da abinda Aunty zulaihat ta miki dan Allah nasan ranki ya 6aci data dangantaki da B??R??UNIY?? tace nakara baki hakuri ga wannan tace nabaki ga kuma dubu hamsin d'in da kika tambayeni"
Yak'arasa zancen yana d'ora mata kud'in a cinyarta wani irin farinciki ne ya lullub'eta batasan lokacin data rungumeshi ba dan tana ta tunanin inda zata samu kud'i dan nasihar da hajia zulaihat ta bata ya shigeta takuma yi alk'awarin daina sata dan badan Allah ya rufa mata asiri ba da khalid yasan ita B'ARAUNIYA CE.
KAUSAR ZAKI IYA KUWA? MUJE ZUWA
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 55-60
Da Kud'in da Khaleed yabawa Kausar ta rage bashin wajen Hajiya SA'A, takuma ringa tunanin inda zata samu sauran kud'in dan tayi alkawari ta daina sata koda kuwa bashi zai kasheta ahaka tayi sati biyu da tarewa tana tunanin samun kud'i.
MAI HALI
Abokanan Khalid ziyara suka cewa Khalid zasu kawo musu daga nan sai matayensu su San juna,cikin murna da farinciki Khalid yasamu Kausar yafad'a mata yace mata ta tanadesu,aikuwa ran lahadi abokanan Khalid suka zo da matayensu,a d'akinta ta saukesu abokanan Khalid su kuma suka zauna apalo kayan saukar baki irin danginsu snacks tafara kaiwa abokanan Khalid kafin takai musu abinci haka ma takaiwa matayensu ta zauna suka gaigaisa tana Satan kallonsu dan kowace sanye take da sarka da dan kunne na gold ga manyan zobuna da alamu dai Khalid shine bashida hali sosai kamar mazajensu,tuni halin nata ya motsa,tafara tunanin yanda zata sace wani abun daga gurinsu dan kwana hud'u kenan wacce tahad'a mata turaren wuta ta matsa mata da ta bata kud'inta kuma bata da inda zata samu kud'i, inda su kuma suke yaba kyaun Kausar suna dama sune.
Matar Babangida ce tafara mik'ewa tace zatayi alwala Badariyya,Kausar taje ta zuba mata ruwa a buta ta nufi band'akin,bayan tafito Fatima matar Aminu tashiga,itama data fito Habiba ta mike sai data fara cire k'aton zoben hanunta tasa ajaka sanan ta nufi band'akin,Kausar kuwa tana ganin tashiga band'akin sauran kuma sallah suke,dasauri ta matsa kusa da jakar ta d'auke zoben dayake jakar bata wani rufeshi ba,barin d'akin tayi tanufi kitchen dan ta duba abincin tana shiga kitchen ta b'oye zoben a breziyarta, tana cikin juye abincin Khalid yashigo kitchen d'in dan ya duba ko tagama abincin murmushi suka sakarwa juna yace,
"Amarya ba agama bane duk kin cika mu da kamshi" murmushi tayi tace"nagama wlh bari nazuba ka tafar muku dashi,"dariya yayi yace "Amaryata ta kaina yanda kike da kyau haka kika iya girki mai dadi kai ita kanta ma Amaryar dadi gareta" rufe fuska tayi tace kai dan Allah wlh ni kana bani kunya" lakuce mata kumatu yayi adai dai lokacin dayake d'aukar farantin data jera kulollin abincin yace mata,
" dan Allah ki tabbata su Badariyya sunci abinci kinji kinsan mazajensu abokanai na ne sosai wlh ina je gidansu zakiyi mamakin irin tarb'ar dasuke min,"murmushi tayi tace ,
babu matsala ranka ya dade,kiss yamata a kumatu ya fice itama ta d'auki daya farantin tanufi d'akinta,azaune ta tarar dasu akan sallaya sunata hira Habibar data d'aukewa zobe sai zuba take suna ganin ta shigo suka hau murmushi suna mata sannu itama a kunyace tace musu yauwa dan dukansu sun girmeta farantin ta ajiye agabansu ta zuba musu abincin takoma gefe suka,suka hau ci dan su basa wani jin kunya,sai da suka kai bayan laasar agidan suka fara shirye shiryen tafiya inda Kausar ita kuma gabanta yahau fad'uwa tana adduar Allah yasa kar Habiba ta duba zobenta har sai sun tafi sai,sai da suka gama shafe shafe da pante pante,Habiba ta d'auko Jakarta ta zura hanunta dan ta d'auko zobe, zobe yace d'aukeni ahankali,gaban Kausar dukan Tara Tara yafarayi dataga yanda fuskar Habiba ya koma Habiba zazzage kayan jakarta tayi tana dube dube hankalinsu Badariyya ne yakoma kanta,Fatima tace,
"Habiba lafiya mai kike nema"? Amsa ta bata da zobenta data cire tasa ajaka take nema,Badariyya d'aurinta tacigaba da yi tace mata " ki maida hankali ki duba sosai Ai bazai bata ba,"Abu kamar wasa Habiba ba Inda bata duba ba bata ga zoben ba,Kausar kuwa cikin K'arfin hali tace"anya kuwa ajakarki kika sa zoben ko zaki duba band'aki ko fad'uwa yayi,"rai ab'ace Habiba tace " wane irin fad'uwa kuma ba agabanki na cire nasa ajakata ba ni bana alwala da zobe ahanuna" Habiba ganin fa dagaske bata ga zobenta ba yasa ta dura ashar tafara "yau zaayi ta agidanan zobena yayi layar zanna banganshi ba,ko sati baayi ba da fahad yasiyo min daga Dubai had'e da sarka da dankunne" su badariyga ma sallati suke suna duduba jakankunansu ,Kausar kuwa cikin tashin hankali tafara dube dube tana ikon Allah abinka da Mara gaskiya tuni tafara gumi,Khalid ne yashigo d'akin yana "madams mai kuke jira ne mazajenku na jiranku fa" ganin suna dube dube ne yasa yace "lafiya kuwa mai kuke nema" Kausar ce tafara magana cikin rawar murya tana masa bayanin abinda ke faruwa, sallati Khalid yayi ya kalli Habiban dake girgiza tana harare harare dan tana zargin Kausar ce ta d'auke mata zobe dan su Badariyya bazasu tab'a d'auke mata zobe ba,Khalid kallan Habiba yayi yace "garin yaya wai kika cire zoben",
Dayake Habiba bata fiye kunya ba bud'ar bakinta sai cewa tayi " Khalid agidanka zobena ya b'ata fa inaga dakazo shekaranjiya nake gaya ma katayani yiwa abokinka godiya na kyautar gold d'in dayamin sai kawai daga zuwa gidan ka na nemi zobe narasa ina bazai yiwu ba afito min da zobena kawai" tak'arasa zancen tana hararar Kausar,Kausar kuwa tuni tafara nadamar d'auke mata zobenta,Khalid kasa magana yayi yana mamakin ya akayi zoben Habiba ya bata,kwalla masa kira su babangida sukayi da mai suke jirana suna bata musu lokaci,jiki asanyaye ya nufi Palo yaje yagaya musu abinda ke faruwa,Fahad mijin Habiba mamaki ne yarufeshi ya k'wallawa Habiba kira tafito ya tambayeta abinda yafaru takara kora masa jawabi,Khalid hakuri yabata yace bari su kara dubawa ko zasu gani,yana shiga d'akin yaga Kausar sai dube dube take tana had'a gumi shima tuni yaji yafara zarginta dan yanayinta yanuna bata da gaskiya,fita yayi daga d'akin Yakoma palo yana cewa Habiba anya kuwa tazo da zoben gidanan"a "fusace Habiba tafara magana " wlh Nazi dashi gidanan agaban amaryarka ma nacire zoben nasa ajaka lokacin su badariyya suna sallah,kaga Khalid babu wani batun boye boye Amaryarka ce ta d'auke min zobe kace mata tabani zobena kawai" Khalid kasa magana yayi yana kallon Habiba dan yarasa tacewa Fahad kuwa yana ganin haka yacewa Habiba ta wuce sutafi careless ness d'inta ne yasa tarasa zobenta,Kausar kuwa data tsaya daga bakin k'ofa dafe k'irji tayi tace yazata ce ita ta d'aukar mata zobe, wani mugun ashar Habiba ta dura mata tace wlh itace ta d'auke mata tafito mata da zobenta kawai "ganin da Fahad yayi inya bar Habiba haka zata yi ta rashin mutunci ga Khalid yakasa magana kuma yanajin kunyar Khalid, tsawa ya dakawa Habiba yace ta wuce su tafi,Habiba tak'i sai daya nuna mata zai sassab'a mata tayi waje tana Allah ya isa taringa cewa Kausar B??R??UNIY??R ??M??RY??,
Fahad hakuri yabawa Khalid yace yashareta ta yar da zoben ne awani wajen batasani ba yabawa Kausar hak'uri,su babangida ma hakuri suka bawa Khalid da Kausar dake ta kuka sukayi waje,Khalid rakasu yayi har bakin mota,Kausar tana ganin sun fita tayi sauri taciro zoben daga breziyarta ta bude drawern mudubinta ta jefa shi aciki,Khalid kuwa rai abace ya dawo ya wuce Kausar dake zaune apalo tayi tagumi tana goge hawayen munafirci,d'akinta ya wuce direct yafara hargitso da kayan ta Kausar kuwa ta tsaya tana kallonsa cikin tashin hankali,tambayarsa tayi ya yard a kenan ta dau zoben,ko kallonta baiyi ba ya cigaba da birkita kayanta,ba Inda bai duba ba har akwatunanta ya sauko dashi, gaban Kausar inbanda fad'uwa babu abinda yake jikinta sai rawa yake, duk karatun dayazo bakinta sai ta karanta,ganin ya nufi gaban mudubi cikinta yayi wani irin murdawa dasauri tasha gabansa tace yanzu ya yarda zata iya sata, tureta yayi daga gabansa dan ransa ya masifar back,haka kawai ya yarda Kausar ce ta d'au zoben,drawern janyo yafara hargitsawa aikuwa sai ga zoben,d'auko zoben yayi ya juya yana kallon Kausar.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??